Harijin Tsoho Page 9 Romantic Hausa Novel
Wata shewa zahra a saki tai wani juyi sannan tace”ay kinyi sake dani na fara auran uban naki,kuma atafin hannuna yake abinda nakeso yakeyi,dole nadan nice wacce ze shawarta ta farko kamin ya amince ya aurar dake gama ko waye bama mahaifinaba,ze aura miki shine kawai idan shi mahaifin nawane yazo yace yana sonki wanda kinsani mahaifina ba abinda zeyi dake domin dasji ka taru aka kashe maganar cikin da habeeb yay miki a ƙoƙarinki nason ganin kin tozartani kingo mezeyi da saura,hajiyat baki da capacityn kishi da uwatadomin takai budurcinta ɗakin mahaifina,”cewar zahra wacce tana gama faɗa mata haka ta koma tai kwanciyarta akan gado.ita ko khhadeeja jikintane yyi sanyi sosai taji kamar ƙasa ta tsage ta shige ciki dan koda wasa bata taɓa sanin zahra tasan batun cikin da habeeb ɗin yay mataba wanda ko daddy besan maganarba wayyo Allah to in zahran ta faɗawa daddynfa ?ya ma akayi zahran tasan habeeb yay mata ciki wannan abune a tasan mahaifin zahra baze taɓa faɗawa koda mahaifiyar zahran bace bare har zahran taji,to ko habeeb ɗinne yafaɗa mata?,kai habeeb baze faɗa mata ba””ki ɗan je daga waje inkin gama lissafin in amsar ta fito se kzo ki faɗamin”cewar zahra dake kwance.Kamar kazar da ƙwai ya fashewa khadeeja ra juya ta fice a ɗakin tana waigen zahran da ta zame mata abar tsoro yanzu.”kikace bakyaji,ashe baki shirya ba?”cewar zahra tana dariya ta maida kanta ta kwantar ana kallon sama hoton abubuwan da suka faru abaya ya fara dawo mata .********FARKON LABARI”Alhaji na zaɓi nakiraka gidane sabida banasn Yasan na kawo ƙararshi,”cewar mamy tana wasa daƴan yatsunta.Murmushi yayi ya gyara zamanshi yace”to Hajiya hafsa ay duk inda akace an kawo ƙara to yazama wajibi wanda ake ƙarar yasan anyi ƙararsa domin abinda akayi ƙarar tasa akai in na biyane yabiya in na denawane ya dena dan haka karki damu faɗamin damuwar insha Allahu zansan ta yadda zan masa bayani ya fahimcemu”ƙasa tai da kanta alamun abinda zata faɗi ɗin me nauyine a bakinta tace akunyace”amininka yaƙi sauyawa har yanzu alhaji tun da ƙuruciyarmu har zuwa yanzu da girma yazo mana ba abinda ya sauya,nayi masa mgn kan ya dinga sauraramin yaƙi wai shi halittarshice haka mabuƙacine,tsofai tsofai dani wlh har wasan ɓuya yake sani yi dashi agidan nan ga yara,yaƙi yarda a girma anzu ba dabane”ta faɗi ana kare fuskartatattaro natsuwarshi yayi dan ya fahimci inda zancan nata yasa gaba kuma abune daya dace ay masa duba na tsanaki,gyara murya yayi sannan yace”hajiya hafsana fahimceki,sede inaso kiyi haƙuri kimaa uzuri,sabida kingake kaɗaice matarsa,kuma shi mabuƙacine inbe karre utuncinshi agidanshiba ƙarewa zeyi a awon bin kwararo azo kuma nutunci na zubwa,shiyasa nake shawartarki daki ƙara haƙuri don Allah zan masa mgn in yaso ko aurene se ya daure ya ƙara dan asamu masalaha”eh wlh garade yayi auren dan nide bazan iya abinda nayi a shekarun ƙuruciya ace yanzuma da shekaruna suka ja in maimaitaba,ku daurede kusashi yayi auren don Allah”cewar hajiya hafsan.”Ba damuwa bari inje office in sameshi insha Allahu zaa samu