Hausa novels

Halysaah Page 169 By Khaleesat Haydar

HALYSAAH PAGE 169…Khaleesat na zaune kan carpet din parlon Hajja ta kwantar da kanta jikin kujeran parlon, isowarsu kenan daga Kano tare da matan da suka taho da ita, duk da bacin ran dake tare da Hajja tuni ta watsake ganin visitors din nata, da fara’a take welcoming mata hudun da suka taho tare da Khaleesat tun daga Kano, Hajja tace “Ku karasa can parlon ciki Raliyah gani nan zuwa” Duk suka karasa can cikin parlon, Hadiyah na kwance parlon abun duniya ya isheta ko kumallo taki yi tun da gari ya waye don ma Hajja na ta lallabata tana bata assurance kan cewar aure kamar an maida sa an gama, Mikewa zaune tayi ta murtuke fuska tana hararan Khaleesat da bata ma san tana yi ba, Hajja ta karasa kusa da Khaleesat ta dafa ta tace “Sannu Jiddah, ya jikin?” Kai kawai Khaleesat ta gyada mata don ba karamin wahala ta sha a hanyarsu ta zuwa ba duk ta jigata, Hajja ta kira mai aikinta da sauri tace “Suwaiba zo ki kai ta dakin da ku ka gyara mata, ki hada mata ruwan wanka a bandaki sai ki ji me take son ci, duk ta wahala a hanya” Suwaiba ta karaso da ladabi tace “To Hajja” Khaleesat ta daure ta mike ta bi Suwaiba zuwa dakin tana jan kafa da kyar, Hadiyah ta wani kalli Hajja tace “Saboda zata dawo daga Kano shi ne sai an mata irin wannan rakiyar Hajja? Kuma na menene zata saukar ma mutane a gidan nan?” Hajja tace “Bata da lafıya ne, shi kuma da yake wawa ne sai ya bar ta wai a gidansu, shi ne na aika aje a daukota don bamu gaji haka ba a gidan sarauta” Hadiyah dake ta kallon Hajja tace “Me ya sameta?” Hajja tace “Juna biyu gareta” Kallon Hajja Hadiyah ta dinga yi babu ko kiftawa with shock, Hajja tace “Bari in je mu gaisa da bakin nan, su Hajiya Raliya ne baki gane su ba?” Daga haka Hajja ta wuce parlon can ciki, Hadiyah ta ciji finger dinta, can ta mike tsaye ta fara zaga parlon a hankali tace “Juna biyu? To wallahi bazai yiwu ba” hawaye taji sun taru idonta bayan ta tuna ita an ma saketa, ta dau wayarta tana goge idonta ta tafi dakinta da sauri. Da yamma Hajja ta fito dakin Hadiyah don tun da ta shiga ciki har yanxu taki fitowa, Hajja ta zauna kan kujera ranta a dagule, har ta gaji da fama da ita kan ta ci abinci, da ba don a gabanta aka haifi Jawwad ba da sai tace canza ma Ahmadu shi aka yi a asibiti, amma ba komai tasan duk uwarsa ce ta sa yayi wannan abun, kuma sai tayi da ta sani, Hajiya A’isha da Kilishi ne suka shigo parlon da sallama cikin shiga ta alfarma, Hajja ta daga kai ta amsa sallamar su, suka karaso cikin parlon duk suka zauna kan carpet suna gaida Hajja, Hajja ta amsa tace “Sannun ku da zuwa” Kilishi tayi kasa da murya tace “Hajja wani labari muka ji mara dadi yana ta yawo a masarauta” Sosai gaban Hajja ya fadi ta fara addu’an Allah ya sa ba maganar sakin Hadiyah bane ya fita yake yawo, cikin natsuwa tace “Wani magana ne wannan Kilishi?” Kilishi tace “Wai Jawwad ya saki Hadiyah” Hajja tayi saurin kallon hanyar dakin da ta sauke bakinta, Kilishi tayi kasa da murya tace “Kina da baki ne halan Hajja?” Hajja ta mike tace “Mu tafi parlor na” Duk suka mike suka bi bayanta, ko zama Hajja bata yi ba tace “Ina ku ka ji wannan magana Kilishi?” Hajiya A’isha ta sauke ajiyar zuciya tace “Hajja ai maganar nan ta gama karade masarauta yanxu, Khadijah ce ta gaya ma Iklima ta waya…” Hajja tayi shiru tana jin wani sabon bacin rai, can tace “Khadijah?” Hajiya A’isha tace “Kwarai kuwa Hajja, don sai da ma na amshi wayar nayi mata fada nace wa ya