Uncategorized

RUMBUN QAYA Hausa Novel – Aihausanovels

RUMBUN QAYA Hausa Novel Written By HAFSAT RANO

Posted by AiHausa Novel
Price 400
Category Hausa Ebooks
Uploaded On 26 Jan, 2023
Upload Time 8:29 pm
Hits 578 Views
Author

Hafsat Rano

Writer Group

Haske Writers Ass.

Novel Genre

Comment No Comments

Rumbun Qaya Hausa Novel Written By Hafsat Rano

 
           Free Page 1

©® *_Hafsat Rano_*


ZAFAFA BIYAR 2023🔥🔥🔥🔥🔥

***Tafiya me tsawon gaske ta iso da su Kano daga Yolar Adamawa, tun tana dauki da mararin zuwa har ta soma sarewa ganin tafiyar ba ta kare bace. Kallon tagar motar tayi lokacin sun iso garin na Kano ana gaf da kiran sallar magriba, karo na biyu kenan da tazo Kano tun bayan barin su, wanchan zuwan din ma ba zata iya dorar da komai akai ba dan bata da cikakken wayo. Motsa kafarta tayi da tayi mata matukar tsami ta tuno gwagwarmayar da aka sha da Dada kafin ta amince ta bar ta, ta taho bautar kasa Kano, sai da aka tabbatar mata da idan bata bar ta taje Kanon ba toh fa kudu za’a tura ta tunda bata da aure kanon ma sai da Lamido ya shiga ya fita sannan aka samar mata. Ala dole babu yadda ta iya ta hakura. Tunda suka dauko hanya take shan kira daga wajen yayyen nata, da Hamma Hydar ya kira sai Bobbo Sadeeq shima haka Lamido kuma duk Dada ce take sakasu kiran taji ya tafiyar tasu. Yanzu ma motar su na tsayawa a tasha kiran Lamido yana shigowa,dagawa tayi tana murmushi tace

“Yanzu muka iso gamu a tasha.”

“Toh Masha Allah, ki kira Addan ki fada mata kun iso.”

“In sha Allah, ina isa zan kira Dada nah, Hamma kace mata ta kwantar da hankalin ta.”

