Ruwan Zuma Page 46 Hausa Novel
(46) Tun lokacin da Mas’ud ya fara yiwa Madu tonon asiri a gaban Ummii shi Madun ya sunkuyar da kanshi k’asa yana jin kamar k’asa ta tsage ya shige tsabar kunya da kuma takaicin abunda yayi, wanda sai yanzu da aka kamashi kuma Alhaji Abdul yaci amanarshi ya fara nadama. “Duk abunda Mas’ud ya furta gaskiya ne?” Ummii ta tambayi Madu cikin kid’ima da kuma rashin yarda. Shiru Madu yayi bai d’ago kai ba haka kuma bai furta komai ba, k’arshe mik’ewa yayi zai fita Ummii ta dakatar dashi ta hanyar mishi tsawa wanda dukkansu sai da suka tsorita don basu ta6a ganinta cikin 6acin rai haka ba. “Ka amsa mini!!” Ta kafeshi da ido wanda hakan yasa ya koma ya zauna yana zare ido yace, “Ummii zamu yi maganar daga baya, kuma wani abun da Jamila ta fad’a k’arya ne wallahi, abunda nayi kuma saboda in kare Laila ce tunda ita lallashi da shawara baya aiki a kanta.” “K’arya kake yi Madu. Furucinka k’arya ne. Ka cuceta, da bakinka an cuci k’anwarka. Ban ta6a zaton zaka yiwa jininka haka ba. Ka bani mamaki kuma nima ka zalunceni da kasa na fara zarginta ina hantararta.” Ummii ta furta hakan a hankali hawaye na taruwa a idanunta na takaici da bak’in ciki. “Ummii….” Madu ya tashi tsaye yana k’ok’arin mata magana ta dakatar dashi ta hanyar d’aga mishi hannu, “Ka fita ka bani guri, wallahi bana marmarin ganinka” Tana fad’in hakan tayi hanyar d’akinta Mas’ud yayi saurin yin kanta shima ta d’aga mishi hannu tace, “Kowa ya koma gidanshi. Duk wanda yayi nagari kansa, wanda yayi akasinsha kuma shi da wanda ya halicceshi. Tashin hankalin ya isa haka, bana son ji komai.” Tana gama fad’in hakan ta shige d’aki Ammi tabi bayanta tana kama kafad’arta domin karkarwa data fara yi tana had’a hanya. “Mas’ud ina tsoron kar ciwon Ummii ya tashi.” Fad’in Laila tana hawaye tana kallon k’ofar d’akin Ummii. “Babu abunda zai faru in Allah ya yarda, idan ma jikin ya tashi Ammi zata yi waya. Mu tafi.” Mas’ud haka ya tasa Laila a gaba har suka shiga motocinsu suka kama hanyar gida. Sai daya tabbatar ta shiga gidanta sannan shima ya kama hanyar gida yana ayyanawa a ranshi cewa basu ta6a ganin rana irin wannan ranar ba. Domin kuwa rana ce mai tsayi, mai cike da hatsaniya da tashin hankali kuma baya fatan su k’ara cin karo da makamanciyarta. A cikin zuriyar Ummii kuwa duk wanda yace yayi bacci mai dad’i a wannan ranar yayi k’arya. Washe gari da safe Laila na shirin zuwa gidan Ummii taji wayarta na k’ara tayi saurin d’auka zuciyarta na bugawa ganin sunan Ummii a jikin screen d’in. “Ummii jikin ne?” Abunda ta fara fad’i kenan bayan ta d’agar wayar tana dafe kirji. “Lafiyata kalau. Kar kice zaki zo, ki zauna a gida ki kuma dinga tunawa da matsayinki a yanzu.” “Zan zo in dubaki ne Ummii.” Laila ta fad’a duk da tasan cewa Ummii baza ta canja maganarta ba. “Bana so. Ki zauna a gidanki.” Ajiyar zuciya Laila tayi kana ta gaisheta tare da tambayar lafiyar Ammi suka yi sallama. Wasa-wasa yau sati d’aya kenan da 6acewar Haydar wanda har sun daina nemanshi saboda sun san cewa shi ba yaro bane zai bayyana duk lokacin da yaga dama. Sai dai za’a iya cewa Laila tafi kowa shiga damuwa bayan Ammi dalilin cewa wai sakinta Haydar yayi sannan ya tafi ya barta da cikin d’ansa, zamanta a gidansu kuwa zama take yi na iddah wanda k’arshensa shine in ta haihu. Kullum Mas’ud sai yazo