Uncategorized

Abban Sojoji Page 48 Book 2 Complete Novel

“`The father Of Soldiers“`

 

Story &  Written 

       By 

      Hafsat Bature

 💋Boss Bature💋

Follow this link to join my tiktok acct 👇

https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1

“What’s it”? Omar ya tambaya yana kallon shi, ganin yarda Omar ke kumshe dariya yasa shi fasa yin maganar ya ɗan ɗaure face ɗinshi yace”omar banason wasa fa pls tell me the truth, Did something happen last night? Naga bed sheet dina duk yayi wani squeezing kamar anyi dambe asaman shi, 

   dariya sosai Omar yayi kafin yace”no ba wani abu just forget about it, na same ka ne kawai a wani yayi na ciwo so na ɗan taimaka maka ne har nasamu bacci ya ɗauke ka,”

  ta6e baki sgr yayi yana kallon shi don bai yarda da abunda ya faɗa mashi ba, hakanan omar bazai tasa shi gaba yana mashi dariya ba just without any reason,

    miƙewa Omar yayi tare da kallon shi yace”bari na sauka down ko kana buƙatar wani abu ne nasa akawo maka”?

  juyawa sgr yayi ya kalli tray din da ke ajiye saman table ɗinshi yace”wannan yarinyar tazo ta tattara wannan kayan,ga bedroom dina ma inaso a gyaramun,”

   “Okey zan faɗa mata, ka huta my man,” 

  Juyawa omar yayi zai fuce har yakai bakin door din ya waiwayo  don ya kalli sgr karaf suka haɗa ido, cikin mamaki yace”Omar nifa wani kallo naga kana min irin kallon jarababben namijin nan……’ ya faɗi yana tsuke mashi fuska,

  Fucewa omar yayi yana ƴar dariya, yamutsa fuska sgr yayi tare da cewa”Omar nason haukata ni, bansan wannan dariyar nashi me yake nufi ba,” yayi maganar tare da kwantar da bayanshi saman lallausar mattress ɗin, kwakkwaran juyi yayi asaman gadon, kai tsaye idonshi ya sauka akan siraran gashin dake zube saman bedsheet dinsa, cikin sauri ya ɗago da kanshi tare da zuba ma gashin ido, mamaki ne ya kamashi taya akai gashin kanshi ya zuba don kuwa yana da tabbacin cewa sumar kanshi bata kakka6a saboda gyaran da take sha, hannun shi yakai a hankali tare da ɗauko siraran gashin guda uku ya zuba masu ido yana kallonsu, dogon gashi ne mai tsayin gaske, sak irin launin sumar kanshi wato dark brown colour, natsuwa yayi yana nazarin gashin, kafin yasanya hannunshi tare da ɗaukar siraran gashin a hannunshi,yunƙuwa yayi tare da miƙewa daga saman gadon, ya nufi gaban dressing mirror dinshi, zama yayi asaman front chair din madubin, sannan ya ajiye siraran gashin asaman shi, hannu yasa tare da tsinko gashin kanshi siriri guda ɗaya, sannan ya ajiye shi a gefen waɗancan sauran guda ukun, within 5 mins ya gane difference ɗin dake tsakanin su,tabbas wannan ba hairs ɗinshi bane to na wanene, asaman bedsheet ɗinshi kuma?  hannu yasa ya ɗauki siraran gashinan guda uku, sannan ya tashi tsaye ya nufi bedside drawer ɗinshi, buɗewa yayi tare da buɗe jotter ɗinshi dake ajiye acikinta, a shafi na farko ya saka siraran gashin sannan ya rufe jotter ɗin, tare da mayar da drwer chest din ya rufe, wuce wa yayi wurin closet ɗinshi domin shirya kanshi,

***********💋 

bayan fitar marshal omar daga part din  Sgr kaitsaye down stairs ya wuce wurin dining area dinsu ya nufa ganin aunty azmee nata faman jera masu breakfast dinsu, tunkan ya ƙaraso ta soma sakar mashi murmushi tana cewa”Omar barka da fitowa fatan ka tashi lafiya,”? 

   fuskarshi asake yace”lafiya lou Alhmdllh,”

   shiru ya ɗanyi kafin yace”am ina wannan yarinyar take ne sehrish”? Har sai da gaban azmee ya fadi rass jin abunda yace,dama tasan saiya tambayeta akan maganar nan,

   murya na rawa tace”bata jin daɗi ne tana a bedroom ɗinta,ni nace mata ta kwanta ta huta shiyasa bata fitowa. Ba…….’

  “Ta sanar dake game da abunda ya faru jiya”? Ya katse ta da tambaya,

   “Eh ta sanar dani komai,” ta fadi adabarbace,

   Omar yace”okey ina son magana da ita, ki ce tazo tasame ni a part ɗina ina jiranta,”

  Cikin sauri ta amsa mashi da toh, sannan ta bar jera abincin da take yi ta wuce ɗakin sehrish,

   A hankali ta tura ƙofar tashiga da sallama, kwance ta same ta sai faman sharar bacci take yi, har lokacin jikinta bai daina yin kerma ba,

   matsawa tayi dab da ita tare da sanya hannu ta ɗan bubbugi kafadarta “Sehrish !!sehrish!!

