Uncategorized

Abban Sojoji Chapter 32 Book 2 Complete Novel

 

“`The father Of Soldiers“`

 

Story &  Written 

       By 

      Hafsat Bature

          (Boss Lady)

Bayan sun fito daga motar kai tsaye suka nufi hanyar da zata sadaka da babban falon gidan, Sehrish sai faman bin ko’ina take da kallo aranta tana cewa”tab ! Mace ta samu wannan amatsayin gidan aurenta, ae kawai ta bi mijinta sau da ƙafa, tabi da addu’a don ni gaskiya na mallaki wannan hamshaƙin gidan amatsayin gidana, ko ƙofar gida bana leƙawa sai in ta kama,’

sai faman zancan zuci take yi har suka ƙaraso wurin wani bene mai kanannaɗa, hawa junaid yayi sannan azmee tabi shi, itama sehrish tabi bayansu, sai faman jinjina kai take yi tana cewa”lallaine Aljanna ta mai rabo ce,”

  daker take tattaka matattakalar benen saboda gajiya don yana da ɗan tsayi, bayan sun kai ƙarshensa, wata haɗaɗɗiyar ƙopa ce wadda kai tsaye in ka bi ta zata sauke ka upstairs inda main falo ɗin gidan yake, 

   key junaid yasanya yabude ƙopar sannan suka shiga cikinsa,wurin ya haɗu an ƙawata shi ahaka ma wai ba furnitures acikinsa, to inaga ansanya mashi kujeru da sauran abubuwan ƙayatarwa,

   Batare da 6ata lokaci ba, sehrish ta buɗe handbag ɗinta, memo ta ciro tare da biro, junaid da azmee suka dunga dudduba falon suna karanto mata abunda za’a buƙata acikinsa, ita kuma tana rubutawa acikin memo ɗin hannunta, bayan sun gama da falon kaf sun lissafa duk wani abu da za’a sanya mashi, 

Sannan acikin babban falon akwai bedrooms guda biyar ƙofofinsu na acikin falon, ciki suka shiga suna dudduba ɗakunan masu girman gaske, nan ma azmee ta faɗa ma sehrish duk abunda za’a buƙata na furnitures ta rubuta, daga nan kuma suka sauko downstairs stairs shima bene ne zai biyo dakai ƙasan,

Agajiye sehrish ta kalli junaid tare da cewa “dan Allah wannan wane irin gidane haka junaid? Nafa rikice wlh, mun shigo ta Upstairs yanzu kuma ga mu  a downstairs yanzu ta ina zamu bi mu fita? Ba dai sai mun koma upstairs ɗin ba don wlh ƙafafuna a sanƙare suke hawa stairs ko wahala,

   Junaid da fuskarsa tayi jawur ya gama cika ya 6atse saboda uwar yunwar da yake ji, ga gajiya duk ta baibaye shi, daker ya iya cewa “wannan ne damuwarki, Ni ta cikina nake yi yaushe har muka kammala muka koma gida ni daga nan ma, ba abunda zan ƙara yi Allah, ku je ku ƙarasa sauran aikin in kun kammala kuyimun magana,”

  Wuri yasamu a sitting room ɗin dake a downstairs saman wani benci ya zauna, da alama tun lokacin da akayi ginin gidan aka barsa, don akwai tarkacen kayan aikin da aka bari acikinsa,

Acikin sitting room ɗin akwai ƙofofin bedrooms guda biyu, sai kitchen mai girman gaske, sunsha aiki kaf sai da suka zagaye gidan bayan sun tabbatar sun bincika ko’ina sun dudduba abunda ya dace duka kaf sehrish ta rubuta a memo ɗinta, Ana cikin kiran Sallar magrib suka bar gidan kowa agajiye, 

