Hausa novels

Asanadin Makwabtaka Book 2 Page 6 Complete Novel

*ASM Bk2006*

 

_Destiny may be delayed but cannot be changed…._

 

 

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

 

 

 

…….bayan sun baro gidan Abbas a wani Shopping complex ya tsaya dasu yace ma Fanan suje suyi shopping ta amsa mashi da owk ta bud’e Motar ta fita shima bud’e kopar side d’inshi yay har zai fita ya dakata ya juya ya kalli Fatuu dake zaune suka had’a ido,

“Ki fito zamuyi shopping” ya fad’a da cool voice d’inshi, girgiza mashi kai tay a hankali tace “ni bani buk’atar komae” wani kallo ya bita dashi da sauri ta sunkuyar da kanta kirjinta na bugawa da sauri da sauri,

“Let’s go Zaraah” wani yamm taji a jikinta duk cikin masu kiranta da Zarah ba wanda ya kai shi iya Fad’a gashi da wani irin sauti mai dad’i sunan ke fita, d’agowa tay suka had’a ido kawae sai ta Fara yamutsa fuska tana ta6e baki alamar zatayi kuka dama har yanzu bata bar ta6e baki ba in zatayi kuka tun yarinta, still yay yana bin ta da ido sai far far take da ido don kada kwallan su zubo mata kawae sai yay wani murmushin gefen baki ya d’an girgiza kai ya fice daga Motar, zagayawa yay side d’in da Fanan take tsaye tana amsa waya tana ganinshi tace ma wanda suke wayan zata kira daga baya tay rejecting call d’in, ganin ba Fatuu tace mashi Zarah fa yace zuje kawae zasu d’aukar mata abunda ya dace ta amsa da Ok, sosae sukai shopping bayan sun gama aka zuba masu a shopping bags aka biyo su dasu, jakar da suka siya ma Fatuu kaya Fanan ta bud’e baya gefenta ta aje sauran kuma aka saka masu a boot daga haka suka shige Motan suka tafi,suna kan hanya jin shirun Fatun yay yawa yasa Fanan ta kira sunanta tana jinta tay mata shiru hakan yasa ta juya baya ta kalleta ganin ta langa6ar da kai gefe yasa tay tunanin bacci take, suna k’arasowa kopar gidansu ta bud’e Motar ta fita Fanan ma ta fito ganin bata d’auki kayan ba yasa ta tsaidata ta bud’e bayan ta d’aukko mata don tayi tunanin ko bata san nata bane har da ledan kayan da khairat ta bata, tana tsayen kafin Fanan ta d’aukko mata glass d’in gaban ya sauka Slowly, da sauri ta kai idonta wurin suka had’a ido dashi da yake akwae wuta globe din gaban shagon kawu Amadu ya haske wurin, ya d’an kwantar da kanshi jikin headrest kasa jure ma kallonshi tay ta sadda kanta k’asa lokacin Fanan ta mik’o mata jaka guda ita ta ruke mata guda tace suje, har lokacin idonshi na akanta ta juya kawae sai taji kaman bata kyauta ba don bai ta6a yi mata abu ba ba tare data gode mashi ba kuma hakan hud’ubar gwaggo ce, tsayawa tay Fanan ta juyo kafin tayi mata Magana tace mata zatai mashi godiya ne ta amsa da Ok tay gaba abunta, a hankali ta nufi Motar kamar wadda kwae ya fashe mawa a ciki ta tsaya gaban kopar tana kallonshi ba tare data ce mashi komae ba shima kuma baida niyyar tanka mata can ta bud’e baki da k’yar tace “Nagode Allah ya saka da Alkhairi” shiru kaman bazai tanka ba sai kuma taji yace “Ameen” k’okarin juyawa ta tafi ta fara yi taji yace “Zaraah?” wani mugun bugu k’irjinta yai dammn ta juyo a d’arare ta kalleshi gently yace “kina da wani problem ne?” a hankali ta girgiza mashi kai alamar a’a,

