Hausa novels

Matar Hariji Page 3 Romantic Hausa Novel

Lkc yanata tafiyarwa Lameer ya kasa sukuni kullum da tunanin Hauwah yake kwana yake tashi idan ya kwanta bashida mafarki sai nata wannan mafarki shine yake dauke masa kewar abubuwa da yawa saboda idan yayishi yakan yini cikin walwala da farin ciki.Watansu biyu suka gama abinda sukaje yi suka fara haramar tahowa gida shidai farin ciki gurinsa baa cewa komai ya rasa meye yakeji game da Hauwah amma yafi alaqanta abin da soyayya to kuma shi wanne irin so yakeyi mata ya zaiyi ma ya tunkari iyayenta yace yana son yarsu?Ya fahimci sudin irin fulanin nan ne masu tsauri sosai a dan shiga cikinsu din da yakeyi ya fahimci sun tsani Bahaushe musamman ta fanni auratayya zaiyi walaha kaji mutanen rugar Sambajo sun aurar a waje ko sun auro.“To wai nima da nake wannan lissafin ta Yaya zan auri mace sama da daya bayan dayar ma bana iya sauke nauyinta dake kaina dari bisa dari?” Ya tambayi kansa yana shafa qasumbarsa tare da lumshe idonsa ya hadiye wani yawu me ciwo shikam yanason Hauwah matsayin Mata to amma ya zaiyi ya riqeta ya sauke mata dukkan haqqoqinta sannan ya zaiyi da Hajiyarsa data tsani ko mgnr kishiya taji wani yayi balleshi da dama kamar ta tsaneshi cikin yayanta ya lura har tafison Mubaraka akansa saboda indai abi ya shafi Mubaraka to yanzu zata rufe ido taci mutuncin sa, “Ni wai ya zanyi ne?” ya fada yana dafe qirjinsa da yakeyi masa zafi saboda ba yau ya fara wannan tunanin ba.Ya jima yana saqawa da warwarewa domin samun mafita amma ya kasa jin Hauwah yakeyi a duk wata kusurwa ta jikinsa. Ji yakeyi dama ace zai sameta batare da yasha wahala ba shikam koma meye zai faru saidai ya faru Hauwah itace muradinsa a yanzu baya fatan ya rasata a rayuwarsa jima yakeyi kamar idan ya rasa Jiddah bazai rayu ba.____________Abubuwa da dama sun faru a cikin watanni biyun ciki harda tsayar da ranar aurenta da Madi wannan abu ba qaramin dagula lissafin Jiddoh yayi ba ta tashi hankalin kowa akan cewa itafa bazata aure Madi ba dan iskane har cewa yayi suzo su zagaya duhun dawa ya gwada mata bindira.Duk yanda tayi tunanin abin zaizo Mata da sauqi ta kasa samun wannan gatan hakan yasa kullum cikin kuka take da damuwa ko zaman gidan ta daina duk da sun hanata fita amma suna fita tallan nono zata haure dangar karar da suka kewaye gidansu da ita ta shiga cikin duhun daji.Sau tari sai baffanta yaje gindin magwaron data mayar gurin zamanta ya korota sannan take tafiya hatta abinci ta dainaci saidai idan taji yunwa Tasha madarar shanu ta kwanta sukam iyayen ko a jikinsu hidimarsu kawai sukeyi.Ana haka ta fara rashin lfy sosai kamar bazatayi ba nanfa hankalin baffanta ya tashi sosai ya shiga damuwa dan baiyi tunanin qiyayyar da takewa dakai har ta kwanta jinya ba.Yaso ya canza raayi amma yayarsa Yadammu tazo har gida ta rinqa sababin bala’i wai ai iskokine da Jiddoh dama haukanta ba irin na masu hankali bane wauta tsokana da rashin kunya duk ta tattara kuma a gurin uwarta ta kwashe komai.Shiga gdan yayi yana fadin “Hari! Hari!! Ke Hari dake nake wannan ja’irar yar taki bazata jamin abin fadaba maza fito Yadammu tace yau Boka bawa yake hawa bori fito da Jiddoh muje yau duk uban aljanin dake kanta saiya sauka kuma aure tsakaninta da Madile babu fashi saidai idan bana raye”Dukkan matan gdan fitowa sukayi suka fara sallalami suna fadin “oya maigida Moddibo Dalha ma yana maganin iskoki basai kaje gurin Boka Bawa ba” Daquwa ya watsa musu yace “kunfini ko kunfi Yadammu sanin abinda ya dashe ne to aradun Allah duk Wanda shi qara buda baki sai ta koma gdan tsohonta almuran banza almuran wofi ai dama nasan kune kuke daurewa Jiddoh gindi takeyin abinda taga dama nan har gda akazo aka yimin gorin nabarta ta gandame