Uncategorized

Dalilin Rashin Zuwan Izzar So Episode 70

 

Kamar yadda aka saba tashar Youtube ta Bakori tv tana sakin Film ɗin Izzar So duk ranar Lahadi, shiri mai dogon zango wanda yake faɗakar, ilmantar gami da nishadantar da masu kallon shirin mai dogon zango.

Sai dai a wannan satin sai akaga ga har lokacin yayi amman mai shirin wato Lawan Ahmad mai doraba, sai dai kuma daga baya ya saki wani bidiyo na aƙalla mintuna 2 ga yawabin da yayi a wannan bidiyon kamar haka:

  Assalamu alaikum jama’a ina yi wa kowa fatan alheri, yau Lahadi ya kamata ace izzar so na 70 zan saki amman na sadaukar da ita ga al’ummar Nigeria musamman yan Arewa da ake yi musu cin kashi kala-kala kuma ana kallo amma gwamnati ta kasa ɗaukar mataki.

To muna kira ga shuwagabannin dan Allah dan Annabi su duba wadannan abubuwa da suke faruwa anan arewacin Najeriya su dinga yiwa al’umma adalci, ba don komai ba sai lokacin da aka ta shi yin zaɓan nan su al’ummar aka nema suka yi zaɓen kuma hataka samu aka kai inda ake so.

Don haka idan wata matsala ta samu suma ya kamata a duba, saboda kamar yadda shuwagabanni suke da hakki akan al’umma, haka suma al’umma suke da hakki akan shuwagabanni.

Also Read

Lallai duk wanda ya zama shugaba to, Allah subhanahu wata’ala sai ya tambaye ka ya ka tafiyar da mulkin ka, sannan ya ka tafiyar da al’ummar daka mulka.

Don haka mu a matsayinmu na wadanda suka taimaka aka yi kamfen har aka samu nasara, domin mutane da dama saboda ni suka fita suka dangwala ƙuri naga ya kamata na fito n ayi magana akan abin da ke faruwa, domin muma muna da hakki mu faɗa wa shugaban ƙasar Najeriya.

Lallai ya kamata a dinga yin adaci akan talakawa.

Ya kamata a dinga yin adalci akan al’umma.

Ya kamata a dinga yin adalci akan mutanen da ake shugabanta.

Saboda haka yau Izzar So Episode 70 zai fita daga ƙarshe ina ƙara yi wa jama’a fatan alheri.

Back to top button