“Then why d change?” wani irin harbawa zuciyarta take ita tsoronta ma kar Fanan ta fito su tutsiyeta tare har su gano abunda ke damunta don a yadda take ji komae zai iya faruwa, “am talking to u zaraah why u look different?” baki na rawa kaman zatai kuka tace “b..ba..banjin dad’in jikina ne ba kasan ban Lafiya ba” shiru yay yana nazarin Maganar calmly yace “Ok i understand, ki fad’a ma grandma d’inki zamuje hospital tomorrow” da sauri ta d’ago ta kalleshi tace “ai ba ciwon Asibiti bane Addu’a ake man kuma anyo man ina sha” ta kai Maganar tana sussuna kai k’asa don wani irin kuka ne ke taho mata, Sigh yay yace mata zata iya tafiya Allah ya bata Lafiya da sauri ta amsa da Amin ta juya a harhard’e ta nufi gidan tana shiga zaure ta lafe a jikin bango ta tura gyalenta a baki ta fashe da kuka,can zuciyarta ta raya mata kar Fanan ta fito ta ganta haka da sauri ta goge kwallan ta d’auki ledan ta shiga cikin gidan, a bakin kopar Parlor ta hangi takalman Fanan ta jiyo muryarta ita da gwaggo hakan yasa ta aje ledar a gefe ta nufi hanyar toilet, jin motsi yasa daga cikin falon gwaggo ta tambayi waye tace itace zata shiga toilet ne, koda ta shiga kukan taci gaba da yi, ita kanta yanzu tsoron fad’i ma Haisam d’in take game da son nashi don ta yarda da Maganar Haulat ta zata jefa kanta a wata Matsalar ne,har saida taji gwaggo ta rako Fanan suna sallama sannan bayan ta tafi ta wanke fuskarta sosae ta d’auro Alwala ta fito cikin sa’a tana fitowa taga gwaggo ta kabbara sallar isha hakan yayi mata dad’i don bata son ta gano kukan da tay, itama sallar taje d’aki tayi bayan ta gama sosae tayi Addu’a kan halin da take ciki daga baya ta kwanta kan abun sallan, tana kwancen gwaggo ta d’aga labulen ta kira sunanta tace ko har ta kwanta, d’an d’ago da kanta tay tace mata eh ta gaji ne sosae bacci take son yi tace “to bazaki ci Abinci bane?” d’aga mata kai tay tace “eh banjin yunwa munci Abinci” jinjina kai tay tace to ta tashi ta hau gado kuma ta tabbatar tayi Addu’a ta amsa mata da to ta juya ta tafi, mik’ewa tay ta cire kayan jikinta har zata nufi gado taji kuma ruwa take son ta watsa ta nufi toilet bayan ta yafa mayafi a kanta, tun bayan data fito ta saka kayan bacci ta haye gado ta dasa sana’ar tunane tunanenta, tabbas tana son ya Handsome sosae to amman ta gane ba samunshi fa zatayi ba matuk’ar yana tare da Fanan yanzu ya zatayi, nan take ta gano bata da wata mafita da ya wuce tay hakuri dashi tayi yak’i da zuciyarta kaman yadda Haulat tace mata, yin wannan tunanin yasa ta saukko daga kan gado ta d’aukko Al’qurani ta fara karantawa acikin zuciyarta bayan wani lokaci ta rufe ta d’aga hannuwa harda kwallanta ta rok’i Allah daya cire mata son Ya Handsome, bayan ta gama ta mayar dashi cikin jakarta ta koma kan gado tay lamo tana cigaba da zubar da kwalla a haka bacci yay awon gaba da ita.

 

Washe gari data tashi ba laifi ta d’an ji k’arfin jikinta bayan tayi breakfast ta fara ayyukanta gwaggo nata jin dad’i duk in suka had’a ido sai tay mata d’an mumushi,da yake aikin safe take Fatun ta tambayeta mi zata dafa kafin ta dawo tace ayyukan bazasu yi mata yawa ba kuwa ko ta samu wani abun taci in ta dawo sai tayi Fatun tace ba komae zata iya, ta fad’i mata abunda zata dafa kafin ta tafi, tana ta ayyukanta tana tunane tunane har ta gama komae tayi wanka tay kwanciyarta, rashin zuwan Fanan ba k’aramin dad’i yay mata ba don ta fahimci duk in ta gansu su biyun k’ara mata ciwon suke,k’arfe biyu da wani abu gwaggo ta dawo lokacin Fatuu nata bacci abunta ba laifi yau ta samu bacci sosae bata tasheta ba ta wuce d’aki ta kimtsa kafin ta fito ta nufi Kitchen sosae taji dad’in ganin Fatun tayi Abincin lafiya lou ga Kitchen din tsaf a cikin ranta take godiya ga Allah da ya amsa addu’arta da take ma Fatun, sai wurin karfe ukku ta farka tayi mamakin irin baccin da tayi da har bata san gwaggo ta dawo ba, ana kiran sallar la’asar ta watsa ruwa tay salla ta fara shirin zuwa islamiyya, bayan ta gama ta lek’a d’akin gwaggo tace mata ta tafi islamiyya tana washe baki ta hau yi mata Addu’oi har da fitowa wai bari tayi ma yar autarta rakiya waje ta rungumo kafad’unta Fatun tasa dariyar da yaushe rabon da gwaggon taga tayi ta, Lokacin data je Haulat bata kai ga zuwa ba nan yan ajin suka hau yi mata ya jiki don Haulat ta sanar da rashin lafiyan nata, lokacin da Haulat ta shigo ajin suna had’a ido da Fatun ta nufeta da yar sassarfa ta duk’a ta dafata tana washe baki tace ta samu sauk’i kenan ta jinjina mata kai kawae, zama tay sosae taci gaba da k’arfafa mata guiwar tayi hakuri ta cire shi daga ranta ba tare da wani ya ji maganar da suke ba a haka har Malam ya shigo, bayan an tashi ma akan hanyarsu ta dawowa shawarwari taci gaba da bata ita dae saidae ta d’aga mata kai kawae duk da tana son amfani da shawarwarin saidae har lokacin ba abunda ya canja na daga son ya Handsome a cikin zuciyarta, bayan ta koma gidane gwaggo ke fad’i mata Fanan tazo tace da daddare zata dawo tace to kawae.

