Hausa novels

Matar Damisa Book 1 Chapter 29 Complete Novel

🐅MATAR DAMISA🐅

(The Wife Of a Tiger)

*written* *and* *story* *by*
*Asma’u Muhammad Auwal*

( *ASMEETAH NOVEL* ✍️)

https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt

*WhatsApp me 09065443871*

*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
___________________________________

https://www.facebook.com/103637491942644/

💫💫 *{{N W A}}* 💫💫

بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم

*BOOK ONE*
🅿️ ——-> 79 & 80 <——-

💫✨.
“A gaskiya Laila baki kyauta ba, saboda rashin Imani da kuma rashin tausayi ki ɗauki hannun mutum mai rai ki ɗora akan wuta? ina ganinki mai hankali…”
A wannan lokacin ran mommy yayi matuƙar ɓaci, ta rinƙa surutai tana balbalawa Laila masifa,
cikin ɓacin rai Laila ta tashi tana gunaguni ta yi hanyar waje zata tafi,
ita kuwa Ayush tana can medicine room ita da Doctor yana duba mata hannun…

yana riƙe da hannunta ya gama ɗaure mata shi da bandeji bayan ya yi treat ɗinta,
“kiyi hakuri Ayushert bansan haka zata faru ba wallahi da bazan barta ta biyo ki ba, yarinta ne yake damun Laila! please forgive her..”

murmushi Ayush tayi sannan tace “babu komai ya wuce, nasan duk akan Yaya Junaid tayi mun haka, but shawarar da zan bata shine taso mai sonta, ta daina son maso wani ka sanar mata saƙo daga Ayushert, na barka lafiya…”
ta fizge hannunta da ya riƙe tayi ficewar ta daga cikin room, zuciyarta cike da ɓacin rai,
kuma abunda ya ƙara ƙona mata rai shine abunda Doctor ya gaya mata wai Laila yarinta ne ke damunta,
tana tafe hawaye na zubo mata ta rasa mai ke mata ciwo a jiki,
shigar ta cikin falo kenam ta tarar da mommy zaune tayi tagumi, ganin Ayush yasa tayi firgitt ta tashi tana faɗin “Ayush yadai hannun nakin, anyi gyaran ko mugani..” mommy ta kamo hannun Ayush ta kuma cewa “Allah sarki ki duba kiga fa duk da an manne hannun da bandeji amma wanda ya gani yasan ba ƙaramin ciwo bane…

Ayush tana kwance saman sofa a falo kanta kuwa yana kan cinyar mommy tana mata wasa da sumar gashin ta, Doctor ne ya shugo idon sa kuwa akan Ayush, yana faɗin “toh mommy ni zan wuce, dan Allah ayi hakuri akan abunda Laila ta aikata…”

Mommy tace “ba komai tsautsayi ne, kuma kowa baya tsallake ƙaddararsa,
kayi mata allura ne..?”

“Eh nayi mata allurai guda biyu sai maganin da tasha insha Allahu zuwa gobe zata samu sauƙi..”
Mommy tace “toh shikenam Doctor, Laila ta yi zuciya ta tafi gida, amma ka rinƙa mata nasiha akan sha’anin rayuwa kar ta rinƙa biye wa zuciya domin zata kaita ta baro ta ne…”
Doctor ya amsa mata da “to ba damuwa Mommy insha Allah zanyi iya ƙoƙarina akanta, nagode” cikin girmamawa ya yi mata sallama idonsa kuwa akan Ayush wacce ta kifar da kanta saman cinyar mom ko kallonsa batayi ba…

*****

Sarki Raamud yana zaune a saman gadon su ya naɗe ƙafafuwa kamar mai zaman cin tuwo, ya riƙe hannunsa na hagun, shi kaɗai ne yake jin wannan raɗaɗin da yake ji bayan Ayush!
tafin hannunsa ya yi jawur, ƙonuwar da Ayush tayi ne shima ya shafe shi sai dai shi bai nuna ƙonuwa ba amma gurin yayi jawur dashi,
Bara’at tana zaune daf dashi sai dumama masa hannun take da ruwan zafi, tana faɗin “kayi hakuri shugaba, wannan ciwon nakan lokaci guda ni na rasa gane maka…”

yana ajiyar numfashi yace “meya faru da Ɓingel ɗina? na tabbata akwai wani mummunan abu daya faru da ita..” ya ƙarasa maganar yana duban hannunsa wanda ya nuna alamun ƙonuwa.
Da mamaki a fuskar Bara’atu idonta akan sarki tace “daman Ayush bata mutu ba??”

kallonta sarki yayi da ɓacin rai yace “Ɓingel bata mutu ba, kuma bata cire zoben dish a cibiyar ta ba, idan kuma kinason ganin bayanta bismillah..” ya ƙarasa maganar yana nuna mata hanya.