gidanta sau biyu ya dubata ya mayar da hakan kamar dolenshi, akwai ranar da yazo da daddare ya sayo mata tsire da fruits tunda yaji ance masu ciki suna da kwadayi, “Na sayo miki tsire amma ban san ko bakya son k’amshinsa ba, hope ba zai sakaki amai ba?” “Mas’ud kenan. Ni ban ta6a yin amai ba, ina ganin shiyasa ban ta6a kawowa cewa ciki nake dashi ba. Mik’o mini tsiren don wallahi tun shigowarka k’amshinsa yake bugan hancina.” Ta mik’a hannunta ya bata. A gabanshi ta bud’e yana mata hira har ta cinye bata mishi ko tayi ba, shi dai kallonta kawai yake yi yana jin mugun tausayinta a ranshi wanda har yake jin kamar wani abu mai d’aci ya mak’ale mishi a wuya. In ba don yasan abunda ta aikatawa Haydar ba daa yanzu ya tsaneshi saboda baya son abunda zai 6atawa yayarsa rai. Tana shan fruits d’in ya mata sallama ya tafi akan washegari da safe zai dawo ya ga lafiyar jikinta kamar yanda ya saba kullum. Sati d’aya da haka wanda ya cika sati biyu da 6acewar Haydar, watarana Mas’ud na shago ya ga kiran Alhaji Abdul a wayarsa yayi ringing har ya gama bai d’auka ba. Haka aka sake kiranshi har sau uku bai d’auka ba, daga k’arshe sai yaji shigowar text ya d’auka ya karanta kamar haka, ‘Na san ni mai laifi ne a zuriyarku gabad’aya, sannan na so in zo muyi magana da kai ne amma naji an ce Madu nemana. Kayi hak’uri ka d’auki wayata muyi magana, wallahi ba cutar daku nake da niyyar yi ba, ina so ne in gyara wani abu a cikin dubbannin da na 6ata. Sannan karka manta Haydar k’anina ne wanda a yanzu nake jin bayan mahaifina babu wanda nake so sama dashi, bayan 6acewar mahaifiyarsa mun nemeta ni da mahaifina har muka hak’ura muka barwa Allah komai. Haydar is all I have don bana tunanin zan yi aure har abada. Please help me make this right, please.’ Mas’ud yana gama karantawa ya ja doguwar tsaki yana ajiye wayar a gefe. A wancan ranar da Alhaji Abdul ya samu ya gudu daga hannun Madu, sun ji labarin ya bar gari ya tafi jinyar hannunshi daya karye da kuma goshinsa da aka fasa wacce aka yiwa d’inki biyar. Madu kuma kamar dole bai fasa neman Alhaji Abdul ba, sai ya zama kamar wani zautacce yau yana wancan garin, gobe yana wancan garin inda yake tsammanin zai samu mak’iyinshi. Jamila kam ba’a maganarta domin daga Alhaji Abdul har Madu babu wanda ya nemeta saboda sun san ta musu nisa har abada, ita ba dak’ik’iya bace da zata zauna a kusa in da zasu ganeta. Awa biyu da tura wannan text d’in Alhaji Abdul ya sake kiran Mas’ud amma yana gani ya k’i ya d’auka. Wayar tana k’ara ringing Mas’ud ya d’auka a fusace yana cewa, “Duk munafurci da cin amanan da kayi bai isheka ba shine yanzu kake tunanin zaka k’ara wasa da hankalina don ka sake a karo na ba adadi? Kai kam baka jin kunya ne? Ko kuma don kaga bamu d’auki mataki bane yasa kake raina mana hankali? Wannan karon ya zama na k’arshe da zaka k’ara kirana ko kuma ka mini text kana damuna, I have no business with you. Don Haydar yana k’aninka kuma ba damuwata bace, I don’t give a fuck ko kai ubanshi ne.” Yana gama fad’in hakan ya kashe wayarsa yana huci domin sai yanzu yake jin bak’in cikin hanashi d’aukan mataki da Laila tayi. Shikenan sun barshi kenan ya cucesu? Sai dai tunawa da yayi cewa sun barwa Allah hukunci yasa yaji d’an dama-dama a ranshi. A ranar da yaje gidan Laila da dare yake fad’a mata yanda suka yi da Alhaji Abdul