Zakuna Biyar Page 50 By Princess Teema
Idanunta a datse gam, sai dai ba barci take yi ba, ga hawaye suna ta faman wanke mata gefe-gefen kunnenta. A rikice ya fara ambatar sunanta, ina bata amsa ba, karisa yaye blanket ɗin nata ya yi. Tana kudundune shiru bata iya motsawa ba.Shi ne ya kai hannu zai ɗagata Zaynish ya shigo. Kallo ɗaya Zaysh ya masu ya ɗauke kai, sai ya ce. “I want to talk to you, idan ka gama ina ɗaki”. Bai jira amsar Noor ba juya ya fita, bai zaci V tana ciki bama da ba zai shigo ba.Ɗagota gabaɗaya ya yi tare da ɗaurata a saman kirjinsa, cikin kiɗima ya ce. “I know that you’re hearing me, please talk to me my Juliet”……. Shiru bata motsa ba, tana dai cigaba da hawayeta. Hannayenta ya riko cikin nasa. “I’m so so sorry my Julie, I know I have wronged you greatly, I have punished you severely, but it is not my fault, it is your intense jealousy that makes me feel hurt when someone interferes in your business or speaks to you”. Yana shafa kanta zuwa bayanta ya faɗa.Ya sake cewa. “You know that i really love you more, right?”…….. Sai a lokacin ta ja doguwar numfashi game da saukewa a hankali, slowly ta ɗan motsa idanunta kafin ta buɗesu. Da sauri ya ɗan datse nasa idanunsa saboda ganin yadda idanunta suka yi jajir kamar wuta.Intently ya waro idanun nasa a kanta. “Sorry my Juliet”. Ya faɗa in a low way. Kallonsa kawai take yi bata yi magana ba. Wayansa ya ɗauko, number Manassa ya kira, bugu ɗaya ta ɗauka, a takaice ya ce. “Comes to my room with your rucksack now”. Daga haka ya katse kiran. Ajiye wayar a gefe ya yi, ya dinga lallaɓata tamkar kwai a saman plate, ya yi nadamar abin da ya yi mata, bai kamata ace ya yi fushi har su kwana waje daban-daban ba, ya zafafa dayawa sosai. Manne da juna Manassa ta shigo ta samesu, sai da ta kame ta sara mashi sannan ta yi dropping rucksack ɗin nata a ƙasa. Kwantar da V a jikinsa da kyau ya yi. “Zo ki duba mun lafiyarta”. Ya faɗa ba tare da ya kalli Manassa ba. Da sauri ta jawo rucksack ɗin ta nufosa tana faɗin. “What’s wrong with her sir?”. ….. Bai iya bata amsa ba sai ido da yake bin V da shi, dik hankalinsa ya gama tashi bawan ALLAH.A kusa dasu Manassa ta ajiye rucksack ɗin nata, ta fito da wata ƴar na’urar gwajin cuta, cike da kwarewa ta fara duba V. Shiru ya yi yana kallon matar tasa, yana jin kamar a dawo mashi da ciwon jikinsa a barta ta huta. After like 10 mins Manassa ta ɗago ta kallesa, a natse ta ce. “Sir wannan ba zazzaɓin kwayar cuta bane, damuwa ce da yawan kukan da ta sha, tana ɗan samun farinciki ya musanya damuwar zata warware”…….. Kai ya jinjina alamar to kafin ya ce. “Thank you sister”.Manassa da rashin ji, tasan V bata son allura, sai ta ce. “But sir, akwai wani injection ɗaya da zan bata yanzu dan ya saukaka zafin jikinta”…….. Ai V bata san time ɗin da ta waro idanunta waje ba, ta sa hannu ta ƙanƙame Noor sosai, da kyar muryarta na rawa ta ce. “My Romeo, don’t let her inject me”. Idanunta na ciccikowa da sabon kwallah ta faɗa. “I can’t”. Ya faɗa yana ɗago da kallonsa a kan Manassa. “Is it really necessary that she must be given injections?”.Manassa looked at him and said. “Yes sir, the injections are very important, they must be given”. She said, trying to suppress the laughter that was about to escape so she wouldn’t ruin her plan, tsabar yarinyar nan bata son zaman lafiya, tana son rikita mana V.Noor turned his gaze back to V and said gently. “Let her give you the injections, okay? It won’t hurt you, I’m here with you, alright, my Juliet?”. He said as he stroked her hair.Immediately she panicked and tightly held onto his hand that was clasped with hers, her eyes trembling as they moved from his face to Manassa’s face. With great difficulty she managed ta ce. “My Romeo, I don’t want those injections, please, I will die if she gives it to me, they are painful, tell her to go so I can feel better”. She ended up almost bursting into tears, crying pitifully as she released a warm, feverish breath.Ganin ta fashe da kukan yasa Manassa yin gaggawar cewa. “Sorry my love, ba da gaske nike yi ba, naga kin ki yi wa sir ɗinmu magana ne yasa na ce let me help him to do something that will make your mouth open and talk”. Ta kai karshe tare da ɗaukar rucksack ɗinta, da gudu ta nufi waje dan kada Noor ya kamata ta saka ƴar gold kuka. Aikuwa ya yi yunkurin kamata ɗin ALLAH yasa ta tsere, kuma dama ya so ajiye mata ko rankwashi ɗaya a kai in da ya kamata, dan ta saka mashi Julie kuka, bata kyauta ba. Ganin ta gudu yasa ya kwantar da V, ya miƙe ya fito. Jim kaɗan ya dawo hannunsa rike da ruwa a ƙaramin bowl. A kusa da ita ya zauna, ya ɗauko hanky ɗinsu na sojoji, a cikin ruwan ya tsoma, sannan ya rabata da kayan jikinta dikka. Dik rashin kunya na yaran GAT sai da ta ji kunyar yadda ya tuɓeta tsirara da ranar ALLAH, da sauri ta takure jikinta waje guda. Ganin haka yasa ya ɗan sunkuyo kanta, suna kallo juna cikin ido ya ce. “What again? Meyasa kike ɓoye jikinki? Is it not my property?”