miƙe wa Bara’at tayi daga zaune tana zazzaro ido tace “ya akayi hakan ta faru? nidai nasan Ayush ba yanda za’ayi ta bar zoben nan a jikinta indai har Junaid ya mutu, idan kuwa Ayush tana raye to tabbas Junaid ma yana raye…” ta juyo tana kallon sarki da murmushi kwance saman fuskar ta.
Shi kuwa hannunsa yakai ya dafe goshinsa kansa yana sunkuye, murya a sanyaye yace
“Hmmm! Bara’at kenam kina tunanin sarki Raamud ɗin baya kamar yanzu yake, na canza tin daga lokacin da Allah ya nuna mun cewa shi kaɗai ne mai mulki kuma shine mai juyar da komai, haƙiƙa na tafka babban kuskure a rayuwata, na zalinci al’umma wanda bansan iya adadinsu ba,
ga kuma ɗan uwana twins ɗina nine nayi sanadiyar barinsa duniya, ina zan ganshi na nemi yafiyarsa? ga mahaifina shima ni nayi sanadiyar hallaka shi shima ina zan sameshi na nemi yafiyarsa? ga Junaid ina zan kai tarin zunuban da na ɗauka, na tabbata alhakinsu ne yake ta bibiyata,
na rasa komai nawa inada manya-manyan aljanu masu bani kariya sun kai trillions amma gashi tashin farko duk na rasa su…” yana zubda hawaye ya tashi ya tsaya a gaban Bara’at yana faɗin “a koda yaushe mutuwa tana ƙara kusanto ni, za’a iya kawo mun hari a ko wani lokaci saboda bani da mai bani kariya….”
kafin ya kai maganarsa ƙarshe Bara’at ta katse shi da cewa “sai Allah, Allah shine mai bada kariya, inda ace tin farko ka riƙe Allah a zuciyarka da baka shiga wannan halin da kake ciki yanzu ba,
su waɗanda kake tunanin zasu baka kariyar suna ina yanzun? babu su asalin mai bada kariyar ya tarwatsa su kuma shi kaɗai ne mai baka kariya, inda ace bai baka kariya ba da yanzu babu kai a doron ƙasa…”

Sarki Raamud fashe wa yayi da kuka ya rungumi matarsa Bara’at yana faɗin “Allah na tuba ka gafarce ni, na aikata babban kuskure, ɗiyar dana haifa a cikina ma gudu na take..”
suna cikin wannan halin suka jiyo kukan mujiya 🦉🦉 a harabar masarautar.
jin hakan yasa sarki ya zabura yana faɗin “Innalillahi wa inna’ilaihi raju’un, *MUNAFURR* yazo shi..”

Bara’atu ta ɗago tana kallonsa ido sunyi zuru-zuru tace “wa ne ne Munafur ku ma..” ta ƙarisa maganar cikin ƙinƙina baki na kakkarwa, ita tsoronta kar a farmake su..

Sarki Raamud jan hannunta yayi yace “muje mu..”
suka nufi wajen masarautar,
a falon masarautar suka tarar da Munafur a gaban Damusa Sujjur yana shafar gashin bayansa tare da rera waƙar isgilanci,

Munafur wani mutum ne mai hatsarin gaske kuma mungun maciji ne, idanuwansa baƙi ƙirin ne ƙananu na maciji, hatta sumar gashinsa zirin macijine ƴan ƙananu, duk yanda ya taka maciji ne yake fitowa, farin mutum ne irin buzayen nan yana tafe da sandarsa mai ƙiran maciji kuma sandar zai iya komawa macijin gaske!
Munafurr ba’a haɗa ido biyu da shi domin makance wa mutum zaiyi…..

Bara’at ganin yanda mutumin yake a take ta faɗi sumammiya,
shi kuma Sarki Raamud farin ƙyalle ya nema ya ɗaure idonsa dashi gudun kar ya haɗa eyes da shi,

Munafur cikin salo ya yi wani irin juyi ya zauna akan kujerar mulki wanda inba sarki ba babu wanda ya isa ya hau kan kujeran nan,
ya tintsire da wata iriyar dariya mai kama da kuka yana faɗin “Masarautar Maƙarƙashe daga yau ya zama nawa!!!
daga yau na koma Sarki Munafurr….”

gaban Sarki Ramud ne yayi wani irin bugawa da ƙarfin gaske, ya durƙusa gaban Munafur yana faɗin “Munafur taya hakan zata faru? bayan ban sauƙa akan mulkin ba..”

wani irin kallo Munafur yake yiwa sarki Raamud yana jujjuyar da kansa, cikin dirarriyar murya yace “haka naso kuma haka naga dama, wannan masarautar ta zama na Munafur…”

