Fentin Zina Page 26 Hausa Novel
🙅♀️FENTIN ZINA🙆♀️🙅♀️EESHERT ADAMUPAGE 26.*****Kiyi hakuri inna ba nufina in bata miki rai ba, cewar fateema tana mai kaskantar da kai.Hum Kasai inna tace ta kashe wayar ta wullar saman gado tayi nufin fita sai tayi ido hudu da baba malam take ta dan dirice ta fara kame kame tana sosa keya.Irin kallon da yake jifanta dashi kadai ya isa ya sanar da ita yaji duk abunda take cewa ta kakalo murmushi tace malam ashe ka shigo.Baice komai ba ya tako ya zauna saman gado yace zauna, ya nuna mata gefen gadon kusa da shi.Ba musu ta zauna sai dai gabanta na faduwa.Rukayya yaushe kika sauya hali ne ban sani ba? Ko da can haka kike sanine kawai ban yi ba?..Ta soma kame kame tace toh…tohh malam me kuma akace nayi.Rukayya zan miki kashedi na karshe akan Ameenatu, wallahi summa tallahi kika kuskura kika kara kiran koda fateema ce kina fadin kalamai marasa dadin ji akan ita Ameenatu idan ranki yayi dubu toh zai baci, ke a tunaninki abunda ya faru a shekarun baya zai tafi a bulus ne? Ya girgiza kai ya kara da cewa ai kama-tudinu-tudan don haka lissafi ya ragewa mai shiga rijiya. Yana gama fadin hakaya mike yayi waje ko waiwayowa baiyi ba, inna ko tabe baki tayi daga bisani ta tallabi kumatunta da duka hannayenta cikin kunar rai tace, me malam yake nufi da maganar sane kam. Taja kwafa ta kada kai.*****An sallami Ameena sun koma gida saidai dada ta kafa ta tsare lallai Ameena bazata kara zama a part din mama rabi ba don haka direct part dinta ta wuce da ita sai fateema ce da mama rabi suka biyo ta da sauran kayakinta nan part din.Kulawa sosai Ameena take samu a duka bangarorin daga dada har mama rabi da kuma fateema sai tayi kiba tayi fresh ta kara haske kamar ka tabata jini ya zubo.Yau Fateema ta tafi don haka sai take jin kewa sosai dukda sunyi waya da baba malam yace da zarar ta kammala jarabawarta zata dawo har sai lokacin dawowarta yayi su koma tare murna ta shiga yi ta masa godiya sosai ta kuma neman gafar da a kullum bata gajiya.Fateema tuda ta koma sai ta kasance a takure saboda halin da inna ta tsiri nuna mata na daure fuska da kuma saurin fushi abu kadan ta hau fada sai ta fara Allah Allah su zana waec din tayi ta koma JOS din, bata samun wata natsuwa yanzu a gidan nasu da kuma gun mahaifiyar su, duk da ba ita ta aikata laifinba amma sai inna take sauke duk wani fushinta akanta ya zama bata jin dadin gidan sai idan baba malam ya dawo zai kirata suyi hira sosai kafin taje ta kwanta.Haka rayuwa ta cigaba da tafiya a duka bangarorin guda biyu har watan haihuwar Ameena ya tsaya lokacin fateema ta jima da komawa JOS abunta kuma har sannan inna bata sauko ba don har mama rabi ta mata magana saita rufe ido ta mata tatas daganan bata sake tuntubar ta ba.*****Yau tunda Ameena ta tashi take jin zazzabi sosai da ciwon kafafu ta sama wajen cinyoyinta sannu a hankali ta soma jin bayanta na rikewa tun tana dauriya har dai ta sanar da dada halin da take ciki, nan take dada ta shiryata ta kira mama rabi dama duk wani abun bukata an tanada shi don haka dugunzuma sukayi sai asibiti ko kafin su isahar ta soma galabaita don tuni jini ya wanke mata kafafunta.Da gudu likitoci suka karbeta suka nufi dakin haihuwa da ita.Bayan dumbin wahalar data sha ta haifi danta na miji fari sol dashi, ai kuwa duk masu makwabtaka da dakin haihuwar nan saida suka shaida anyi sabon haihuwa don yadda jaririn ya dinga callara kuka sai abun yaso baka mamaki.Nurses din suka tsaftace jaririn suka sanya masa kayansa suka nade shi a towel suka mikawa su dada shi.Ameena kuwa wahala bata kare ba don jaririn ya karata sosai ta yadda dole sai an mata dinki, tako sha azaba don sai taji kamar dinkin yama fi zafi.Bayan kamar awowi biyu aka maidata dakin hutu sai a lokacin aka baiwa su dada izinin shiga su ganta.Ita kadaice a dakin suka shigo dada idonta akan Ameena tace sannu ‘yar nan wannan katon yaro haka ai dole dama nasan sai kin karu, yaya jikin babu inda kike jin yana miki ciwo