. Tana kallonsa bata iya amsa mashi ba, ya ɗan ɗaga jikinsa daga sunkuyon, ya jawo blacket ya ɗan rufeta zuwa ciki ganin ta takure kanta sosai. Sai ya ɗauko hanky ɗin, ya matse ruwan kafin ya fara mammanna mata a fuska zuwa sauran jikinta. Tin tana ɗan noƙewa har ta sakar mashi kayansa, dama jikinsa ne, ya bi ko’ina ya dinga sanya mata ruwan hanky ɗin har sai da jikinta ya yi sanyi, sannan ya rabu da ita tare da ɗaukar ruwan ya fitar waje.Ya dawo ya ɗauki abinci, ya ɗauketa cak ya ɗaura a saman laps ɗinsa bayan ya mayar mata da kayanta, sai ya fara bata abincin a baki. Shagwaɓa ta hau zuba mashi kan ita ba zata ci ba, ita dai ya kyaleta, shi kuwa ya ce ɗure zai yi mata, ganin da gaske ne yasa ta hakura ta fara karɓar kaɗan kaɗan, yana bata yana lallaɓata kamar wata ƴar baby, bata san time ɗin da ta ci dayawa ba, bayan ya tabbatar ta ƙoshi sai ya kwantar da ita ya miƙe da plate ɗin ya fito.After like 5mins ya shigo hannunsa rike da robar, a gefe ya ajiye game da komawa kusa da ita, ya zauna yana kallonta. Lumshe idanu ta ɗan yi, can ƙasan maƙoshi ta ce. “Forgive me my Romeo, it won’t happen again”. Hannayenta ya riko cikin nasa. “Forgive me too my wife, nima na yi laifi kin ji?”………. Buɗe mashi hannayenta ta yi alamar ya zo, da sauri ya kwanto kanta yana kallon fuskanta. Ɗan ɗago kai ta yi, ta sumbaci lallausan cheek ɗinsa. A tare suka sauke cool ajiyar zuciya, ya ɗan saki one side smile kafin ya sumbaci cheek ɗinta shi ma…… “I love you more my Julie”. Ya faɗa yana kai hannunsa saman gashin kanta, ya fara shafawa a hankali. Samun damar sauke double ajiyar zuciya ta yi, take ta nemi zazzaɓin ta rasa, ya gudu, dama na kewan masoyi ne, to daga dawowansa ya gudu, ta ji wani karfi ya zo mata, da sauri ta miƙe zaune, ya ɗan ɗagata ya zauna shima, faɗowa jikinsa ta yi tana murmushi, one side smiling ya saki tare da rungumeta sosai, yana jin tamkar ya tsaga kirjinsa kawai ya sanyata ciki ko zai huta, musamman yadda ta bashi abu mai darajarta watau budurcinta, ba zai taɓa manta wannan rana ba, shi kaɗai yasan irin musulmin daɗin da ya ji, sonta ya ninku a zuciyansa sosai da sosai kuwa. Haka suka wuni cikin farinciki da farantawa juna rai, ya kara mannewa da ita, yau tin safe bai fita koda bakin ruwa bane, yana kwance cikin tantinsa tana kwance a kirjinsa, ko yaya ta motsa sai ya ce me take so, a nan aka kawo masu abincin rana, suka ciyar da juna cike da so, yana jin kaman kada ya motsa ko nan da can. Sai around 4:30, sun yi sallar la’sar, ya dawo cikin tantinsa, nan ya iskota tsaye tana ƙoƙarin sanya botir na wandon jeans ɗin jikinta, ta yi wanka dan ta samu lafiya sosai, fitansa ya je wajen sallah ne ta samu damar yin wanka. Tana ƙoƙarin jan zip ɗin sama sai ganin hannunsa a kan zip ɗin ta yi. Ya kama zai zuge mata sai taga ya zuge ƙasa.Ɗago kai ta yi zata yi magana ya yi gaggawar haɗe bakinsu, daga nan ya ɗauketa sai saman mattress, gabaɗaya ya manta bata da lafita, ya aikata abin da bai yi ba jiya, ya yi mai gabaɗaya, yana mata kuka tana mashi kuka ita ma, yana sambatun daɗi ita kuma tana na azaba. Dik ya wanke mata gefen wuya da hawayensa na kukan daɗi. Sai da ya samu gamsuwa mai kyau sannan ya kyaleta, ya ɗan rungumota ya hau rarrashi bayan ya goge nasa hawayen kenan. A lokacin saura 20 mins su tafi wannan aiki. Bai sanar da ita akwai in da zasu je ba, da ya kammala rarrashinta sai ya ce. “Kada ki je ko’ina, ki zauna a nan zamu je wani waje, and ki kunna laptop ɗinki, get ready and wait for my call”. Tana turo baki ta amsa da. “To amma kada ka jima”…… Kai kawai ya jinjina mata, dan yasan jimawa kam dole ne, in sun yi sauri ne su dawo gobe cikin dare, wajen yana da nisa. Haka ya lallaɓata kafin a gurguje ya miƙe ya je ya yi wanka, ya fito ta taimaka mashi ya shirya cikin normal kayan ba uniform ba, sai yabon kyansa take yi, musamman European hair ɗinsa dake nannaɗe kamar indomie. Ya jawota jikinsa ya rungume, yana shafa bayanta, ya ɗan sunkuyo kanta kaɗan, a kunne yai mata raɗa kamar haka. “This thing is so sweet, over and over, zan tafi ina farinciki matuƙa, my God bless you my wife, i love you forever and ever”…….. Ta rikosa ta bayansa kafin ta ce. “Take good care of yourself my Romeo, ka dawo da wuri, dan ka fara saba mun da kwanciya a jikinka, bana jin zan iya barci ba tare da kai ba”. Ya ɗan sumbaci forehead ɗinta, yana kokarin saketa ta yi gaggawar ɗaga kafafuwanta ta haɗe bakinsu. Cikin zafa ya fara kissing ɗinta yana lumshe idanu, a can bayan wasu duwatsu dake nesa da tantinsu kuma su Zaysh suna tsaye suna jiransa, dik ya susuce a kanta, yana jin tamkar kada ya tafi, kaman dai ya zauna da ita, sai ma da ta kara zautar da shi, a cewarta wai dan kada ya daɗe, dan ta yi maganinsa yasa tana tsaka da kissing ɗin nasa ta ɗaura hannunta kan gaban wandonsa.Lamarin da ya kara gigitar da shi, yana jinsa da karfi da lafiya, yana jin kamar idan aka barsa daga nan har washegari da safe zai ta yi babu hutawa ne, gani ma yake yi ko mata irinta cikin trailer aka kawo mashi kafin wayewar gari zai gama da su, yana jin kamar ta mashi kaɗan ita kaɗai.Tana ɗaura hannu kan gaban wandonsa ya rikice mata, tuni ya tura hannunsa cikin rigarta ya fara wasa da kirjinta, dama ba dan ya ƙoshi ba ɗazun ya saketa, sai dan tausaya