Murmushi yayi ya katse kiran ta duk’a kad’an ta dauki jakar hannun ta sannan ta shiga jan akwatin ta zuwa hanyar fita daga tashar. Duk da kasancewar duhun dare ya soma yi amma garin tarwai yake da hasken fitilun dake haska kan titin. Tsayawa tayi daga nesa da Titin ta ciro wayar ta kira Addan. Napep tace mata ta hau ya kawota hotoro idan sunzo sai ta kirata. Maida wayar tayi cikin handbag dinta ta tsaida napep din ta fada masa in da zai kai ta, kasancewar unguwar ba boyayyiya bace yasa bata wani sha wahala ba suka iso, ta sauka ta bashi kudin sa ta sake kira. Tana tsaye a wajen yaron Addan Muhammad yazo ya tafi da ita dan daga titin gidan su layi daya ne ba nisa
  Da murna Adda maimuna ta tarbe ta, hakan yasa ta sakewa sosai dan dama ita tun asalin ta bata da duhun kai, kuma tana da masifar son mutane, sam bata san wani abu wai shi bacin rai ko kunci ba dan ita din yar lele ce a gidan su, duk abinda take so shi ake mata. Abinci taci tayi la’asar da magriba da suka risketa a hanya ta dan zauna kad’an ta jira isha sannan tayi suka cigaba da yar hirar su da Asmau ita ma yar gidan Addan tasu ce kuma zatayi kusan sa’ar ta a shekaru amma ita yanzu take 200 level a university. Kasancewar ita dukkan stage din karatun ta da wuri tayi shi shiyasa ta gama da wuri gashi har zatayi service. Sai dare chan suka kwanta dan hirar suke tamkar ba zasuyi bacci ba.
  Da safe ta tashi da dan ciwon kai kad’an saboda gajiya da rashin bacci amma zuwa gabannin azahar ta ware ta sake jera kayanta sosai da zata bukata a camp dan gobe iwar haka tasan tana Perm Orientation Camp dake Kusala Dam Karaye. Wajen la’asar suka fita tare da Amina ta rakata karshen layin suka karbo dinki sannan suka biya gidan wata kawar Aminan Hadiza anan suka kai har wajen magriba suna tutorial sannn suka dawo gida. Sallar magriba tayi ta zauna waya da Dada tana kara jaddada mata kama kanta da mutunci a duk in da ta samu kanta, maganar dai itace tunda aka soma maganar zuwa camp din dan har ga Allah Dada bata so dan karatun dai yazo da haka ne. Bayan ta gama wayar ta kwanta lamo tunanin Abbinta ta ya shiga zuwar mata, kasancewar ta a Kano babbar dama ce da zata je ta ganshi ita kadai ta gaishe shi, wannan shekaran ce shekarar da ake saka ran fitowar shi, duk karshen watan duniya Hamman ta suna zuwa su ganshi su kawo mishi abubuwan da zai bukata amma sam basa zuwa da ita sai dai idan sun je su kira waya a bashi su gaisa da ita, tana son mahaifin ta duk kuwa da ba zata dorar da rayuwar su tare ba dan ba wani wayo ne da ita sosai sanda abin ya faru ba, babban abinda ya jawo musu barin gari suka koma sabuwar rayuwa me cike da wahala. Hamman ta sun sha fama matuka wajen ganin sun gina rayuwar su ita da Dada sannan suma suka gina tasu har suka zama abinda suka zama a yanzu, basu taba barin ta, tayi kukan rashin uba ba, basu taba bari ta nemi abu ta rasa ba, zasu iya yin komai akan ta ga duk wanda yace zai sakata zubar da hawaye. Ita kanta bata san wani abu wai kunci ba, rayuwa take me cike da farin ciki har zuwa tahowar ta Kano wanda take ganin yana daya daga cikin cikar burin ta. Ko ba komai zata ga Abbinta yaga yadda Raihanan sa ta girma sosai ba a waya ba. Murmushi ne ya subce mata da ta tuna kalar farin cikin da suke ciki na fitowar Abbin, dan shine kadai damuwar su a yanzu, akwai abubuwa masu yawan gaske game da fitowar tasa, wanda ake ganin zai iya kawo karshen wasu mutane masu yawan gaske, sai dai zasu barshi ya sake jefa rayuwar sa a irin hatsarin da ya saka kansa a baya? Ko zai sake tsayawa gaskiya kamar wanchan lokacin? Manyan kasar basa san gaskiya ba kuma sa barin duk wani wanda zai fada musu ita. Cikin tunanin bacci ya dauke ta, dan bata farka ba sai kusan sha biyun dare, ko abincin dare bata ci ba haka ta tashi tayi sallar isha ta sake komawa dan baccin ne akanta sosai.

KARANTA ZAFAFA 2023

*IDON NERA By Mamuh ghee*

    Tunda suka tashi da asubah ta hau shiryawa, a sanyaye take komai sai take jin kamar ta fasa wani irin feeling, she’s nervous dan bata kuma san rayuwar da zatayi ba, haka ta daure ta karasa shiryawa dan ma Amina zata karata tare da Muhammad din, mota aka samo musu dama tun jiya drop da zata kaisu Lamido ne yayi duk wannan suna karyawa driver yazo suka fita, suka dauki hanyar Karaye suna dan taba hira har suka isa, sai da suka jirata ta shiga ciki bayan an gama duk arrangements din da akeyi a wajen gate sannan suka juyo suka barta da kewa. Rayuwar ta a sati ukun nan ta koyi darasin rayuwa sosai, sannan ta hadu da mutane kala-kala mabanbanta, kasancewar tazo da enough kudi yasa rayuwar bata yi mata wahala sosai ba dan har wasu suna mata kallon yar masu kudi saboda yanayin ta. Cikin nasara da kamewa ta gama sati ukun nan. Hamma Haydar ne yazo mata surprisingly tare da wannan driver motar da Muhammad wannan karon ba Amina dan tana da lecture, farin cikin ta ya gaza boyewa dan bata zaci zasu zo ba. Tare suka karasa komai suka dawo gidan Adda Maimuna daga nan ya koma dan dama zuwan nata ne hade da ganin Abbi dan Lamido baya nan sun yi wata tafiya a wajen aikin su, shi kuma Haydar ya zauna da Dada. Taso ta bishi amma dole ta hakura dan kwana uku aka basu zuwa ranar da zasu karbi posting letter din su.
  