 Suna ƙarasawa gida daga babban falon kowa ya wuce ɗakinsa, shaf shaf junaid ya tu6e kayan jikinsa ya faɗa toilet donyi wanka, haka itama sehrish tana shiga ɗakin nata bayan tayi wurgi da handbag ɗinta saman gado tare da memo da biron duka, kai tsaye ta tu6e Jalbab ɗin dake ajikinta, ta cire rigar jikinta, cikin sauri ta faɗa toilet wanka tayo tare da Alwala, tana fito ta ɗaure da towel ta bude wardrobe ta ciro wata doguwar rigar mara nauyi ta zura, daker tasamu tayi sallah bayan ta kammala ta baje saman gadonta, bata ƙara sanin meke faruwa ba sam ta manta da batun jera abinci adining, gana babban yaya da zata kai mashi bacci kawai take kwasa,

 Azmee ce kawai tayi ƙoƙarin fitowa bayan ta canza kayan jikinta, tunda ta leƙa tasamu sehrish na jan minsharin wahala, bata tashe ta ba kitchen kawai ta wuce ta shirya masu abincin dinner ɗinsu ta dunga kaiwa a dining tana jerawa harta kammala,

 Daker junaid yasamu ya fito sai da yaci ka cikinshi sannan ya wuce masallaci yin sallah,

Sai bayan sallar isha’i sannan sehrish tafarka tana faman zazzare ido, agogon bangon ɗakinta ta duba kusan ƙarfe goma da rabi cuf, arazane ta miƙe tana faman dafe ƙirji tuna cewa bata kaima SGR dinner ɗinsa ba, cikin sauri ta ɗauko mayafi a wardrobe tayi lagensa a kanta, sannan tafito dakin azmee tafara wuce wa don taji ko takaimasa, kwankwasawa tayi sannan ta jira ta buɗe mata,

   A lokacin azmee bacci takeyi jin bugun ƙofar sehrish yasanya ta, farkawa daga baccin nata, tasowa tayi ta buɗe  mata ƙofa,

  Ganin sehrish yasa ta cewa “ashe kin tashi daga baccin? Lafiya naganki ko akwai wani abune?

   Sehrish tace “dama babban yaya na manta bacci yaɗauke ni ne, bankai masa ɗina ɗinsa ba, shine nazo na tambaya naji ko ankai masa,”

  Azmee tace “Ae basu kai ga dawo cikin gidan ba Shi da Omar, pls kada ki koma bacci ko kuma ki sanya alerm na wayarki in sun dawo ki tabbatar kin kai masu abincinsu, sannan kada ki manta ki bama Omar list din da mukayi masa acikin memo dinki,’

  Sehrish ta amsa mata da cewa “to shikena insha Allah zan bashi, mu kwana lafiya,”

  Tayi ma azmee sallama sannan ta fito ta wuce nata ɗakin, gefen gado tasamu ta zauna sannan ta miƙa hannu ta ɗauko handbag ɗinta, wayarta ta ciro daga ciki sannan ta shiga dannata, Tunawa tayi da maganar Azmee da tace mata in zatayi amfani da data, wi-fi kawai zata kunna, Cikin sauri tasanya yatsanta ta janyo top of the screen din wayar ta, danna wi-fi ɗin ya kunnu, tsayawa tayi tana tunanin me zata fara yi da wayar yanzu, tana cikin tunanin nan taji ƙarar shigowar motocinsu cikin gidan kusan ƙarfe 11-30 na dare, mayar da wayar tayi saman bedside drawer ɗinta ta ajiye asamanta, miƙewa tayi tana jiran su kammala shigowa sai taje ta kai masu, sai da tabari 12 tayi dai-dai a lokacin tasan sun kimtsa kowannansu na a bedroom ɗinsa,

Sannan ta fito ta wuce kitchen ba ƙaramin daɗi taji ba ganin azmee ta kammala zuzzuba musu komai na dinner ɗinsu, a cikin tray guda biyu ta jera masu asaman table na kitchen ɗin,