mata kawai. Cak ya ɗagata sai kan mattress, ya manta da cewa zai yi tafiya, ya hau ƙoƙarin rabata da kayanta sai ga kiran Leo ya shigo wayansa. Da kyar ya iya zaro wayan, bai lura da waye mai kiran ba, idanunsa sun rufe ya yi picking up, cikin romantic voice ya ce. “Hello”……… Tin da Leo ya ji haka ya gane karatun, sai ya ce mashi. “One minute”. Daga haka ya katse kiran. Zaynish da Vash suna zaune a kan duwatsu suna ɗan hira sama-sama.Ai Noor jifa yai da wayar dik da ance mashi one minute, bai saurara ba, ya rabata da kayanta ya sake gwangwajewansa, sai da ya samu natsuwa ne ya tina da abin dake faruwa. A gurguje ya diro kasa, in less than 5 mins ya watsa ruwa a jikinsa ya dawo, this time ƴar kaniya tana kwance ta gagara miƙewa, idanu sun raina fata, ta yi kuka har idanun suka kumbura bai sarara mata ba, da ta ce bata ji, jiki dik ya yi laushi. Ta gagara miƙewa tai wa masoyi rakiya.Sai shessheƙa take yi, a gabanta ya tsuggunna bayan ya kammala shiri, ya riko hannunta ɗaya, ɗayan hannunsa ya ɗan shafa kanta. “Ki shirya mun kanki, in na dawo sai mu yi round 3 ko my wife?”. Ya faɗa cikin zolaya kuma cike da sabuwar kaunarta. Kallonsa kawai take yi ta gagara yin magana. Ya sumbaci cheek ɗinta kafin ya sama albarka, sannan ya miƙe, yana kallonta cike da so, tamkar kada ya tafi ya barta, haka ya jure ya fito, kai tsaye ya nufi in da suka yi zasu haɗu. Ita dai tana kallonsa har ya kurewa ganinta sannan ta lumshe idanu.Mu koma baya kaɗan. A tare Jehan da Arya suka wuni, sai dai wunin yau gabaɗaya ya karewa Arya ne da tinanin Leo da kuma tunanin tausar da yai mata a cikin ranta, ga shi bata samu damar ganinsa ba, dan bai fito waje ba, yana cikin tantinsa sai lokacin sallar azahar ya fito, a lokacin ita kuma ta je wajen korama, ta yi wanka, tana dawowa rike da hannun Jehan suka ratso ta wajen da suke yin sallah.Tin daga nesa ta zuba mashi idanu, yana cikin tsantsar natsuwa, kallonsa a gabansa in da zai sa goshinsa na sujjada, yana karatun Alqur’ani cikin tsantsa natsuwa. Gabaɗaya Arya rasa natsuwarta ta yi, ta dinga kallonsa har suka wucesu, sai da ta sake waigowa har ta kusa cin karo da itace. Jehan kuwa ta ce mata da fillanci ita ma zata yi sallah, dan ta iya, tana yi wajen fulanin can. Ta kwatantawa Arya game da nuna mata su Leo ta ce irinsa zata yi, Arya ta ce to su je cikin tanti su yi, Jehan ta ce zata yi alwala, Arya ta sake rakata bakin ruwa, ta jirata ta ɗauro cikakken alwala mai kyau, sannan ta fito suka koma cikin tantinsu, ta ɗauko mayafinta da Arya ta wanke mata, wanda ƴan fulani suka bata, ta yafa shi kafin ta tada sallah.Arya ta zuba mata ido tana kallonta, sai ta ji tana sha’awar addinin, musamman yadda taga Leo a cikin addinin, sai take jin zata iya bin wannan addini, addini mai natsuwa da haifar da kwanciyar hankali. Shiru ta yi tana tinanin yadda za’ayi ta koyi addini, ya za’ayi ta yi register, wajen waye zata yi? Dan ta ɗauka register ake yi a shiga.Tana zaune har Jehan ta idar da sallah, ta ware hannu ta yi addu’a sosai, sannan ta shafa game da miƙewa ta koma kusa da Arya ta zauna. Arya na son tambayarta game da addinin amma bata san da wani yare zasu yi magana ba tin da bata jin na Jehan ita ma bata jin nata, sai ta yi deciding ta fara koya mata turanci da kuma reading, wannan tunani yasa ta fara ƙoƙarin koyawa Jehan karatu da kuma turanci.Daidai wannan lokaci Angelina ta shigo ta ɗauki mouse ɗinta ta fita, kai tsaye tantin Zaynish ta koma, tana zuwa ta zauna a gaban laptop ɗinta, ta jona mouse kafin ta laluɓo number Aunty Ummie a wayarta.Bugu ɗaya tai mata Aunty Ummie ta ɗauka, cikin girmamawa Angelina ta ce. “Hello Aunty ina wuni”…… Aunty Ummie dake hospital tana bin layi ne ta amsa da. “Lafiya lou sister ɗita, ya aiki ya gida dasu mama?”…… Angelina tana murmushi ta amsa da. “Sunanan lafiya sun ce in gaisheki”. Dik da Aunty Ummie bata jin daɗin jikinta hakan bai hana ta saki murmushi ba jin cewa iyayen Angelina na gaisheta, bata jin dadin jikinta haka ta daure ta biyewa Angelina suka dinga hira har lokacin da Angelie taga Zaynish zai shigo cikin tantin, da sauri ta cewa Aunty Ummie. “I will call you back Aunty”. Bata jira amsarta ba ta katse kiran.Take ta haɗe natsuwanta kafin ya shigo. Yana shigowa a gefenta ya zauna game da kai hannunsa ya jawo laptop ɗinta, a natse ya hau duba abin da yawakana. Har around 3 suna tare, sai 3:30 ne Aunty Ummie ta kira numbersa. A natse ya fara bin wayar da kallo, ita dai tana ta kallonsa, watau natsuwar Zaynish daban take a cikin sauran sojojinsu bayan Leo, ko shekara goma zaka zauna da mutum biyun nan Leo da Zaysh ba zaka iya faɗar ainahin halinsu ba, Zaysh yana da kamewa da sirri matuƙa, zurfin cikin bala’i ne da shi, a yanzu dik duniya mutane biyun nan kawai ya yarda dasu, team 1 nasu da Aunty Ummie, ko uncle ɗinsa bai yarda da shi ba, yana dai bashi girma, kuma dik duniya team 1 da Aunty Ummie kawai suke sanin me yake ciki, Aunty Ummie ma wani abin yana ɓoye mata, kamar yanzu da ya ɓoye mata suna daji, and ko su Leo wani abin yana ɓoye masu kamar yadda Leo ɗin ma yake ɓoye masu wani abin, kunga Leo ya ɓoye masu