Uncategorized

Wace Ce Ita Chapter 35 Complete Novel

 

WACE CE ITA⁉️ (WHO IS SHE⁉️)

Unique Barakancy

             THIRTY-FIVE📍

        Numfasawa tayi tashiga basu labarin WACECE ITA!!!………

       Jingine take a jikin wani uncompleted building dake bakin titin unguwar, kuka take sosai kamar wacce ranta ke shirin barin gangar jikinta, irin kukan da tinda tazo duniya bata taba irinsa ba, a lokacin ko zaka shekara kana tambayarta sunanta bata saniba saboda ba karamin buguwa tayi ba, dukda shan datayi na ranar yafi na ko yaushe amma be mantar da ita damuwar da take ciki ba saima kunci daya kara mata, goge hawayenta tayi ta tashi tayi ta karasa gurin wani me taba dayake bakin titin dukda bata taba sanin dashi a layin ba sai ranar….. 

      “Dan Allah ka bani sigari, zan kawo maka kudin anjima”….

Ta fada a sanyayye kamar yanda yanayin muryarta yake a koda yaushe hakan kuma ya hadu da yanda take a bige ya karasa muryar yin kasa…….

     “Ke ko mezakiyi da sigari yar yarinya dake?”….

Me taban ya tambaya cikeda mamaki…..

    “Aikena akayi in siyo shine kudin ya fadi bansani ba, kasheni zaayi idan na koma bashi”……

Tausayi ta basa yaji ya yarda da abinda ta fada har cikin zuciyarsa tinda yasan yarinya kamarta ba abinda zatayi da sigari, kuma shi begane komai a yanayin muryarta ba tinda ba saninta yayi ba……

Dauka yayi ya bata sannan yace tabar kudin…

Rokonsa tayi ya kunna mata dan a kunne take ake aikota ta siyo, ba musu kuwa ya kunna mata ya bata……

Dawowa uncompleted building din data tashi tayi, kalle kalle ta hauyi taga ko me taban yana ganinta, ganin baya hangota yasata gyara zama sannan tashiga busa sigarin, zuka take ba kakkautawa tana fatan zataji sanyi a ranta saidai inaa kamar kara mata abinda ke damunta akeyi…. 

Cillar da guntun daya saura tayi tana dana sanin sha dan shanta na uku kenan amma ta kasa gane dadinsa shiyasa tayi sticking to syrup datasan inta sha ze bugar da ita a take yasata bacci ko banza zata manta duniya da damuwar dake cikinta…….

        A nitse yake driving har yasha kwana ya shiga street din, a fizge ya hango kamar mutum a jikin sabon ginin da akeyi a unguwar inba kizo idonsa ke masa ba kamar kuma mace ce yarinya karama, kasancewarsa mutum me tausayi sai ya kasa hucewa, dawowa yayi yayi parking a daidai inda take, alama ya shiga mata data taso saidai sam bata gane abinda yake nufi ba, tana dai kallonsa amma batasan me yake cewa ba, fitowa Alhaji Ibrahim yayi daga motarsa ya karasa inda take……

     “Me kikeyi haka a zaune ke kadai anan?”…..

Ya tamabaya yana kara screening gurin……

     “Bakomai”…..

    “Where are your parents?”…..

    “Sun mutu!”….

    “Subhanallah! Toh me kika fitoyi anan?”…..

    “An koreni daga gidan danake aiki!”…..

    “Innalillahi aikatau kikeyi?”….

Alhaji Ibrahim ya tambaya yana namakin yanda take sanye da sitirun arziki amma aika tau take, koda yake ai shugabanninsu suna basu kaya, hakan yasa ya kauda tinanin……

     “Eh!”…..

    “Waya kaiki gidan aikatau din?”…

     “Nina kai kaina!”…

Jinjina kai daddy yayi yana mamakin wannan izza tata gashi daga gani she’s smart shine zaa bar yarinya ba karatu wai aikatau ta kai kanta, shi kuma gashi mutum me balakin son karatu, a take yaji yanaso ya taimaketa ya inganta mata rayuwarta…..