  Har cikin dodon kunnanta taji kiran a firgice tafarka tare da miƙewa tsaye tana cewa”La’ila ha’ilallah………’ rufe mata baki azmee tayi tare da cewa”ki natsu ni ce” a hankali tashiga sauke ajiyar zuciya tana kallon azmeen da idanunta da suka canza launi saboda bacci,

 Janye hannu azmee tayi daga bakinta sannan tace”Omar ne ke son magana dake yace ki same shi a part ɗinshi yanzu,”

   zare ido sehrish tayi murya na rawa tace”Aunty azmee ni kuma…..na shiga uku….me zai tambaye ni……’. Katse ta azmee tayi tare da cewa”kada ki damu nasan game da allurar nan ne zai tambaye ki, kawai ki fada mashi gaskiya a wuce wurin,” 

   fuskarta tamkar za tayi kuka tace”Aunty azmee ina tsoro fa kada naja ma kaina,”

   girgiza kai azmee tayi tare da cewa”ba wani tsoro omar zai fahimce ki, kina 6ata lokaci fa ki tashi ki tafi,

 Tana kai ƙarshen maganar ta juya ta fuce daga ɗakin, jiki asanyaye sehrish ta sauko daga saman gadon, hannu tasa ta ɗauki hijab ɗinta wadda ta ajiye asaman gadon milk colour ta zura ajikinta,

  Buɗe ƙopar ɗakin tayi ta fito tare da miƙar hanya ta wuce part dinsa, tsayawa tayi daga ƙopar shiga tana ƙoƙarin dai daita natsuwarta,sallama tayi mashi amma shiru ba’a amsa ba, ƙafa tasa tashiga daga ciki,babu kowa a falonsa komai anatse yake sai ƙamshi dake tashi,

   Shiga ciki tayi tare da samun wuri ta tsaya a kusa da royal sofa din dake a kewaye, gabanta sai faɗuwa yake yi kamar mara gaskiya,

    “Ya Allah ka bani ikon amsa tambayar da zaiyi mun,bana son nashiga matsala da kowa acikin gidan nan, nasan zasu iya zargina wayyo Allah na,” ta furta tana faman yarfa hannunta, cike take da zullumin me zai biyo baya,

  tana cikin wannan tsayuwar wayar shi ta shiga ringing a firgice taɗan ja da baya saboda bata tsammaci jin sautin wani abu ba, bin wayar tayi da kallo tana ajiye asaman 3 seater din don anan yabarta,

    katsewa kiran yayi sai ga wani ya kuma shigowa, matsawa tayi a hankali saitin kujerar tana kallon wayar, ranta ne yabata ta ɗaga kiran taji wanene wata’kil kiran gaggawa ne,

   Tamkar ana tunzurata haka taji, hannu takai tare da ɗaukar wayar tayi picking call din tare da karawa a kunannta, tun kafin tayi sallama taji ance”Ya Omar shi ne jiya kace in ka koma zaka kira ni awaya amma naji shiru ko? Muryar hossana ce ke magana,

  Shiru sehrish tayi tana sauraron maganarta,.  

 Acan kuwa jin tsit Omar ɗin yayi mata shiru yasa ta cewa”kana ji na kayi mun shiru ko, Allah idan bakayi magana ba yau ko breakfast bazanyi ba….’ ashagwa6e tayi maganar,

   murmushi sehrish tayi jin yarda yarinyar ke magana, sai a lokacin tace”bashi bane, baya kusa ne,” 

  Jin muryar mace yasa hankali hossana tashi ruƙe qugu tayi dama tana atsaye jikinta nasanye da kayan bacci riga da wando red colour, ta ƙara kara telephone din a kunnanta, tace

  “ƙanwarshi ko budurwarshi ko matarshi wacece ke aciki ? ta tambaya a ƙule, 

   “Matar shi ce,” sehrish ta faɗi cike da zolaya, aikuwa nan take hankalin hossana ya tashi, muryarta tamkar zatayi kuka tashiga kwalama jahad kira tana cewa”Jahad!!Jahad!! ashe dama ya omar yana da aure shine bai fadamana ba,

    Yadda hossana ke kwala mata kira yasa ta fitowa daga kitchen cikin sauri ta nufe ta tana cewa”Hossana lafiya meya faru ne kike kwalamun kira? Ke da waye a waya? Ta tambaya a yayin da take ƙarasawa wurinta,

  duk sehrish ta kasa kunne tana jinsu, 

Cikin shessheƙar kuka hossana tace”Ashe dama ya omar na da aure bai fadamun ba,” 

  Cike da mamaki jahad tace”kai haba wai dagaske? 

  “Eh mana gatanan muna magana awaya,” ta faɗi rai a6ace tana miƙa ma jahad telephone ɗin,,

  Hannu jahad tasanya ta kar6i wayar sannan anatse tace”Assalamu Alaikum,”

  fuska dauke da murmushi sehrish tace”Wa’alaikum salam,” 

 Jahad tace”ina kwana aunty,” 

  “Lafiya lou,” sehrish ta amsa,

 Jahad ta kuma cewa”dagaske ne kece matar yaya Omar”? ta tambaya tamkar tana a gabanta, Sehrish tace “eh nice,”

  jinjina kai jahad tayi tare da ɗan ta6e baki tace”Amma bai ta6a sanar mana ba, dan Allah sabon aure ne ko tsoho “

  Ƙiriss ya rage sehrish ta fashe da dariya daƙyar ta basar da ita tare da cewa”tsoho ne, mun jima atare ynx haka ma ina ɗauke da juna biyu ina fata zaku zo suna in na haihuwa,”

   Jiki asanyaye jahad tace”insha Allah idan ya barmu zamu zo, amma aunty baki faɗa mana sunanki ba”?