ko?.Ta girgiza kai kanta a kasa tace babu dada sai baccin da nike ji kawai.Allah sarki bari yanzu zasu sallame mu tunda babu wata damuwa sai kiyi wanka kiyi baccin.Kallon fateema dada tayi ta mata nuni da hannu kan taba Ameena yaron.Mika mata tayi Ameena ta karbe shi da bisimillah, kallon farko data masa saida gabanta ya fadi domin sak kamannin mahaifin shi ya dauko, nan ta shiga tofeshi da addu’o’i sai kuma ta manna shi a kirjinta tana jin wani irin soyayya na musamman akan wannan jaririn yana ratsata ta lumshe ido ta budesu ta ci gaba da kallon yaron tana jin dadi yana bin dukkan jijiyoyin jikinta.Mama rabi ta katse ta da cewa idan kin gama kallon dan naki sai mu gaisa.Kunya Ameena taji ya lullubeta sai ta mikawa fateema jaririn tana sunne kai tace yi hakuri mama.Kedai kwantar da hankalinki Ameenatun baba malam ya jikin?Alhamdulillah da sauki sosai mama.Daidai likitar da ta karbi haihuwar ta shigo ta karbi babyn tana furta masha Allah sannu mai jego.Murmushi kawai Ameena tayi likitar ta ci gaba da cewar ga wannan! Ta mikawa mama rabi peper dake hannunta da leda baka mai dauke da magunguna a ciki tace tunda kun biya duka bills dinku kuma babu wata matsala an sallameku zaku iya tafiya gida sai dai kada tayi amfani da ruwa mai zafi wajen wanka duba da cewar tana da hawan jini, sannan yaron ma kada kusa masa ruwan zafi sosai idan kun surka ruwan kada yayi irin zafin nan kafin ku masawanka dashi. Ta maida kallonta kan Ameena tace ki kula da jikinki sosai kada kiyi seatbath da ruwan zafi gara kiyi tsarki dashi, normal ne zaki iya tsarki da ruwan zafi amma banda wanka banda seatbath kinji ko? And yanzu idan kika koma a tafasa ruwan zafi da gishiri a barshi ya dan huce yanda zaki iya amfani dashi sai ki rika tsarki dashi Allah ya bada lafiya.Ameen sukace gaba dayan su nan suka hau shirin tafiya gida.Jego mai kyau Ameena tayi domin dada da mama rabi suna matukar kokari wajen bata duk wata kulawar data face sai tayi kyau abunta ita da jaririnta wanda aka sakawa suna AHMAD ana ce mishi shureim. Gata ta ko ina tana samu don tamkar ba dan gaba da fatiha ba kowa sonsa yake.Inna ce dai har yanzu babu wata hulda a tsakanin su amma baba malam yazo ya dubata a kwanakin can.Ganin innabazata sauko bane yasa dada ta nemi alfarmar a bar mata Ameena a hannunta har sanda zata samu miji tayi aure ba tare da jaa ba baba malam ya amince sai dai yace fateema ta koma gida ai kuwa fateema ta shiga magiya dakyar baba malam ya kara mata lokaci kan lallai da zarar lokacin ya cika ta komo gida, tayi godiya sosai.*****A kwana a tashi yau shureim yake cika shekaru uku a duniya, ya tashi da zazzabi sosai don har suma yayi sau daya, lokacin fateema tazo musu hutu suka shirya suka kaishi asibitin da aka kwantar da ita lokacin ciwonta na farko gurin doctor Anas.Da mutumci ya karbesu kasancewar tun wancan lokacin mutumci ya dan kullu tsakaninsa da fateema.Nurses gida biyu ya Kira ya basu umurnin suje da yaron suyi mishi duk abunda ya dace yana nan zuwa yanzu. Cikeda ladabi suka amsa sukayi waje fateem da Ameena na binsu a baya.A kofar shigowa office din Ameena ta kusa yin karo da wani handsome guy ta Shiga bashI hakurin bata sani bane hankalinta baya jikinta, baija mganar ba ya gyada kai ya tura kofar ya shiga ciki.A’a mutumin yaushe a gari? Aida ko waya zaka mun ko?Kaidai bari kawai wallahi wani daurin aure ne ya kawo ni nan Abba ne ya turo ni in wakilce shi and ga dukkan alamu nima anan za’a daura aurena domin nayi gamo da sahibata anan a yau kuma a yanzu, ya karshe yana dan latsar kasan lebben shi.Imagination looking Anas take bin abokin nashi dashi yana cewa are u kidding?Kai da gaske fa nike maka.Girgiza kai Anas yayi yana cewa toh bani labarin kan ta huce!……….KUYI HAKURI BAMUDA LFY NE DAGA NI HAR YARA NA NAYI IYAKACIN DAURIYA NE KAWAI🙏kunga yau ko editing ban tsaya yi ba zazzabi nike yanzu haka cikin bargo nike typing dinnan, ku daure ku sakani a addu’o’inku🙏EESHERT ADAMUMATAR MAJEEDADI✍️