     “Kiyi hakuri wata rana sai labari, taso muje kinji ko?”……..

Ba musu ta mike ta bishi dan har a lokacin bata cikin hayyacinta…….

Shida yazo da niyar zuwa ya gaida amininsa sai gashi yayi reverse ya koma da ita gidansa……..

Tinda suka dau hanya yake mata tambayoyi akanta, amsa take bashi kawai batareda tasan me take fada ba, shikuma ya hau ya zauna akan duk abinda ta fadamasa dan dagaske a yanayin maganarta bazaka gane a bige take ba….. 

   Suna zaune a main parlor suna jiransa dan tin kafin ya karaso ya kirasu yace su jirasa a parlor gashi nan…..

   Hade baki sukayi wajan amsa sallamar Alhaji Ibrahim dayake tafe da yarinyar da basu gane wacece ita ba…..

     “Yauwa sannunku, wannan yarinya a kula da ita a bata abinci taci, bari naje nayi sallah na dawo”…..

Yana fadin haka ya fita daga parlourn……

      “Kutumar uba mu Alhaji ze renawa hankali, ya sunkuto zukekiyar yarinya kamar wannan yace mu kula da ita kamar marasa aikin yi? Allah ya kiyaye wallahi!”….

Budar bakin mama(hafsah) kenan bayan fitar alhaji daga parlourn……

       “Wasa ma yake wallahi, ba bayani ba komai kazo ka ajye mana yarinya kace ka tafi masallaci?”……

Momma(maman khaleel) ta kara da hakan…..

     “Ke wai baki iya gaisuwa bane?”….

Cewar mama da abun yafi damunta kasancewarta mutum me zafin kishi….. 

 Kallonta rashin fahimta fatima zainab ta mata dan bata gane me take cewa ba saboda wani bacci daya fara fuzgarta a gurin, a hankali tace;

      “Tohhh”…..

    “Wace irin fitsararriyar yarinya alhaji ya kwaso haka? Ina ce miki kiyi gaisuwa kina cemin wani tohhh”……

        “Yausheee?”……

    “Ikon Allah kin jimin yarinya maganar da nake daban abinda take fada daban!……

     “Hafsah anya yarinyar nan baa bige take ba kuwa? Kigafa yanda take magana kamar ki tureta ta fadi”…..

      “Babu tantama a bige take, toh wallahi bazata sabu ba, yazo yaga abinda ya kwaso dan baze kwaso abinda ze lalata mana tarbiyyan yara ba”……

     “Wallahi kuwa, mu jirasa ya dawo daga masallacin”……

Haka mama ta cigaba da zaginta ta inda take shiga batanan take fita ba, itako batasan ma anayi ba dan tariga tayi nisa batajin kira………

        “Ashe baku da kirki baku da mutunci! Ince a kula da yarinya kafin in dawo sai kuka mayar dani kamar shashasha kuka banzatar da maganata, kunsanni sarai bana tolerating nonsense toh duk zanyi maganinku wallahi!…..

Alhaji Ibrahim da shigowarsa kenan ya ganta a inda ya barta ba wani alamar chanji ya fada rai a bace…….

Da sauri momma ta tashi ta kamo hannunta tana fadin;

    “Allah ya wuci zuciyarka Alhaji, tuba muke”…..

Sannan tayi part dinta da ita……..

Bece komai ba mama tazo itama zata bada nata hakurin ya daga mata hannu yana nunamata hanyar kofa…….

Abincin momma ta bata dukda batayi niya ba saidan gudin abinda zeje ya dawo dan tasan hankalin alhaji na kan yarinyar yau, koda ta bata abincin bata taba ba ta shiga bacci a gurin, tabe baki momma tayi ta cigaba da sabgoginta…… 

       Bayan sallar isha ya sake tarasu a  part dinsa, kashedi da jan kunne ya musu akan kula da yarinyar sannan ya dankata amana gurin momma dan yafi yarda da ita gashi ita ta fara daukan yarinyar dazu….

      “Alhaji duk munji sharudanka kuma Insha Allahu zamu kiyaye, saidai baka fadamana wacece ita ba?”….

