Mijin Marigayiya Page 25 Hausa Novel
Tun kafin ta tayar da sallah cikinta yake kugi saboda jiya bata ci abincin dare ba ta kwanta, don haka tana idar da sallah ta gama azkar dinta ta bude kofar dakin ta fito ta wuce kitchen; a lokacin Rashida da su Afaf babu wanda ya tashi domin dama itace take tashin Rashida kafin tayi sallah su kuma su Afaf bayan ta idar da sallar. Tana shiga ta dora ruwa kofi daya ta jira ya tafasa, ta hada shayinta mai kauri a babban kofi ta dauki burodi ta gutsura ta dauka ta nufi daki. A falo ta ci karo da shi ya shigo daga masallaci, ya dubeta yace ‘Shayi zaki sha da sanyin safiya kuma.’‘Um.’ Ta bashi amsa sannan ta wuce dakin.Da hanzari ya bita don kada ta rufe kofar, ya cimmata a daidai lokacin da take zama a kan dadduma tana ajiye shayin nata. Ko kallon inda yake bata yi ba balle ta nuna ta san mutum ya shigo. Ya karasa ya zauna a gefen gado yana cewa ‘Sai kin gama zaki taso yaran ne? akwai school fa.’Ta gutsiri burodi ta tsoma a shayin sannan tace ‘Bani da lecture sai 9am so idan na gama zan dan koma ne na rage bacci zuwa kamar 8am sai na tashi na shirya.’Ya dan yi dariya a kaikaice don ya san kwanan zancen, yace ‘Haba dai, ai kya daure ki shirya yaran kafin ki koma ki kwanta ko?’‘Oh, ai kuma ka cire al’amarinsu daga hannuna ka saka a hannun sakatariyark kamar yanda ka sanar da ni a aikace jiya don idan ban manta ba ma itace ta kawo muku dinner. Ko ba komai ma ka huta da mita ta.’Ta dauki kofin sahyinta ta cigaba da kurba.Ya dan tsaya yana kare mata kallo saboda yanda ya kasa fassara yanayin fuskarta domin kamar ranta ba a bace yake ba kamar ma dai tana cikin yanayi na nishadi. Yace ‘Common Khadija, na riga fa nagaya miki cewa ban sameki a waya ba shi yasa nace ita taje ko? Ko da wani abu ma ai sai ki shiryasu idan na kaisu makaranta sai mu karasa maganar kinga lokaci yana kurewa.’‘Babu ma wani abu, na riga na fahimci sakon.’Ya mike yana cewa ‘To don Allah ki fito ki shiryasu kinga idan suka makara rufe gate za ayi.’Ta cigaba da shan shayinta kamar ba da ita yake magana ba, ya fara kosawa don haka kamar a hasale yace ‘Kina ji ina miki magana ko?’Ta kalleshi suka hada ido tace ‘Na ji.’Ya kalli agogon bangon da yake dakin ya ga karfe shida saura kwata, ya juya ya fice ba tare da yace komai ba. Ya wuce dakin yaran don ya kula so takeyi su makara. Idan ya tasosu in ya so sai suzo da kansu su gaya mata ta taso ta shiryasu.Yana ficewa ta tashi ta tura kofar a hankali ta mayar ta kulle ta bar mukullin a jiki, domin yau babu wanda zata shirya sai dai ayi duk abinda za ayi. Tana zama a kan daddumar taji Nasreen tana buga mata kofa tana cewa ‘Anti mun tashi.’Har ta gaji da bugun ta ruga bandaki ba a bude mata ba.Ya fito daga dakin nasu Rashida tana biye da shi, ya dubeta yace ‘Je ki tayat mana ku shirya yara, kun kusan makara fa.’Ta wuce kitchen yayinda ya nufi dakin Khadeeja, ya murza hannun kofar yana turawa ya jita a rufe ‘Ya juyo da mamaki yana hango kitchen yana cewa ‘Ko kina kitchen ne?’Ya wuce ya nufi kitchen din, yana shiga ya dubi Rashida yace ‘Bata fito ba?’Tace ‘Eh.’Yayi tsaki ya juya ya fice. Ya koma kofar dakin nata ya kara kwankwasawa, sai sai har ya gaji da kwankwasawa bata bude