Hausa novels

Kanwar Maza Page 63 Complete Novel By Ayshercool

Page 63

 

Sai da falon yayi tsit na wucin gadi, Adam bai taɓa tunanin wautar rumaisa ta tsananta har haka ba. Ji yake tamkar yayi layar zana ya ɓace daga wurin.

 

Ta kuma cewa “Ammi, kuma yana yawo babu riga a cikin gidan nan, kuma alhalin ni ba muharammarsa ba ce, Yaya usy ya ce yayyena ne kawai muharramaina, amma yake yawo ba riga, ina kallonsa, ko kunya ba ya ji”.

 

Wani kallo ya yi wa rumaisa, amma ta share shi ta ce “Ai dama na rantse sai na faɗa mata, ammi ta ce duk abun da ka yi mini na rashin kyautawa na gaya mata. Hmm ni  ko za a shekara nawa idan aka yi abu bana mantawa, ina riƙe da shi a zuciyata, ina sane sai yau na ce bari na gaya wa ammi”.

 

Ammi ta yi murmushi cike da dattaku ta ce “Haba dai, wace irin kishiya ana zaman lafiya, tsokanarki yake yi kawai, wanda yake da wannan zuƙeƙiyar yarinya, ina ruwansa da wani ƙara aure. Kuma in dai saboda wannan abun ne, rai dai an fille wa fara kai, muna zaune Allah zai kawo su”.

 

“Ammi ai hijjabi zan koma sakawa, ya daina saka mini ido, dama na ce gara in gaya miki, ba zan gayawa mama ba, saboda na fuskanci yanzu mama ta fi son sa a kaina, cewa za ta yi ƙarya nake yi, kuma ita ta ce duk wanda ya gaya mini maganar banza, wadda ta saɓa da tarbiyyar da take yi mana, in je in gaya mata. Shiyasa nake gaya mata komai, amma na san a wannan karon da zan gaya mata abun da ya yi, ba zata yadda ba”.

 

“Da gaskiyarki kam, mama ta yi iya ƙoƙarin ta a kan tarbiyyar ku, bai kamata ta rushe ba, Allah ya cigaba da dafa muku, bar mini litattafan naki na cigaba da gani, duba ɗakina, ko Sabir ɗin ya tashi, zamu yi wani sirri da ke”.

 

Rumaisa ta tashi ta nufi ɗakin Ammi, ka sa haɗa ido Adam ya yi da ammi, ji yake kamar ya zama guguwa ya bar wurin, saboda takaici da kunya.

 

“Takawa” ya ɗan ɗaga kai amma bai kalli ammi ba.

 

“Ka din ga sanin me zaka gaya mata, tun da ta ce ko za a shekara nawa ba ta manta abu, na ga hakan a cikin idonta, a hankali zaka nusar da ita abun da ya shafi sirrin aurenku naku ne, ta daina faɗa, na san kana haƙuri amma ka ƙara nan gaba zaka ci ribar hakan in sha Allah”. Ya jinjina wa Ammi kai ya tashi ya nufi ɗakin ammi, bin bayan rumaisa.

 

Ammi ta ce “Dan Allah kar ka yi mata wani abun, Allah ya taimake ka, daga ni sai ku ta faɗa, Iman ta riga ta tafi amsa waya, kar ka ce zaka yi mata wani abu”.

 

“Babu abun da zan yi mata, Sabir kawai zan gani, a nan za ta wuni, a haɗa masa kayansa, da shi zamu tafi, zan kaita gidansu gobe in Allah ya kaimu za su wuni a can, ba ta taɓa zuwa gida ba”.

 

Ammi ta ce “Masha Allah, babu laifi”

 

Rumaisa tana zaune a gaban sabir, da yayi ruf da ciki a kan gado, yake ta bacci, sai shafa sumar kansa take yi tana murmushi. Da hannu ɗaya ya ɗaga rumaisa ya juyota tana fuskantar sa.

 

“Me na yi maka?”.

 

“Ban sani ba, ke wace irin yarinya ce sai ka ce na’ura mai ƙwaƙwalwa, kanki gaba ɗaya baya gaya miki abun da ya dace, iya abun da aka zuba miki shi ne yake aiki a kanki, ammi fa sirikarki ce, ya dace ki gaya mata wannan maganar?”.