Momma ta tambaya…..

    “Wannan ba hurumunku bane, kawai kuyi abinda na saku, zaku iya tafiya, yauwa ki turomin yarinyar yanzu!”……

    “Amma alhaji me zatazo tayi yanzu yarinyar daba muharramarka bace!”…..

    “Bakida hankali ne?, ni kike gayawa me zanyi da ita, toh inyi me da yarinya karama kamar wannan, fita ki bani guri hafsah, fita nace!!”…….

Alhaji ya fada cikin tsananin bacin rai, ya rasa meyasa kishi kesa wasu su rasa lissafinsu kamar dai hafsah…..

Kamar yanda ya umarta haka momma ta kawota part dinsa bayan ta samu ta tashi da kyar daga baccin datake tin dazu…..

      “Wai harta kwanta? Naga kamar daga bacci kika tasota ko?”……

     “Eh wallahi, amma tindazu take baccin, naga kamar a gajiye take shiyasa na kyaleta”…..

Momma ta fada kamar gaske….

    “Kwarai a gajiye take, kin kyauta da kika barta tayi baccin, nagode sosai uwargida sarauniyar gida”….

Murmushin yake tayi kamar taji dadin abinda yace nan ko ita kadai tasan abinda takeji a zuciyarta…..

      “Keda kike san ya’ya mata gashi Allah ya baki, sai ki riketa amana kamar yarki, sai kiga Allah ya baki lada”…..

    “Insha Allahu, Allah ya tayani ruko”…..

    “Ameen ameen, yauwa daukomin ajiyar dana baki jiya”…..

      “Okay, bari na dauko”….

Tana fita daddy ya dawo da hankalinsa kan fatima zainab da abun ya saketa kasancewar tayi bacci ta tashi……

    “Ya sunanki daughter?”….

    “Fatima zainab!”….

   “Wannan wani kalan suna ne haka, kodai sunanki fatima uhm?”…..

     “A’a alhaji duka biyun ne sunana”…..

     “Call me daddy! Ya akayi duka biyun ya zama sunanki?”……

    “Haka naji ana cemin, a school ma haka nake amfani”…..

     “It’s alright, wani class kike?”…..

        “ss1”

    “Going to ss2 kenan?”….

       “Eh”….

     “Waya saki a school”…

     “Inda nake”…,

Beyi mamaki ba dan akwai gidan dakesa masu aiki a school ko islamiyya”…….

     “How old are you?”….

     “14”…,

    “That’s good, da fatan dai babu matsala? Akwai wanda ya miki abu da kikazo?”…..

Gizgiza kai tayi alamun babu kuma hakan take har cikin zuciyarta dan batasan anyi ba……

      “In akwai fa don’t hesitate to tell me?”…

     “Babu!”.,,,

    “Good, gobe zamuje ayi enrolling dinki a boko da islamiyya dan banaso yaro ya zauna ba karatu, ai kema kinaso ko?”….,,

    “Ehh, nagode daddy”…

    “Karki karamin godiya, ki daukeni kamar mahaifinki kinji ko?”….

     “Insha Allah daddy”….

     “Good, inaso ki manta da duk wani kunci da kika shiga na rayuwa, study and make your daddy proud okay?”……

Gyada kai tayi tana murmushin daya kasa barin fuskarta, ta dade bataga mutum me kirkin daddy ba a rayuwarta…. 

Shigowar momma ne ya katse conversation dinsu, sakon ta mika masa yace ta zauna….

    “Gobe zamuje dake muyi enrolling dinta a school da islamiyya, inaso mu tsaya akan al’amarinta kamar iyayen da suka haifeta zasuyi”…..

    “Insha Allah alhaji, yanda kace haka zaayi”…

Momma ta fada tanaji kamar zuciyarta zata fado wai su tsaya mata kamar iyayenta, ko ya’yansa na cikinsa be musu haka ba, saidai taga kamar hakan ze kara mata kusanci dashi, saboda haka zatayi using advantage din wajan cusawa mama bakinciki……

     “Ya kamata muje ayi mata shopping ma naga batazo da kaya”..,,,

     “Yauwa kin kawo shawara me kyau, shiyasa nake sonki wallahi, Allah ya miki albarka”…..