    Ranar da zata karba da kanta ta shirya a cikin NYSC khaki dinta ta fito ta samu napep tace ya kaita Gwarzo Road, tana zuwa bata wani bata lokaci sosai ba ta karbi posting letter din ta hade da ATM card dinta sannan ta fito. Wani me napep din ta sake samu ta tsayar tace ya kaita KURMAWA PRISON, sai da ya dan kalle ta sannan yace ta shigo, ta shiga ta zauna cike da zumudin ganin Abbin ta, ta bud’e posting letter din ta, taga an tura ta wata makaranta a Kumbutso local government, yanayin address din ya tabbatar mata kauye ne sosai, ji tayi duk babu dadi haka ta maida ta saka a jaka ta cigaba da kallon titi har suka iso, daga nesa da wajen yayi parking sannan ya nuna mata wajen da hannu, sauka tayi ta bashi kudin sa idanun ta akan wajen sun ciciko da kwalla. Kokarin tsallaka titin take kasancewar babu ababen hawa sosai, kai tsaye ta shiga tsallakawa bayan ta dan duba kad’an. Kamar daga sama taji an ture ta da abu me karfi, kafin ta gano menene ta kai k’asa baki daya jakarta ta watse ita kuma tayi nata wajen. Parking yayi a gefe ta balle murfin motar da sauri ta fito.

“Raihana..”

Ta riko ta da sauri tana kokarin daga ta daga faduwa da tayi, gefen hannun ta har ya soma jini saboda gurjewar da tayi.
   
“Subhanallah, Me ya faru Hajiya?” Wani mutum da yazo wucewa ya fada

“Wallahi sam driver be lura da ita ba, shine ya dan taba ta, bari akwai clinic nan kusa tashi mu kaiki su duba ki.”

“Allah ya takaita ma, Allah ya kiyaye gaba.” Yace yana wucewa

Kanta da ya dan yi dum ta rik’e kafin ta mike da k’yar dan har guiwar ta sai da ta dirje, ta taimaka mata ta saka ta cikin motar shi kuma driver ya kwashe kayan ya maida mata cikin jakar sannan suka bar wajen
   Wani hadadden clinic ta kai ta, aka duba ta aka gyara mata hannun da guiwarta, aka bata pain killer sannan suka fito.

“Sannu kinji? Ina ne gidan ku mu ajiye ki?”

“Hotoro.”

“Ok, amma in da muka ganki din inane? Ko chan zamu maida ke?”

“Eh babana zan kaiwa ziyara a prison.”

Dan kallon ta tayi kad’an kafin tace

“Ai yau ba lokacin ziyara bane ba, kuma kinga yanzu ma be kamata ya ganki da ciwo ba, ki bari idan kika samu sauki sai kije ki ganshi kinji? Ni zan shige miki gaba ki ganshi.”

“Ok tam, dama yau akayi posting dina ne shine zan je na ganshi na nuna masa.”

“Bautar k’asa kike yi?”

“Eh…”

“Ina aka tura ki?”

“Kauyan Kumbutso.”

“Wai… Gaskiya yayi nisa, kina so ki chanja?”

“Eh…” Ta gid’a kanta

“Shikenan zan baki address dina, Monday kizo gida ki karbi sabuwar posting letter kinji?”

Fuskar ta dauke da farin ciki tace

“Nagode sosai Allah ya saka da Alkhairi.”

“Ba komai, muje na ajiye ki a gida kar mamanki taji shiru.”