   Ƙara kashe murya sehrish tayi tare da cewa”sunana Zainab amma mijina yana kira na da Hayaty,”

KARANTA ZAFAFA 2022

Gurbin Ido… Na Huguma (Zafafa2022)

Inaya By Mamuhgee (Zafafa2022)

Sanadin Labarina By Hafsat Rano (Zafafa2022)

Babu So… By Billyn Abdul (Zafafa2022)

Farhatal Qalb By Mss Xoxo (Zafafa 2022)


  Jinjina kai jahad tayi tare da kallon hossana wadda ke tsaye cikin ƙunar rai,

  Sun jima suna waya da sehrish kafin suyi sallama, mayar da wayar sehrish tayi ta ajiye saman seater ɗin, sannan ta koma tana faman tiƙar dariya,

   ɗagowa jahad tayi ta kalli hossana gaba ɗayansu jikin su yayi mugun sanyi, duk basu ji daɗin cewa ya omar yana da mata ba, sam hossana ta gaza jurewa komawa tayi saman 2 seater ta faɗa tare da kifa kanta tana kuka, jahad kuwa kitchen ta wuce saboda tabaro dankalin da take soya masu, ita kanta jurewa kawai take yi amma ba ƙaramin ɗaci taji ba na jin cewa ya Omar dinsu yana da aure, tsayawa tayi agaban fan din dake asaman gass sam ta kasa juya dankalin saboda tashin hankali, cikin sanyin murya tace”koma wacece matar shi ina tayata murna sosai, domin kuwa tayi dacen miji nagari……..’ kwalla ce ta zubo daga idonta ɗas ta zuba ƙasa, 😖

   Shigowa omar yayi cikin falon nashi, sehrish na ganin shi nan da nan ta shiga natsuwarta, 

  “Ina kwana ya omar”? 

 kallonta yayi tare da sakar mata murmushi yace”lfy lou Alhmdllh, ki zauna mana,” ya faɗi tare da samun wuri ya zauna asaman 3 seater, 

wuri tasamu itama ta zauna suna fuskantar juna,

   sunnar dakai tayi ƙasa tana jiran jin mai zai ce mata,

  Cikin natsuwa ya soma magana “Am really  sorry abt wht happend last night, banji daɗin abunda sgr yayi maki ba, nasan abun zai tsaya maki aranki,amma inaso ki sani ba yin kanshi bane! wannan allurar ce da kika kai mashi ya sanar dani cewa ke kika kai mashi ita………..’ hankali tashe sehrish take kallon shi a tunaninta sgr ya tuna abunda ya faru ne, 

  Cigaba da magana omar yayi anatse yace”Calm down ur mind, sgr ba zai iya tuna abunda ya faru ba a yanzu amma fa dole ya tuna wata rana abun zai dawo mashi ne akan shi, so nake ki fadamun a ina kika samu allurar da kika kai mashi ? Da sanin ki kika kai mashi ita? Ya tambaya yana kallon fuskarta cike da tuhuma ,

  Lokaci guda duk ta dabarbarce ta rasa natsuwarta, 

    ” Tell me the truth who brought it to u? don nasan ba ke kika dauko ta ba, in fact bamu da irinta acikin gidan nan…’

   shiru tayi tana kallon shi zuciyarta na raya mata ta fada mashi gaskiya kawai,

    murya na rawa tace”Ya omar ni ba da sani na ba Allah, babban yaya yayi mun rubutu a paper ya bani, ko a lokacin sai da nace mashi ni bansan meya rubuta ajiki ba, amma yace mun naje na ɗauko mashi kawai saboda baya cikin hayyacin shi ne, lokacin dana fito da takardar a hannuna  ina zullumin meya rubuta ajiki shine kawai sai ga h…..h…..’ wani irin ruƙo taji anyima maƙoshinta tamkar wani abu ya tokare wurin,nan take taji numfashinta na shirin ɗaukewa gaba ɗaya, kakari tashiga yi tana ƙoƙarin furta sunan haroon amma sound ɗin ya ƙi fidduwa daga bakinta, abun mamaki abun al’ajabi, 

  Ganin yarda zufa ke tsattsafo mata gefe da gefen fuskarta gashi sai faman numfarfashi take yi sama sama,

  Hakan ba ƙaramin tayar mashi da hankali yayi ba cikin sauri yace”Ke lafiya meke faruwa ne? Ko baki da lafiya ne?

   cikin kuka tace”maƙoshina ne ke mun ciwo, nagaza furta sunan wanda yaban allurar raɗaɗi nake ji a wurin,

    tashi marshal omar yayi tare da ƙarasawa wurin frigde din dake a falon shi, buɗe wa yayi tare da ɗauko bottle water mai sanyi, sannan ya dawo ya zauna dab da sehrish ya buɗe murfin robar ya miƙa mata, cikin sauri ta kar6a tana sha sai da tashanye kusan rabi sannan ta janye tana faman sauke ajiyar zuciya,

  Hannu omar yasaka tare da kar6a robar daga hannunta yasanya murfin ya rufe sannan ya ajiye robar ruwan a ƙasa, mayar da idonshi yayi akan sehrish sannan cikin natsuwa yace”pls taimako nake so kiyi mana,bansan wacece ke ba amma har a raina naji, na yarda dake dan Allah karki sa na fara zarginki, ki fadamun gaskiya wanene ya baki allurar da kika kai mashi? allura ce mai haɗarin gaske a lokacin da Allah baisa na faɗo na ceceki a hannun shi ba tabbas ba zaki rayu ba….

   Hankali atashe sehrish ta ɗago idanunta tana kallon shi, nan da nan taji wasu hawayen sun sake wanko mata fuskarta cikin shessheƙar kuka tace”ya omar wlh ni bansan komai akai ba bazan iya cutar dashi ba kuma nima bazan so na cutar da kaina ba……….’

   jinjina kanshi yayi tare da cewa”to ki fadamun wanene ya baki allurar”? 

  buɗe baki tayi zata furta haroon nan take ta sake ji an damƙi maƙoshinta saboda zafin da taji kawai saita fashe mashi da kuka saboda ta rasa yarda zata yi ta sanar mashi……..’ 

