Uncategorized

Mijina Yana Kallon Finafinan Batsa (Blue Film)

 

MIJINNA YANA KALLON HOTUNAN BATSA (BLUE FILMS)

:

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓

:

Mallam mijina ne baida aiki sai kallon hoton mata tsirara. babban abun bakin ciki shine shi da kansa yake tambayesu su aiko masa dashi. idan yagani sai kaji yace yayi missing ɗinsu kuma dasuna kusa da sai yayi making love dasu, duk lokacin da na buɗe wayansa zanga ire-iren wannan pictures a wayarshi. wanima zakaga mace da namiji suna sex ni kuma narasa ta inda zan masa magana saboda zaice ina masa bincike awaya. kuma zamuyi faɗa da shi, kullun hankalina atashe yake bana samun isashshen barci. idan na tuna halin da mijina yakeciki, malam tambayata anan ya halatta narika daukan nawa hoton tsirara ina tura masa a waya kozai rage kallon na matan banza ko kuwa? ina neman shawara da addu’arka Mal. wassalam.

:

𝐀𝐌𝐒𝐀:👇

:

Hakika abinda mijinki yake aikatawa, ko kaɗan bai dace ba. ya kauce ma hanyar Allah. Kuma ya afka cikin manyan manyan ALKABA’IR.

Shi dai kallo izuwa ga matar da ba taka ba, haramun ne koda ba tsirara take ba. Shi kuwa kallon tsaraici, Allah (Swt) ya la’anci masu yi, kuma ya la’anci masu nuna tsaraicin nasu da gangan don akalla.

Mijinki yana nuna miki Qarara cewa Shi mazinaci ne kenan. Saboda haka shawarar da zan baki anan it a ce : Ki bi abun ahankali. kar ki sanya gaggawa ko husuma acikin sha’anin. in ba haka zai iya rikicewa.

1. Ki samu mijinki kiyi masa wa’azi cikin murya mai sanyi. Ki gaya masa cewa Allah (swt) ya umurci muminai maza su rintse idanuwansu, su kiyaye al’aurarsu daga zina da dangoginta.

Manzon Allah ﷺ acikin wani hadisi yana cewa :

“SHI KALLO, KIBIYA NE MAI TSANANIN GUBA DAGA CIKIN KIBIYOYIN IBLIS. DUK WANDA YA BAR KALLON DON TSORON ALLAH, TO ZAI SAMU (QARUWAR) IMANI WANDA ZAI RIKA JIN ZAQINSA AZUCIYA”.

Kiyi masa wa’azi sosai ki tsoratar dashi game da mummunan Sakamakon da zai riska idan bai tuba ba. Ki gaya masa yaji tsoron ranar tashin Alqiyamah, ranar da Allah zai sanya gabobin jikinsa su rika magana suna bada shaida akan laifuffukan da ya aikata.

2. Idan yaki jin wa’azin naki, to babu laifi ki hadashi da wani mai hankali daga cikin abokansa domin yayi masa nasiha. Insha Allahu zai ji kuma zai yarda.

3. Kar ki dauki irin mummunar hanyar da wadancan matan suka bi. Domin kuwa idan kika zuba masa Hotunanki Tsirara acikin wayarsa, zata yiwu watarana wani daga cikin abokansa ko ‘yan’uwansa ya dauki wayar kuma ya leka ciki ya ganki tsirara. kinga wannan bai yi daidai ba.

Babban abinda mijinki yake bukata daga gareki shine ladabi, biyayya, da nasiha agareshi cewa yaji tsoron gamuwarsa da Ubangijinsa.

4. Ki matsa ma mijinki ya rika halartar jam’in sallolinsa a masallaci, kuma ya rika karanta Alqur’ani ayawancin lokutansa.

5. Ki sanyashi cikin addu’o’inki ako yaushe. Kuma muma muna yi miki fatan Allah ya shiryi mijinki ya cire masa son zina. ya cika masa zuciyarsa da tsoron Allah.

WALLAHU A’ALAM.

Ku kasance damu domin ilimintarwa da Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.

TELEGRAM:👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

FACEBOOK👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

WHATSAPP👇

https://chat.whatsapp.com/EPG7wVPlgxRFR4R9CdR8xY

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

Back to top button