batun aikinsa na shi da Arya, baka isa iya gane ainahin zuƙatan mutane biyun nan ba, dik abin da ka ga ka sani a kansu to su suka yi ra’ayi suka faɗa maka, suna da banbanci wasu halaye, Leo yana da saurin fusata, Zaynish yana da hakurin sai ka turasa bango, Leo idan ya fusata ya yi faɗa komai ya wuce, Zaynish ba’a saran mumini sau biyu a rami ɗaya haka yake, in ka mashi sau ɗaya, ya hakura har ka turasa bango to fa ko waye kai zai zubaka a kwanton shara ne, dik basu da yawan magana, amma in suka fara magana Leo yana faɗar magana kai tsaye daga zuciyansa, ba ruwansa tai maka daɗi ko kar ta yi maka shi dai ya faɗa, ma’ana baya tauna magana, yana da ɗabiar IRON FIST na baka da wuta kuma baka da aljanna bare su ji shakkar mutum.Zaynish ba shakkar kowa yake ji ba, kawai dai ɗabia ce ta namu na ƴan Afrika, sai mun tauna magana muke yinta, dan haka baya magana kai tsaye, sai ya tauna, idan yaga faɗarta ya fi alkhairi zai faɗa, idan kuma ya ga faɗarta ba alkhairi bane yana fasawa. Dik suna da dogon nazari a kan abu, kuma in suka yi nazari suka yanke hukunci sai an sara masu, suna da mugun natsuwa, Zaynish yana da girmama nagaba da shi sosai, yana da ladabi, Leo baya ji guy ɗin nan, ya raina kowa, gani yake kowa a kasan shi yake, zaka iya nunawa Zaynish iko ya ɗauke kai ya rabu da kai, ka kuskura ka nunawa Leo iko in ta zo da tsautsayi sai dai wani ba kai ba, dikkansu idan suna son abu soyayyar gaskiya suka iya, basu iya rayuwar munafurci ba.Hannu ya miƙa ya ɗauki wayar, ya katse kiran nata tare da shiga account ɗinsa, ya sayi kati na kamar 10k a kuɗin Naija, sannan ya bi kiran nata. Cikin sanyin murya ya ce. “Assalamu alaiki”…… Daga ɗayan ɓangaren ta amsa da. “Wa’alaikumussalam”…….. Wani irin natsuwa ya kara yi, cikin nuna kulawa ya ce. “Aunty Ummie lafiya na ji muryarki haka? Baki da lafiya ne?”. “Eh to ina zazzaɓi ne, na zo asibiti a dubani, ba wani ciwo bane”….. Kai ya ɗan jinjina, sai kuma ya ce. “Ina yaya Faisal?”……… “Ya dawo jiya yana gida”. Shiru ya ɗan yi, ya ɗan yi mamakin jin amsarta, sai kuma ya ce. “Yah Faisal yana gari kuma bai kaiki hospital ba, meyasa?”……. “Babu komai, jiya fa ya dawo da daddare, ya gaji yana barcin huce gajiya”.Tin daga kan yanayin maganarta ya gane karya kawai ta yi mashi, saboda bata saba karya ba, in ta yi sai ya gane. Nisawa ya ɗan yi kafin ya ce. “Bari in kirasa mu gaisa”. Ya faɗi hakan ne dan ya fahimci gaskiyarta, baya son ya ce tai mashi karya saboda na ce maku yana da girmama manya, amma yana da hanyoyi da dama da yake bi dan gyarawa manya kuskure idan suka yi cikin sauƙi.Da sauri ta ce. “A’a kada ka kirasa yanzu, please ka bari sai anjuma in na koma zan haɗaku, yanzu yana barci ne”….. Ya gama gano akwai matsala, yadda muryarta ke rawa take ƙoƙarin hanasa kiran……. Kai ya jinjina kafin ya ce. “To yanzu dai an gama dubaki ne?”. “Am….. In…. To …. Dama likita ne ya ce yana son yin magana da mijina, kuma yayanka yana barci shi ne na kira ka yi magana da shi matsayin yayanka”. Ta faɗa murya na rawa………. Ɗago idanunsa a kan Angelina dake kallonsa ya yi, mamakin Aunty Ummie yasa ya ji kamar ana kiran sunansa a waje, a ransa ya ce faɗa suka yi da Faisal ɗin ne? Menene yakefaruwa da har take son ya yi magana matsayin mijinta? Me yake damunta? Lallai akwai gagarumin matsala.Jin ya yi shiru ne yasa ta ce. “Ba wani abin bane fa, nasan halinka yanzu zaka ɗauka ko wani abin ne”…… Uhm ita da bata yi karatu bane wai take shirin yi mashi wayau, dik da dai ance babba kam babba ne, amma ai ta kwafsa tin a farko, babu rami me ya kawo batun rami da zata ce babu wani abu dan tasan zai ɗauka akwai wani abin, akwai ɗin kenan.Nisawa ya ɗan yi, ya mai da kallonsa kan laptop na Angelina dan ya ga giftawar wani abin ta gaban drone ɗinsu, hannu ya kai saman mouse ɗinta kafin ya ce da Aunty Ummie. “Babu komai, haɗani da likitan, sannan kafin nan faɗa mun meyakefaruwa da Yah Faisal? Please kada ki ɓoye mun”.Shiru ta ɗan yi, sai kuma ta ce. “Gaskiya zan faɗa maka shi ne matsala muka samu da shi, ya dawo gida tin last week ba jiya ba, ya dawo da makudan dukiya, da na tambayi in da ya samesu sai ya ce a haƙar gold yai nasarar samun wani dutse mai daraja ya kai kasuwa, ban yarda da shi ba, na damu sosai, da na tsananta damunsa da tambayar ya faɗa mun gaskiya ina mashi nasiha shi ne ya fara faɗa, ya ce mu koma sabon gidan da ya saya a GRA, na ce ni ba zan koma gidan da ban san da kuɗin me aka saye shi ba, shi ne ya yi ta faɗa wai ina zarginsa, ya ɗauki amaryarsa suka koma can, ni suka barni a tsohon gida wai idan na ga dama in dawo sabon gida in samesu, shi ne takaicin yasa kirjina ya fara ciwo har dai na ɗan kwanta gajerar jinya, yau naga abin yai yawa na zo asibiti”. Tin da ta fara magana ya shiga dogon nazari, gabaɗaya ya ji abin yai mashi some how haka. Sai da ta gama jawabi tas, sannan ya ce. “Haɗani da likitan, sannan kada ki koma sabon gidan, ki jira kira daga gareni tukun nan”. A takaice ya faɗa……. Kai ta jinjina alamar to, still ya fahimci akwai abin da take ɓoyewa ba iya maganar kenan ba, amma ya gano bakin zare a iya ɗan wannan bayani da ta mashi, dan haka a