Uncategorized

Wace Ce Ita Chapter 4 Complete Hausa Novel

   WACE CE ITA⁉️ (WHO IS SHE⁉️)

~Unique Barakancy~

                  FOUR📍

          Eesha dake kwance ta mike zumbur,tana rarraba ido,yau taga ikon Allah,gabadaya saita nemin ciwon marar tarasa batareda tasha magani ba,mamaki ne fal cikin ranta tana kara bin hannunta da kallo,tana kara tinanin wani kalan sura Allah ya zuba a wannan halittar,hannunta kawai ma ta gigice,toh inaga fuskarta,karshen tikatiki idan da’ namiji yayi arba da ita fa,yaya zata kasance? Anya bazaa sume ba?…. Dawowa tayi daga shirmamman tinaninta jin anyi banging kofar………. Itako Fatimah Zainab ranta inyayi dubu ya baci ganin yanda shashashar yarinyar tacigaba da binta da kallo,hanglove din hannunta ta mayar,tana kakkabe jikinta kamar wacce aka zubawa kashi bayan ko ruwan be tabata ba,chan kuma ta figi jakarta ta fita a fusace,tana buga kofar…………

Direct lecture hall ta nufa,kawai saitaji kuma bazata iya bata lokacinta ta saurari wani lectures ba,sai ta chanja akalar tafiyar ta zuwa hanyar gate………..

Tana fita ta hango motar a fake kamar yanda tayi expecting,yana ko zaune a ciki yadan kwantar da kujerar baya yana bacci,bude daidai driver sit tayi,ta mishi nuni daya fito…….. A zabure ya mike yace “Good morning ma’am,I’m sorry if I do anything wrong” ya fada hankali tashe dan wlh shikadai yasan yanda yakeji da aikin nan nashi,wani inya ganshi saiya dauka wahala kawai yakesha,amma irin kudin dayake samu da wannan aikin yasan ko kwalin degree dinshi bazai bashi ba,shiyasa duk wanda Allah ya taimakeshi ya samu aikinnan,yake kapkap dashi,dan wayanda sukayi a baya sun bashi lbr,bazata ce maka komai ba saidai kawai kaji notice daga sama an koreka,shiyasa suka bashi dan wani tactics da suke tinanin red button dinta ne akan zata kori mutum,shikenan ko yaya yaga reaction dinta ya chanza saiya fara bata hakuri…………….. Girgiza mishi kai tayi alamun ba komai ta kuma bude jakarta tazaro bandir din kudi bata ko kirga ba tamika mishi,tana mishi nuni daya tafi gida kawai sai gobe……. Tsugunawa yayi harkasa yanata mata godiya kamar ze mata sujjada dan murna da farinciki….. Ko kallonshi batayi ba tashige motar,taja tinted glass din sama,ta fizge niqab din sannan ta figi motar a guje,ya bita da addu’ar Allah ya tsareta………..

 Tafiya tayi na kusan 30mins,dama tasaba idan zatayi irin wannan tafiyar ita kadai take zuwa,achan jikin wani kango tayi parking tana kalle kallan ta’ina zai bullo,kawai sai jitayi mota tayi horn a bayanta,mamaki ne yakamata yau kuma da mota yazo?, batace komai ba ta fito shima ya fito suka hade, basuyi magana ba ta zaro wayarta tamasa transfer din 5m a take,ta jiyo da fuskar wayarta tana masa nuni da ‘transaction successful’,gyada kai kawai yayi ya mikamata box din dake hannunsa,shigewarta mota tayi taja a guje tabar wajan…………

    Harta dauki hanyar transcorp sai kuma wani tinani ya fadomata arai,guntun murmushi tayi tana ayyana ta kwana biyu bataje gidan tayi tijara ba,gashi kuma tasan irin wannan lokacin kowa na gidan na nan,kawai saita juya akalar motar ta dauki hanyar gidan……..

    Horn tayi da karfi,gateman ya fito da sauri ya bude mata gate,daidaita parking dinta tayi sannan ta dauki karamin box din tajefa a cikin jaka,ta fito a hankali ta nufi main entrance din gidan……. Mai wankin mota naganin tashige ya taso da sauri ya rufe motar domin al’adar tace inta dawo da mota bazata kara fita da itaba,sannan yafara goge sauran motocin dake parking lot din dukda gabadayansu sababbi ne………..