      “Ameen mijina!”…..

    “Ki mayar da ita ta samu ta kintsa, in kin gama saiki dawo ko?”….

Ya fada yana kashe mata ido daya kasancewar itake dashi a ranar…..

Kashemasa ido itama tayi ta rike hannunta suka fita daga part din…..

 Bata nuna mata komai ba tasata tayi wanka tayi sallah, ta kuma bata abinci sannan ta kaita wani spare room tace ta kwanta, part din Alhaji ta koma suka raya daren cikin aminci, alhaji sai nan nan yake da ita……..

  Tinda momma ta tafi ta barta ta kasa bacci, babu abinda takeso illa taga tasha kwalbar codeine dan shi kadai ne ze iya sata bacci a halin da take, da abin duniya ya isheta sai ta tashi da niyar fita ko Allah zesa ta samu me bata codeine kamar yanda wanchan ya bata sigari dazu, saidai kash tana zuwa taga kofar parlourn a garkame, ashe momma ta kulleta ta waje kamar tasan zata fita…… 

Komawa dakin tayi tanajin yanayinta na dan chanjawa, chan kuma saita fara birkicewa saboda tanaso tayi baccin amma ta kasa, kuka ta hauyi me karfi amma ba wanda ya jiyota ballatana akawo mata dauki, haka ta cigaba da kukanta har akayi kiran sallar asuba lokacin idonta yayi ja kamar gaurashi, tayi kukan tayi kukan harta gaji, da kyar ta daure tayi sallar asuba dan lokacin zazzabi harya fara kamata……

Karfe bakwai momma tashigo part din, sosai hankalinta ya tashi a halin data ganta dan alhaji yace da wuri zasu fita, idan yaga yarinyar a haka ai sai ya dauka wani abun aka mata bayan jiya har kyauta ya mata……

 Tambayarta ta hauyi meya sameta saidai kememe taki cewa komai har ran momma ya fara baci, daurewa tayi ta sata tayi wanka ta gyara mata fuska dukdan kar daddy ya gane komai sannan ta mata breakfast ta bata taci tanata lallabata, a haka alhaji yazo ya samesu ya kuma ji dadin yanda momma keta nan nan da ita, sai hankalinsa ya kwanta ya bawa momma yarda dari bisa dari…… 

Kamar yanda ya fada haka suka sata a school da islamiyya, suka kuma kaita shopping yace ta dauki duk abinda take so, kasa dauka tayi sai momma ce ta saki jiki ta dinga jidar mata abubuwa kamar gaske….

Hatta drivern da ze dinga kaita school saidai daddy ya daukar mata daban dan be hadata school daya da ya’yansa da suke boarding ba saboda yasan halin mama yanzu zata tada fitina akan hakan, sai ya bawa drivern kudi yace yana bata kullum idan ya kaita school, be bawa momma ba saboda hali irin na zuciya kartasa mata sake saken yana yiwa yarinyar hidima da yawa…..

A washe gari kuma urgent tafiya ta taso masa, dole yabar kasar ba shiri bayan ya tabbatar ya mata providing komai…….

A kuma lokacin fatima zainab tagane shayi ruwa ne a gurin momma, da farko kitchen ta maida mata gurin kwanciyarta, haka zatace taje ta kwanta ba shinfida ba komai tsabar mugunta, na biyu abinci sai taga dama take bata abinci a rana so daya, wataran in bataci saa bama bata bata, sannan zagi da cin mutunci ya biyo baya, bata sata koda dauke tsinke ne  wai karta koya mata abubuwa ta moru a gidan mijin, gwara duk wanda ya kwasa ya sakota dan babu wanda ze yarda ya zauna da wacce ko shara bata iya ba…… 

A lokacin fatima zainab ta kara kulla aminta da codeine shiyasa duk abinda momma take baya damunta, kudin da daddy yasa ake bata kullum akan siyan codeine yake karewa kamar wacce aka yiwa baki, data siya abinci taci ta gwammace ta siya codeine tayita sha, tana sane da cewa smokers and drinkers are liable to die young amma she doesn’t care anymore dan tayi nisan da bata jin kira, abun nata har ya wuce addiction ya zama disorder….. 