kofar ba, yana kallo ta kasan kofa ya ga duhu alamr an kashe fitilar dakin. Ya ja tsaki ya wuce dakinsa, yana shiga ya dauki wayarsa ya fara kiran lambarta. Sai dai har ya gaji da kira bata dauka ba. Don haka ya ajiye wayar a kan gadon ya fito daga dakin ya wuce kitchen, yana shiga ya tarar da Rashida tana tattare fulawar da ta kwaba jiya za ayi shawarma wadda Khadijab ta barta a nan a bude ta kwana har ta bushe. Yan shiga ta bar abinda takeyi ta tsaya tana kallonsa. Yace ‘Ya baki fara komai ba kika tsaya kina kallona?’‘Uhm ai ban san me zan fara ba.’‘Me kuke yi ke da ita idan zata shirya ‘yan makaranta?’‘Um, ai itace take yin abincin ni tayata nake yi, kuma yanzu ban san me zata dafa ba.’‘Mtsewww!’ Ya ja tsaki sannan ya juya kamar zai fice sai kuma ya dawo yace ‘Ki dora ruwan shayi mana da abincin tafiya makaranta.’Ya juya zai fita tace ‘Um to abincin makarantar me za a dafa?’Ya kalleta cike da takaici; wai wannan wacce irin dakikiyar yarinya ce? Yace ta dafa abincin ma sai kuma ya gaya mata abincin da zata dafa. Kamar zai fice kuma sai ya tsaya yace ‘Ki dafa indomie.’‘To.’ Ta amsa jikinta na rawa ta juya ta shige store domin dauko indomie.Yana dawowa parlor din ya jiyo Afaf tana hayaniya da Shukra a kan shiryawa, har ya nufi dakin sai kuma ya fasa ya wuce kofar daki Khadeeja ya kwankwasa kofar a hankali yana cewa ‘Khadija ki bude mana.’Babu wanda ya bashi amsa don haka ya koma parlor din ya zauna yana jiyo hayaniyar yaran a dakinsu suna shiryawa. Jimawa kadan ya tashi ya nufi dakin inda ya sa hannu ya fara kokarin tayasu shiryawa. Nan da nan suka gama sannan ya tasosu a gaba suka fito inda ya saka su a gaba suka sha shayi da burodi sannan a gurguje Rashida ta zuba musu indmie dinsu a flask ya tasa su a gaba suka fice.Khadeeja tana jin fitarsu da mota ta fito daga dakin a shirye ta sallami Rashida ta sanar da ita idan ya dawo ta fice ta tafi makota in ya so idan zai fita sai yayi mata magana ta dawo; Haka suka saba tunda Shukra ta shiga makaranta; idan dai ba tare da yara zai fita ba sai dai Rashida ta je makota ta jira idan ya gama zai fita sannan ta dawo ta shiga gidan.Bayan ta gama sallamar Rashida ta fice ta tafi makaranta.………Suna dab da karasawa makarantar aka rufe gate din, gaba daya masu gadi da sauran ma’aikatan suka shige ciki suka rufe kofa; wanda hakan yake nufi babu yaron da zai sake shiga. Ya tsaya ya cije lebe na dan lokaci sannan ya kunna motar suka kama hanyar komawa gida.Nasreen tace ‘Mun makara, gashi bamu taba makara ba.’Yace ‘E, kun tsaya kuna ta fada baku shirya da wuri ba.’Afaf tace ‘Abba Anti bata lafiya ne?’Ya shafa kansa yana cewa ‘Eh, bata jin dadi.’Suna Shigowa gidan suka tara da Rashida a tsaye a bakin kofa kamar yanda ta saba jiransa, tana ganin su ta bisu suka shige. Shi kuma Abbansu ya karasa kofar dakin Khadeeja ya fara kwankwasawa yana yi yana cewa ‘Khadeeja daAllah ki bude mana.’Rashida ta fito daga dakin su Afaf tace ‘Antin ta tafi makaranta.’Ya kalleta da mamaki yace ‘Makaranta? Yaushe?’