tayi shiru tana sauraranshi, bayan ya gama bata labarin tace, “Ko dai da gaske yake yi yayi nadama yana kuma son neman Haydar? Mas’ud ka gwada sauraranshi mana.” “Ke har zaki iya yarda da wannan munafukin after all abunda yayi? He is the reason why your son is in rehabilitation! Shine munafukin da ya hanaki kwanciyar hankali duk tsawon wannan lokacin, shine zaki ce a saurareshi? Me zai ce ko kuma me zai mana? Wallahi ba zan ta6a yarda dashi ba Kalti.” Tagumi kawai Laila tayi tana kallon yanda Mas’ud yake huci kamar ya daki abu, sai daya huce sannan ya fad’a mata Ammi da Ummii zasu tafi Maiduguri nan da sati d’aya. “Amma kana ganin har yanzu Kaala Abdi bai ji labarin an sameta ba?” Laila ta tambayeshi. “Babu wanda ya fitar da maganar, jiya na kirashi har muka gaisa da Abul amma ban ga alamar ya sani ba.” Kad’a kai Laila tayi domin itama jiya ta kirashi don taji lafiyar Abul yake fad’a mata ana ganin alamun nasara a tattare dashi, sai dai ita ta daina cewa a bata yaron su gaisa dalilin bak’ak’en maganganun da yake fad’a mata wanda suke damunta. “Ni zan tafi, kina buk’atar wani abu ne?” Mas’ud ya tambayeta yana tashi tsaye. “Babu komai, Alhamdulillah. Amma don Allah ka daina zuwa gidan nan da daddare saboda kana shiga hakk’in matarka. Ka duba yanzu k’arfe goma da kwata wanda yaci ace har kun yi bacci amma kana nan. Ko ni a daa bana son Haydar yayi dare.” “Itama tun last week take fushi dani bata kulani wai nafi fifitaki akan ita matata. Tace idan naga dama in dawo gidanki da zama ta yafeni.” Ya kwashe da dariya ba tare da ya ga halin da Laila ta shiga ba daga jin kalamanshi. Tsagaita dariyarsa yayi yana duban Laila da take kallonshi fuskarta cike da damuwa tace, “You are making a huge mistake ba tare da ka sani ba Mas’ud, kuma matarka gaskiya take fad’a maka ban ga laifinta ba.” Tana gama maganar yayi saurin taran numfashinta yace, “Ni ban ma san ya aka yi bakina ya su6uce na fad’a miki ba. Sai da safe.” Yayi hanyar k’ofa zai fita Laila ta dakatar dashi suka fuskanci juna. “Ina sonka Mas’ud shiyasa zan fad’a maka gaskiya, ina kuma sonka shiyasa zan ku6utar da kai daga fushin Allah. Wallahi kafin Allah ya tambayeka yanda kake kula dani sai ya fara tambayarka yanda ka kula da iyalinka daya baka amanarsu a hannunka. Bata da kowa sai kai, a k’arkashinka take, ita d’in nauyinka ce top priority Mas’ud, ni kuma on the other hand Haydar ne mai mini duk wannan dawainiyar ba tare da ya fara yiwa kowa ba sai ni. So karka 6ata rayuwar aurenka don neman faranta mini, kar kuma ka wofintar da amanar da Allah ya baka don kana sona, domin kuwa ita ta fini matsayi a gurinka a idon Allah. I’m your sister ita kuma matarka ce wacce aka halicceta daga hakarkarinka. Ina lura kuna yawan fad’a da ita wanda yawanci duk a kaina ne saboda irin fifitani da kake yi a kanta, wallahi dole tayi fushi saboda tafi buk’atar ta samu soyayya da kulawa daga gareka sama dani. She deserve your love, time and affection more than me, karka 6ata rayuwar aurenka a kaina don bazan ta6a son hakan ba. Please ka kula da matarka kar fushin Allah ya sauk’a a kanka, please Mas’ud.” Laila ta k’arisa maganan tana kamo hannunshi cikin son ya d’auki maganarta yayin da shi kuma yake kallonta baya ko kiftawa can yace, “Kin yi gaskiya and Insha Allah zan yi k’ok’arin in gyara kuskurena. But, Kalti