  Zuba mata ido yayi yana kallonta tana ta faman shan kuka, tuni yaji tsananin tausayinta ya kamashi,musamman daya dinga ganin fuskarta kamar su jahad ne ke kuka, 

   Cikin sauri ya dakatar da ita da cewa”its okey, kiyi hakuri banyi hakan dan na 6ata maki rai ba, inaso kawai na gano wanda ya baki allurar ne don inyi investigation akan shi, amma tunda bakison faɗi, zaki iya tafiya, 

   tsagaitawa tayi da kukan tana kallon shi cikin sanyin murya tace”dan Allah  kada ka zargeni wlh bazan iya cutar da wani acikin gidan nan ba, saboda na ɗauke ku tamkar ƴan uwana na jini na…….’

     murmushi Omar ya ɗanyi kafin yace”don’t worry ur self nima kamar yarda kika ɗauke mu haka muka ɗauke ki, ki kwantar da hankalin ki komai ya wuce insha Allah,amma aduk lokacin da kika tuna sunan wanda ya baki ita, ki hanzarta sanar mun pls……’

   “Insha Allah zanyi hakan,” tashi tayi tare da yi mashi sallama ta nufi hanyar fita daga falo dinsa, a hankali take tafiya hannunta dafe da saitin zuciyarta, muryar shi ce, ta sake katse ta da cewa”yana buƙatar a gyara mashi bedroom ɗinsa yakamata ki je, a firgice ta juyo tana kallon shi, ganin yarda ta razana ne yasa shi cewa”ki kwantar da hankalin ki, kada abunda ya faru jiya yasa ki dinga jin tsoranshi, nasan ko wanene ɗan uwana, am really proud of him, ki saki jikin ki in ba haka ba zai gane cewa wani abu ya faru adaren jiya,

   jinjina mashi kai tayi tare da cewa”toh zanyi yarda kace,” tana fadin hakan tasa kai ta fuce,

   Murmushi Omar yayi saboda tunawa da babban aikin da sgr yaso yayi jiya, tabbas da yarinyar ta rasa ranta don ayadda yake jin wannan ƙarfin ba ƙaramin illatata zaiyi ba,

   “godiya ta tabbata ga Allah subhanahu wata’ala da yabani ikon zuwa adai dai wannan lokacin har na ceci rayuwarta, na kuma taimaki ɗan uwana daga aikata wannan aika aikan,” ya furta yana faman sauke ajiyar zuciya,

*************💋

Gaba ɗaya sun hallara a saman dining chairs suna yin breakfast dinsu, Abban su tare da junaid, sai Ayaan da jahan ga kuma su irfan khaleed da jabeer da kuma Fawan, har yanzu bai fara sanya riga a jikinshi ba sai dae gajeran wando kawai yake zurawa yayi ta yawon shi,

  “Aunty azmee ina reesh take ne, banganta ba”? Junaid ya tambaya yana kallon azmee dake tsaye tana saving dinsu, 

   Abbansu ma yace”tun ɗazu nake so in tambaye ta nima, yau banga daughter ɗita ba ina tashiga ne?

  Murmushi azmee tayi tare da cewa”tashiga sashen Omar ne,” 

  cike da mamaki jabeer yace”wacece kuma sehrish? ko dai wannan yarinyar dana gani tana yawo acikin gidan nan? Ya tambaya yana kallonsu,

  irfan yace”nima ina taso na tambaya wlh, naga kyakkyawar yarinya tana ta yawo acikin gidan nan gwanin burgewa,”

  da buɗar bakin fawan sai cewa yayi “Oh wai dama mutun ce? Ae ni nayi tunanin ko idona ne ke ganemun ita shiyasa ban ta6a tambaya ba,” dariya suka fashe da ita gaba ɗayansu banda shi fawan din da yayi mgnr, saboda shi bada wasa yayi maganarshi ba, duk a tunanin shi ko ya samu ta6uwa ne shiyasa yake ganinta, 

     “Sunanta Sherish tare da azmee suke aiki, amma na mayar da ita ƙanwarku ina fata zaku ji daɗin hakan, tunda dama baku da ƙanwa mace,” acewar abbansu,

   kallon juna su kayi atare kafin fawan ya kuma cewa”ni duk ba wannan ba, wai ina tukur mai aikin mu ne? Nayi kewar shi sosai tunda muka dawo banga gifcin shi ba acikin gidan nan,”? ya tambaya yana kallon junaid dasu twins,

  murmushi suka shiga saki gaba ɗayansu batare da sunce komai ba, 

   Khaleed yace”wannan sullu6iyon mai aikin namu, dama nasan bazai kai labari ba halan an kore shi daga aikine”?

   Junaid ne yace”kai yaya fawan yanzu kuna nufin baku gane wanene tukur ba? Wannan yarinyar fa itace fa tayi shigar maza tana mana aiki……..’ 

  Saboda tsabar ruɗu har suna haɗa baki wurin cewa”Are u serious!? ɗaga kai yayi tare da jaddada masu maganar shi yace”of course ku tambayi abba kuji,” 

   Kallon abban nasu sukayi suna jiran jin bayani murmushi yayi tare da cewa”itace mai aikin da kuka bari a matsayin namiji,” 

   cikin mamaki suke kallon shi sam sun gaza cewa komai saboda abun yafi ƙarfinsu wai tukur mai aikinsu ne ya koma mace ? dama maca ce tayi shigar namiji kenan? Murmushi fawan yayi aranshi yace “lallaikam nama har gida,” kamar abbansu yaji mai yace sai ɗagowa yayi ya kalli fuskokinsu yace”ko da gigin wasa bana son wani ya ta6a mun ɗiyata,ko kallon banza wannan ban amince wani yayi mata ba,” 

   har suna haɗa baki wurin cewa”Insha Allah hakan ma bazata faru ba, ae ƙanwarmu ce,” dariya junaid yayi ƙasa ƙasa saboda yasan halinsu sarai musamman fawan,

 Sehrish~

 

Koda ta fito daga part ɗin omar, wuri ta samu anan upstairs ɗin ta zuƙunnna tana shan kuka ba don komai ba sai don baƙin cikin kasa furta sunan haroon da tayi, taso ta sanar ma Omar kodan ta fita zargi amma hakan yaci turo saboda maƙoshinta da taji an shaƙe mata shi, babban abunda take fargaba shine kada su fara zarginta akan abunda ba laifinta bane, yanzu kuma duk ranar da sgr ya tuna da wannan abun daya faru a tsakaninsu dole ya tuhume ta, batasan wane irin kallo zaiyi mata ba,😖