‘Bayan kun fita.’Ya wuce dakinsa ya barta a nan.To me Khadija take nufi ne? Daga yin abu ta ma ki ta zauna ayi magana tana ta wulakanci, gashi har ta sa yara sun rasa makaranta. Yanzu gashi dole ya fita ya barsu a gidan su kadai abinda baya so. Amma wannan wulakancin na Khadeeja fa ya fara yawa, ta ma ki ta saurareshi gaba daya. Yanzu ya take so ayi?Haka ya wuce dakinsa ya zauna ya fara kiran wayar Khadeeja amma har ya gaji da kira bata dauka ba. Ya duba lokaci yaga karfe takwas da rabi, gashi yana da meeting karfe tara. Don haka a gurguje ya tashi ya shiga wanka ya shirya. Ko abinci bai tsaya ci ba ya fice ya bar yaran.……….Babu wanda ta gayawa yanda suka yi da Mustapha, don ko su Rahma bata cewa komai ba; su kuma da suka kula bata son magana sai kawai suka kyaleta. Haka tayi zamanta a makaranta har wajen karfe biyar na yamma sannan ta kamo hanya ta dawo gidan. Tana shigowa yara suka fara yi mata oyoyo; da murnarta ta amsa sannu da zuwansu kamar yanda ta saba. Ta kalli Afaf tace ‘Bari na je daki na sha magani na huta, kaina ciwo yake yi.’Ba tare da ta saurari amsarta ba ta shige dakin ta turo kofa.……….Sai bayan sallar isha’i sannan ya dawo, lokacin Afaf ta sa Rashida ta dafa musu taliya sun ci abncin dare saboda Khadeeja tace kada wanda ya sake buga mata kofa.Yana shigowa gidan ita ya fara tambaya suka ce masa tana daki, sai dai ga mamakinsa yana taba kofar ya jita a rufe. Nasreen ce ta sanar da shi cewa tace a dina buga mata kofa bata lafiya. Don haka shima sai kawai ya kyaleta ya cigaba da harkokinsa har sai da yara suka kwanta.Wajen karfe goma na dare ya sake kwankwasa mata kofar, tayi banza da shi bata ce komai ba. Ya matsa jikin kofar yace ‘Wallahi Khadeeja idan baki bude kofar nan ba zan balla ta.’Tana daga ciki ta dauki ‘yar saman rigar baccina ta saka sanna ta zo ta bude masa kofar tana rike da wayarta tana chatting. Ta koma ciki ta karasa kan gado ta zauna ta mike kafarta ba tare da ta ce masa komai ba. Yana daga tsaye ya kare mata kallo sannan yace ‘Wai wanne irin wulakanci ne wannan kike yi ne Khadeeja? Kin bar min yara sun makara a makaranta kuma kin fice kin bar gida ba tare da wani bayani ba?’‘To ai ka san dai yau ina da lecture ko?’ ta bashi amsa sannan ta sake mayar da hankali a kan wayarta.‘To don me baki tashi kin shirya yara ba kuma da kika dawo kika sake rufe kofa kika barsu.’‘Au wai Najan bata zo ba? Ai na zata tayi musu komai tunda yau itace da aiki.’Ya cije lebe sannan ya ja dogon tsaki ya fesar da iska saboda yanda Khadeeja take kureshi ‘Na gaya miki babu komai atsakanina da ita sakatariyata ce kawai, don Allah wai me kike so nayi miki ne a kan wannan maganar. Idan kuma don taje makarantar yara ne to kiyi hakuri ba zata sake zuwa ba, babu wata alaka tsakanina da ita dama sai ta office.’‘Ai naga alama.’ Ta fada ba tare da ta daina kallon wayara ba.A fusace yace Khadeeja ni nake miki magana kina danna waya ko kallo ban isheki ba?’Ta ajiye wayar a gefenta ta kalleshi tace ‘Shike nan, na ji duk abinda ka fada.’‘Please kada ki sake rufe kofar nan, kuma ga yara can sun kwanta da safe ki tashe su da wuri kada su makara.’‘Ok.’Har ya juya zai fita ya dan tsaya yace ‘Kuma kin san kema ba a nan kika saba kwana ba.’‘Ok.’Ya fice ya barta.Ta murguda baki kamar yana kallonta tace ‘Dan rainin hankali, baka yi laushi ba tukunna kaje ka dauko Naja ta zo ta dinga yi maka hidimar kai da yaran…