wannan shine babban reason d’in daya hanani aure tun shekarun baya, nasan ba kowacce mace bace zata ga yanda nake baki kulawa mu zauna lafiya ba, she will want me all by herself ba tare dana had’ata da kowa ba. And hakan ba zai yiwu ba saboda dani dake babu mai rabamu saboda a tare muka tashi muke kula da junanmu sama da kowa a gidanmu. Zan gyara and thank you.” Yana fad’in hakan ya zare hannunsa daga nata ya fita daga gidan. Ajiyan zuciya Laila tayi kana ta koma ta zauna taci gaba da tunanin Haydar da kuma halin da take ciki kamar yanda ta saba kullum, wani mugun kewarshi take ji har tana tunanin muddin ya kai wani lokaci bai dawo ba zata iya shiga halin rashin lafiya mai tsanani wanda a yanzu ma dauriya take yi a gaban mutane, amma idan ta kad’aice sai ta zubar da hawaye musamman in ta zo bacci. Haydar ya samu gurbi mai yawan gaske a zuciyarta ba tare da ta gane ba sai data rasashi. Ashe haka take sonshi? Sannan ina zata sameshi? Ya za’a yi ta gyara duk zaman da suka yi tana cutar dashi? Kamar wacce aka tsikara ta tashi tsaye ta shige d’akinta ta d’auki wayarta ta danna kiran wani number, “Laila!”Shine abunda aka fara fad’i cikin rashin yarda da kuma mamaki. “Ka fad’awa Mas’ud cewa kana son neman Haydar duk inda ya shiga, idan da gaske kake yi I will help, amma idan ka kuskura ka munafurceni ko kad’an ne wallahi, wallahi sai na watsa videos da pictures d’inka kai da Jamila, a nan ne mutanen duniya zasu gane wanene kai. So what do you say?” Yawu Alhaji Abdul ya had’iye mai kauri cikin fargaba, domin shi har yanzu yana mamakin dalilin da ya hanasu tona mishi asiri duk da cutar da yayi musu. A yanzu da yake neman gyara kuskurenshi he’ll never crossed the line again, har ya samu Haydar ya kuma nemi gafararsa saboda yana son k’aninshi tun lokacin da yaji labari a gurin babanshi cewa yana da k’ani ko k’anwa. “Ina son baki hak’uri amma nasan hak’uri yayi kad’an akan abunda na miki, sai dai zan nemi yafiyarki idan zaki iya yafe mini.” “Baka bani amsa ba.” Laila ta katseshi saboda ta gaji da surutunsa. “Na yarda.” Ya amsa mata kana ta fad’a mishi ya zo ya sameta a gida gobe da rana. Tana gama wayar ta koma falo ta kulle gidan wanda a yanzu take jin ya mata girma ita d’aya. Ina ma Haydar ya dawo su zauna su kad’ai! D’akinta ta shiga ta rage kayan jikinta sannan ta kwanta tana shinshinar kayan da Haydar ya cire a ranar da zai tafi. Hawaye masu zafi suka gangaro kan k’uncinta har na wani lokaci mai tsawo kafin bacci 6arawo ya saceta. Washe gari da rana Alhaji Abdul ya isa gidan a wata Taxi wacce ta tsaya tana jiranshi a waje, maigadi na ganinshi ya bud’e mishi k’ofa kana ya nuna mishi wasu fararen kujeru biyu a can gefe yace ya zauna Hajiya na fitowa, wato kenan ba zai shiga cikin gidan ba. Yana zaune amma zuciyarshi na d’ar-d’ar domin ba wai ya gama yarda da Laila bane, zai iya yiwuwa had’a baki tayi da Madu don ya ritsashi a gidanta amma haka ya daure ya zo domin shine mai neman taimakonta. Ya kai minti biyar a zaune sannan Laila ta fito jikinta sanye da hijab har k’asa fuskarta babu annuri ko kwalliya ko kad’an. A can nesa dashi ta zauna kana ta dubeshi tana jinjina k’ok’arin Madu wajen lahantashi da ya kusa yayi, wanda har yanzu goshinsa a rufe take da bandage sannan hannunsa a d’aure yake bai warke ba. “An wuni lafiya?” Ya fara aika mata