haɗa shi da likitan bayan sun gaisa ya ce mashi. “Dr ina son sanin me yake damunta”. Likita ya hau mashi bayani sosai. “Ta kamu da ciwon zuciya saboda tsananin damuwar da take ɓoyewa a ranta, sannan hawan jini yana gab da kamata, shekarunta sun yi kankanta da damuwar da take tarawa kanta, dole kullum kirjinta ya dinga ciwo sosai”……. Ni kam na ce ba dole ta damu ba, ga rashin haihuwa, ga kishiya, ga bala’in dangin miji, ga ba uwa, ba uba, uncle ɗinta ɗaya tilo gidansa babu daɗin kai ziyara saboda bala’in matarsa, babu ta in da Aunty Ummie ke juyawa ta samu saukin rayuwa face wajen Zaynish kawai, shi kaɗai take kira ta ji daɗi, kishiya ta balbaleta da masifa, ta daketa ta zubar mata da ciki, mijin dake bin bayanta yanzu ya samu abin duniya true color ɗinsa yana shirin bayyana, ya ALLAH, ina ake son wanna baiwa ta tsoma kanta ta ji daɗi ne? Ta ji da zafin rashin haihuwa ne ko damenene?.Bayan likita ya gama mashi bayani Zaynish ya ce. “Na yi tafiya ina nesa, yanzu kai mata dik abin da ya dace, sannan ina son kai mata scanning, ka dubata sosai, idan ka yi scanning ɗin ka duba yanayin karfin ciwon zuciyar tata ya yake, ina jiran ji daga gareka, dik wani kuɗi da za’a kashe ka haɗa mun bill ɗin ka bata ta turo mun”. Yana gama magana ya katse kiran, ya kira mai yi mashi canjin kuɗi ya sanar da shi akwai account da zai turo mashi ya saka mashi kuɗi. Mutumin ya ce ba matsala.Angelina dik da bata jin yaren Hausa ta fahimci lallai Zaynish yana cikin tashin hankali da damuwa. Yana ƙoƙarin bin abin da ya gifta ta gaban drone nasu kenan kiran Aunty Ummie ya sake shigowa. Katsewa ya yi ya kirata yana aikin nasa bai dakata ba. Tana ɗauka ta ce. “To na sallameka ne da zaka katse?”……. “Sorry, na bada damar a duba mun ke sosai ne”……. Kai ta jinjina kafin ta ce. “Dik wani ɓoye-ɓoyenka dai na ganoka, yanzu dai ina kanwar tawa take?”……… Cike da mamaki ya ce. “Aunty ban gane ba”. “Ina Angelina?”. Ta faɗa kai tsaye. Ɗago da dara-daran eyes ɗinsa a kanta ya yi, mamaki yasa ya ɗan kyafta idanunsa sau biyu a kanta, while ita ma shi take kallo, tin da yake bai taɓa karewa fuskanta kallo ba sai yau, ba shakka ya shaida kyakkyawar gaske ce. Ɗauke kallonsa daga kanta ya yi kafin ya ce. “Aunty a ina kika santa kuma?”.”Awwwww baka ɓoye mun ba? ALLAH ya dubi rokona ne ya bayyana mun ita, maza bata waya in ji ko kuna tare”….. Slowly ya saukar da waya daga kunnensa ya miƙawa Angelina bayan ya sanya a H-Free, yana ta kallonta mamaki ya hana shi kwakkwarar motsi. Karɓar wayar Angelie ta yi tana wani sunkuyar da kai. “Hello my Aunty”. Angelina ta faɗa. Can ya ji Aunty Ummie na dariya kaɗan-kaɗan kafin ta ce. “Fatan kina kula mun da kanina sosai ko?”. Ɗagowa Angelie ta yi, ta ɗan saci kallonsa, taga dai ita yake kallo, yasa hannu ya riko haɓarsa yana mamaki, kasa ta yi da kai kafin ta ce. “Sosai Aunty, ina bashi kulawa na musamman”. Zazzaro ido Zaynish yai a kanta, a cikin ransa ya yi salati ya kai sau 10, wai tana kula da shi, ko yaushe hakan dik yake faruwa bashi da labari?……..”To Please ki kara kula mun da shi sosai, ya fi zinari daraja, sannan in yai maki abu kada ki yi fushi dashi kin ji? Ki faɗa mun in ɗau maki fansa”….. Aunty Ummie bata son su rasa Angelina dan ma kada su rasa samun haihuwar ƴan 4, shiyasa kullum take faɗa mata idan Zaynish yai mata abu kada ta yi fushi da shi ko ta daina kulasa, ta faɗa mata zata ɗauki mataki.Ai Zaynish kam yanzu kansa ta gama ɗaurewa………. “Ba zan yi fushi da shi ba Aunty, zan kula sosai”…… Fara’a Aunty Ummie ya ninku, bata da lafiya amma tana dariya saboda son da take yi wa Angelie, ta dinga zuba mata ruwan albarka kafin su yi sallama, bata sake cewa a baiwa Zaynish waya ba ta katse kiran. A ransa ya ce awww saboda wannan ta sake kiransa kenan, lallai ma Aunty Ummie, watau yanzu kishiya zata yi mashi a cikin zuciyarta, mata kenan.Miƙo mashi wayan Angelina ta yi tana ɗan ɗagowa ta saci kallonsa. Bai karɓa ba sai ya ce. “A ina kika san Aunty Ummie?”. Ya yi maganar babu wasa a tattare da shi…… Can ƙasa ta ce. “Maso tsuntsu shi ke binsa da jifa ai”. Ya jita sarai, amma yai kamar bai ji ba, ya sake tambayarta ina ta san Aunty Ummie. Ɗan turo baki ta yi wanda ya ƙara mata kyau, tana ƴan kame-kame, sai ta ce. “I took her number from your phone, dana ga hotonta ne naga ta mun kyau shi ne na ji ina sonta sosai, shi ne fa na kirata muka gaisa, daga nan ta zama Auntyta nima”. Sosai ya ji daɗin kalamanta, musamman yadda ta ce daga nan ta zama Auntynta, amma bai nuna alamar ya ji daɗin ba, sai ya ɗaure fuska game da cewa. “Waye ya baki izinin taɓa mun waya?”.”Sorry sir”……. Cikin faɗa ya ce. “Waye ya baki izinin taɓa mun waya i said?!”…………. Muryarta na rawa ta ce. “All because of you ne”…… “Because of me?”. Ya faɗa yana pointing kansa da yatsa. Ya tamke fuska tamau, babu wasa a tattare da shi…….. Kai ta jinjina. “Yes, because of you sir”. “How because of me?”