Uncategorized

Auren Sha’awa A Maganar Musulunci

 ✴BISMILLAHI RAHMANIR RAHIM✴

           ◼ GABATARWA ◼

dukkan godiya sun tabbata ga Allah ubangijin talikai ,tsira da aminci Allah tabbata ga Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa da Wanda ya bisu har zuwa ranar alkiyama..

     bayan haka zamu gabatar da post mai suna AURE SHA’AWA

  dalili wannan post da zamu fara dashi yazo daidai ne a lokacin da ake bukatar samun sa saboda magance wasu daga cikin halaye na kangarewa da wasu daga cikin mata suka samu Kansu a ciki, Wanda hakan ke haifar musu har zuwa wurin bokaye, saboda jahilci dasu matan suke fama dashi..

  Kuma hakan ya haifar da kasuwar bokaye da malaman tsubbu sai kara samun ciniki sukeyi ,duk da haja wadannan bokaye ya kai matuka wajen kazanta da muni da rashin biyan bukata, amma babban hadarin a rasa duniya da lahiran gaba daya..

Ina rokon yan’uwa da suyi mini nasiha, da zaran am fahimci kuskure a cikin wannan post

muna rokon al’umma mu dinga ◾SHARE ◾ saboda sauran al’umma su samu Allah ya bamu ladan..

      ◼ SHIMFIDA ◼

kafin mu shiga cikin wannan post akwai mukaddama da nake so in gabatar mana⚫

  yan’uwa Abu farko: dole ne mu yarda da cewa mu musulmi ne, muna da addini, karmuyi rayuwa kamar rayuwa wadanda basu da addini, wajibi ne mu yarda cewa muna da addini, kuma muna da Tsari⚫

sa’annan :mu musulmi baki daya mun yarda da kadaitakar Allah mun yarda da cancantar Allah da bauta mishi shi kadai bashi da abokin tarayya⚫

mun yarda da manzoncin Manzon Allah (S.A.W) Allah ya aiko manzonsa domin ya shiryar da mu zuwa ga tafarkin Manzon sa , Wanda ya yarda haka,kuma ya karbi haka na cewa zai tafi kan wannan tsarin to ya rabauta, rabauta na har abada.. Wanda ya kauce wa wannan tsarin zaiyi asara, asara madauwamiya..

         ⬛ MENENE SHA’AWA⬛

shidai sha’awa, abinda rai yakeso,

annabi(sallal-laahu’alaihi-wa-sallam) yake cewa: an kewaye aljanna da abinda rai baya so⭐

sa’anan an kewaye wuta da abinda rai yakeso❇✳✴

amma mu Wanda muke magana akai

✳✴ A GUJI AURE SHA’AWA ✳✴

shine ita shari’a bata gina aure ne kawai akan abin da mutum akan so ba, akwai manufar da akeso gina mutum a kai, Wanda Allah ya daura nasaran mutum a kan wannan abun,

shiyasa Annabi ( sallal-laahu’alaihi-wa-sallam) yana cewa: wadansu suna aure

✴ KYAU ✴

to kaga Wanda yayi aure don kyan yayi auren sha’awa ne.

Annabi Muhammad (S.A.W)  yace wani yana aure saboda

✴KUDIN MATAR✴

Wanda yayi aure saboda kudi shima auren sha’awa ne.

wani yana aure saboda matsayi

✳IYAYE✳

to, duk wani abune na burge ko a ji dadi yaja mutum kawai baya daura bukatun sa akan abinda manufar da ita shari’a ta daura munufan akai ba, to ana ce masa

✔ AURE SHA’AWA✔

saboda haka mu abinda muke magana akai shine,kamar yadda annabi ya ambaci dukkan wancan, sai yace na bore ku da mai

✔✴ADDINI✴✔

to wannan mai addini shine manufa da Allah da manzonsa suka umurci bayi dasu.

duba abinda sharia takeso, to, sai ka sami biyan bukatun kada duk abinda kakeso..

         ◀ NEMAN AURE  ▶

AURE a musulunce ibada ne, nassosi da yawa sun zo al’kuran

Manzon Allah ( sallal-laahu’alaihi-wa-sallam) ya ambaci AURE wurare da yawa a cikin sunar sa wadansu wurare, umurci yake yi kai tsaye annabi yace yaku matasa duk Wanda ya sami iko, da hali yayi AURE,to annabi yace yayi AURE, haka Malamai sun yarda cewa aure ibada ce, yan’uwa kafin zuwa a nemi aure a kwai Abubuwan da musulunci ya shar’anta maka,Wanda wajibi ne a kanka  kafin ka tunkari NEMAN aure ya zama wadannan Abubuwan suna cikin zuciyar ka gina zamantakewar aure a Kansu Abu na farko..

➡ ka kudura a zuciyar ka cewa aure hanya ce da ake shiga aljanna dashi.

al’iman nawawi yace’ “ya ishi aure shida a matsayin ibada ,abinda Manzon Allah ( sallal-laahu’alaihi-wa-sallam) ya ga yawa sun mata gameda sha’anin AURE yace”

➡MIJIN KI SHINE WUTAR KI ◀

Kuma shine aljànnarki

Back to top button