“Ok tam.” Tace cikin jin dadi, ba dan abinda ya faru din ba me dadi bane ba, da sai tace ita gwara ma hakan da ta faru dan da bata san yadda zatayi ta san matar ba, matar da kana ganin ta kaga babbar mace me aji da kudi, gata sam bata da girman kai idan wasu ne tafiyar su zasuyi su barta.
  Har kofar gida aka kaita sannan ta dauko kudi me yawa ta tura mata a jakar ta, tayi godiya sosai sannan ta fito rike da complimentary card din matar dake dauke da number wayar ta wadda zata kirata idan taje gidan. Har ta soma takawa zuwa gate din gidan suna tsaye basu tafi ba, wani tunani ne ya fado mata, ta juyo ta dawo wajen motar sannan ta dan duka a hankali tace

“Dan Allah kin san sunana dama?”

“Ni a ah, ya akayi?”

“Sanda na fadi naga kin fadi sunana, sannan a clinic din ma…”

“Oh wannan? I’d card dinki ne da ya fado anan naga sunan ki.”

“Oh okh, nagode sosai.”

“Karki damu kinji? If you need anything just call me, kinga dama bani da ‘ya mace, shikenan na samu ‘ya.”

Murmushi tayi wadda yake bayyanar da zahirin kamar ta da mahaifiyar ta

“Sunana Hajiya Zeenat, shiga gida zamu tafi, karki manta ki kirana Monday.”

“In sha Allah.” Ta sake godiya kafin ta juya ta shige, murmushi Hajiya Zeenat tayi ta girgiza kanta tace;

_“What a small world! bayan duk tsawon shekarun nan, yau ga yarka a tafin hannu na Nasir, let see how it will end.”_

“Muje.” Tace tana relaxing sosai, a cikin zuciyar ta, ta shiga sak’a yadda abubuwan zasu kasance

_“Sai nayi wasa da rayuwar ka Aryan, sai na nuna maka na fika sanin rayuwa. Muje zuwa.”_.

Ta yi dariya tana tuna zamanin baya, tun daga lokacin har zuwa yanxu dai itace a sama, zatayi komai, domin ganin ta cigaba da rike mutuncin ta.

*_ZAFAFA BIYAR 2023_*🔥🔥🔥
_*Sabuwar shekara sabon salo sabon taku,*_
_*Makaranta littafan hausa kuma masoya marubutan zafafa kuzo ga sabuwar tafiya zazzafa tazo karku bari ayi babuku *_

_*Zafafan alkaluman haziqan maruban zafafa biyar kowa yasan na daban ne,wannan karon ma sunzo da sababbin salo me kama zuciya.*_
_*ZAFAFAN MARUBUTAN SUNZO DA SABABBIN LITATTAFANSU NA 2023 Kamar haka,*_

_*IDON NERA*_
    Mamuhgee

_*DAUDAR GORA*_ ciki ka shata
    Billyn Abdul

_*RUMBUN QAYA*_
     Hafsat Rano

_*KI KULANI*_ mallakin zuciyata
    Hafsat Miss Xoxo

5   _*A RUBUCE TAKE*_ qaddarata
    Safiya Huguma

_DUKA GUDA BIYAR DIN ZAKA SAMESU A FARASHIN 1200_

Guda 5 1200
Guda 4 1000
Guda 3 800
Guda 2 600
Guda 1 400

_*zaku saka kudin a wannan account din👇*_

_*0022419171 Access Bank Maryam sani*_

Saiku tura shedar ta👇

_*09033181070*_

Idan kuma katin Waya ne zaku tura katin MTN ta wannan layin👇

09166221261

TEAM ZAFAFA BIYAR🔥🔥
MUNGODE🙏🙏❤️

Download

Click the below button to download, pls in case you get trouble trying to download kindly drop a comment.


Download any type of hausa novel which include Hausa Love, Adventure, fiction, Fantasy and other genre Hausa Novel paid and free and read them in confort of your zone at ArewaBooks.Com

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

 

Author’s Contact

  • Name : Hafsat Rano
  • Wattpad Handle : @ 
  • Nick Name : Hafsat Rano
  • Whatsapp Number : 
  • Nationality : Nigeria
  • Email :
  • Group : Haske Writers Association

The Book is not free

Back to top button