……… Ta ɗago ta kallesa, ido cikin ido, babu tsoro kafin ta ce. “Because I love you, and I love those who are close to you, shi ne yasa na kirata, i like her from the button of my heart”……… Ya rabb, kashe mashi baki ta yi, bai taɓa jin kalmar love daga bakin wata daban ba Aunty Ummie ba sai yau, sai ya ji wani iri. Hannu ya miƙa ya karɓi wayansa, ya ɗauke kallonsa daga kanta, ya rasa amsar da zai bata sai ya jawo laptop ɗinta dan su cigaba da aiki. After like 5mins yana nazarinta a cikin ransa sai ya ce. “Shekarunki nawa da har kika san wani abu wai love?”. Ya yi maganar ba tare da ya kalli in da take ba. “16 years now, and nasan komai ne because of you, i love you and i love everything about you”……. Bai ɗago ya kalleta ba ya ce. “Don’t say this word out again, bana soyayya kuma ba zan yi ba, kada ki sake cewa kina sona!”. Ya kai karshe tare da miƙewa ya fito dan shirin yin sallar la’asar. Ita kam ko a jikinta, gargaɗinsa bai shiga kunnenta ba, ta ɗago ta bisa da kallo har ya kurewa ganinta, murmushi ta ɗan yi kafin ta ce. “Sir baka san wacece Angelina ba, wait and see, zaka fara soyayya ne ma babu wanda ya sani, dani kake magana”.Ta cigaba da aikinta, ta dinga kewaye da drone ɗinsu a wajen tana tina kalar abin da zata dinga mashi. After some minutes, around 4:30 ya dawo cikin ɗakin. Normal kayansa jeans and t-shirt ya ɗauka ya fito waje, da kallo ta bisa tana tina in sun fara soyayya ita zata dinga saka mashi kaya, dan tasan wanka zai je ya yi ya shirya, ta ɗan yi tagumi tana tinanin irin kulawar da zata bashi.A haka ya dawo ya sameta, ya ce. “Bani drone ɗinki”. Ya faɗa ba tare da ya kalli in da take ba. Da sauri ta fito mashi da su guda 10, dama 12 aka basu, ta tura biyu cikin daji. Drone ɗin ya karɓa, ya duba karami a ciki, ya ce ta mashi connecting da laptop ɗinta, ba musu ta yi, tana gamawa ya miƙa mata hannu kan ta bashi drone ɗin, da sauri ta ɗaura hannunta kan nasa tana kallonsa, ta zaci ya miƙo hannu zai kama nata hannun ya miƙar da ita ne, dan tasan in sun haɗa drone ai sakinsa suke yi ya tashi, shi kuma me zai yi da shi da zai karɓa? Shiyasa ta zaci hannunta zata bashi.Ɗago da kallonsa a kanta ya yi. Da sauri ta ɗauke hannunta, tamke fuska tamau ya yi kafin ya ce. “Bani drone ɗin”. A hanzarce ta miƙa mashi tana haɗe natsuwanta waje guda……. “Akwai in da zamu je, so expect my call at anytime”. Ya kai karshe tare da ɗan satar kallonta, dan yaga tana ƙoƙarin miƙewa.Miƙewa ta yi, ta haɗe natsuwanta kafin ta ce. “Safe journey, and take good care of yourself”. Ta haɗe hannayenta tana ɗan jujjuyawa cikin salon soyayya ta faɗa. Bai kalli in da take ba ya juya da sauri ya nufi fita. Gab zai fita muryarta ta katse shi da cewa. “Sir”……….. Cak ya tsaya, ya ɗan juyo da kansa ban da jikinsa, fuskanta ya kalla yana jiran jin me kuma. “Don’t forget that I love you, kada ka mana wasa da kanka, ka sani ni da Aunty Ummie kana ranmu, ba zamu iya juran wani abin ya sameka ba, ka kula sosai please, good luck in whatever you go to do, I like you and I love you, I can’t change that, because it’s not something I chose for myself, I will wait until the day you begin to feel for me the same way I feel for you in my heart”. Cikin raunin murya ta kai karshe, da ɗan shagwaɓa mai karawa kalaman soyayya armashi ba romantic shagwaɓa ba.Bai yi magana ba, ya juya kawai ya fice da sauri. Da sauri ta biyo bayansa, ta zubawa tafiyar jarumtarsa idanu har sai da ya kurewa ganinta, ta ɗan jingina da jikin tantin tana tina ina ma ace ya yi accepting soyayyarta, ai da ta bashi kyakkyawar kulawa kafin ya tafi wanda har ya je ya dawo ita zai dinga tunawa. To mu sake ɗan komawa baya kaɗan a side nasu Manassa. Da yake yau suka fara aiki a tare, sun wuni suna ɗaki, suna aiki yana tsokanarta, ya ce mata. “Ba wai bana sonki bane, amma akwai dalilin da yasa dole zai daina sonki”. Ta tambayesa meyasa baya kulata sosai ne, kuma ya ce yana sonta.Tana aiki tana ɗan turo baki ta ce. “Wani dalili”. Sai da ya ɗan faki idanunta ya saki one side smile kafin ya ce. “Saboda a gida an ban mata, ance dole ita zan aura, bani da zaɓi”. Jama’a ba sai ga Manasa da ruwan hawaye ba? Da sauri ta ɗago ta kallesa, idanunta suka cicciko tab da kwallah, kirjinta na bugawa da karfi, ta gagara iya yin magana. Ganin haka yasa ya ja hankalinta a kan aiki, ya nemi mantar da ita maganar, amma a cikin ransa ya yi alkawarin hukuntata ta wannan hanya, ba yanzu zai bayyana mata cewa ita yake so ba, sai ya yi wasa da hankalinta da sunan yana da mata a gida kamar yadda ta yi wasa da hankalinsa a kan iya aljana ce.Ai wunin wannan rana dai wanna aiki ta yisa ne kawai, amma bata san me take yi ba, har lokacin da ya zo tafiya, ya shirya ya zo sallamarta bayan sun yi connecting na drone ɗin. A dake ya ce. “Zan je wani waje, wait for my call”. Kai kawai ta jinjina taki yin magana, taki ɗagowa ta kallesa. One side smile ya ɗan saki tare da riko hannayenta. “Baki mun fatan in dawo lafiya ba, ko dai kin fasa sona ne?”. Cike da sonta ya faɗa…… Tana gab da fashewa da kuka, tana wani irin huci na zuciya a kusa ta ce. “Ba zan taɓa daina sonka ba, amma ai za’a rabani da kai, kawai ka je”.Tausayinta ne ya ɗan kama shi, amma ya basar da cewa. “Ba za’a rabamu ba, zan cigaba da rokan Abba ya barni in aureki, so ki kwantar da hankalinki kin ji?”