 

Gaba d’aya satin guje ma duk wani abu da zai kaita gidan Hajiya take in gwaggo tace taje da ta fito sai ta wuce gidansu Haulat, Fanan har Maganar rashin zuwan nata tayi don a tunaninta ta samu sauk’i tace mata islamiyya take zuwa da yamma da safe kuma ita ke aikin gidan, sosae ta fahimceta bata sa komae a ranta ba ita taci gaba da zuwa, ba laifi kuma Fatun ta d’an k’ara sakar mata jiki, a cikin satin Haisam ya kaita gidansu Khairat ta wuni bata samu kara zuwa gidansu Nana ba amman ita tazo harda k’annenta yan mata guda biyu suka kawo mata kaya harda atampopi don ranar Monday zata tafi, Feenah ma tazo itama ta kawo mata abubuwa d’inkakkun Material masu kyau da tsada kala biyu sai kayan kamshi su humra da kullacca har gidansu Fatuu taje ta k’ara yi mata ya jiki suka gaisa da gwaggo Abdul yaji dad’in ganinta tana ta mashi dariya har yana cewa da yasan ta samu sauk’i da yazo da tab d’inshi sun yi game, Feenah tace shi damuwarshi kenan game ko duk suka yi dariya gwaggo tace ina ruwan yaro, daga baya suka yi masu sallama suka tafi Fatuu ta rako su kopar gida, Ranar Friday da safe gaba d’aya Haisam da Fanan da Hajiya suka tafi Daura suka zaga dangi Fanan ta gaisa da su sai washe gari da yamma suka baro daurar suka biya Ajiwa Dam sosae wurin ya burge Fanan Hajiya ma taji dad’in zuwa wurin Fanan tay masu hotuna ba kamar ita da Haisam sai bayan Magrib suka dawo ta gaji sosae shiyasa bata je gidansu Fatuu ba sai Washe gari lahadi bayan sun gama breakfast ta shirya ta nufi gidan Harda tsarabar Daura, lokacin data je Fatuu bata nan tana islamiyya hira suka d’anyi da gwaggo tay mata godiyar tsaraba, Fanan d’in tace in ta dawo ace mata tana nemanta gwaggo tace zata fad’i mata da ta dawo, bayan Fatun ta dawo ta canja kaya gwaggo ta kirata ta sanar da ita sak’on Fanan na tana son ganinta har saida ta d’anyi jimm don rabonta da gidan Hajiya tun wanccan satin haka haisam ma rabon data sanya shi a idanunta tunda suka je gidan Abbas sosae take guje ma ganinshi ba kuma don bata son ganinshin ba, bayan taci Abinci tayi sallar Azahar Gwaggo tace mata taje kar Fanan d’in taita jiranta ba yadda ta iya dole tace to bayan ta fito zata tafi ne ta kirata ta bata wata leda dake k’ulle tace ta kai mata, tunda ta tunkari gidan kirjinta ke bugawa hakanan ta daure ta k’arasa har Officer nace mata kwana biyu dama tana gari ta amsa mashi da eh kawae ta shige, da zata wuce har saida ta kalli Corridor d’in shiga part d’in Haisam ta d’an girgiza kai tunowa da baya yanzu shi kanshi mai part d’in ma gudunshi take rayuwa kenan, lokacin data shiga Falon Hajiya gaba d’aya suna zaune harda shi Haisam d’in kamar ko yaushe dai Fanan na manne dashi jikinta sanye da rigar shan iska wadda iyakarta guiwa santala santalan k’afafunta dake jajur a waje kanta a bud’e tayi parking gashinta a tsakiya yayinda daga k’asa wani ke zube, shima Haisam riga armless ce ajikinshi da wando 3 quarter, tana yin sallama duk suka juya suka kalleta Fanan ta mik’e zaune tana mik’a mata hannu tana mata murmushi nufarta tay tana zuwa ta kama hannunta ta zaunar da ita gefenta, gaida Hajiya dake kallonta tay tace “Oh Fateema k’iri k’iri dae kinyi mana yaji ko?” d’an guntun Murmushi tay a