Halysaah Page 219 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 219…Da sauri Ajay ya dora Babyn dake tsala ihu a saman Hijab dinta that is close to her, he was full of emotions at this moment, ya rungumota sosai a jikinsa amma ya kasa ce mata komai, kawai hawayensa taji a bayanta, cikin breaky voice yace “You are the best thing that have happened to me Jeeddah, God bless you Jeeddah, Allah ya maki albarka, Allah ya maki albarka” Lokaci daya ya saketa after realizing she is bleeding, ya mike da sauri zai bata taimakon gaggawa…. Ajay ya shigo Bedroom dinsa rike da cup din tea ya nufi Khaleesat da ta fara bacci a kan gado, ko minti biyar bai yi da zuwa hado mata shayin ba amma kafin ya dawo har ta fara bacci, har lokacin kuma bai sanar ma kowa cewar ta haihu ba a gidan, ya ajiye cup din ya zauna gefenta ya saka hannunsa cikin nata yayi pecking lips dinta a hankali yace “Wife” Ta bude idonta slowly tana kallonsa, cikin sanyin murya yace “Allah ya maki albarka Jeeddah, thank you so much for this precious gift, thank you for making me a father…..” Ta lumshe ido ta bude, dagota yayi zaune ya sa mata pillow a bayanta ta jingina jiki, cikin kwantar da murya yace “Take the tea before sleeping” Tun bayan da ya taimaka mata ta gyara jikinta tayi wanka sannan ya gyara babyn take jin wani irin bacci kamar an aiko mata shi, ta kwantar da kanta jikin pillow tana lullumshe ido, a tare suka juya jin kukan jaririn dake gefensu yana ta mutsul mutsul da baki alamar yunwa, Ajay bai bi ta kansa ba cause he gat to attend to his wife first, ya dauko shayin da ya ajiye zai fara bata da kansa, ta amshi cup din a hankali tace “Zan sha da kaina, ka dauki babyn” Juyawa yayi ya kalli babyn dake tsala kuka ya hade rai yace “Kayyy” Khaleesat ta wani kallesa, murmushi yayi, yayi kasa da murya yace “He have to be patient let me attend to my wifey first, yaushe na san shi da zan kyale ki saboda shi….” Yana ganin ta ɓata rai ya tafi da sauri ya dau yaron dake kuka, iya rabin cup kawai khaleesat ta sha shayin, duk da Babyn dake hannunsa haka nan ya kwantar da shi ya karbi cup din hannunta yayi dropping akan bedside drawer sannan ya taimaka mata ta kwanta ya ja mata duvet ta lumshe idonta, shi dai kallonta kawai yake, he still can’t fathom that she delivered her baby her self, bai taɓa zaton karfin halinta ya kai haka ba, he never knew she was this strong, throughout today ashe nakuda take amma ta boye masa, ya sauke wani ajiyar zuciya yana kara jin sabon sonta a ransa, tana fara bacci ya fita parlor da babyn ya zauna don kar ma kukan sa ya dinga interrupting baccinta cause she needs rest, kallon agogo yayi yaga karfe biyu har da kusan rabi na dare, ya maida dubansa kan jaririn hannunsa ya dinga kallon yaron babu ko kiftawa at the same time abinda Jay yace masa ya dinga dawo masa kai, and he realized Jay only deceived him, a hankali ya dago babyn ya kai bakinsa saitin kunnensa ya lumshe ido yana masa rada, bayan minti daya ya maida bakinsa daya kunnen also murmuring into his little ear, har asuba Ajay na zaune parlor da jaririn a hannunsa yana dirka masa ruwa don sai kukan yunwa yaron yake, shi kuma bazai tashi matarsa ta fara basa nono ba don tana bukatar peaceful sleep, jin za a tada sallah a masallaci ya tafi Bedroom din Khaleesat ya kwantar da babyn don kar ma ya kai sa nasa dakin motsinsa ya tashi wife dinsa, ya duka yayi kissing dogon hancin babyn, before entering into the bathroom, bayan an idar da sallan asuba Ajay ya fito masallaci tare da Jay, ya ɗan kalli Jay yace “I have to show you something” Jay ya kallesa yace “Something?” Ajay yace “Yea, mu je part dina” Jay bai yi musu ba ya bi sa but