Sarki Ramud cikin ɓacin rai yace “hakan bazai taɓa yuwa ba domin wannan masarautar ya fara ne daga tin kakanun kakanun iyaye na kuma haka zai cigaba da tafiya har kan jikanu na, wanda zai mulki wannan masarautar shine ɗan ɗan-uwana koda bayan rai nane…….” tin kafin ya ƙarasa maganar Munafurr ya wurga masa sandarsa lokaci guda sandar ta zama maciji ya naɗe wuyan sarki Raamud, ga ido kuma a ɗaure da farin ƙyalle baya ganin abunda ke faruwa…

Munafurr ya kalli Damusa sujjur ya tintsire da dariya sannan yace “jinin yaron da kake son bawa mulkin maƙarƙashe yana jikin Damusaaa….” yana nuna Damusar tare da jann maganarsa cikin salo da isgilanci,
ya kuma cewa “tayaya maƙiyinka zai zamo masoyinka Raamud? shin ka manta da yarjejeniyar da mukayi ne?….” ya ƙara tintsirewa da dariya yana ambaton
“Junaid! Junaid!! Junaid!!! yau kwananka ya ƙare, tinda maƙiyinka ya fara ƙaunarka ai lamarin ya ɓaci, saboda haka zan kashe Junaid tare da shi wannan Damusar, kaima idan kamun tirjiya zan hallaka ka in mayar da matarka baiwa ta…”

Sarki Raamud yana karkaɗa hannayensa alamar bada hakuri, babu halin magana sakamakon sandar macijin daya zagaye wuyansa ya shaƙe sosai ko yawu baya iya haɗiya…”

shi kuma Munafur gashin kansa da ya zama na macizai ne suke ta buɗe baki suna kaiwa sara abun farmaka suke nema,
hannu yasa ya figi ɗaya daga cikin macizain gashinsa ya wurga wa Damusa, macijin ya shige cikin gashin Damusan…

cikin zafin nama Munafurr ya tashi yana faɗin “zan tafi amma zan juyo bada daɗewa ba, ganan Damusar ka ga can Junaidu ka cecesu idan zaka iya….”
yakai hannunsa ya ciro sandarsa daya zamo maciji daga wuyan Sarki Ramud yayi ficewarsa,
kai tsaye harabar masarautar ya nufa yanda wata ƙatotuwar mujiya take a tsaye, girman mujiyar yakai raƙuma haka Munafur yayi tsalle ya hau kan mujiyar suka bar masarautar….

a gaggauce sarki Raamud ya finciki ƙyallen daya rufe idonsa da shi, ya dubi yanda Damusar yake, da gudu ya nufi gurin Damusar yana faɗin “Sujjur! Sujjur!! Sujjur!!! ka miƙe kada ka mutu dan Allah..”

Damusar yana kwance sai shure-shure yake tayi yana shirin mutuwa ga jinin dake zuba a bakinsa, idon Damusar ya koma launin Jaa daga blue…

*****

Ayush ce take taka matakalar beni a hankali, tana ɗangale hannun data ƙone!
ta nufi ɗakinta zata shige ji tayi gabanta yana ta faɗuwa, jikinta ba ƙwari, ɗan tsuka ta ja sannan ta rufe ɗakinta kai tsaye ɗakin Junaid ta nufa…

itama Mommy tana zaune akan sallaya yanda ta idar da sallah bata tashi ba,
ƙirjinta sai bugawa yake yi, gabanta na faman yanke wa,
a hankali tace “mai yake shirin faruwa dani ne?..”
kafin ta kai ƙarshen maganar zucin ta tajiyo ihun Ayush ta ƙwallawa Mommy ƙira,
a gigice Mommy ta zabura tana faɗin
“La’ilaha illa anta subhanaka inni kunta mina zalimin,
Allahumma ajurni fii musibati wa akhlif lii khairan minhaa….”
Mommy ta gagara tashi jikin ta sai kakkarwa yake sai faman jero addu’o’i take…

Shi kuma Junaid shima ya yi irin abunda Damusa yayi, sai shure-shure yake bakinsa yana bleeding jini, idonsa yayi jawur yana ta kakkarwa,..
Ayush ta durƙusa ƙasi sai faman jijjigar sa take tana ihu…

Domin sauke CikakkenLittafin Sai Ku Danna bulun Rubutun dake kasa 👇👇

Matar Damisa Book 1 Complete Novel Document 

*🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝*
*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦300
2GB = ₦600. 2GB = ₦600
3GB = ₦900. 3GB = ₦900
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500

*GLO* . *9MOBILE*
1GB = ₦350. 500Mb ₦500
2GB = ₦700. 1.5GB ₦1100
3GB = ₦1050. 2GB ₦1600
4GB = ₦1400. 3GB ₦2000
5GB = ₦1750. 4GB ₦2500

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
*🪀08066268951*

*ASMEETAH NOVEL✍️✍️*

Back to top button