tambayeta don muna tare da Iklima lokacin da ta kira” Kilishi tace “Ba kowa zai sa Jawwad yayi wannan danyen aikin ba sai uwarsa, nima wallahi daga masarauta aka kirani ake gaya min wannan mummunan labarin, duk na gigice na taho nan, a bakin gate din gidan nan muka hadu da A’isha wallahi Hajiya A’isha tace “To kasa sukuni nayi shi ne kawai na shirya taho nan, gwara a dakatar da yayada wannan magana haka, ai komai na son sirri Hajja tace “Allah ya kyauta, amma kuma ai ya maidata a yau, kuma kun san baza a zuba ido a kyale lamarin haka ba, komai ya dai daita yanxu kam” Kusan a tare Hajiya A’isha da Kilishi suka ce “To Alhamdulillah, ai haka ake so….” Hajja ta mike tace “Ina da baki, bari in je wajensu” Fita tayi daga parlon nata zata tafi dakin Hadiyah, su Kilishi suka kalli juna, Hadiyah na zaune tsakiyar gado waya kare a kunnenta tana sauraron uwarta, a hankali tace “Wallahi sai ma kin ga yanda take taraiyarta tana lallabata Ummi, convoy guda fa aka taho da ita daga Kano, sai wani daga min hanci take ita me ciki, ai ko yanxu zan shirya in fita zuwa pharmacy din…. Ummi tace “A’a kar ki fita gudun zargi, gwara ki kira wannan kawar taki da ta karanci likita, ki nuna mata ke zaki yi amfani da shi cause you are not ready, za ku yi tafiya” Hadiyah tace “Kuma haka ne fa Ummi kin kawo shawara, bari in kira Amina yanxu kuwa zaki ga ta kawo min” Ummi tace “Duk yanda ake ciki ki kirani ki sanar min” Hadiyah tace “To Ummi” Katse wayar tayi ta fara kiran kawarta, bayan sun gaisa tace “Amina wani alfarma nake son ki min don Allah, nasan babu me min wannan abun sai ke Amina tace “Ina jin ki kawata, anything for you” Hadiyah tayi kasa da murya tace “I just found out I am pregnant Amina, don Allah abortion pills nake so don ban shirya ba wallahi, kuma fa tafiya za mu yi da shi Amina ta zaro ido tace “Ke Gimbiya haka kawai ki sa Yarima ya daureni?” Hadiyah tace “C’mon ta ya zai sani, har yanxu bai ma san da cikin ba, don Allah I need it today Ina gidan Grandma kafin in koma gidan Sarki” Amina tace “Gaskiya kam it’s too early, duka duka yaushe aka yi auren har za ayi ciki, ko amarcin ba a gama ci ba” Hadiyah tace “Shiyasa nake son ki Amina don akwal ki da ganewa… Hajja ce ta shigo dakin Hadiyah tayi saurin katse wayar ta ajiye, Hajja ta kulle kofar cikin fada tace “Ke Hadiyah gaya ma Khadijah kika yi Jawwad ya sake ki bayan duk kwabar da na maki kan cewar kar ki gaya ma kowa wannan mummunan maganar?” Hadiyah ta juya tana kallon Hajja tace “A ina na ganta zan gaya mata, ko kuma meye hadina da ita da zan gaya mata, wato har an fara yamadidi da ni a masarauta kenan?” Sai kuma ta fashe da kuka sosai tace “Ni wallahi wajen dangin babana zan wuce tunda Jawwad ya fi karfin kowa, wallahi bazan zauna garin nan ba gwara inje inda za a amsar min yancina….” Hajja tace “Ikon Allah, to shi Yusuf fulani ya sanar ma wannan maganar har ta gaya ma ‘ya yanta suke yamadidi da shi a masarauta? Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un” Bakin ciki yasa Hadiyah ta dinga kuka don dama ba shiri take yi da duk yaran Aunty ba. Wajen karfe shidda Hadiyah ta shiga kitchen din Hajja ta ga Suwaiba ta dama ma Khaleesat kunu zata juye a tsadadden flask din da Hajja ta bada a zuba mata a ciki, Hadiyah ta dauko cup babu yabo babu fallasa ta mika ma Suwaiba tace “Zuba min kunun Suwaiba ta amsa cup din da ladabi ta dibar mata, Hadiyah ta amsa ta fita daga kitchen din, dakinta ta koma bayan ta ajiye kunun ta zauna gefen gado ta dauko