mafita”yana kaiwa nan ya mi,ƙe yay mata sallama ya wuce.direct iffuce ɗin Alhaji sammani canji ya nufa wanda a kasance amininsa un suna yara harczuwa girmansu vasu sauyaba.da faraa Alhaji sammani canji (uncle)ya tarbi amininsa Alhaji jaafar (mahaifin zahra)bayan sun gaisa ya gabatar masa daabun shane Alhaji jaafar yadubeshi yace”mutumina yaufa ƙararka aka kawomin”gyara zama yayi yana dariya ace”ay dama tunda naga bace sena dawo an ansamin ciki ciki nasan yau rawa seta Allah””Au kasan ma me ƙarar taka kenan to Alhamdulillahi””nasan me ƙara amman bansan laifin daake ƙarata akaiba”cewar uncle yana dariya.Gyara zama Abban zahra yayi sannan yace”Alhaji eyasa kake akura hajita a buƙatunkane fusabilillahi,niwlh danaga an kwana biyu bata kawo ƙararba na ɗauka kadena ne ashe hali yananan”ya faɗi yana kalln amininnasa.zare glass ɗin idonsa uncle yayi sannan yace ciin natsuwa”Alhaji wlh ko yanzu da nake maka mgn acikin buƙatuwa nake tason na tara da iyalina,amma haƙuri nake,atunzamana da hajiya wlh duk wannan ƙorafin nata ban taɓa zuwa biyar akantaba,itade kawai tana da ƙarancin buƙatane,to yanzu kuma ma so take gaba ɗaya ta maidarmin da auren namu auran zuba ruwa abuta,ita kawai insa iddo inkalleta wai ita ta tsufa,47years wai tana faɗin zikiri a rage mana mui tayi nida ita, bawai sex ba”cewar uncle yana duban aminin nasa.”To Alhaji tunda abun hakane meze hana bazaka ƙara aureba ka auri yarinyar mace da zata horu dabuƙatun naka kaga shikenan base ansake jin kankuba”cewar abban zahra.Murmshi uncle yayi yace”ay kuma kunya zanji nide a yadda nake kuma wai aganni naje neman aure gurin ƴar cikina ay bansanma ta ina zan faraba wlh dan haka mubar mgnr nan muyi de wata”ya faɗi yana dariya.”dole kayi aure Alhaji tunda matarkama ta nuna gara kayi auran ita zatafi son hakan akan ka dunga takurata”cewar abban zahra.Shuru uncle yayi na yan mintuna kamin yace”xanyi tunani akai”sunjima tare abban zahra na bashi shawarwari masu kyau kamin suyi sallama su rabu.KAD POLYzaune suke akan kujeru da aka tanada domin zama a dede gaban ƙofar shiga capteria.kowaccensu ranta a ɓace yake se duba takardun hannunsu sukeyi.zahrace ta fara mgn ranta a ɓace”wallahi sena nuna masa kuskurensa akanme zeba bestie carry over sekace besan tare mukeba”ta faɗi tana ƙwafa.”sam be duba ba wlh ay zaman tare yafi gaban wasa bare khadija wlh da ƙoƙarinta,”cewar halima itama ranta aɓace.murmushi khadeeja tayi tace”don Allah kudena damuwa wallahi babu komai nifa ko ajikina domin daddy dama yace be gamsu da karatu a ƙasarnanba waje ze kaini”cewar khadeejan tana dafosu.”Komade meye ayshi daddyn in yaji bazeji daɗiba “cewar zahra.Suna cikin maganar ya ƙaraso gurin a motarshi,ya faka ya fito ya tunkarosu fuskarsa ɗauke da murmushi yace yana kallon zahra”princess se kirankinake baki ɗagaba hope de ba laifi nayiba”ya faɗi yana zama kusa da ita.kauda kanta gefe tayi tace ranta aɓace”nifa da kaba khadeeja carry over ni ka barni in tsallake wallai gwanda ni kabani ita ka barta,habacdon Allah ni gaskiya baka kyautamin ba sir habeeb”cewar zahra cikin fushi.