 

Ta kalleshi ta ce “Meye wani sirika kuma, ni ammi babata ce, haka mama ta gaya mini, ka ci sa’a da ba komai na gaya mata ba, har da cewa nonona bai fi girman wake ba, duk wannan rufa maka asirin da na yi ba ka gode ba, ga  gingimen asirin da na daɗe ina rufa maka”

 

Adam ya dafe kai ya ce “Innalillahi wa Innalillahi raji’un, ba dai aure ba, zan ƙara aure ba zan zauna da ke ba kamar namiji ba, ba zan iya ba daga nan ki je ki cigaba da faɗa”

 

“Ni ba zan kula ka ba baban sabir, na san haushina ka ke ji saboda na faɗi abun da ka ke yi, ni da kai idan na ce zan yi maka nasiha, ba yadda za ka yi ba, amma yanzu na san idan ammi ta yi maka faɗa zaka yadda”

 

Rumaisa ta zubawa sabir ido, Ammi ta shigo, ta ce “Maman sabir, Haryanzu ba ki gama ganin sa ba?”.

 

“Wallahi kuwa ammi, bana gajiya da kallonsa ni ai”.

 

Ammi ta zauna a gefen gado ta ce “Zo ki zauna a kusa da ni mu yi sirri ƴar auta”.

 

Rumaisa ta tashi ta zauna a kusa da Ammi, Ammi ta ce “Kin ga dai ba kya so ya yi miki kishiya ko?” Rumaisa ta ce “Eh”.

 

“Meyasa ba kya so?”.

 

“Kai, ammi duk mata kowa sai na ji ta ce ba ta son kishiya, shiyasa nima na ce ba na so”.

 

“To ki saurareni ki ji, Abun da nake nufi da duk abun da ya yi miki na rashin kyautawa ki gaya mini, ba yana nufin ki din ga faɗar sirrin aurenku ba, ya ce mini da wasa yake yi miki, kin ga kin sa ya ji babu daɗi”.

 

Ruma ta ce “Ammi, ba dan ya ji haushi na faɗa ba, kin ga tsoro nake ji kar na yi wani abu da idan mama ta ji, ba zata ji daɗi ba, ta ce na watsar da tarbiyyar da ta yi mini”.

 

“Ba za ta ce haka ba, ai shi mijinki ne, sannan kar ki sake ki faɗi irin wannan a gaban wani kin ji?”

 

“To ammi, in Allah ya yarda”.

 

Ammi ta dafa kafaɗarta ta ce “Yauwwa yarinyar kirki, Allah ya sa kin fara makaranta a sa’a, idan aka kwana biyu mai koya miki girki zan ɗauko, har gida ta din ga koya miki “.

 

“Ammi na iya girki fa, ki tambayi iman ki ji, har shi papa ya san na iya”

 

Ammi ta ce “Waye papa kuma?”

 

“Baban Sabir ”

 

Ammi ta yi murmushi, ta ce “Masha Allah, Allah Ya albarkaci aurenku”

 

Rumaisa ta yi gum ba ta amsa ba, dan ita auren nan ya isheta.

 

Rumaisa ta dage ta bi Iman kitchen, har da ammi a yin girki, sai dai ammin ya jinjinawa basira irin ta rumaisa, da ka ga yadda take gudanar da girkin zaka san, ta horu.

 

Wuni ta yi tare da ammi, ga iman ga sabir, jin su take tamkar wani ɓangare na rayuwarta, da ganinsu kawai ke samar mata da nishaɗi.

 

Da yamma, rumaisa ta silale ta fita harabar gidan, ba tare da sun sani ba, ta din ga zagaya fulawoyin gidan, da manyan bishiyu.

Wani zomo ta gani, fari tas da shi, yana tsalle-tsallen sa, ga sauran tsuntsye da suke kaiwa suna komowa.

Da sauri ta bi zomon, tana son ta kama shi, sai dai ta ga ta ɓullo wani wuri.

 

Yana zaune a kan fararen kujeru, gabansa da litatafai, da system, ya tattara nutsuwarsa sosai a kan abun da yake yi.

 

Bayansa ta gano ta ce “Papa” a hankali ya waiwayo ya kalleta, ta ɗan tsura masa ido, sai kuma ta ce “Laa ashe ba papa ba ne kai ne, na gane ka, da ka taɓa sawa na shigo gidan nan” ta yi maganar tana ƙarasawa in da yake.

 

Ya ce “Wow, ashe zamu sake haɗuwa, sannunki, ya ki ke?”

 

“Lafiya ƙalau” ta ƙarasa maganar tana zama a kujerar da ke facing ɗin sa.