. Kai kawai ta jinjina tare da fashe mashi da kukan da take ƙoƙarin rikewa.Kafin ya yi wani yunkurin rarrashi ta faɗo jikinsa, ta rungumesa tightly, tana cigaba da kuka. Ai wani irin jim ya ɗan yi, sai ya ji dik wasu sassa na jikinsa suna amsawa, wani irin yawu ya haɗiya gwad har sai da maƙogwaransa ta yi sama ta sake yin ƙasa, da kyar ya sanya hannu ya rabata da jikinsa. A gurguje ya ɗan rarrasheta, baya son ya tafi ya barta cikin kunci, da suna tare ne ya dinga janta ta tsokana, saboda yana ganinta, amma baya nan gara ya barta cikin farinciki, sai ya ce mata ai zasu shawo kan Abba zai yarda, da wannan kalaman ya yi amfani wajen shawo kanta ta hakura. Sannan yai mata sallama ya fita bayan tantin, to shi ne suka tsaya jiran Noor. To mu koma kan labarinmu.Dikkansu ƴan matansu sun samu damar kallonsu kafin su tafi, amma Arya bata samu daman ganin Leo ba, Noor na zuwa suka kama hanya, babu wanda yasan basa nan sai ƴan matan nasu, suma matan basu san in da zasu je ba, sun dai san sun tafi wani waje kawai. Suna barin wajen waɗannan duwatsu suka kama hanya sai ga wani soja daga cikin sojojinsu ya fito daga bayan wata dutse, yana rufe da fuskansa da nose mask, ba zaka iya gane wanenen bane. Wayan dake hannunsa ya fara daddannawa, jim kaɗan ya kara a kunnena, baka iya gane muryansa sosai saboda nose mask ɗin, ya ce. “Sir sun fita yanzu”. Ba’a iya jin me ake cewa a ɗayan ɓangaren, sai kai da sojan ya jinjina game da cewa. “Okey sir”. Daga haka ya katse kiran ya gudu ya koma cikin sansani.Su kuwa suka cigaba da tafiya suna tattauna yadda zasu shawo kan wannan gagarumin aiki na gabansu a kan ƴan ta’addar nan.A tsakiyar dokar daji suka yi sallar magrib da ishai, while Unays ya ja sojojinsu sallar a sansani, amma ya yi mamakin ganin su Leo basu fito sallah ba, ya je room ɗinsu basa nan, ya kirasu basu ɗauka ba. Ya tambayi Arya ta ce mashi sun je zagaye a daji ne, zasu dawo anjuma. Ya yarda, dan haka ya jasu sallar magrib da ishai, su kuwa su Leo sun yi tafi mai mugun nisa, har wuraren 8 na safe suka samu damar isa wajen hayakin, nan suka isko wani irin wearing na wutar lantarki mai mugun ban mamaki da karfin tsaro. Amma abinku da renon AZURE cikin karkashin wasu wayoyin yantarki suka kutsa, kun tuna an koya masu horon rarrafe a cikin laka a barrack?.To yau ga ranar amfanin wannan rarrafe, sai da suka yi wa su Arya message kan su kunna laptop ɗinsu, sannan suka kunna bluetooth ɗinsu da already sun yi connecting da laptop ɗinsu Arya a sansani, sannan suka kwanta a ƙasa cikin ciyayi, suka fara rarrafawa ta ƙasan waɗan nan wayoyi. Tsaro mai matuƙar karfin gaske ne a wajen yasa drones ɗinsu Arya suka gagara ketarawa. Sun yi tafiyar good 30mins a rarrafe cikin ciyayi kafin su samu damar ketarawa cikin wajen, ta wannan hanya da suka shigo cike yake da ciyayi matuƙa, basa iya ganin gabansu, har suka kutsa cikin wajen ciyayi ne dogaye da bishiyoyi. Suna samun damar ƙetarawa ciki suka saki drones dake hannayensu, sannan suka taɓa bluetooth na kunnuwansu game da tambayar su Arya shin komai ya tafi daidai?. Matan dik suka amsa masu da e komai daidai kuma suna iya kallon komai sosai.Leo ya ce da Arya. “Start moving the drone zuwa wasu wurare ki duba mana hanya, ki duba mana tsaronsu, su waye a kan hanyarmu kuma me suke tare da shi, wasu irin makamai ne a hannunsu da sauran bayanai na aiki da kika sani”. Da okey sir ta amsa, da yake bata samu damar ganin fitansa ba sai ta juyo da drone ɗin ta samu damar kallon kyakkyawan fuskansa cikin helmet ɗinsu ma soji kafin ta juya kan drone ɗin ta fara ƙoƙarin nema masu hanya kenan sai ta ji Leo ya ce. “Oh s***”.Jin haka yasa ta juyo da drone ɗinta, me zata gani? Gabaɗaya su Leo kewaye suke, an masu zobe, wasu riƙaƙun mutane da baka iya ganin komai na daga jikinsu ne suka kewayesu da manyan bindigun da suka fi na su Leo ɗin, da alama already sun san da zuwan su Leo wajen, dan ta ko’ina sun kewayesu, sun ɗaura masu bindugu a kai, zasu kai mutum 15 haka, ashe sun ɓuya a cikin ciyayin ne suna jiran shigowarsu, sun yi kwantan ɓauna.Ya rabb, ya sojojin AZURE zasu yi? Captain ya yi gaskiya, a cikin soja akwai maciya amana, dik yadda aka yi akwai sa hannun wasu manya a kamasu, wani soja ne daga sansaninsu ya ci amanarsu? Waye ya bashi aikin? Ya zasu yi kenan? Suna tsaka mai wuya! Ace cikin abokan aikinka ma maciya amana, cikin manyanku maciya amana, ina ake son su sanya ransu? The game is over but over masu waye? AZURES SOLDIERS OR THE GANGSTER’S?. Let’s meet in part 2 to see what’s going to happen!. ———————–🔥WS-HOSPITAL.Tsaye Dr Kamal and Dr James suke a ɗakin da darling yake kwance, Dr Mark bai dawo ba. Dr James ya zubawa darling idanu yana ta kallonsa, mamaki yasa sun gagara kwakwarar motsi.Darling ɗan tahalikin da bai san komai ba, kwance yake a cikin glass ɗin da suka sanya shi, ya ɗage kafafunsa sama yana ta wasa sosai, alamar kyakkyawar lafiya da kuzari sun wanzu a jikinsa, fatar jikinsa ta canza ta koma ta ainahinta, sai dai kurajen nan ne da suka fito mashi ne suka ke nan, amma lafiya kam ya sameta matuƙa, ƙurajen ma sun fara raguwa, ruwan cikinsu na bushewa.Lamarin da ya gigita 3D kenan, ya