  Hannu kawai tasanya ta ɗauki tray ɗaya ta wuce dashi sashen marshal Omar sallama da ƙarfi tayi saboda yaji ta da kyau, kasancewar yana acikin bedroom ɗinsa bayan tajiyo Muryarsa yana amsa mata sallamarta ta, sai ta shiga cikin falon nasa ta ajiye masa tray ɗin asaman table, sannan ta fita cikin sauri tunawa da Memo ɗin da azmee tace ta bashi, bedroom ɗinta ta shiga ta dauko memon data bari asaman gadonta, sannan ta koma part ɗin nasa a lokacin har ya fito jikinsa sanye da jallabiya ash, wuri yasamu yazauna saman sofa fuskarsa ɗauke da ɗan murmushi ganin Sehrish,

  Ƙarasawa tayi inda yake tare da gaishe shi “Yaya Omar barka da dare, ya gajiyar aiki,” ? 

“Alhamdulillah miss Sehrish, ya maganar aikin dana saku? Ina fata komai ya tafi dai-dai, sannan ya gajiya nasan kun kwaso ta ko? 

  Murmushi tasaki tare da miƙa masa memo ɗin hannunta tace”Gashi nan, mun dudduba gidan duka kuma mun rubuta duk wani abu na furnitures da za’a buƙata acikinsa,” 

  Jinjina kai Omar yayi bayan yasanya hannu ya kar6a yana duddubawa yace “Very good, naji daɗi sosai gaskiya kunyi ƙoƙari, insha Allah zuwa gobe zanyi oder na duk wannan abubuwan da kuka lissafa ana buƙata acikin gidan, zuwa dai next week zan sake tuntu6arku,”

 Sehrish tace “toh Allah ya kaimu lafiya,” 

  Har ta juya zata tafi ya kuma cewa “kina zuwa school ne? Ko baki fara ba?

  Sehrish tace”a’a ban fara ba, amma aunty azmee tace zan fara cikin kwanan nan,”

  Omar yace “Owk, inaso ne suma yaran da nakeson kawo wa cikin gidan can, su fara zuwa school amma zan jira naga wadda zaki fara zuwa, in yaso suma saina sanya su amakaranta ɗaya dake,”

Murmushi sehrish tasaki tare da cewa “mata ne suma? ta tambaya tana kallonsa a lokacin harya fara cin abincinsa yace “Eh ƴan mata ne, kyawawan gaske inason yaran sosai tun dana ganki sai na ga fuskarki tana koma mun irin tasu, nasan saboda son da nake masu ne da kuma kewarsu da nake yi,……’ ya ƙarasa maganar asanyaye,

  Hakanan sehrish taji gabanta ya ɗan faɗi raaasss! amma batasan dalilin faɗuwar gaban nata ba, taso ta tambaye shi sunayen su amma tunawa da cewa ba ta kaima babban yaya abincinsa ba yasa ta saurin cewa “Allah sarki yaya Omar Allah yabaka ikon Kula dasu, yasa su zama alkhairi agare ka,’

Ya amsa mata da “Amin,” 

Sannan cikin sauri ta fuce ta koma kitchen sai da tafara haɗa masa yankakkun fruits acikin madai-daicin plate ta azashi asaman tray ɗin sannan ta fuce hannunta dauke da tray ɗin acikin babban falon suka ci karo da haroon wanda fitowarsa kenan daga part dinsu, night dress ne ajikinsa riga dai-dai guiwa, kawar da kanta tayi tare da miƙar hanya tana jiyo shi yana cewa “a rinƙa haɗawa da sallar dare ko an samu adace asamu shiga,”  

Murmushi sehrish tasaki batare da tace komai ba bayan ta isa part ɗinsa da sallama tashiga, baya acikin falon nasa ƙarasawa tayi ta ajiye masa asaman table dinsa, sannan ta tattaka izuwa bedroom ɗinsa tsayawa tayi abakin ƙopar ɗakin nasa, sallama tayi masa amma shiru babu amsa hakan na nufin yana cikin toilet ko kuma bacci ya ɗauke sa ne, aranta tace “Allah yasa baiyi bacci ba,” 