 

“Yau ya aka yi aka bari ki ka shigo, har ki ka zo nan?”

 

Da ɗan mamaki ta ce “Wa zai hanani shigowa, to shi ya kawoni”

 

Mahmud ya ce “Shi wa?”

 

“Baban Sabir, ba ka san yanzu mijina ne ba?”

 

Ya ɗan yi turus, sai yanzu ya gane zancen da Mummy suke yi ita da su Samha ɗazu, amma bai gane ba, kasancewar tun da ya dawo sai yau ma ya fito.

 

“Da gaske ke adam ya aura?”.

 

Rumaisa ta ce “Hmmm, ya aka yi baka sani ba? Ba a gidan nan kake ba, ba ka zo bikinmu ba kenan?”.

 

“Ina ƙasar waje ai, can makaranta, labarin bikin kawai na ji”.

 

Cikin mamaki rumaisa ta ce “To ta yaya kuna gida ɗaya, amma ba ka sani ba, wai ku ba ƴan uwa ba ne?”.

 

“Eh, kowa babarsa daban”.

 

“To, ku ƴaƴan kishiyoyi ne?”.

 

Yayi dariya, tambayarta ta yi yawa amma ya ce “Eh”.

 

“Taɓ to ni wallahi ba za ayi mini kishiya ba, amma to dai meyasa ba ka zuwa wurin su, baka san yayi aure ba?”.

 

“Ni ma ba ya zuwa wurinmu”

 

Ruma ta ce “Ai papa sai fatan Allah ya shirya shi”.

 

“Ke ma yana yi miki halin na sa kenan, na rashin kirki?”

 

“Hmm, ai ba dan Sabir ba ko, ba zan aure shi ba, amma dai ya sakani a makaranta mai kyau na ji daɗi”.

 

Mahmud ya tattara nutsuwarsa a kan ta ya ce “Da gaske dai, ke ki ka dawo da jaririn nan?”

 

“Wai meyasa ƴan dagin nan naku, suka damu da lamarin nan ne? Wato an rainani ko? To anty aisha da kanta ta bar mini jaririn nan, kuma har da zobunanta da ɗankwalinta, ta bani, ni fa bana damuwa da kowa sai ya yadda da ni a duniyar nan, malaminmu ya ce idan Allah ya yarda da kai, ka huta, shiyasa ni ban damu da kome za a ce a kaina ba”.

 

Mahmud ya yi dariya ya ce “Wow, i like your confidence ”

 

“Wai kai ya sunaka ne?”.

 

“Mahmud” ya bata amsa, ɗan turus ta yi tana kallon sa, “Dan Allah da gaske?”

 

Ya ce “Eh”

 

Ta ce “Innalillahi, sunan babana, sunan ɗa na”

 

ya ce “Shikenan na yi ƴa, na zama daddynki”

 

Ta yi dariya ta ce “yauwwa to ka taɓa zuwa ka ga ɗa na? Ranar nan na ce ka je wurin ammi ka ganshi”.

 

“Zan je wataran”.

 

Rumaisa ta ce “A’a, yanzu dai mu je in ga mamanku, ita ce ban taɓa gani ba, kai ma sai mu je ka ga ɗa na, mai sunan ka”.

 

Mahmud ya ce “mijinki ya huta kallon Tv, ke kaɗai kin isa ba shi dariya”.

 

Ta ce “Taɓ, sai ka ce wata cartoon, mu je ka nuna mini ita” ya tashi tsaye, yayi gaba, ya jagoranci rumaisa har tsakiyar falon Mummy.

 

Ya ce “Mummy, ga amaryarku fa ta ce na kawota ta gaida babata”

 

Gaba ɗaya suka juya suna kallon rumaisa da ke bin su da kallo.

 

Samha ta fara ganewa a cikin su, ta kalli Fauziyya da ruƙayya, sai dai suna haɗa ido da Mummy, jikinta ya yi sanyi, gaban Mummy kuma ya yi mummunar faɗuwa.

 

Mummy ta ce “Wace wannan?”

 

Samha ta yi tsaki ta ce “Matar Adam ce, saboda asara, kalli abun da ya kwaso saboda ba ya gudun abun kunya”.

 

Mahmud ya kalli Samha ya ce “Ba ruwanki, ba wurinki na kawota ba” ya kalli rumaisa ya ce “Daughter, ga mamana nan”

 

“To ya na ga ba ka kama da ita, kana kama da ammi?” Ji yayi wani irin gumi ya tsatstsafo masa ta kafar gashin jikinsa.