he was wondering me zai nuna masa da asuban nan, ganin Jay ya tsaya a main parlor bayan sun isa bangaren, Ajay yace “Mu je ciki” Jay yace “Look, ka gaya min menene? What’s happening?” Ajay bai tankasa ba ya nufi corridor din dakuna, Jay ya bi sa da kallo, kawai ganin Ajay is very calm ne yasa hankalinsa bai tashi ba but still his mind is not at rest, bin bayansa yayi daga karshe, Ajay ya bude kofar dakin Khaleesat gently, tana zaune gefen gado rike da babynta da ta kafa ma ido babu ko kiftawa, ta daga kai ta kalli kofar da aka bude, Jay ya zaro ido sosai yana kallon Ajay with so much surprise, at the same time ya bar bakin kofar dakin cause her body is not fully covered, ya koma parlor ya tsaya yana kallon Ajay da ya biyo sa yace “Wattt?? When did she put to bed Junaid??” Ajay na murmushi yace “Ina can ina bacci, she delivered her self bruh….” Jay ya bude baki ba tare da yasan yayi hakan ba with shock, kawai ya nufi dakin sanin yanzu dai ta kintsa, Khaleesat na sanye da hijab dinta har kasa ta koma can edge din gado ta zauna ta kyale babyn Jay ya shigo ya sameta, Jay couldn’t hide his joy yana kallonta yace “Sannu Halysaah, sannu….” Direct ya nufi jaririn yana kallonsa with happiness yana murmushi ya duka ya daukesa ya dinga kallonsa babu ko kiftawa don kamar Ajay yayi khaki, komai nasa na Ajay ne har complexion din, Jay ya lumshe ido ya manna masa kiss a soft cheeks dinsa, sannan yayi masa rada a both ears dinsa, ya daga kai yana kallon Ajay dake ta kallon Khaleesat kamar zai hadiyeta, ita dai kanta na sunkuye, Jay na murmushi yace “He is little Mai martaba….” Ajay ya girgiza kai a hankali yace “He is Ahmad Jawwad (Lil Jay)” Jay dai ya dinga kallonsa, sai kuma ya maida dubansa kan jaririn hannunsa, and he immediately felt the connection between him and the little baby, bazai iya misalta irin soyayyan yaron da ya mamaye zuciyarsa tunda ya dora ido a kansa, Khaleesat dai ta sauke idonta bayan taji sunan da Ajay ya sa ma yaron, and she was very okay with it, Jay ya juya ya kalleta a hankali yace “Thanks for bearing us a little prince Halysaah, Allah ya maki albarka, Allah ya baki lafiyar shayar da shi” Ita dai kanta na kasa tana wasa da yatsun ta. Mami Jay ya fara zuwa ya sanar ma haihuwan with excitement, Mami was shock da taji Khaleesat da kanta ta haihu, ko second daya bata kara a dakinta ba ta ajiye carbin hannunta ta nufi bangaren Ajay da sauri, Jay ya tafi part din Hajja don tana gidan har sannan, suka gaisa da Hajja dake rike da Eeman, Hajja dai sai kallonsa take ganin yanda ya shigo da fara’a kamar wanda aka yi ma wani albishir me dadi, Hadiyah dai na kwance idonta a rufe, Jay na murmushi calmly yace “Halysaah ta sauka lafiya Hajja….” Hajja ta zaro ido tace “Ta sauka? Yaushe?” Hadiyah ta mike zaune jin abinda Jay yace don dama ba bacci take ba, Jay na murmushi yace “Jiya Friday kenan za ace, wajen karfe sha daya da wani abu ta haihu” Hajja ta saki kabbara ta mike tsaye tace “Allahu Akbar, shi ne ba a sanar mana ba tun a jiyan bayan har kusan karfe biyu idon mu biyu Aseeyah ba ta bari muyi bacci da wuri, suna asibiti ne?” Jay ya girgiza kai yace “A gida ta haihu….” Hajja tace “A gida ya amshi haihuwar? Me ta samu?” Jay yace “Namiji” Hadiyah ta dinga kallon Jay babu ko kiftawa jin abinda yace, Hajja ta zaro ido tace “Namiji? Alhamdulillahi, Alhamdulillah, Allah mun gode maka” Hajja ta fara matsar kwalla tace “Allah me kyauta da ƙari, kwanaki sha biyar tsakaninsu da Hadiyah, Allah mun gode maka da wannan ni’ima da ka mana, Allah mun gode maka” Komawa Hadiyah tayi ta kwanta, Hajja ta tafi ta kwantar da Eeman kusa da ita ta fita daga dakin zata tafi part din Ajay, Jay ya