ta zama uwar mata a gda tunda rugannan take babu yar data tabayin shakara sha hudu a gdan iyayenta sai ita kunsani yarinya tun tanada shekara tara ake dauranta aure a rugannan amma ita saboda bakin jininta da mugun halinta gatanan daqyar ta samu Madilen ma ya tsaya yo banda sharrin iskoki inane zatashe batasonshi har tani jinya yo kwarankwatsa saidai tayi bunga”Shiga daki goggonta tayi tana tashinta amma fir taqi tashi saida sukakai ruwa rana sannan da taga Baffa ya dauko kokara zai sabeta yasata tashi ta fice da gudu tayi bayan gdan gudu takeyi sosai bata tsayaba saida tayi nisa da rugarsu ta shiga wata fadama ta samu gindin bishiyar kashu ta zauna tana haki dafe da qirjinta saida tayi me isarta sannan ta hade kanta da gwiwa taci gaba da rera kukanta zuciyarta na tuno mata da Kado tana tuna rana ta farko da suka fara haduwa dashi.WAWAYE_________Goggonta ta dora Mata tallan nono su Idin Tasha suka shanye Mata harda sanyata ta siyo musu sukari ta zuba musu suka tashi zasu tafi tace su bata kudinta suka kama zaginta harda dungure mata kai Mati ya zare Wuqa yace zai yankata idan bata tafiba babu arziqi ta tashi ta dauki qorenta ta nufi hanyar rugarsu tana tafi tana waiwaye batayi auneba kawai taji ta bugi mutum tayi baya da sauri jikinta na rawa ta dago ta kalleshi kyakkyawan Saurayi me cikar zati dago kakkaura wankan tarwada sanye da kayan turawa injita da fada.Shima kallonta yakeyi cikin hasala yace “ke wacce irin yarinya ce kina tafe kamar makauniya kalla yanda kika batamin jiki da nono….”Daga hannunta tayi tana ajiyar zuciya da niyyar bashi haƙuri bata iya buɗe bakinta ba saboda kukan da yaci ƙarfinta kawai sai ta kama ƙafarsa ta fashe da kuka.Jikinsa ne yayi sanyi tunaninsa mgnr daya fada mata ce tasata kuka shima durƙushewa yayi ya sanya hannunsa ya ɗago fuskarta ya zuba mata kyawawan manyan idanunsa ƙirjinsa na bugawa da sauri da sauri yace “meye dalilin kukan?”Cikin in…ina tace “su… su Idi da Mati suka shanyemin nono har sukashe ni siyo masu sukari da ciniki na kuma suka hanani kuɗin kuma sukashe idan nace sune sai sun kasheni kullum sai sunsa Goggona ta bugeni idan kuma na hanasu su shunamin karnukansu suyita yimin haushi kwanaki wani har cizona yayi” ta zauna sosai ta bude masa gurin saman santala santalan sangalalin qafarta farare tas da suka cika da suma kwantacciya lufluf dashi ya sauke idonsa a gurin da karen ya cijeta gurin har yayi rami sai ruwa yake zubarwa………..Rintse idonsa yayi da sauri yace “subhanallahi meye yasa bakije an wanke miki gurin ba?” Shiru tayi tana sharar hawaye kafin ya miqe yace “zo na wanke miki nasa miki magani” batayi jayayya dashi ba ta miqe tabishi yasa ta zauna a gefen motarsa shikuma ya dauko hydrogen da corton ya fara wanke Mata tana kuka tana ciccije leɓe yanayi Mata sannu lkc zuwa lkc yana ɗagowa yana kallon kyakkyawar fuskarta data jiqe sharƙaf da hawaye yanajin wani tausayinta yana kwarara a sassan jikinsa.Koda ya gama yayi mata plasting ɗin zama yayi ya zuba mata ido yana kallon kyakkyawar halittar bafulanar yanajin wani shauqi na taso masa, a hankali cikin dashewar murya yace “Ya sunanki?” haɗiye kukanta tayi tace “Jiddoh Arɗo Jibir” iska ya furzar ya miƙe yace “ok gobe kizonan idan kin ɗauko nonon ki kawo min zan siya zan taho da likita yayi miki allura kinsan cizo kare dafine dashi ƙafarki zata iya ruɓewa idan baayi miki allura ba, na nawane nonon dasu Idin suka shanye miki”Shiru tayi kamar bazatayi mgn ba ta fara haɗe kayanta bayan ta gama ta miƙe zata tafi ya riƙe hijjab dinta fuskarsa murtuk ya zaro dubu biyu ya bata yace “ki ajiyemin canji na gobe zan karba kada Goggo ta dakarmin ke” ƙememe taƙi karɓar kudin wai dukanta zaayi nononta na jaka huɗu da rabi ne.

Back to top button