 

Mummy cikin jarumta da iya duniyanci ta ce “Ikon Allah, da ba a kawo mini ita mun gaisa ba, kai ka kawo mini ita, takawan ne ya ce ka kawo ta mu gaisa?”

 

Mahmoud ya ce “A’a, cewa ta yi zata zo ta gaida babata”.

 

Fauziyya ta ce “Tirƙashi, ashe da muka ganta a wurin dinner ta fi cika ido, ni Wallahi ban gane ta ba ma”

 

Samha cikin ƙuluwa ta ce “Mummy wai meyasa ki ke wani sakar mata fuska, meye alaƙarta da ke, tun da ba ɗanki take aure ba, kuma ba ayi niyyar kawota ta gaishe ki ba?”

 

A fusace rumaisa ta ce “Baiwar Allah wai me na yi miki ne? Kullum ki ka ganni sai kin zageni, ba ruwanki da ni, ni ba wurinki na zo ba”.

 

Mahmud ya ce “Samha ba ruwanki da ita please, ki ja girmanki, daughter ga mamana”.

 

Rumaisa ta kalli mummy, ta risuna kamar yadda ta ga ana yi ta ce “Barka da wannan lokaci ”

 

Mummy ta ce “Barkanmu dai, kuna lafiya?”.

 

“Lafiya ƙalau”

 

“Ya mijin naki, ya Sabir? Ko da yake fushi nake yi da mijinki, ba ya zuwa in da nake, kuma ba ya kawo mini ɗan naki, Allah sarki fulani, ashe tare aka yi garkuwa da ku?”.

 

Rumaisa ta yi shiru, ba ta ce komai ba.

 

Mummy ta ce “Ruƙayya, ki saka a kawo mata abinci”.

 

“A’a na ƙoshi, yanzu muka gama cin abinci da ammi”.

 

Cikin ƙarfin hali Mummy ke magana, domin wani irin bugu ƙirjinta yake yi, har hakan na neman bayyana a fuskarta.

 

“Ni ma ai babar takawa ce, ki zauna mu yi hira mana, da takawa, da aisha, duk ƴaƴanmu ne, haka muka ji rasuwar ta, mun shiga tashin hankali da ruɗani, babban abun takaicin yadda ta haihu a hannun ‘yan bindiga, abun bai yi mana daɗi ba”.

 

Maimaita rumaisa ta amsa mata, sai ta tashi ta ce wa Mahmud “Daddy mu tafi mu je ka cika mini naka alƙawarin” kallon rumaisa suke yi, da tunanin anya ma ba ta da taɓin hankali kuwa? Abun da ake tambayarta daban, abun da take yi daban.

 

Yayi murmushi ya ce “To mu tafi, tun da kin ga mamana, kin gaisheta”.

 

Rumaisa ta ce “Eh, Mummy sai anjima ”

“To amarya, sai mun zo gidan naki kuma”

 

Allah ya kawo ku.

 

Mahmud ya nuna mata Fauziyya da ruƙayya ya ce “Wannan ƙannena, ga Fauziyya ga ruƙaiyya”

 

Kan ya ce wani abu a kan Samha ta ce “Ita kuma wannan na santa, mai zagina ta na ce mini ƴar aba, na santa a gidan baba farin rawani, mai girma turaki, baban anty aisha, shikaɗai ya yi mini mutunci a gidansu”.

 

Yayi murmushi ya ce “To shikenan mu je” suka fita.

Samha ta tashi zaune ta ce “Na shiga uku, na rasa me ma zan yi? Kaina ya gama kullewa”.

 

“Jikina ya na bani akwai wani abu ɓoyayye a game da yarinyar nan, dole zan ganta a karo na biyu, kuma ya zama dole baba uwani ta sanya mini ido sosai a kan su”

 

Fauziyya ta ce “Ji munafuka kai, wai Mahmud ba ya kama da ke, kin ga idonta a tsaitsaye”

 

Mummy ta ce “Na gani” nan suka cigaba da tattaunawa a kan abun da yakamata su yi a kan rumaisa.

Kanwar Maza Complete Novel Document Txt

Ammi kuwa sai neman rumaisa suke yi, basu ma san in da ta yi ba, ammi har hankalinta ya ɗan fara ɗagawa.