  “Ashe so yayi ya kashe ni !” ta furta cikin sanyin murya, “ni bansan me nayi mashi ba, ya Allah ka kare ni daga sharrin shi, ya Allah kada ka bashi nasara akaina,” 

  tana cikin wannan tunanin sam bata ji takon tafiyarshi ba, fitowarshi kenan daga part dinsa ya kimtsa cikin suits farare ba ƙaramin kyau suka yi mashi ba, 

  tsayawa yayi yana kallon ikon Allah yarinyar da yake ta faman jira ta gyara mashi bedroom dinshi itace zuƙunne tana shessheƙar kuka, cike da mamaki ya ƙarasa har inda sehrish take sam bata zaci ganin shi ba, sai dae taga ƙafafunshi masu sanye da haɗaɗɗun takalma, gabanta ne taji yayi wani irin bugu duk da bata san wanene ba amma tana da tabbacin cewa shi neeee saboda ƙamshin turaren nan nashi,

   ƙara ƙanƙame jikinta tayi tana faman zazzare ido a tsorace, muryarshi ce ta ratsa kunnanta da cewa”ke tashi tsaye,” 

  cikin sauri sehrish ta miƙe tsaye jikinta na kerma kamar wadda taga wani horror sam taƙi yarda ta kalli fuskarshi saboda ta tsorata dashi, 

    shiru ya ɗanyi baice komai ba tamkar mai nazarin wani abu, hannunta yabi da kallo sai faman kerma yatsun hannun suke yi, 

  “Are u okey”? ya tambayeta,cikin sauri tace”eh” 

   “Okey agyaramin bedroom ɗina,” yana faɗin hakan ya kama hanya  ya wuce,

  Sam takasa janye idanunta daga kallon bayanshi  har sai da ya 6ace ma ganinta, sannan ta wuce part din nashi, lokacin data shiga bedroom dinshi ba komai ta tuna ba face abunda ya faru atsakaninsu daren jiya, bin shimfiɗeɗen gadon shi tayi da kallo har yanzu zanin gadon a cukuikuye yake, saboda damben da suka sha jiya, hannu takai tare da yaye bedsheets ɗin nashi ta rungumo shi a kirjinta tana shinshina ƙamshin turarensa, ita kaɗae tasan irin yanayin da tashiga a wannan lokacin duk da firgicin da take ci amma hakan bai hanata jin wannan yanayin ba………….💋😉

*💋Boss💖Bature❤*✍️

A galabaice take hura wutar murhun wani irin uban hayaƙi yake fitowa baƙiƙƙirin duk ya cika kitchen din, idanunta sunyi jawur kamar na mai shan taba, matashiyar yarinyace da bazata wuce shekara goma sha huɗu ba aduniya, a wani matsakaicin gida na masu rufin asiri, jikinta na sanye da koɗaɗɗen zani na atampha tayi ɗaurin gaba dashi, duk ya yayyage jikinshi yayi baƙiƙƙirin saboda dauɗa, gaba ɗaya ita kanta yarinyar abun ban tausayi ce, ta bushe ta rame ta ƙanjame yadda kasan skelaton haka take, saboda kasusuwan wuyanta da suka firfito mata waje kamar zasu fito daga fatar jikinta saboda tsabar rama, saboda koɗewar da fatar jikinta tayi baza ma a iya tantace launin fatarta ba, fara ce ko baƙa 😢

sai faman goho take yi agaban murfin tana hura wutar da bakinta amma wutar taƙi kama wa, zuƙunnawa tayi gaban murhun ta zabga uban tagumi hawaye na faman kwararowa daga idanunta, cikin murya kuka ta soma cewa”Ya Allah ka kawomin karshen wahalar da nake sha acikin gidan nan……..’ 

   Muryar mammynsu ce ta katse ta da cewa”AMAL!! wai uban wa kike so yayi wankin nan ne? zaki fito kiyi shi ko saina maki dukan tsiya ne? Hankali atashe tace”mammy iccen girkin ne ɗanye baya ci, tun ɗazu nake faman wahalar hura shi amma yaƙi ruruwa,” 

  Uban tsoki matar ta buga tare da cewa”wannan ba damuwa ta bace ba, ki tabbatar da kin hura wutar ta kama,sannan ki fito ki wanke mana kayan mu, bayan kin gama kuma ki share gidan,” 

   cikin ƙunar rai ta amsa mata da “toh,”

Sannan taci gaba da hura wutar don ta kama, 

   cigaba da magana matar tayi tana cewa”Yayarki nacen gidan huta, ta manta dake gaki nan a wulaƙance kin zama tamkar baiwa a wurin mu, da ace tana sonki ae bazata barki a hannun mu ba,”

   Shiru Amal tayi hawaye na zuba daga idonta, har yau tagaza yarda cewa yayarta zata iya yi mata hakan, saboda me zata tafi tabarta hannun waɗannan mugayen? Ta tambayi kanta,

   muryar mammyn tasu ce ta sake katse ta da cewa”hmmm dama tsiyar talaka kenan anyi mata hanyar arziƙi amma ta manta da mutane, baƙin halinku iri ɗaya dana uwarku, ae duk laifin laila ne ko uban waya faɗa mata ana yiwa ƴa’ƴan kishiya abun arziƙi,” tana zaune saman gujera ƴar tsugunno sai faman sambatu takeyi kamar zautacciya, wata tsamurarriyar mata ce fara siririya ta fara tsufa don gashin kanta harya fara hurhura, jikinta na sanye da atampa riga da zane, ta tsoge ɗaurin ɗankwalin nan ture kaga tsire, hannunta na ruƙe da aswaki sae faman kwalkwalar haƙoranta takeyi wadanda sukayi jawur saboda tsabar cin goro, kai kana ganin ta zaka shaida cewa ba ƙaramar jarababbiya bace, irin tsaffin nan da basa gajiya da mita,