maganin da Amina ta kawo mata not long ago, tashi tayi ta shiga bandaki ta zubar da kunun da ta shigo da shi sannan ta dauraye cup din ta debi ruwa dan kadan ta fito, gaba daya pills din goma ta jika a ruwan cikin cup din tana dan murmushi, tana ta zaune dakin har sai da pill din suka narke, sai kuma ta mika ta dau Hijab dinta har kasa ta saka, tana rike da cup din ta cikin hijab din ta fita, kalle kallen parlon ta dinga yi, taga alamar Hajja na can parlonta ta karasa dakin da Khaleesat take kwance ta bude a hankali, ta ganta tana bacci ga flask din kunun da Suwaiba ta ajiye a dakin, trying not to make any sound with her toes ta karasa cikin dakin ta duka kusa da flask din ta bude sannan ta juye dissolved pills din gaba daya cikin flask din don ba a cike yake ba, cikin hanzari ta mike zata fita daga dakin suka kusa cin karo da Suwaiba, da sauri Hadiyah ta koma baya ta fara boye cup din hannunta, can sai ta hade rai tace “Naji kunun yayi dadi, kuma kamar babu yawa a flask din shi yasa ban diba ba” Suwaiba tayi kasa da kai da ladabi tace “To ki diba ranki shi dade sai a dama wani” Hadiyah ta yatsine fuska tace “Bar shi kawai” Daga haka ta fice daga dakin da sauri, Suwaiba ta bi ta da kallo sannan ta kalli flask din kunun ta karasa ta ajiye warmer din Farfesun hannunta da Hajja ta sa ayi ma Khaleesat, zuwa sannan Khaleesat ta bude ido jin voices dinsu amma tana ganin Hadiyah ta mayar da idonta ta rufe don ko ganinta taji bata son yi. Bayan Magrib Khaleesat na zaune kan darduma bayan ta lallaba tayi sallah da kyar, aka bude kofar dakin ta daga kai a hankali, suna hada ido ta sauke idonta, ya karaso cikin dakin ya kulle kofar yana kallonta, ita dai bata sake kallon bakin kofar ba, walking slowly ya isa har inda take zaune ya duka yana kallonta cikin sanyin murya yace “Jeeddah” Taki cewa komai, a hankali yace “Ya jikin?” Nan ma dai shiru tayi kuma bata yarda ta kallesa ba, shi dai kallonta kawai yake babu ko kiftawa don har ta dan rame, bude kofar dakin aka yi ya juya, sai ga Hajja ta shigo dakin tace “Ina Suwaiba ta zo ta zuba maki kunun ki sha tunda kin yi sallan” Khaleesat ta sunkuyar da kanta don duk tunaninta zai matsa kusa da ita da Hajja ta shigo cause he was very close to her, sai taga bai tashi ba, instead ya kalli Hajja yace “Ina kunun?” Hajja tace “Ga can flask din kunun” Mikewa yayı ya dauko flask din dake kan table da cup dake kife kan tray, ya bude flask din ya zuba kunun a cup, ya kalli Hajja yace “But it’s very hot” Hajja tace “To ina ruwan ka, ko kuma me sanyi kake son a bata” Bai tankata ba ya dau spoon ya fara juya kunun saboda ruwan da ya fara zuba daga cikin flask din kafın kunun ya biyo baya duk zatonsa steam ne na kunun, ita dai Khaleesat kanta na kasa, bayan ya gama juyawa ya kai baki, kallon Hajja yayi after some seconds yace “Why is it so bitter? Ko haka yake?” Ya ajiye cup din ya tafi bandaki ya kuskure bakinsa don kadan ya kai baki kuma bai hadiye ba, Hajja tace “Bitter kamar yaya? Ni bana son sanabe fa, in kuma in baka ita ka tafi da ita ne to, meye bitter kamar an dama mata shuwaka” Tana fadin haka ta dau cup din ita ma ta dandana kunun, kallon cikin cup din ta dinga yi, shi dai Ajay na tsaye yana kallonta shi ma, can ta ajiye cup din ta fita zata je ta samu Suwaiba taji me ta zuba kunu ke dacíkamar an zuba tazargade, lallai lallai an zuba abu a kunun nan dama gashi su Hajiya A’isha basu tafi ba suna gidan har lokacin kuma sun san Khaleesat na gidan ganinta ne