 

Rumaisa kuwa da suka fito harabar gidan, sai surutu take yi wa Mahmud, kamar dama can sun saba, ya fi takawa sauƙin kai da sakin fuska, a wajejen harabar sashin ammi ya tsaya ya ce “To shikenan, ki gaishe mini da takwarana”. Ta kalleshi ta ce “Haka muka yi da kai, ba na gaida mamanka ba, ni ma ka zo mu je ka gaida tawa”

 

Ya ɗan yi jimm yana kallon rumaisa, “Dan Allah haba daddy, ni fa a gidanmu ban san babana ba, sai yayyena su bakwai, komai nake so suna yi mini, dan Allah mu je ka ga Sabir”.

 

“Ki shiga ki ɗauko shi, ki kawo shi na ganshi”.

 

Ta noƙe kafaɗa, kawai ya tsinci kansa da bin rumaisa.

 

Ba Ammi ba, har iman sai da ta razana, ganin Mahmud a filin falonta, shi kansa tsayawa ya yi yana bin su da kallo, rabonsa da falon nan, kusan shekara da wani abu, da Ammi ta neme shi, ta nemi alfarmasa kai tsaye ya ce ba zai yi ba.

 

Ammi ta ƙure shi da ido, kamar yau ta fara ganinsa.

 

Kallo ɗaya ya yi wa ammin, ya sunkuyar da kansa, ƙasan zuciyarsa yana tuna abun da ya yi mata na ƙarshe da ya kasa mantawa.

 

“Ashe ka dawo, ya makarantar?”

 

Ba tare da ya ɗago kai ba ya ce “Lafiya lau”

 

Ruma ta ce “Ka zauna mana” ta nufi in da Sabir yake wasa da kayan wasansa, yana ta rarrafe yana ɓarna, ta ɗaukko shi ta kawo masa shi.

 

Ya karɓi sabir, ya zauna da shi a jikinsa, ta kalli sabir ta ce “Waye wannan?”

 

Sabir ya ƙura masa ido, Mahmud wani murmushi ya saki, ya shafa kan Sabir, wata irin ƙaunar yaron ta shiga ransa, da yake jin tamkar daga jikinsa ya fito. Har aka yi dambarwar nan aka gama, bai taɓa ganin Sabir ba.

 

Cikin murmushi ya ce “Na yi kama da babanka ko, nima babanka ne”

 

Su Nusaiba kamar tv, haka suke kallon Mahmud da rumaisa.

 

Ruma ta ce “Ba papa ba ne, uncle ne wannan”

 

Mahmud ya ce “A’a Daddy dai” ya miƙe da Sabir a hannunsa ya nufi hanyar waje yana faɗin “Allah ya bani  ɗa ba mata”

 

Ruma ta bi bayansa tana cewa “Ai wallahi gara in bar maka takawa da in bar maka Sabir”

 

Ammi ta ce “Kun ga ikon Allah, me rumaisa ta gaya wa yaron nan ya yarda ya zo in da nake?”

 

Nusaiba ta ce “Wallahi ammi ni ma mamaki abun ya bani, wancan karon fa, kalli yadda aka kai ruwa rana, kan ya zo kiran da ki ka yi masa, bai kuma zuwa ba, kin ga ikon Allah yau shi ne har cikin falonki, kai lamarin baiwar Allah nan yana ɗaure mini kai”

 

Kasa jurewa Ammi ta yi, ta fashe da kuka, nan da idonta ya yi ja.

 

Iman ta ce “Ammi dan Allah ki yi haƙuri, ki cigaba da jurewa, jikina ya na bani komai ya kusa zuwa ƙarshe”

 

“Allah ya sa, ina fatan hakan”.

 

Yauwwa share hawayen, iman ta yi maganar tana gogewa Ammi hawayen fuskarta.

 

Mahmud kuwa ba abun da yake sai dariyar shirmen rumaisa.

 

“Ka ga daga nan, ba zan ɗara ko ina ba, sai ka bani ɗa na, daga gani sai ka ce zaka tafi da shi, to in gaya maka yau gidanmu zamu tafi da shi, sai ranar Litinin za a dawo da shi”.

 

“Ta yaya zaki kula da shi? Kema baki wuce a kula da ke ba ai”

 

“Zan iya, wanka ne dai, sai in saka ko baba uwani, ko su barira su yi masa wanka”.

 

Ya ce “Baba uwani kuma?”

Ta taɓe baki ta ce “Na fasa ba ta, ni matar nan ba ta yi mini ba, dan dai kawai ammi ta ce ta zo ta zauna da ni ne, ta yi saka ido, kamar mara gaskiya”.