   daƙer Amal tasamu wutar ta huru, sannan ta fito agalabaice, kai tsaye ta wuce inda uban kayan wankin suke dila guda,gaba ɗaya kayan sawarsu ne su duka dana uwar dana su abra da hayam, ga zannuwan gado da barguna duk sun tara mata su don ta wanke, abun babu imani acikin shi, babu irin wahalar rayuwar da yarinyar bata shaba,uƙuba iri iri suke yi mata, ko bacci bata samu, in ma tayi baccin da duka suke tashinta, ko kuma taji saukar ruwa bokiti guda ajikinta, fatar jikinta duk cizon sauro ne gashinan ruɗu ruɗu, saboda awaje take kwana, su kuma su shige ɗaki sai ita kaɗai ga tsora da Allah yayi mata, kullum cikin zullumin mai zai faru da ita take yi, duk yarda taso su haɗu da yayarta abun yaci tura, a halin da ake ciki ita kanta Amani batasan cewa yarinyar na raye ba, tun wani zuwa da tayi suka sanar da ita cewa yarinyar ta 6ace an neme ta an rasa, hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba, a lokacin tasha kuka sosai wurin neman yarinyar amma babu ita babu alamarta, tun tana sanyawa a nemo mata ita har tagaji ta daina saboda kullum babu labarin anga yarinyar shiyasa ta fidda rai da ita, ashe lokacin 6oye yarinyar sukayi a gidan makwabtansu acikin wani ɗaki aka rufe ta kamar akuya, duk in amani zataso maiduguri sai su kaita can gidan ajiya har tazo ta tafi bazata sani ba, hakan yasa basu ta6a haɗuwa da ita ba tun auranta da Abbas na wata takwas a lokacin abun ya faru, taso ta ɗauki yarinyar ta zauna a wurinta amma saboda baƙin hali irin nasu sun hanata ganin ƴar uwarta….😭

    “Maza ki hanzarta ki wanke mana kayan,” muryar mammynce ta katse ta,

    Hannu tasa ta ɗauki bokitin dake ajiye awurin kayan, sannan ta wuce izuwa inda fanfonsu yake,ruwa ta tarbo acikin shi sannn ta ɗauke shi tadawo ta ajiye, ledar klin ta dauka tare da fasawa ta zazzaga aciki sannan tashiga tsoma kayan aciki tana wankewa idonta na zubar da kwalla,

     suna cikin wannan zaman suka ji ƙarar dirar mota a ƙofar gidan, washe baki mammy tashiga yi tana cewa”ƴar albarka ta iso, nasan tadawo mana da abun arziƙi, ni dae naji daɗi ƴa’ƴana badae farin jini ba……..’ bata ƙarasa maganar ba Hayaam tashigo cikin gidan  ba ƙaramin wanka ta ɗauka ba, jikinta na sanye da swiss lace ash colour, doguwar riga akayi mata dashi, ta matse ta tsam tamkar in tayi motsi rigar zata yage saboda yarda tayi tighting ɗinta, ta  kashe ɗaurin kallabi nan, mayafin kuma ta aza shi a kafaɗa,

   fuskarta ɗauke da murmushi ta ƙarasa wurin mammyn tasu, tashi tayi ta rungumeta tana cewa”ƴar albarka sai yau zan saki a idona”?

  Murmushi hayamm tasaki tare da cewa”Ammi yau ɗin ma sa’a kika ci, ki gode ma Allah da kika ganni yau, domin kuwa gobe zan wuce abuja nazo ne nayi maki bankwana saboda zan koma can da zama ina fata Aunty laila ta sanar dake game da komawa ta can? Ta tambaya tana kallonta,

   gaba ɗaya Amal ta kasa kunne tana sauraronsu,

   Washe baki tayi tare da cewa”ta sanar dani mana, ae ba ƙaramin daɗi naji ba kwara ki tattara ki tafican kema ki shafo mana arziƙi,”

    Fari da ido hayaam tayi tare da cewa”baki da damuwa in dae nice mommy, arziƙi mun gama yin shi, muddin burina ya cika tuni zan canza maku tamfatsetsen gida na kece raini, na siya maku manyan motoci na alfarma sannan na biya maki aikin hajji, mommy kuɗi fa har sai kin gaji dasu wlh,” ta faɗi tana faman sakin murmushi,

   Cike da farin ciki mammy tace”Allah?

  “wlh kuwa mommy,” hayamm ta bata amsa, 

   ganin amal na kallonsu yasa mammyn kwatsa mata tsawa tace”zaki mayar da hankalin ki kan kayan da kike wankewa ko saina zo nan na karya maki wuya, magulmaciyar banza ƴar sa ido,” jiki na rawa amal ta mayar da hankalinta kan kayan da take wanke wa,

     ruƙo hannun hayamm mammyn tayi sannan tajata suka shige cikin ɗakinsu, don kar taji me zasu ce,

    a hankali take wanke kayan  tunani iri iri na zuwa mata aranta, tana yawan jin suna ambaton abuja abuja, kodai can aunty amani take zaune ne? Ta tambayi kanta, jinjina kai tayi tare da cewa”ina da tabbacin cewa auntyna tana zaune acan itama, dole na nemi mafita bazan zauna su kashe ni ba, zan gudu ne batare da saninsu ba,” ta fadi tare da tsame rigar da ta sanya acikin ruwan wankin……….’😳

  ****************

A 6angaren su hossana kuwa saboda damuwar da suka shiga na jin cewa ya Omar ɗinsu na da aure gaba ɗayansu ba wanda yayi breakfast saboda damuwa, su kansu sun rasa gane dalilin dayasa suke jin kishin matar shi data kirasu a waya,  abincin da jahad ta shirya masu har yayi sanyi saboda tun safe yake ajiye saman dining table babu wanda ya ta6a shi, gashi har ƙarfe ɗaya yanzu yayi na rana, 