A gurin abdul kanin khaleel kadai take samun sauki saidai shi ba mazauni bane dan a boarding school yake shima, sosai yake shiga damuwa akan yanda take inactive koda yaushe, wani zubin yana mata magana batasan me yake cewa ba, haka zatayi ta bashi unrelated answers, tun yana karyata zuciyarsa harya fara zargin shayeshaye take saidai binciken duniya ya kasa gane abinda takesha cuz she knows how to play her game, gashi be isa ya kulata a gaban momma ba dan yanzu zata hau masa fada ta inda take shiga batanan take fita ba, momma ma nasane da shayeshaye takeyi tinda ko a ranar datazo gidan a bige tazo saidai ko a kasan slippers dinta, inma duniyar duka zata shanye bata damu ba…… 

Mama da aka ware gefe tana sane da muguntar da momma take ganawa yarinyar, sannan kuma ta mata daidai bakincikin ta daya yanda taga momma na wani faffadi akan lamarin yarinyar tana nunawa alhaji tana kula da ita, shikuma sai yayita jin dadi yana mata kyauta yana ji da ita…..

Takaici ne ya isheta ta fara shirya yanda zata tonawa momma asiri har tasamu yarinyar ta dawo hannunta itama ta dandana mata kalan nata azabar batareda daddy da momma din sunsani ba….. 

Yanke shawarar kiran alhaji tayi lokacin daya kusa dawowa kasar, da farko kin yarda da abinda ta fada yayi dukda tana kuka tana gayamasa yanda irin muguntar da ake yiwa yarinyar yake mata ciwo, harda cewa tasan ita tanada zafin kishi amma hakan bazesa tayiwa mutum mugunta haka ba, sannan tace mishi tasan baze yardaba tinda bajin maganarta yake ba amma yayi bincike akan lamarin…. 

Sosai jikinsa yayi sanyi dan yasan abinda zesa hafsah kuka ba karami bane, sai ya mata alkawarin zeyi bincike….

     Koda ya dawo be nunawa momma komai ba dan tanata nan nan da yarinyar kamar yanda yasan tanayi da, sai ya fara dan bincike har Allah yasa ya kamata red handed, lokacin sun dawo daga masallaci shida abdul a ka’ida baya shiga part dinsu a irin wannan lokacin, ranar sai yabi abdul suka shiga, abun al’ajabi suka samu momma nata jibgar fatima zainab dake bacci a kitchen, dukan duniya kuma taki tashi saboda yanda tasha tayi makil bayan sallar asuba, tana dukanta tana zaginta harda fadin batace mata tadinga barin kitchen da sassafe ba, sai tayita bacci saboda alhaji yazo yaganta  ya gane a kitchen take kwana……

Karap wannan magana a kunnen daddy da ya zama very shocked tinda suka fara jiyo maganganun momma…… 

Abdul ne ya ankarar da momma da tsayuwar daddy, ta jiyo sukayi ido hudu da daddy daya dafe kansa yana jinsa highly betrayed!…. 

Zatayi magana kenan ya daga mata hannu sannan yace ta tafi gida sai ya nemeta dan yasan inta cigaba da zama a gidan yana ganinta komai ze iya faruwa…

Har kasa ta tsuguna tana basa hakuri daya bata second chance zata rike yarinyar da gaskiya dan denying be taso ba tinda ya riga ya kamata red handed……

Dago fatima zainab yayi data riga ta farka ya rike hannunta yayi hanyar fita da ita……

     “Kullum saina tambayeki a waya babu abinda ake miki sai kice min babu, meyasa baki taba fadamin abinda take miki ba daughter? Meyasa?”…..

      “Tace zata kasheni idan na fadamaka”….

     “Karki damu babu abinda ze sameki da yardar Allah, daga yanzu duk wanda ya miki wani abu a gidannan ki fadamin kinji daughter?”…..

      “Toh daddy”…..