gaisuwa wanda ta share kamar bata ji ba. “Ta yaya zaka nemoshi?” Shine abunda ya fara fitowa daga bakinta tana tsareshi da ido. “Shiyasa nake buk’atar taimakonku domin ni ban san ina zai iya zuwa ba, ina kuke tunanin zai je?” Shima ya mayar mata da tambaya. “Duk inda muke tsammanin zai je baya nan.” Shiru Alhaji Abdul yayi yana tunani sannan can yace, “Menene ainihin abunda ya tunzurashi ya tafi? Tarihin mahaifiyarshi ce ko kuma wani abun ne daban? I need to know.” Laila ta tashi tsaye a fusace ta dubeshi tace, “That’s none of your business, idan zaka yi abunda kace zaka yi kayi in kuma dama k’arya kake yi ka fita mini a gida.” A take a lokacin kuma fara dana sanin sauraronshi tun farko, domin sai a yanzu taji baza ta iya yarda dashi ba har abada. “Laila ki saurareni, wallahi yanda kike son Haydar ya dawo haka nima nake son ya dawo. Ki zauna in fad’a miki abunda baki sani ba a kaina. Kiyi hak’uri.” Yayi maganar a sanyaye cikin lallashi. Zama tayi bayan ta mishi wani mugun kallo kana tace, “Ina jinka” “Bayan an bayar da aurenki ga Aliyu Rufa’i Babana ya turani America na je na k’arasa karatuna, sanin cewa ko na dawo bazan sameki ba yasa nayi zamana a can ban dawo ba sai dana samu labarin mijinki ya rasu. Kafin nan ina son ki san irin relationship d’in da yake tsakanina da mahaifina. Baba yafi mahaifiyata sona sannan yafi kula dani da kuma bani lokacinsa fiye da ita. Hakan yasa na tashi nima bana son 6acin ranshi wanda a dalilin hakan nayi hak’uri na barwa Aliyu Rufa’i ke, na kuma bar muku k’asar gabad’aya. Wallahi Laila in ba don Ina gudun 6acin ran Babana ba daa a wancan lokacin na yiwa Aliyu abunda bazan iya furtawa ba. Bayan na dawo daga America na samu mahaifina a wani irin hali na damuwa wanda na alak’anta hakan da rashin matarsa wato mahaifiyata wacce ta rasu ina America. Ko dana mishi zancen k’ara aure yake fad’a mini ainihin abunda yake damunshi wato na rashin matarsa ta biyu da kuma cikin data tafi dashi na wata bakwai. Nayi mamakin yanda ban ji labarin Babana yayi aure har matar ta gudu ba saboda a lokacin ina Kano ina secondary school, kenan an 6oye mini maganar ne. It turns out lokacin da mahaifiyata take gadon ajalinta ta nemi gafarar Baba bayan ta sanar dashi abunda ta aikata ga matarsa wanda hakan yasa ya nisanceta har ta koma ga mahaliccinta bai k’ara zuwa inda take ba. Bayan na samu labarin ni da kaina naci gaba da bincike wanda babu nasara a ciki ko kad’an illa kashe kud’i da muke yi a banza amma ban fasa ba. Nasan mahaifiyata ta cucesu amma ina son in nema mata gafararsu, sannan ina son nima in ganni tare da wani wanda za’a iya kiranshi d’an uwana saboda ni kad’ai iyayena suka haifa na rayu yayin da sauran biyun Allah ya amshi kayansa tun kafin su zo duniya. Sai dai duk da halin da muke ciki ni da mahaifina na rashin masoyanmu bai hanani aikata mugunta a gareki ba tare da iyalinki. Sai gashi Allah ya kamani yasa Haydar da nake yiwa mugunta shine k’anina da nake nema duk tsawon wannan lokacin. Nayi danasani na kuma yi nadama akan duk abubuwan dana muku da kuma wanda nake shirin aikatawa amma Allah bai nufa ba ya tona mini asiri, I hurt someone wanda nake son karewa da dukkan k’arfina and hakan ya koya mini darasi ne kan cewa; abunda baka so kar ka yiwa d’an uwanka, sannan munafurci dodo ne yakan ci mai shi. Bayan Madu