    A tare suke kabbara sallah bayan sun kammala suka zauna suna addu’o’i, shiru jahad tayi tana sauraron addu’ar hossana da take yi,

   “Ya Allah kasa mafarki ne ba gaske ba na cewa ya Omar yana da mata, in ma dagaske ne ya Allah kasa ya sake ta su rabu, zuciya ta tafarfasa takeyi mun bazan iya jurewa ba……..’ 

   katse ta Jahad tayi da cewa”hossana kina a hayyacinki kuwa? ya sake ta fa kika ce? Idan yana son matar shi fa? 

  harara hossana ta jefa mata tare da cewa”waya faɗa maki yana sonta? Auren dole ne akayi masu, da ace yana sonta ae da bai 6oye mana cewa yana da mata ba har da ciki…’ 

      Itama jahad ɗin harar ta mayar mata tare da cewa”baki da hankali wlh,dagaske ɗin ke zararriya ce, yaya omar yana son matarshi, ke bakiji muryarta ba yarda take magana daga gani tana cikin kwanciyar hankali, kuma tana samun soyayyar mijinta tunda gashi har tana da ciki zata haifa mashi baby……….’ jahad bata ƙarasa maganar ba, hossana takai ma wuyan hijabinta cakuma tana cewa”Ni ce zararriya? ɗaga kai jahad tayi alamar e,

    Bugu hossana tashiga kai mata, ganin bazata iya jurewa ba yasa suka kacame da faɗa, abu kamar wasa sai da dukkansu suka sha kuka, dama ransu a6ace yake, duk don saboda matar Omar,

   (Sehrish tayi tsiya)

tsaf ta kammala gyara mashi bedroom dinshi da toilet dinshi da falonsa duka ko’ina a kimtse tabar mashi shi, fitowa tayi ta sauko down stairs a lokacin duk sun kammala yin breakfast ɗin nasu babu kowa a falon, kai tsaye ta wuce bedroom ɗin Haroon gabanta na faduwa rass rass, ƙopar a rufe take don haka saita sanya hannu tare da yin knocking ɗinta, daga cikin ɗakin tajiyo muryarshi yana cewa”Wanene”?

   “Ni ce,” ta bashi amsa cike da ƙarfin guiwa,

   buɗe mata ƙopar yayi fuskar nan ɗauke da murmushi, jikinshi na sanye da singlet fara tare da shorts baƙi, 

  “shigo daga ciki mana,” ya faɗi yana nuna mata hanya, kallon shi kawai takeyi , sa kai tayi ta shiga ciki  daga tsaye ta tsaya tana kallon shi, rufe ƙopar yayi sannan ya juyo ya kalle ta yace “wlh har naji sanyi araina dana ganki cikin ƙoshin lafiya,ae nayi tunanin  e warhaka kina asibitin kwance magashiyyan rai hannun Allah…..’ bai ƙarasa maganar tashi ba tace”me nayi maka? Meyasa kake son kashe ni? saboda me ka bani wannan allurar?

    tafi yayi da hannunshi yana dariya, wuce ta yayi tare da samun wuri daga gefen gadonshi ya zauna yana facing ɗinta yace”Ko da ace zan iya kashe kowa a duniyar nan, ni bazan iya kashe abunda raina ke so ba!!! nasan cewa ba zaki mutu ba, akwai wanda zaizo ya taimake ki shiyasa nayi hakan ! kinfiye taurin kai shiyasa na gwada maki kaɗan daga cikin shaiɗancina, kin manta maganar da kika faɗa mun nacewa NAMIJI kike kallo? Shiyasa na haɗaki da namijin………..’ ƙarasa maganar yayi yana faman tiƙar dariya, sakin baki sehrish tayi tana kallon shi. Da ƙyar ya tsagaita da maganar tashi yana kashe mata ido yace”Yarinya taji maza,baki ban labari ba ya kuka ƙare jiya? 

   shiru tayi tana kallon shi kawai saboda abun yafi ƙarfinta haroon ba ƙaramin shaiɗani bane, 

    ta6e bakin shi yayi yana kallonta sannan yaci gaba da cewa”wannan allurar da na baki, miyagu irina suke amfani da ita, aduk lokacin da mutun yayiwa kanshi allurar nan, imanin shi gaba ɗaya take cire wa, zai iya yi ma mata sama da goma sha biyar raping a lokaci guda batare da ya gaji ba tamkar engine zai dinga aiki, sannan koda ace mahaifiyarshi ce akusa dashi itama hakan ce zata faru da ita ba zai iya tantance fari ba balle baƙi, saboda gaba ɗaya take tayarwa mutun da wata irin jarababbiyar shawa’a da kuma ƙarfi na ban mamaki, kuma muddin a lokacin bai samu ya kawar da sha’awarnan  ba, to fa zuciyarshi zata iya bugawa nan take,…….’ 

  tunda ya soma bayani sehrish ke kallon shi cikin tsananin tashin hankali har sai da yakai ƙarshe sannan cikin sanyin murya tace”me yasa ka fita daban acikinsu ne? Saboda me kake son cutar da shi ne? idan ni nayi maka laifi saboda me laifin zai shafe shi? 

     shu’umin murmushi haroon ya saki  kafin yace”tun ina yaro nake da son yin mugunta, ni ko dariya ban cika yi ba sai in anyi abun mugunta sannan take zuwa mun, burina kawai naga kowa cikin masifa da tashin hankali,natsani inga ana ta rayuwar farin ciki mai ɗaurewa, wannan ne dalilin dayasa nakeson in kawo canji acikin gidan nan,”. Hankali kwance haroon ke kora mata bayani batare da nuna alamun wasa ba, 

   tuni taji idonta sun ciko da kwalla cike da takaici tace “tausayinka nake ji ! kana bani tausayi saboda kai abun tausayi ne, ban ta6a tunanin cewa a jinin abba za’a samu mai irin waɗannan mugayen ɗabi’un da halayen irin naka ba, saboda me yasa kai ba zaka yi koyi da sauran ba? ka zama mutumin kirki tamkar sauran”? 

   tasowa haroon yayi daga zaunen da yake ya ƙarasa dab da inda take  a wannan karan fuskarshi babu wasa acikinta yace”kina so in shiryu ne? In zama mutumin kirki?