Part dinsa ya tafi da ita yana kiran mama a waya…. Shigowa mama tayi da sallama hankalinta na kan fatima zainab, guri daddy ya nuna mata ta zauna, yayi gyaran murya ya fara magana;

     “Hakika hafsah kinmin abinda ban taba tinanin zuciyarki zata bari kiyi ba, kin ankarar dani muguntar da akeyiwa marainiyar Allah da bataji ba bata gani ba, a yanzu bazan iya bari ta kara zama a gurinta ba, bansani ba ko ke zaki iya rikemin ita amana?”…..

     “Nasan kanamin kallon wacce bata da kirki saboda yanda nake nuna kishina akan ka a fili, inaso ka sani son da nake maka ne yasa nake behaving haka, amma wallahi Alhaji bazan iya cutar da kowa akan hakan ba, ka jarrabani zan rike maka ita fiyeda yanda kake tinani”…….

      “Kinyi alkawarin zaki riketa tsakani da Allah? In kinsan bazaki iyaba kema gwara ki sanar dani in nemi inda zan kaita”…

Daddy ya sake tambaya dukda ya gamsu da maganganunta, ya kuma yarda tana son shi sosai kamar yanda ta fada, kuma ko ba komai gwara ita tinda tana nuna abinta a fili akan momma me munafurci……..

     “Nayi wallahi, tawo daughter kinci abinci kuwa, taso muje naga kamar ma bakya jin daddy”…..

Murmushi daddy yayi yacewa fatima zainab ta tashi ta bita…….

Daganan wani sabon phase na rayuwarta ya sake budewa, inda ta gwammaci zamanta a gurin momma so dari akan mama, a takaice dai  lamarin rayuwarta sai ya kara hargitsewa, da farko mama ta dan fara sata aiki saidai ganin yanda take kwabamata yasata gane bata iya komai ba, nan tace bazata zama me koya mata ba wallahi gwara ta saura a haka yanda duk inda taje bazata moru ba, ada da take kwana a kitchen sai mama ta maida gurin kwananta store, batasan store din ya fiye mata kitchen ba dan koba komai yafi dimi dukda ba fanka ba fitila ga beraye, nan fa shayeshaye yaci uban na da dan wani zubin sai tayi kwana biyu a kulle a ciki, gane hakan ne yasata take siyo codeine in excess tazo ta boyeshi tayita sha tana mayenta ita kadai, gashi mama ta iya takunta dan daddy ko momma basu taba gane halin da take ciki ba, daddy har dena tambayarta yayi ko akwai abinda ke damunta ganin kamar mama na iya bakin kokarinta akanta, a lokacin duka yayan mama boarding sukeyi amma in suka dawo hutu suyita mata rashin mutunci iri iri, momma da take hanata abinci na kwana daya sai gashi tagamu da mama da sai tayi sati biyu abinci, abu daya ke taimakonta kusan kullum sai daddy ya kirata sunsha fruits a part dinsa hakan yasa ta saba da rashin cin abinci, sai ya zamana ko an bata abincin batasan ci dan bata saba ci ba, shiyasa gatanan kullum sai a hankali ba auki sai shegen kyau, taimakonta daya tanada diri sosai kuma duk raman da zatayi iya fuska ne da wuya amma mazaunanta da hips dinta basu san anayi ba, kadama boobs dinta suji labari…..

Sai da aka kai ruwa aka kai rana kafin daddy ya yarda momma ta dawo gidan da sharuda dayawa…

Haka mama tayita gana mata azaba kala kala hartakai ss2, a lokacin jikinta ya kara fitowa gata da wani kyau na ban mamaki, kowa ita kowa ita, in dai ta sake ta fita sai ance fiyeda mutum goma na sallama da ita kuma duka ya’yan manya kasancewar unguwar ta manyan mutane, sosai abun ya fara damun daddy dan shi burinsa ta samu ilimi me inganci gashi sai hari ake kawo mata, sai yasata ta dena fita sai fitar ta zama dole har lokacin kuma besan da wahalar datake sha a gurin mama ba, abu daya yasani in tazo part dinshi ya mata tayin abinci sai taki ci saidai kayan fruits, daga baya sai yace kullum tana zuwa tanasha tinda tanaso….. 