ya kawo mini Audio na tarihin Ammi na gane wacece ita domin mahaifina bai rage mini komai ba daga labarin yanda suka had’u, da irin yanda ya samu labarin d’aure maigadinta da aka yi da kuma jinin daya 6ata falonta. Baba kasa hak’uri yayi ya saka muka kamo hanyar Kano a ranar ba tare dana huta ba, a hanya na fad’awa Baba abunda na muku har da k’anina Haydar ban 6oye mishi komai ba. Baba yayi fushi dani, fushi mai tsanani saboda ya sha mini nasiha kan cewa kar in cuci d’an Adam da arzik’in da Allah ya bani wanda shi ya tara ya dank’a mini ragamar dukiyar a hannuna bayan na dawo daga America. Muna shigowa gari a gidanku muka sauk’a har Madu ya samu daman mini haka. Laila har yanzu Baba bai daina fushi dani ba, saboda yana ganin a dalilina d’anshi ya k’ara shiga duniya. Ina son nemo Haydar ina son nunawa Baba cewa ni bazan ta6a cutar da jininshi ba.” Ya k’arishe maganan yana kawar da kanshi kamar wanda baya son Laila ta ga fuskarshi. A sama yaji muryar Laila tana mishi magana, tace, “Haydar yana son tara iyali tunda ya taso ya ganshi shi kad’ai, hakan yasa ya nemi in haihu ni kuma na nuna sam ba haka ba. A hakan na samu ciki na kuma nemi zubarwa har na tafi asibiti ya bini a baya, ya zo ya samu ana mini scanning sai ya d’auka na zubar da cikin ne yayi fushi ya tafi gidan Ummii, a nan kuma ya tarar da labarin mahaifiyarsa wanda bai mishi dad’i ba wanda wad’annan abubuwa biyun ne suka mishi yawa ya tafi.” “Ciki kike dashi?” Abun da Alhaji Abdul ya fara fad’i kenan cikin tsananin mamaki yana duban Laila. Gyad’a mishi kai kawai tayi ranta a 6ace domin bata ga abun mamaki a ciki ba. “Kuma baki zubar ba har yanzu yana jikinki?” Ya k’ara mata wata tambayar yana gyara zamanshi. “Eh ban zubar ba, kuma daa a yanzu zan samu seconds uku tare da Haydar abunda zan fad’a mishi kenan ya dawo gareni don nasan ba zai ta6a gudun d’ansa ba.” “Alhamdulillah!” Shine abunda Alhaji Abdul yayi ta maimaitawa idanunshi na tara hawaye yana kallon Laila wacce itace wannan karon take kallonshi cike da mamaki. Wani irin so yake yiwa Haydar? Kafin tayi magana taga ya d’auko wayarsa a aljihu ya kira Babanshi wanda shi ya fara magana amma bata ji ba, sai ji tayi Alhaji Abdul na cewa, “Ba’a sameshi ba Baba. Amma zan maka albishir ne ko hankalinka zai kwanta kad’an. Matarsa Laila na d’auke da ciki, zaka ga jikanka Baba.” Bata ji me Baban ya fad’a ba sai gani tayi ya mik’o mata waya yana murmushi amma ta k’i ta amsa. Duk yanda yayi da ita bata kar6a ba don wani kunya da kuma haushin Alhaji Abdul d’in take ji na saurin sanar da Baba batun cikinta da yayi. “Baba yace zai zo ya dubaki anjima tunda kin k’i kar6an wayar.” Ya fad’i hakan murna fal a fuskarsa wanda Laila kuma take jin kamar ta kifeshi da mari. “Don Allah ka bashi hak’uri saboda kwanan nan bana ganewa kaina sannan a yanzu ni ba matar d’ansa bane. Damuwata da kuma burina a yanzu shine a samu Haydar.” Gyad’a kai Alhaji Abdul yayi sannan yace, “Shin akwai wani programme da Haydar yake yawan gani wanda baya wucesa?” Tunani mai zurfi Laila tayi sannan ta d’ago da kanta fuskarta cike da annuri idanunta na tara kwalla, cikin sanyin murya tace, “Meyasa ban yi tunanin hakan ba? Wannan shine hanya mafi sauki da zan aikawa Haydar sak’o. Akwai wa’azin wani Malami da yake kallo kowanne sati ranar asabar. Akwai.”
Mum Fateey 👌