karasa ya zauna kusa da Hadiyah ya dau Eeman, yana kallon Hadiyah yana murmushi yace “Kin ji Halysaah ta haihu ko….” A takaice Hadiyah tace “Allah ya raya” Jay ya dinga kallonta, after some seconds ya ajiye Eeman ya mike ya fita daga dakin, Hadiyah ta bi sa da kallo hawaye suka fara zuba idonta, da sauri ta rufe fuskarta da pillow tana kuka a hankali….. Kan kace me labarin haihuwan Khaleesat ya karade duk masarauta, aka dinga shigowa ganin baby ana mata barka, farin ciki gun su Kilishi ba a cewa komai barin da suka ga namiji ta haifa, burin su kawai dama bakin ciki ya kashe Hadiyah da uwarta a gidan, karfe takwas na safe Mai martaba ya shigo har part din Ajay yayi ma Khaleesat barka sannan ya dau grandson dinsa yana kallo, babu abinda ya zo ransa sai ranan da aka haifa masa Ajay, don yaron sak Ajay a sanda aka haifesa, shi ma kuma a gida mahaifiyarsa ta haifesa ita kadai a daki kuma ranan juma’a, sai jin kukan yaro jakadiyarta tayi, and this memory really broke the king down, he wish his beloved wife is around to see her first grandchild, a hankali yayi ma yaron addu’a sosai sannan ya kalli Ajay, calmly yace “What did you name him?” Ajay ya sauke idonsa a hankali yace “Ahmad Jawwad” Mai martaba yayi murmushi cause that is the name he have for the baby also, yana jinjina kai yace “Allah ya raya sa a bisa tafarkin addinin Muslunci” Jay dake zaune kusa da Ajay a parlon yace “Ameen ranka shi dade” Mai martaba ya mika ma Jay yaron sannan ya fita daga parlon, Jay sai kallon babyn yake yana murmushi, he is so in love with the little boy, can ya kalli Ajay yace “To wani bola za mu kai sa tunda ba mace bane?” Ajay ya jefa masa wani kallo yace “Wallahi sai ka maido min dubu dari na, kaji na rantse” Jay ya dinga dariya don shi kansa bai san ma ya aka yi ya shirya masa wannan karya ba a cikin few seconds kuma ya yarda. Sai wajen karfe goma Hadiyah ta shigo yi ma Khaleesat barka a part din Mami don an maida ta can, a haka ma Hajja ce ta matsa mata taje tayi barkan don cewa tayi bata jin dadin jikinta ko kadan, ko breakfast bata yi ba, haka nan dai ta tafi saboda addabar ta da Hajja tayi, tana rike da Eeman a shoulder dinta ta shigo part din Mami ta tafi har dakin da Khaleesat take, Kilishi da Hajiya Habibah ne a dakin a zaune sae jakadiyar Khaleesat dake ta jera kayan baby, Kilishi kuma na rike da babyn, Hadiyah ta gaishesu ba tare da ta kallesu ba sannan ta zauna kan kujera tana kallon Khaleesat tace “Congratulations Halysaah, Allah ya raya baby….” Khaleesat tace “Ameen, Nagode” Hadiyah bata ce a bata babyn ba, Kilishi ma bata mika mata shi ba, dama kuma ga Eeman a kafadarta, Kilishi sai kallonta take kasa kasa, Khaleesat na kallon Eeman tace “Bacci Eeeman take?” Hadiyah tace “Ehh” Kilishi tana murmushi ta kalli Hajiya Habibah tace “Yaron sak ubansa wallahi kamar an tsaga ƙara” Hajiya Habibah tace “Kwarai kuwa, Allah dai ya raya mana Ahmad (Jawwad) Ahmad Yusuf….” Hadiyah ta ɗaga kai ta kalli Hajiya Habibah jin sunan da ta kira yaron, Kilishi ta sumbaci kumatun yaron tace “Ahmad Jawwad karamin yariman masarautar mu in sha Allahu, Allah ya sa ya gaji masu sunansa, wato takwaransa Jawwad, ga kuma ubansa ma Ahmad, sannan wan kakansa Ahmad Allah ya kai rahama garesa, wannan yaro ɗan gata ne ta ko ina, tsabar sarki yasan muhimmancinsa sai da ya tako har nan don ganinsa, Allah dai ya kai mu ranan bikin sunan ka, anko kala uku za mu fitar in sha Allahu don ba karamin taro za mu yi ba” Hadiyah ta mike tace “Sai na leko anjima Halysaah, zan je inyi breakfast….” Khaleesat tace “To Nagode” Juyawa tayi ta fita daga dakin tana dauke da Eeman a kafadarta….. Halysaah is now saying good byeee fa…..🥰