dai Hajja bata basu fuskar yi ba, Suwaiba ta marairaice tace “Wallahi ranki shi dade ban zuba komai ba, me kuwa zan zuba a kunu ranki shi dade, iya garin kunun ne sai tsamiya kadan” Hajja tace “Nasan baza ki zuba komai ba Suwaiba, muna tare dake shekara sha biyar kenan fa nasan halinki, tambaya nake ko kin ga wani ya shiga dakin bayan kin kai kunun kin ajiye? Ko kuma sanda kike dama kunun a kitchen?” Suwaiba ta gyada kai tace “Eh Hajiya Hadiyah ta shiga dakin na ganta da wani kopi a hannu, sanda nake dama kunun ma ta shigo kitchen” Hajja ta zaro ido jin abinda Suwaiba tace, can ta fara kalle kalle tace “To ki ja bakin ki kiyi shiru kawai Suwaiba, je ki kawai, bana son jin komai kuma daga gare ki” Suwaiba tace “To in sha Allahu Hajiya” Daga haka ta juya ta bar wajen, Hajja ta tafi dakin Hadiyah da sauri bayan ta kulle kofa tace “Ke Hadiyah uban me kika je kika zuba ma yarinya cikin kunu yayi daci haka?” Hadiyah ta wani hade rai tace “Wani shegen ne yace na zuba abu?” Hajja tace “Haba Hadiyah, me yasa zaki yi haka? Me tayi maki zaki aikata mata wannan aiki?” Hadiyah ta murguda baki ta kauda kai, Hajja tace “To Allah ya shirye ki” Daga haka ta juya ta fita daga dakin don duk Hadiyah ta gigitata, Ajay na durkushe gaban Khaleesat yana kallonta a hankali yace “Ko kina son mu tafı gida Jeeddah?” A karo na farko ta daga kai ta kallesa, after some seconds ta gyada kai, ya kamo hannunta zai yi magana sai ga Hajja ta shigo dakin, Khaleesat ta janye hannunta daga nasa da sauri, Hajja ta nufi inda flask din yake tayi saurin daukewa tace “Babu wani abu da aka saka a kunu kawai yanayin garin kunun ne haka, amma ni ma bazan bari ta sha ba gwara aje a zubar, da kaina zan mata Custard yanxu….” Ajay ya daga kai ya kalli Hajja yace “Ina son zan tafi gida da ita” Khaleesat ta kauda kai saboda wani kunya da taji ya rufeta, Hajja tace “To hakan ma ba laifi, tunda nasan zaka kula da ita ga kuma wannan mata Yakumbo naga tasu ta zo daya matar na sonta, ni kuma duk bayan kwana biyu zan dinga zuwa dubata in sha Allahu, naga ma ita laulayin ba me zafın nan take yi ba, da lokacin Sallah yayi zata tashi tayi, tunda suka zo ma ban ga tayi amai ba” Tun a hanya Ajay yayi ma Yakumbo waya tayi ma Khaleesat kunu kan su isa, Khaleesat dai na kwance back seat ta fara bacci tun fitowar su daga gidan Hajja, saboda ita yake tafiya gently don baya son stressing dinta bayan long journey da suka yi da safe da za a taho da ita daga kano, basu isa masarauta ba sai bayan kusan awa daya, yayi parking ya dau wayarsa jin shigowar message, yana dubawa yaga Jay ne yayi masa text, ya bude text din yaga kawai yana gaya masa ne ya shirya gobe su tafi Calabar din, Ajay ya dinga kallon text din, kawai ya saka ranan da yayi suiting dinsa not minding if everyone else is ready, ya saka wayar a aljihu ya sauka daga motar ya zaga ya bude back seat yana kallonta, baccinta take kamar tana kan gado, ya kai hannu forehead dinta yaji jikinta babu zafı, he wish a gidansa suke inda suke da enough privacy da kawai daukarta zai yi zuwa cikin gida without bothering to wake her up, but that will never be possible a masarautar nan, dukawa yayi ya fara tashinta gently yace “Jeeddah, we are home” Ta bude ido a hankali, sai kuma ta mike zaune tana kalle kalle, ya kama hannunta helping her to come down from the car, yace “Sannu” Taki kallonsa ta hade rai, ya rufe motar ko cire makulli bai yi ba yana rike da hannunta ya nufi cikin gida da ita….

Back to top button