 

“Daughter, ki kula sosai da lamarin gidan nan kin ji ko? Sannan kar ki yadda wani ya din ga sanin abun da yake faruwa a gidanki, mussaman baba uwanin”.

 

“Kai ma ka lura ta na da saka ido ko?”

 

Mahmud ya ce “Eh to kusan haka, sannan ki kula da takwarana sosai, da sosai”

 

“Taɓ, ka manta ni na kula da shi ranar da aka haife shi ranar majaifiyarsa ta bar duniya, kwananmu uku muna bulayi a daji, bamu samu hanya ba, na zaci ma mutuwa zai yi ” ya ɗan ware ido ya ce “Haba dai”

 

Ta yi ƙasa da muryarta ta ce “Wallahi da gaske nake, ka san yadda ake garkuwa da mutane kuwa, to in gaya maka har sunan wasu na ji, Anty Aisha fa wasu ne suka saka a saceta, saboda papa” kallon ruma yake cikin mamaki. Ta cigaba da cewa “Kuma wai ƴan gari ba su san meyafaru ba, suka ce shi ya kasheta yayi tsafi da ita, na san abubuwa da yawa, na ƙi gaya masa, ya fiye fushi da zafin zuciya, shiyasa maƙiyansa suke nasara a kansa. Ai ni na fi shi wayo fa, in gaya maka ranar da muka tafi katsina a kan bullet da bindigogi na zauna, jakunkunkunan, duk an yi musu lamba, duk na haddace lambobin. Har da wani gari da na je, an ƙona garin, na ga wani tsoho, muka yi hira da shi”.

 

“Amma Meyasa ba zaki gaya masa abubuwa da ki ka sani ba?”

 

“Sai abu biyu ya faru, ya daina saurin fushi da zuciya, na biyun kuma ba wanda zan gaya wa”

 

Murmushi yake yana kallon rumaisa, ta fiye surutu, but she’s very talented akwai hikima, da kaifin basira a maganganunta.

 

“Me ki ke yi a nan wurin?” Ta ji muryar takawa a kausashe.

 

“Daddy na kawo wa Sabir, ya ga takwaransa”.

 

“Uban waye ya ce ki bashi ɗa na?”

 

Ya tunkari Mahmud, zai karɓi Sabir, amma Mahmud ya riƙe Sabir, by force Adam ya hankaɗe shi, ya karɓi ɗan sa, har ya yi gaba ya dawo, ya fizgi hannunta ya nufin sashin Ammi da ita.

 

Ya balbleta da bala’i “Kin san hatsarin da yake cikin abun da ki ka aikata? Kin san me gayen nan zai iya yi, da ki ka ɗauki ɗa na ki ka bashi, What if yayi amfani da hakan against me? Wani irin gargadi ne ban yi miki a kan yadda za ki zauna da mutane a gidan nan ba?”

 

Rintse idonta ta yi, saboda yadda yake ta zazzaga mata masifa.

 

Ammi ta taso, ganin yadda jikin Adam yake rawa, ta karɓi Sabir, ta ja Adam ta zaunar da shi, ta ce “Wannan haƙilon na meye haka? Ka kwantar da hankalinka ba abun da zai faru”.

 

“Ammi yarinyar nan ba ta jin magana, duk abun da zan gaya mata ba ta ji”.

 

“Ni dai na san ba da kunnen wani nake ji ba, kuma na san abun da na aikata dai-dai ne, ko ba komai na saka uwa ta ga ɗan ta, tun da har ammi ta ji daɗin abun da na yi, ta ga ɗan ta, na ji daɗi, Kuma ni yana yi mini kirki ina ruwana da faɗanku, ni duk wanda yake son sabir ina son sa, na ga kai har cewa ka yi kar a sake bari na shigo gidan nan, shi ya ce a bar ni na shigo, na roƙe shi ya zo ya ga Sabir, ya zo ya ganshi, ya kaini na gaida mamansa, duk da na san ba mamansa ba ce ba”.

 

Adam ya sunkuyar da kai, ya dafe kansa, me zai gaya wa wannan burkitacciyar yarinyar da zai sa ta gane, irin hatsarin da wautar ta ka iya jefasu, da ta wanke ƙafa ta tafi sashin Mummy.

 

Ammi ta ce “Rumaisa waye ya gaya miki ɗa na ne?”.

 

“Da ke yake kama ai, ba ita ba, kuma wannan matar da zata gaya mini magana ya tare mini, to ammi ni sai in shiga faɗan da ba ruwana? Kuma ɗan uwan baban mutum babansa ne, dan haka shi ma baban Sabir ne”.