rabb, ta ya aka yi darling ya samu lafiya? Dr James ya yi iya dube-dubensa bai samu wani dalili ba, sai dai yana zargin kamar akwai wanda yai mashi alluran maganin cutar NEXAPOX-31 ɗin nan, domin da ya binciki jinin darling ta na’ura ya gano akwai sinadarin da ta keta cikin jininsa kwanaki biyu baya! Dik yadda aka yi akwai abin da ya saɓa. To waye yai mashi alluran maganin? Waye ya kirkiri maganin bayan shi kansa wanda ya kirkiri cutar bai gama haɗa maganinta ba, yanzu ake ƙoƙarin haɗata, wani mai basirar ne ya rigasa haɗa maganinta?.Jama’a waye kuke tinanin ya ceci ran darling? Waye yai mashi alluran maganin cutar nan? How? Ta yaya? Yaushe? Waye kuma a ina? Ni kaina na kiɗime da ganin wannan abin, akwai dai abin da ya saɓa! Ko dai a cikin 3D ɗin ne ɗaya imani ta shigesa ya ga ba zai iya barin darling a cikin wannan cuta ba sai ya bashi maganin? Wani bawan ALLAH ne yai wannan aiki? Ga project na kwarin nan da suka jima suna yi IRON FIST sun kama container, ga kuma darling ya samu sauki, kuna tinanin zasu yi shiru ne?.Jama’a su waye WORLD SYSTEM dake ɗaukar nauyin 3D suna shuka fasadinsu a bayan ƙasa? Su waye ainahin IRON FIST dake ƙoƙarin cetan duniya daga musifun WS, shin WS mutane ne ko kuma dai na’urorin ne dake juya duniya? Idan mutane ne a ina suke? Su waye su? Me makomar DOL? Zasu kwaci kansu ko za’a kashesu? Ga Lazy ga IRON FIST! Shin IRON FIST zasu bayyana wa duniya? Idan suka bayyana me makomarsu? Seraphina, Aryan, Rimsha, ya zata kaya? Me a cikin containers da IRON FIST suka kama? Me ake yi da ɓargon jariran nan? Mun ji abin da ake yi da jininsu, me ake yi da ɓargo da ƙashinsu? Wasu irin magunguna ake mana gaurayensu? Menene maganin cutar NEXAPOX-31? Nasan zaku so ganin yadda 3D zasu haɗa maganin ko dan ku ajiye saboda tsaro.Tambayoyin suna da mugun yawa, amma alƙalamina zai amsa maku komai.Jama’a labarin yanzu zai fara, STEP 1 dik sharar fage ce, yanzu zamu shiga ainayin labarin.Gajeriyar note daga gareni zuwa ga readers masu albarka. Kamar yadda na faɗa a littafina na baya a yanzu ma zan sake maku nasiha. Ƴan mata har ma da matan aure, novel ana karanta shi ne dan a ɗauki ilmin da darasin dake ciki kawai, ba dan ki sanyawa kanki samun irin rayuwar dake ciki ba. Dani daku dik mun san hakan ba abu bane mai yiwuwa, meyasa muke yaudarar kanmu? Dik wani luxury life da nike sanyawa a cikin novel ina sanya shi ne kawai dan ƙawata labarin kuma dan ayi nishaɗi ba dan komai ba, na faɗa maku da babban murya irin wannan masifaffen luxury life ɗin, ayi ta zuba kuɗin masifa ba dai a duniya ba, sai a aljanna idan rabbi ya kaimu, ki yi aiki tukuru ki samu aljanna ninkin ba ninkin rayuwar novel zaki samu a can, kada ki yi karatun novel ki yaudari kanki da samun irin wannan rayuwa su yawon ƙasashe da wannan soyayya, ki yi karatun novel dan ki ɗauki darusan dake ciki, ki mai da hankali kan gina lahira ki samu aljanna. Akwai kyawawan maza a gaske fiye dana novel, amma ke da kanki ki faɗawa kanki gaskiya, ace namiji mai kuɗi, mai mulki, mai isa, mai taƙama, under 30 years, ya cike 100 ciff, bashi da naƙaso, ai kema kin san sai aikin kirkira irin tamu, idan ba’a faɗa maku gaskiya ni Princess Teema na faɗa maku a baya kuma na sake faɗa yanzu, alƙalaminmu ne kawai suke kirkirar irin rayuwar, ki samawa kanki lafiya, ki daina yaudarar kanki, na fita hakkinku na faɗa maku gaskiya a littafina na baya yanzu ma na sake faɗa maku, babu novel life a zahiri hajiyata! Sai dai ba za’a rasa maza masu kamantawa ba! Amma hundred irin mijin novel kam ki daina yaudarar kanki babu su hajiya, sai a littafanmu kawai suke! Masu son mijin novel ku shafawa kanku lafiya na faɗa maku! Ku daina yaudarar kanku a kan abin da alƙalaminmu ya kirkira.A gurguje STAR LADY, LADY TEEMA taku ce ta amana, inaiwa kowa fatan alkhairi, ALLAH ya saka maku da gidan aljanna, my people na STAR LADY TALKZONE and my WHATSAPP CHANNEL saƙon jinjina a gareku, ALLAH ya bar kauna ya kare munku a dik in da kuke, masoya da abokan arziki inai maku fatan alkhairi da fatan gamawa da duniya lafiya, a dik in da kuke alkhairin ALLAH ya kai maku, naga kauna da so, ALLAH ya dawwamar daku cikin musulmin farinciki.Nan na kawo karshen littafin ZAKUNA BIYAR STEP 1, sai mun haɗe daku a STEP 2 wanda zai zo maku nan hada jimawa ba. Kuɗin karatun STEP 2 1K rak yake, ki biya ki sha karatu cikin kwanciyar hankali da natsuwa, my sister zaki karu da littafin nan fiye da yadda zato zai zata, zai taimaki lafiyarki, zai taimaki lafiyar ƴan uwanki, zai iya taimaka maki daga faɗawa wata halaƙa, zai taimaka maki ki san ainahin wacece ke! Zaki san abin da yakamata ki ci kai harma da yadda zaki sarrafa abu ko ba kyau ki ci lafiya lou, zaki samu ilmi na wuce misali, zaki samu karin hasken rayuwa, zaki tsira da abubuwa dayawa, ALLAH ya bamu dacewa jama’ar arziki.*In kin shirya makin payment ga account ɗina, 2308489938, Musa Fatima Zahra UBA bank. Sai ki turo mun evidence ta wannan number 08161390581. Mutanen Niger ku mun magana ta numberta sai in baku my nita ɗin da zaku yi payment ɗinku a ciki, idan kuma kati ce ku mun magana dai zan faɗa maku komai.*