sanyaye tace “a’a Hajiya na koma islamiyya ne da safe kuma dana yi ayyuka na gama sai lokaci ya k’ure” da k’yar ta k’arasa Maganar saboda fargaba, Hajiyar tace “ai lokaci kam na gudu wllh Allah ubangiji yasa mudace” ita da Fanan suka amsa da Amin, d’an juyawa tay ta kalli Haisam da idonshi na akan tv ta gaidashi shiru bai amsa ba saida Fanan tace mashi Zarah na gaidashi sannan ya d’an kalleta ya amsa kafin ya mayar da idon ta lura da yadda ya amsa mata duk sai taji dama bata zo ba kaman ma ta mik’e ta tafi hakanan dae ta daure dama ita yarinya ce mai tsananin k’arfin hali ba k’aramin abu ne kesata raunin zuciya ba, mik’a ma Fanan sak’on gwaggo tay ta amsa da farinciki tun kafin ma taga miye aciki lokacin data bud’e kayan Fulani ne Navy blue riga da zani da kallabi harda mayafi sai abubuwan ado su sark’a yan hannu harda na sawa a kai,kayan sun yi kyau sosae da ganinsu masu ingaci ne ba tagajan tagajan ba, su kansu kayan sun sak’u sosae musamman gwaggo ta kira kawu shi6ado ta fad’a mashi tana son kayan shi kuma yaba wani abokinshi sautu ya aiko mashi dasu jiya kawun ya bada sak’on Mota aka kawo ma gwaggon, wata k’arar farinciki Fanan tay ta mik’e tana nuna masu abunda aka aiko matan hajiya na dariya ta shiga yabawa cike da zumud’i ta sungumi ledar kayan tace bari taje ta gwado Hajiya ma ta mik’e tana Fad’in bari ta biyota tana son shiga toilet, ya rage daga ita sai shi a falon kowa yayi tsit gashi duk ta sha jinin jikinta kasancewar akan kujera d’aya suke, a hankali ta d’an juyo zata saci kallonshi karaf suka had’a ido dashi da alama dama kallonta yake, idasa d’agowa tay tana kallonshi tana motsa baki kaman zata ce wani abu sai kyakkyafta ido take still idonshi na akanta yana mata wani kallo ko kyaftawa baiyi hakan yasa duk ta dabarbarce ta fara yamutsa fuska kaman zata yi kuka kawae sai gani tay yay dariya har fararen hakoransa suka bayyana ya dan ta6e baki ya maida idonshi kan tv ita kuma ta sadda kanta k’asa ji take kaman ta rusa ihu, fitowa Fanan tay cikin kayan Tubarkallah ma sha Allah fad’in kyaun da tay 6ata lokaci ne Hajiya ta taimaka mata tasa komae tay kyau Over harda takalma masu tsini ta sawo ta tunkari Haisam tana cat walk idonshi akanta yana Murmushi Fatuu ma idonta na akanta tana kallonta da d’an Murmushi, tana isowa gaban Haisam ta wani jujjuya tana fari da ido tace “how do i look babe?” dage gira yay slowly yace “like a bride” dariya tasa tace “yeah it’s true am ur bride” tana yin Maganar ta fad’a jikinshi tana dariya shima dariyar yake ta d’auki wayarshi ta fara yi masu selfie duk wannan abun idon Fatuu na akan tv tun sadda ta fad’a mashi ji tay bazata iya cigaba da zama ba tana niyyar mik’ewa Fanan ta nufota da wayar ta zauna gefenta ta d’aga alamar itama hoton zatayi da ita, ba yadda Fatuu ta iya dole ta tsaya ganin bata murmushi fanan tace “Smile Zarah” dole haka ta daure ta rink’a yin murmushin yak’e ta rink’a d’aukarsu, can Fatun tace mata tafiya zatayi lokacin islamiyya ya kusa dama gwaggo ce tace tana nemanta tace eh ta mik’e hannunta cikin na Fatun ta jata d’akin Hajiya bayan taba Haisam wayarshi, lokacin da suka shiga Hajiya na kwance akan gado Fanan ta nuna mata stool tace ta zauna, kit d’in kayan