ɗan sa ƙafarta tayi cikin ɗakin nasa ta shiga ciki sai uban ƙamshi ke daker hancinta kamar wadda tashiga gonar turare, samun shi tayi baje a saman gadonsa daga shi sai Short ajikinsa, ji tayi gabanta ya faɗi rass saboda yadda surar shi ke ɗaukar idonta, 

   sam tarasa me zatayi ta tashe shi don tasan dole akwai yunwa atattare dashi, kuma in ya tashi da safe yaga ba’akai masa abinci ba zai iya tuhumarta,

  Shawara ta rage ma mai shiga Rijiya, tana cikin wannan tsayuwar abakin ƙopan ɗaki nasa ƙafarta har ta soma rawa saboda gajiya da tsayuwa, 

Wani irin Juyi taga yayi daga saman gadon nasa gaba ɗaya ya tafi dukansa zai faɗo daga saman gadon, agigice sehrish ta watsa ciki da gudun gaske ta ƙarasa tare da kai hannu zata tarbesa sai gashi ya buɗe blue eyes ɗinsa kuma nan take yasanya hannusa ɗaya ya dafe ƙasan yarda bazai faɗi ba,

  Tsayawa tayi tana faman sauke haki tare da sauke ajiyar zuciya, matsawa yayi tare da cire hannunsa ya gyara kwanciyarsa saman bedmattress ɗin sannan ya ɗan ware idonsa akan Sehrish dake atsaye, mamaki ne ya kamasa ganin ta tsaye dab da gadonsa me hakan ke nufi badai tazo bane don ta hanasa faɗuwa ba, ƙarfin halin ta yabashi mamaki shin ko ta ina zata iya ruƙoso daga faɗuwar da ya kusan yi? tabbas da ace sehrish  takai hannunta da nufin ta dakatar dashi daga faɗowa daga saman gadon,ƙarshenta ya faɗa mata ajikinta ya danneta tagaza tashi don kuwa ko kusa sehrish bata da ƙarfin da zata iya taimakonsa daga faɗuwa,’ 

Sunnar da kai ƙasa sehrish tayi cikin jin kunya sam tarasa gane ma kanta, ita dai kawai burinta karya faɗo ƙasa yaji mummunan rauni shiyasa tayi yunƙurin tarbosa,

Kasalalliyar muryarsa ce ta ratsa ta da cewa”Sannu da ƙoƙari, amma kada kiyi attempting cewa zaki ruƙoni next time, if not jikinkin ki nei zai gaya maki,” 

 Jinjina kai sehrish tayi tare da cewa”kayi hakuri bazan ƙara ba,”

 Shiru yayi tare da mayar da idonsa ya lumshe su, yana faman sauke ajiyar zuciya,

  ɗagowa ta danyi tare da kallonsa tace “dama……na kawo maka dinner ɗinka ne, yana a falo na ajiye,”

Kusan minti 5 da yin maganarta ta sannan yace”Shigomin da fruits tare da Coffee, su kawai nake buƙata,” 

  Juyawa tayi cikin sauri ta koma cikin falon hannu tasa ta ɗauki plate ɗin dake dauke da fruits ɗin ta shigar masa dashi saman front table ɗim gadonsa ta ajiye masa, sannan ta koma ta dauko masa hadaɗɗen Coffee din dake acikin Cup ta dawo ɗakin nasa a lokacin har ya tashi zaune ya sauko da ƙafafunsa ƙasa, 

a gefen plate ɗin ta ajiye masa sam yagaza buɗe idanunsa da alama ba ƙaramin bacci yake ji ba, sai faman cizon pink lips ɗinsa yake yi,

   Ita dai  burinta ya buɗe idonsa yafara shan fruits ɗin kafin ta tafi, don batason ya kwanta bai ci komai ba acikinsa 😒

   Muryarsa taji yace”What are u waiting for? Ko zaki ban abaki ne? ya faɗi a time din yaɗan ware idanunsa masu ɗauke da bacci,