   ɗaga mashi kai tayi alamar eh,

  Murmushi haroon yayi kafin yace”kece mutun ta biyu, da kikayi mun fatan shiriya arayuwata, sai dae kash hakan bazai ta6a yiyuwa ba sehrish ni ba cikakken mutun bane kamar yarda kike tunanin………………..’ a wani irin firgice sehrish ta ɗago tana kallon cikin idanunshi fuskarta cike da tsoro tace”kana nufin kai ba mutun bane”? 

   dariya ya ɗanyi kafin yace”kona faɗa maki ba zaki yarda ba, amma bari na sanar dake wani abu da baki sani ba, ni da kaina na turo marshal Omar ɗakin sgr domin ya taimake ki ! kuma ni ne nan na hana ki furta sunana agaban Omar, na shaƙe maki maƙoshinki na hana sautin fita daga bakin ki, shin bakiyi mamakin taya akai duk nasan da wannan ba !!!!!!!!!!!

   Zazzare ido sehrish tayi gabanta na faɗuwa, tuni zufa ta soma tsattsafo mata, ja da baya da baya tadinga yi tana kallon shi…..

  dariya sosai haroon yayi kafin yace”Shiyasa nace ki nemi tsari daga sharrina wlh ni shaiɗanin aljani ne ba mutun ba……….’ 

 tunkan ya ƙarasa maganar tashi  Da gudun gaske sehrish ta  juya tare da buɗe ƙopar ɗakin nashi ta fuce ji kake garam !!!! Ƙopar ta datse,

   Fashewa da dariya haroon yayi hada dafe cikin shi, daga bisani kuma ya ɗan tsagaita da dariya tare da cewa “Yarinyar tana da kyau, shiyasa na tsoratar da ita saboda inga kyawawan idanuwan nan nata masu kashe mun zuciya,” ya furta tare da kai hannun shi saitin zuciyarshi yana faman sakin murmushi……………😳 tashin hankali anya kuwa haroon 👹😈

   

 Ko kallon gabanta ba tayi saboda gudun da take yi gaba ɗaya ta gama firgita da haroon, bata yi wani aune ba ta faɗama junaid wanda ya nufo part din nasu, aikuwa gaba ɗaya suka faɗa ƙasa a manne da juna, atare zuciyoyinsu ke bugawa, musamman sehrish yana jin yarda zuciyarta ke faman bugawa da ƙarfi da ƙarfi, sun jima a haka kusan 8 mins sannan junaid ya ambaci sunanta “Sehrish,” 

   lamo tayi a jikinshi tana faman sauke ajiyar zuciya sai da ta samu natsuwa sosai sannan ta ɗago daga jikinshi,tayi gefe guda zaune dirshan tana kallon shi, tasowa yayi daga kwancen da yake yana faman sakar mata murmushi, tun safe yakeson ganin ta amma basu haɗu ba sai yanzu, shima zama yayi suna fuskantar juna da ita, wankan jeans da t shirt red colour ne ajikinshi, sai faman ƙamshi yake yi, 

     “Me ya faru ne naga kina ta tiƙar gudu kodai motsa jiki kike yi ne? ae muna da wurin gym acikin gidan nan,’ 

  Ya faɗi yana kallonta, tayi mashi zuru da ido,

   Ganin bata da niyar yin magana yasa shi cewa “Labari mai daɗi “! cike da zumuɗi tace “dagaske ? Wani irin labari ne wannan,

 “Mafarki nayi jiya,” 

“Me ya faru acikin mafarkin”? ta tambaye shi cike da son ji,

    gyara murya yayi tare da cewa” mafarki nayi da wani narkeken zaki acikin wani ƙurmin daji ya biyo ki da gudun gaske, kamar zaki tashi sama haka kika dinga gudu kina ihu, kinsan waye ya cece ki a wannan lokacin”? Ya jefa mata tambaya, hankali tashe tace “A’a,” ƴar hararar ta yayi tare da cewa”Ni ne nan, nazo da suffar jemage na ɗauke ki da fika fiki na mukayi sama can cikin gajimare………..’ ganin yarda sehrish ta fashe da dariya yasa shi dakatawa da labarin yana kallonta, nuna shi tayi ta yatsa tana cewa”junaid kaji tsoran Allah, jemage fa kace? taya jemage zai iya ɗaukar mutun ? sannu malam fesal ka feso mun ƙarya, 

 gaba ɗaya suka sanya dariya, ba ƙaramin nishaɗi junaid ya sanyata ba duk da fargabar da take ciki, sun jima a zaune ƙasa suna fira, kafin daga bisa ni suka tashi, shi ya wuce mosque ita kuma  ta wuce bedroom ɗinta saboda tayi sallar itama,

  

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

    

 

*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃

*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*

*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI.  MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*

*LOCATION KANO*

08062073990

Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka 

Wadrobe balls 

Madarar kulleccham 

Vaseline kulleccham 

Kajiji

Halut

Couscous 

Khumrah 

Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku

Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka 

Wadrobe balls 

Madarar kulleccham 

Vaseline kulleccham 

Kajiji

Halut

Couscous 

Khumrah 

Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku

It’s not just good …it’s finger linking good faster than fast food, better fine dining.

Snack

Awarah 

Farah

Zobo

Samosa

Cup cake etc 

Contact me 09063302182or 09012179727.

Back to top button