Kimiya da Fasaha

Yadda Zaka Samu Kudi Ta Hanyar Daukan Hoto Da Wayar Ka

Assalamu alaikum barkanmu da wannan lokaci da fatan kowa yana cikin koshin lafiya.

Kamar yadda kuka sani samun kudi a online ba sabuwar hanya bace domin kuwa mutane da yawa samun kudi online na daga cikin hanyoyin cin abincin wasu, aciki har da ni, domin bansan iya adadin kudi  dana samu a online ba,  kuma a yanzu hakama Alhamdulillah duk wata nakan samu kudi a online.

Saide samun kudin a online ya kasu kala-kala akwai wanda zakayi aiki a biyaka,  akwai wanda zaka sayar musu abu su biyaka, akwai wanda zakayi dillanci nanma a biyaka sannan akwai wanda zaka koyar da wani abu daka iya shima a biyaka.

A wannan darasin zan nuna muku hanya mai sauki wacce zaka samu kudi a online ba tare daka biya kudi ko wani ya koyamaba, abun da kawai ake bukata kawai shine wayar ka, musamman wayar Android ko Iphone.

Hanyar dazan nuna muku hanyace mai sauki kuma bata bukatar wani abubuwa masu yawa, abun da kawai take bukata shine bin dokokin da suka gindaya.

Ita wannan hanyar samin kudin itace: daukan hoto a wayarka sannan ka dorashi a internet kuma a biyaka kudi ta dalilin wannan aikin da kayi.

Yadda abun yake shine:

Akwai mutane dayawa wanda suke bukatar samun hotuna na abubuwa daban daban,  misali hoton,  wani waje, ko yanayi,  kokuma hoton abun al’ajabi kokuma na mamaki, to akwai irin mutanen da suke bukatar irin hotuna wanda babu wanda yake dasu, sai kai daka dauka ka dora, masu bukata suna shiga shafukan yanar gizo domin neman ire iren wannan hotunan, hakanne yasa wasu daga cikin manyan masu kirkira suke kirkirar manyan shafuka su bada dama ayi register domin ana dora hotunan da ake dauka a waya sukuma.idan kadora sai su biyaka. Daga cikin irin shafukan da suke wanna aikin akwai Freepik.com wanda dashi zamuyi aiki.

Yadda zakayi Register domin fara samun kudi ta hanyar daukan photo da wayar ka.

Da farko ka shiga wannan Link din na kasa

https://www.freepik.com/

Bayan ka shiga ya bude saika duba daga sama zakaga SIGN UP saika shiga, anan zai baka dama kayi Register sai kayi register da email dinka.

Daga nan bayan ka gama Register zai dawo dakai cikin shafin,  anan sai kayi chan kasa ka duba inda aka rubuta Sell Content saika taba wajen.

Kalli wannan videon dake kasa domin ganin yadda zakayi harka fara samun kudin.

Back to top button