 

Ammi ta ce “Gaskiya ne, je ki ki shiryo, ki zo ku tafi, dama neman da muke miki kenan”

 

Ruma ta wuce ta je ta haɗo kan jakarta, da kayanta, ammi ta din ga yi wa Adam faɗa tana rarrashinsa, a kan ya bi rumaisa a hankali.

 

Ganin adam ya tashi zai tafi, ya sanya Ruma cewa Ammi Sabir ɗin fa.

 

“Yayi fushi ne, ki yi haƙuri gobe in Allah ya kaimu, za a kawo shi, ku tafi, ki rabu da shi yau ya ɗau zafi”.

 

“Ammi, meyasa papa da ɗan uwansa suke faɗa? Ni fa a gidamu ba haka muke yi ba, ya za ayi ƴan gida ɗaya su din ga faɗa?”.

 

Ammi ta ce “Kar ki damu, zaki fahimta, bi shi, kar ya sake fushi”.

 

Rumaisa ta bi bayan takawa, suna tafe a hanya, yayi shiru fuskar nan a haɗe. Oganniyar ko a jikinta, zura kai ma ta yi taga, tana neman magana.

 

 

Tun da suka koma gida, kowa ya kama gabansa, har wayewar gari, ba ta sake sanya takawa a idonta ba.

 

Ba ta da masaniya ma a kan yana nan ko ba ya nan, dan ko ɗakinsa ba ta je ba yau.

 

Ta gama gyaran saman benen nan, duk da yana bata wahala, saboda girman saman.

Yau har da kunna turaren wuta, tana kallon yadda falon ya yi kyau.

 

Ƴar siriryar muryar iman ta yi sallama, rumaisa ta ce “Anty iman”.

 

“Ki shirya, takawa ne ya je gida, ya ce Sidi ya zo ya kai ki gida, na ce bari na biku, na gaida mama, na wuce gidan sarki na ɗorayi, na karɓo mata saƙo.

 

Tsalle rumaisa ta yi, ta na murna ta ce “Jirani, na shirya”

 

Kamar za ta tashi sama ta shirya, ta fita mota suka tafi.

 

Da gudu ta shiga gida, ta bankaɗa ɗakin mama, ta rungumeta.

 

Mama ta ce “Kai rumaisa, babu ko sallama, wannan ai sai ki karyani”

 

Kuka rumaisa ta saka tana cewa “Mama ba kya so na, kin ƙi zuwa gidana, kin ce kuma kar kowa ya je”.

 

Aliyu ne ya ga Iman a waje, ya karɓo sabir, ya shigo da shi gidan.

 

Iman ta ɗauko manyan ledojin da takawa ya yi sayayya, ya ce su tafi da shi, dan da shi yayi niyyar kai rumaisa, ta ɓata masa rai.

 

Iman suka gaisa da mama, mama ta ce “Iman tun da a kai biki, kin daina zuwar mini, maimakon tun da na baku rumaisa, ni kuma hajiya ta bani ke”

 

Murmushi Iman ta yi, nan da nan ƴan mazan mama, suka cika ɗakin mama, cike da murnar ganin ƙanwarsu.

 

Usman ya ce “Ke me yake baki ne ki ka fara ƙiba haka?”

 

“Me kuwa yake bani, abinci, yaya kun ga makarantar da aka saka ni? Kullum sai na hau lilo, malamanmu, har da turawa”.

 

Aliyu ya ce “Babu a makaranta, idan ki ka faɗi daga lilon, ki ka fasa kai ba zaki koma ba”.

 

Mai sunan baba ya yi sallama a falon mama, suka amsa rumaisa ta tashi da gudu ta rungume mai sunan baba.

 

Ya ɗan yi murmushi, ya dafa kafaɗarta.

 

Iman ta ce “Ina wuni”

 

“Lafiya ƙalau” ya amsa, ya saka hannu ya ɗauki sabir yana ɗaga shi sama.

 

Iman na son ɗaga kai ta kalli mai sunan baba, amma ta kasa, shi kuma a wayance yake ƙare mata kallo.

 

Iman ta tashi ta ce “Mama bari na tafi, zan je aiken mama, maman sabir ga kayan abincinsa nan a wannan jakar”.

 

Mama ta ce “Iman ki bari ayi azahar ki ci abinci”

 

“A’a mama, na ƙoshi ni sai na kai yamma daga yanzu, ban ci abinci ba ma”.