  Cikin sauri sehrish tace “a’a sai Allah yakaimu, mu kwana lafiya,” 

  ta fadi tare da juyawa cikin sauri ta fuce daga ɗakin nasa sai da tafara tsayawa ta dauki food stuffs din dake acikin tray ɗin da ta ajiye masa sannan ta fuce dasu, a kitchen tasamu wurin ta zauna saman dining table ɗin ciki, buɗe kayan abincin tayi tazauna ta shaƙe plate tana ci, bayan ta kammala ta koma bedroom ɗinta sai da tafara yin sallar isha’e sannan tayi addu’ar yin bacci taja bargo ta lullube jikinta cikin wani irin yanayi na abunda yafaru tsakanin ta da SGR,

***************AUNTY BABBA**********

Da kanta ta girka masu hosana da jahad lafiyayyen abinci ta kuma jera masu shi adining, su duka suka halarta suna ci jahad na kusa da uosana polyayin da Hafsat ke kusa da mommynta dama mai 4 seats ne,

  Duk sun kasa sakewa suci Abincin saboda fargabar da suke ji aransu, kwarama hussana tasamu tana shan kakkauran tea ɗin data haɗa mata tare da bread wanda yaji butter ajikinsa,

  ɗagowa Aunty babba tayi ta kalli jahad tare da cewa “My daughter me yake faruwa ne? Naga tun ɗazu sai fama juya cokali kike yi acikin plate, yakamata ki fara cin abincin ko saiya huce”? ta tambaya cikin nuna kulawa, 

  murya na rawa jahad tace “babu komai Aunty zanci ne yanxu,” 

   Jinjina kai aunty babba tayi tare da cewa “kwara dai kici ta da zafin ta, saboda in ta huce baza tayi maki daɗin ci ba,” 

   Jahad ta amsa da toh sannan ta soma cin taiyar pasta din dake agabanta,

  Mayar da idonta tayi kan na  hussana tace “Yawwa my daughter, ae ke na lura bakya wasa da abinci da alama, kamar ni kike, shiyasa gani nan kamar buhun masara sai uban auki,”

   Jin abunda tace yasamu fashe wa da dariya su duka banda hafsat dake satar kallon mommyn nata, abun ɗaure mata kai yake ganin yadda lokaci guda Mommynta ta sakewa yaran aranta tana cewa “gaskiya Mommy ba ƙaramar ƙuruwa bace wurin iya tsara tuggu, ta iya shu’umanci Allah kaɗai yasan me take shirya wa, koma dai menene nidai ina nan ina zuba ido in gani……👀

Murmushi Aunty babba tasaki tana kallonsu ganin yarda tasanya su nishaɗi aranta tace “haka nake so don kutmar ubanku a hankali zan canza muku tunani har na cimma burina,” a fili kuma ta washe baki tana cewa “ku hanzarta ku kammala ci dare yayi sosai yakamata ace yanzu kun kamma yi nisa a bacci, sannan jahad kada ki manta kafin ku kwanta ki tabbatar kin ba Hussana maganinta, 

  Jahad ta amsa mata da “toh,” 

Bayan sun kammala yin dinner ɗin nasu suka wuce  bedroom din hafsat bayan hussana tasha maganinta sannan suka kwanta, bacci mai nauyi ya ɗauke su………….

Kallon Hafsat aunty babba tayi a lokacin itama idonta nakan Mommyn nata, 

  “tun ɗazu na lura da satar kallona da kike yi  shiru kawai nayi,” aunty babba ta fadi tana kallonta 

 Hafsat tace “hmmmm mommy kenan ni so nake ki faɗamun abunda kike shiryawa game da twins ɗin nan yakamata na sani,”

  Dariya aunty babba tayi kafin tace “bai da amfani koda kin sani hafsat ! ki ma daina tambayata domin kuwa bazaki ta6ajin mutuwar sarki abakina,!”