     Da sallama ciki ciki tashiga main parlour din,tana bin ko ina dawani mugun kallo,Abdul ne yafara hangota,aiji yayi kamar ansashi a aljannah da ganinta,ganin kuma tacigaba da takowa yayi sauri ya dauke kai…… Suko sauran occupants din parlourn ji sukayi kamar an aiko musu da mala’ikan mutuwa,sunsan zuwanta sam babu alkhairi a ciki,haka dai suka daure kowa ya daura murmushi a fuskarsa badan yasoba……. Zama tayi a daya daga cikin kujerun falon tana dora kafa daya kan daya,ai da sauri yanmata guda uku dake parlourn suka sube kasa suna gaisheta saboda gudun abinda zeje ya dawo…. Ko kallonsu batayi ba bare tasan Allah yayi halittarsu a wajan,amma haka suka tashi jiki na rawa suka cikamata gabanta da kayan ciye ciye…. Abdul na kokarin gaisheta shima ta daga mishi hannu………

“Welcome my daughter” ta tsinto muryar momma na fadin hakan,kallon kasan ido tabita dashi batace komai ba….. Budar bakin mama itama sai tace “Daughter wata sabon gani yau kintina damu”….. Ko kallon mama batayi ba sai girgiza kafa datakeyi akan kujera……… Momma bata gaji da halin ko inkula data  mata ba,ta sake cewa “Daughter ya Khaleel,kuna waya dashi kuwa? Sai a lokacin ta dago ta kalleta ido cikin ido,budar bakinta keda wuya tace “Ni zaki tambaya danki? bakisan inda yake bane?” Karab sai mama tace “In banda abinki daughter meye toh dan an tambayeki masoyinki? Hade girar sama da kasa tayi tace “Ba ruwanki,ni tashima ki dafamin indomie dan bazanci jagwalgwalan da ya’yanki suka ajyemin ba”……… Jiki na rawa mama ta tashi,tanajin wani farinciki a ranta,tana ayyana yanda zata jefi tsuntsu biyu da dutse daya,this is the perfect opportunity that she has been seeking for,yau kuma Allah ya bata so bazatayi wasa dashi ba………….. 

   Bata taba bata lokacinta akan tsarawa wani girki irin na yau,duk da indomie ce kawai amma sosai ta baje basirarta yanda kamshinta mutum yajima kawai zai gigice bare kuma ace ya kai baki,sosai ko gidan ya dime da kanshi kamar wani liyafa akeyi,sadap sadap takoma taki ta dauko wani abu a leda batareda kowa ya ganta ba…..Saida ta tabbatar babu wanda yake ganinta sannan ta kwance ledar tayi injecting content din cikin syringe din zuwa indomie,tana wani farin ciki a ranta,tasan dai komai yazo karshe a yau dinnan,gwara mayyar yarinyar nan tabar duniya kowa ya huta………

        Fitowa tayi tana murmushi ta ajye well ganished indomien akan center table din dake kusa da Fatimah Zainab,sannan ta kalleta still murmushi daure akan fuskarta tace “Done daughter” …. Dagowa tayi zatayi magana kenan sukaji sallamar daddy…… Kowa na parlourn ya amsa amma banda ita,karasowa yayi yana mamakin ganinta,sai ya boye mamakinshi yace “Daughter yau kece a gidan haka,toh ya karantu,I hope kina maida hankali sosai”….. Kallonshi tayi tace “Not really” kamar batasan magana…… “Haba daughter nafiso kimaida hankali sosai domin ki zamo wata a rayuwa” Bata fuska tayi tace “Ni duk mubar wannan maganar,dama gurinka nazo,so nake amin processing visa zantafi US nan da one week” ….. Cikin mamaki yace “me zakije kiyi a US?”…… “Gurin danka zani” Ta bashi answer kai tsaye…… Zama yayi a chair din dake facing dinta sannan yace”Amma daughter ba soon zaku fara exam ba,why not bazaki bari in kun gama ba,yanada kyau ki maida hankalinki sosai akan jarabawarki,kuma bakima fadamin takemaimai me zakiyi a US ba”…… Hade girar sama da kasa tayi tace”Haba daddy ya zaka dinga min irin wannan question a gaban yara,kuma ni ba abinda zanyi a US,danka kawai nakesan gani?” ….. Girgiza kai kawai yayi yace “It’s alright,I’ll send you the details when the visa is processsed,sai ki zama cikin shiri”……. Batace komai ba ta bude murfin hadaddan unbreakable din da aka zuba mata indomien a ciki,take ko kamshin ya daketa,sai kuma ta fara bin abincin da kallo,smirking tayi tace “Mama bismillah fara ci” Daddy haryamike yaji mama na cewa “Bangane in faraci ba” Sai ya dawo ya zauna incase in wani fitinar fatima zainab zata tada ya tareta,dan sarai ya sani duk sanda tazo saita hada wani gurmi take tafiya…………. 