gyaran gashinta ta d’aukko ta aje a gaban Fatun ta d’aukko wata babbar leda itama ta aje a gabanta tace gasu nan tana tunanin kayan ciki zasu yi mata tayi amfani dasu ta janyo k’aton trolley d’inta ta bud’e tace ta k’ara dubawa in akwae abunda take so karta ji komae ta d’aukka, gaba d’aya Fatuu ji tay ta rasa mik’e mata dad’i kawae sai ta fashe mata da kuka, (Allah sarki Fanan baki san Fatuu ba wannan take bukata a wurinki ba), Sosae Fanan ta rud’e ta hau lallashinta tana cewa tayi shiru ai ba abun kuka bane Hajiya dake kwance ma tace mata tayi shiru ai ba wani abu bane tunda ita ta bata, da kyar ta daina kukan fatun tace mata ba abunda take so suma wanda ta d’aukkar matan ta barsu Fanan d’in tace a’a ai ita ta bata, ba yadda ta iya dole ta d’auki kayan harda kit d’in tay mata godiya harda Hajiya, tare suka fito ta rik’e mata kit d’in har lokacin Haisam na zaune Fanan tace mashi zata je ta dawo ya d’aga mata kai kawae, akan hanyarsu Fanan d’in ke ce mata zatai missing d’inta sosae amman dae ai zata zo bikinsu ko fatun ta d’aga mata kai kawae,lokacin da suka isa gidan gwaggo ta ga abubuwan data ba Fatun sosae tay mata godiya had’i da Addu’oi tay fatan Allah ya nuna masu Aurensu lafiya, bayan wani lokaci tay mata sallama gwaggon tace zata shigo su k’ara yin sallama da daddare, bayan sallan isha gwaggo taja Fatuu ba don taso ba suka je gidan, Washe gari da Safe misalin karfe takwas da wasu mintuna Fanan ta rafka sallama tana sanye da skinny jeans da riga long sleeve ta d’an saukko mata kanta ta yafa mayafi ta fito a Baturiyarta, fitowa gwaggo tay daga cikin Kitchen tana ganinta ta nufeta tana fadin “y’ata har an fito” tace mata eh zasu tafi, gwaggo tace “to Allah ubangiji ya tsare, mungode, mungode Allah ya k’arawa rayuwa Albarka yasa ki gama da iyayenki lafiya, ki gaida mana da yan gidan sai munzo biki in sha Allah” d’an side hug tay ma gwaggon tana Murmushi tace “nima nagode da kulawa granny” suna cikin haka Fatuu ta fito jikinta sanye da doguwar riga kanta ba kallabi duk maganganun da suke tana ji kasa jurewa tay ta fito Fanan na ganinta ta saki gwaggo ta bud’a mata hannuwa, nufarsu tay tana zuwa ta fad’a jikinta idanuwanta sun cicciko da kwalla har sun fara zubowa, d’agota fanan tay ta shiga share mata tana Fad’in ta daina kuka ai zasu ci gaba da communicating kaman da, horn d’in da akai a waje yasa ta saki Fatun tace babe na jiranta tare zasu tafi ta juya suka rakota bakin kopa anan suka tsaya don ita Fatuu bata da kallabi ita kuma gwaggo ba mayafi, bud’e kopar Motar Haisam yay shima yayi gayun k’ananan kaya ya gaida gwaggo tay mashi Allah ya tsare ita kuwa Fatuu kasa ce mashi komae tay ta bishi da ido har ya koma Fanan na d’aga masu hannu suma suna d’aga mata ta bud’e gaban Motar ta shige yaja suka tafi, wani irin sanyi jikin Fatuu yay gwaggo ma har ta fara jin kewarta, juyawa sukai suka koma cikin gidan…….

 

Wacece Fanan? Ya akai suka fara Soyayya da Haisam?

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 400 ne za’a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za’a turo shedar biya ta wad’annan nos din 09013804524 ko 08169856268._

Asanadin Makwabtaka Book 2 Complete Novel Txt

Back to top button