  Jinjina hafsat tayi tare da miƙewa daga kan dining ɗin tace “Shikenan Mommy kwarama ki ruƙe sirrinki, yarda in asiri ya tashi tonuwa ke kaɗai zakiji jiki ban dani, ni dae nayi nan,” tana faɗin hakan ta wuce cikin bedroom ɗinta, 

 Saman Sofa ta kwanta tare da jan bargo ta lullu6e jikinta, 

Shu’umin murmushi Aunty babba tasaki tare da cewa “Yanzu wasan ya soma, ” 😳 Nikuma nace Allah yaba mai rabo SA’A

***********AFTER 1 WEEK*********

BAYAN SATI ƊAYA 

Acikin waɗannan kwanakin Jahad da hussana ba ƙaramin kwanciyar hankali suka samu ba, sun samu ƴanci sosai acikin gidan jikinsu yayi kyau ba laifi sun ɗan murmure, gashi hafsat bata gajiya da ɗawainiya dasu har fita takeyi dasu yawan shaƙatawa, su fita shan ice cream ko kuma ziyarta gidan friends ɗinta, Aunty babba dae ta zuba ma sarautar Allah Ido burinta kawai Baba alamu ya diro Garin kaduna kafin Zuwan Omar, don tuni Baba Alamu yasanar da ita cewa suna kan hanya yau Litinin zasu sauka kaduna, 😳

A 6angaren Sehrish kuwa tana cikin farin ciki matuƙa saboda makaranta da zata fara zuwa, an riga da an kammala yi mata komai hatta Uniform ɗinta an kawo mata su kusan kala 3, ga sandals ɗinta masu kyan gaske, ga jibgegiyar school bag ɗinta da aka siya mata tare da textbooks na amfani da sauransu, abunda ya rage mata yanzu shine fara zuwa makarantar acikin satin nan, 😇

 Tuni Marshal Omar yayi oder na haɗaɗdun furnitures made in dubai, kamfanin da yayi siyayyar kayan su da kansu, suka tsara mashi gidan wa’iyazubilla wurin kyau ba’a magana, komai sabo fal acikin gidan, kayan kitchen ne kayan ɗaki kayan falo komai fa wannan an zuba acikinsa ba abunda ya bari, bari in taƙaice muku zance hatta wannan kayan store na abinci yasa an jibge masu shi, duka freezer ɗin dake acikin gidan yasa an cike masu shi da Kayan marmari dana sha, komai fa Omar ya tanadar musu na jin daɗin Rayuwa, dama abunda ya hana shi zuwa kaduna kenan saboda yafi son saiya fara gyara masu gidan ya sanya musu komai na more rayuwa acikinsa sannan ya je yaɗauko su, kuɗi sosai Omar yaba Sehrish da azmee don suje yi musu siyayya, koda suka tambaye shi size dinsu na kayan da zasu siya masu gudun kar ayi kuskure, sai yace musu komi zasu siya irin na Sehrish saboda yana da tabbacin cewa tsayinsu da komai na jikinsu bazai wuce na SEHRISH ɗin ba, da sukayi masu siyayyar kaya masu yawan gaske kamar irin na sehrish amma nasu yafi yawa saboda su biyu ne, ƙarshe sai dai motar kamfanin da su kayi siyayar   ta kawo musu kayan har gidan Abusufyan saboda motar junaid bazata iya kwashe su duka ba, saboda shine ke ɗawainiya dasu duk in da zasu fita, finally dae komai ya kammalu,👍

Ga masu karantawa a facebook indai kuna son Cigaba da kawo muku littafin Abban sojoji to ku hanzarta yin payment recharge card zaku tura ta wannan numbar 08103884440, 200 ne saura 3 pages free ya qare, Ga masu acct gashi nan 3196407426 first bank, Bature hafsat Muhammad, wanda sukayi payment ina sane dasu kuma kuɗinsu bazai tafi abanza ba🙌

Back to top button