 

Mai sunan baba ya kalli iman ya ce “Nemi wuri ki zauna” tsit kowa ya yi yana kallon mai sunan baba, ai ko motsin kirki ba ta yi ba,ta zauna ta na wuri-wuri da ido.

 

Ya basar kamar bai yi komai ba, aka cigaba da hira har da shi, haka nan yau yake jin daɗin ganin rumaisa a gida.

 

Sai dai bai ji daɗin yadda iman ta takure sosai ba.

 

Har azahar iman ba ta samu umarnin tafiya da ga mai sunan baba ba, sai da aka gama girki.

 

Sabir sai rarrafwa yake, kwano-kwano ya ci na wannan ya ci na wancan.

Yadda rumaisa take a cikin yayyenta, ba ƙaramin burge iman yayi ba.

 

Sai da mai sunan baba ya fita, sannan iman ta samu ta tafi.

 

Rumaisa da yaya usy ta keɓe, suna magana.

 

“Yaya yaushe za ka zo, akwai labari fa?”

 

Usman ya ce “Labarin me?”.

 

“Ni dai kawai ka zo dan girman Allah”

 

Ya ce “Kar ki damu, zan zo in sha Allah”.

 

Ana idar da sallar magariba, Adam ya zo tafiya da rumaisa, amma ta ce Alla kar ta ba in da za ta” sai da aka kai ruwa rana, sannan ta ɓanɓaru daga gidan nan, suka tafi, sai dai ta sha kuka sosai da sosai, mama ta harhaɗa mata ƴan kayayyakin amfani da za ta tafi da shi.

 

Sam Adam bai kulata ba, har su ka je gida, dan haryanzu bai huce da abun da ta yi masa ba.

 

Ya ajiyeta a gida, tana jiran ta ga ya fito daga motar, ta ga ya juya ya tafi da sabir.

Hakan ba ƙaramin haushi ya bata ba, hakan ya sanya ta shiga ɗakinta, ta yi ta aikin kuka.

 

Da ya dawo daga mayar da sabir, bai nemi ruma ba, sai da safe, shi ma dan yana tsoron, kar ya kawar da kai a kan ta, ta yi wani rashin jin.

 

Sai dai ya tarar tana banɗaki, ya ƙarasa gaban gadon, ya kai hannu ya ɗau littafin da yake buɗe, da fensira a kai.

 

“Duk wanda ya duba littafin nan, ba da izinina ba, Allah ya isa!!!”

 

Tsaki yayi, ya buɗe shafin gaba.

 

“Zan so ace ni marubuciya ce, da sai kun fi fahimtar abun da zan rubuta, amma gaskiya ba zan iya ba, ban sani ba ko ku gane me nake nufi, idan na zana abu mai muhimmanci da ya sameni a rayuwa, da wanda ya tsaya a zuciyata har in mutu ba zan manta ba, ina fatan ku ji irin abun da na ji, ko za a samu mafita”.

 

Zane ne tiryan-tiryan, zane mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali, daga fitarsu daga gida zuwa tasha, tare da taƙaitattaun bayanai, a gefe, na abun da ya faru”. Nutsuwa ya nutsu yana bi, sai dai duk da haka ta cire wasu abubuwa masu muhimmanci.

 

Daga banɗakin ta fito, tana kokowa da towel, sai dai ta yi turus da ganinsa, saboda ba ta san ma yana gidan ba.

 

Kallon-kallo aka shiga yi tsakaninsa da ita, kamar ɓarawo da mai kaya.

 

“Meye wannan?” Yayi maganar yana nuna mata littafin.

 

“Waye ya ce ka ɗaukar mini littafi? Ba ka ga gargadin da na yi a farko ba?”.

 

“Me wannan zanunnukan suke nufi, bayan kin ce mini, ke baki san komai ba? Meye ƙarashen wannan zanunnukan, kuma a wace tashar motar ku ka hau mota?”

 

Tura baki ta yi ta kawar da kai, ya nufeta gadan-gadan, nan take ta ga idonsa ya fara wannan hayaƙin.

 

“Yi haƙuri, ka bani zan yi maka bayani”

 

Ya miƙa mata littafin, sai dai tana karɓar littafin, ta riƙe towel ɗin ta, ta kasa da gudu ta bar ɗakin.

 

 

READ ƘANWAR MAZA PAGE 64 HERE


Proceed with your download by clicking the below button

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button