Sake kallon mama tayi tace”Saifa kinci zanci,do quick yunwa nakeji”…… Hade rai mama tayi ta kuma cewa “Bangane sainaci ba ni nace miki inajin yunwa ne?”……. Kallon daddy tayi daya zama speechless tayi kwafa  tace “Daddy ka fadawa matarka taci abincin nan in anason asamu zaman lfy a gidannan”…… Da sauri dan shima bayasan tashin hankali yace “Hafsa dauki abincinnan kici ko one spoon ne a wuce wajan,bansan ana jan magana”…… Kame kame ta farayi ta kafe akan ita fa bazata ciba,daga abin arziki sai a bita da rashin mutunci,Ita kuma fatima zainab ta kafe akan ko taci abincin ko duk abinda ya faru a gidan ita tajawo…… Daddy ganin abin na nema yazama babba yace”Ke husnah dauki kici,tinda uwarki taki ci” ya fada yana kallon daya daga cikin yanmata dake zaune a parlourn, tasowa tayi zata dauki abincin,mama ta daka mata tsawa tace “karki kuskura ki taba abincinnan” …… Haka yace duk sauran yaranta suzo suci,amma dukta hanasu….. Sosai ranshi ya baci da rainin hankalin mama,Itako Fatimah zainab bata kara cewa komai ba tin bayan ta bada warning dinta….. Wani idea ne ya fadowa daddy,sai yace “hafsah idan kika bari nayi bincike akan abincinnan nayi finding out wani abu zan dauki mummunan mataki akanki,gwara tin muna mu biyu kice”…… Sosai gabanta ya fadi amma ta dake zuciyarta na bata assurance din ba abinda ze faru……  Binsu da kallo daya bayan daya daddy yayi,sannan yace”zan kira Doctor yazo yayi taking sample din abincinnan yayi test a ganomin in akwai wani abun a ciki ko babu…….. Ya fada yana fito da wayarshi daga aljihu tareda dialing number Doctor din…..  Wani dadi ne ya lullube mama tinda tasan family doctor dinsu ze kirawo,wannan kuma bata da case dashi tinda tare suke kulle kullensu,Infact shiya kawo mata injection dinma………… Katseta daddy yayi da maganar daya farayi bayan an daga wayar “Doctor kana abuja kuwa”? Basuji me akace ba sukaga yace “I have some urgent issues I want you to attend to,pls come to my house now”…….. “Thank you” sukaji ya sake fada….. Murmushi mama ta karayi aranta tana cewa  “Allah ya taimakeni ya dawo shekaranjiya,da yanzu saidai a kira wani,haka kawai yazo ya tonamin asiri”…..

           Tafiya yake da niyar yaje barbing salon domin ya rage gashin kansa,kasancewarsa me tarin suma,shiyasa kusan duk sati sai yaje barbing salon,sai kawai ga kiran alhaji,batareda tinanin komai ba ya juya akalar motarshi zuwa gidan alhaji….. Horn yayi mai gadi ya taso da sauri ya budemishi gate,shiga yayi cikin gidan ya nemi guri yayi parking….. Kiran alhaji yayi a waya yasanar dashi zuwansa….. Fitowa yayi daga cikin mota ganin alhaji na nufoshi,karasowa alhaji yayi ya dafa kafadarshi yace “Welcome Dr Deen,my son”…… Murmushi yayi suka gaisa sosai da alhaji,sannan alhaji ya mishi jagora zuwa ciki………

     Tinda suka tinkaro parlourn yaji gabanshi yayi wani mugun faduwa,kuma ya fara jin irin abunda yakeji a duk sanda ze ganta,toh ko ina yaje a abuja saita bishi ne?,to wai ‘WACECE ITA?’ Ya fada yana kalle kallen ta ina ze hangota….. ‘Tabbas haduwarmu bazaiyi kyau ba koma wacece ke!’ Ya fada suna shiga parlourn……………..

 

   ~Unique Barakancy~

Back to top button