A lokacin data kai ss3 sai abun yaci uban nada dan babu lafiyayyen namijin da zai kalleta ya dauke kai, wani mugun farin jini ne da ita naban mamaki, harda marasa kunyan abokan daddy wai sunaso, saida ya taka musu birki sannan ya samu sa’ida….

Kyakkyawace sosai son kowa kin wanda ya rasa dan karyar mutum ya kalleta ya kushe duk hassadarsa kuwa, fara ce kal irin farinnan me shegen daukan ido, fatarta kamar ka taba jini ya fito tsabar yanda take sheki toh ba aikin fari balle baki what do you expect?, fararen idanune da ita masu maiko da daukan ido idon ta waresu, saida shayeshayen da takeyi yasa idonta na dadewa bedawo daidai ba, kullum sai kaga idon yayi wani kala shiyasa koda yaushe idanunta a lumshe suke gudun kar a gane halin da take ciki, pointed nose ne da ita me kyau irin wanda daga nisa sosai kana iya hango karan hancin mutum kadama azo maganar kwanceccen gashin girarta dayake baki wuluk da in mutum be santa ba saiya dauka tint tayi , bare reddish soft pouted lips dinta dayake hargitsa lafiyayyen namiji shiyasa kowa ni kare da doki sai yace yanaso saboda jikinta suke bi badan Allah ba, gashi ko yayan mama sun aske mata shi yafi sau goma saboda bakin ciki amma nan da nan sai ya fito yafi nada yawa, wani kalan silky hair ne da ita me tsawo da cika gashi har tsakiyar bayanta, sosai jikinta yakeda laushi dan kwata kwata batasan wahalar aiki ba, gatadai mace har mace amma a zahirin gaskiya muna macece dan ko rike tsintsiya bata iya ba, a takaice dai bata iya komai na mata ba……. 

On this very faithful day, bayan ta gama shan fruit a part din daddy sai ya bata sako ta kaiwa momma, ba musu ta tafi part din momma, karban sakon momma da take jin haushin fatima zainab har lokacin tayi sannan tace ta tsaya, tsintsiya ta bata tace ta sharemata parlor dukda tasan bata iya ba so take kawai tagana mata azaba da ayyuka ranar….. 

A ranar ne kuma khaleel yayi gamo da ita bayan ya dawo daga tafiyar da rabonsa da gidan kusan shekara hudu kenan, a lokacin dayayi tozali da ita ya kuma fada sonta a take wanda san da khaleel ke mata shine asalin samun yan’cinta a gidan…..

And when the table turns around she make sure kowa yayi reaping abinda ya shuka a gidan daga momma har mama, saida ta zame musu worse nightmare gashi a lokacin daddy ya ninka mata kulawar da yake bata, abun yaso ya bata mamaki ganin yanda yake fifitata akan kowa har matansa gashi har part dinta yamata daban a gidan dukda kankantar shekarunta amma sanin waye daddy tin farko saita watsar da zancen sannan kuma son da yake yiwa khaleel tasan ze iyasa ya mata komai, sai tayi using opportunity dinta wisely ta zame musu fitina da bala’i, take juya musu miji da da’ ba kuma yanda suka iya!!! Sai ta zama kamar dodo a gidan wanda har daddy dayake nuna mata baya rashin kunya take masa in abunta ya motsa, sai sangartarta ya kara yawa dalilin zuba mata masu aiki da khaleel yayi, shiyasa haryau babu abinda ta iya, shaye shaye ko har bunkasa yayi dan har abinda batasha da yanzu sha take saidai baya wani affecting dinta sosai yanzu saboda abin ya riga yabi jikinta, shiyasa batayi mamaki ba da akace kidney dinta is failing, zata yiwu karshenta ne yazo!, da abu daya kawai ta tsira a rayuwarta shine ibada da ilimin addini, duk rintsi duk wuya bata wasa da sallah!!!! Banda wannan she’s a very big zero!!!!

Hmmm🌚

Back to top button