Hausa novels

Ruwan Zuma Page 22 Hausa Novel

(22) Ummii ce ta fito tsakar gidan bayan an kai mata rahoton gida babu lafiya ana ta hayaniya. Laila ce ta fara hangota tayi saurin barin jikin Haydar ta koma kusa da Mas’ud tana ganin yanda Madu ke yiwa Alhaji Abdul magana k’asa-k’asa daga baya ya d’auka masa wayarsa da ya watsar a k’asa ya sanya masa a aljihu. “Me yake faruwa ne naji ana ta hayaniya?�? Ummii ta k’ariso gurinsu tana tambaya cikin kullewar kai. Alhaji Abdul ya gaisheta kana ya fice daga gidan cikin sauri ba tare da yace komai ba, hasalima ko kallon inda Laila da Haydar suke bai yi ba. Madu yayi wa Laila kallon tsana yace, “Wannan butulun ce ta fasa aurenta da Alhaji Abdul ta auri wannan yaro da suke yawon barikancisu tare. Laila kin bani mamaki kin kuma cuci kanki.�? Yana fad’in hakan shima yabi bayan Alhaji Abdul. Ummii ta dubi Laila hannunta na rawa tace, “Me nake ji Laila? Mas’ud me yake faruwa?�? Ganin haka yasa Mas’ud yayi saurin isa gurinta ya jata zuwa d’akinta bayan ya fad’awa kowa a basu guri zasu yi magana. Laila da har ta fara tara kwalla sanin Ummii baza ta ta6a amincewa da wannan aure nata ba ta bi bayansu jiki a sanyaye. “Haydar ka shigo.�? Mas’ud ya kira Haydar wanda shima ke tsaye amma hankalinsa na kan Laila wacce take cikin damuwa. Ko dai wannan shine dalilinta na k’in aurensa? Dukkansu suna zaune a k’asa yayinda Ummii ke zaune a kan kujera tana ta kallon Haydar wanda ta tabbatar cewa shine mijin Laila. A nan Mas’ud ya bata labarin duk abunda ya faru kana yayi shiru ya barta tana tunani. “Allah ya sanya alkhairi yasa gidanki ne na har abada. Hakan yayi daidai.�? Fad’in Ummii kenan wanda yasa kowa ya d’ago da kanshi cikin mamaki don basu tsammaci zata d’auki abun cikin sauk’i haka ba. “Ummii kina nufin hakan ya miki?�? Laila da bata gaskata kunnenta ba tayi wannan tambayar tana zura mata ido. Gyad’a kai tayi ta murmusa kad’an wanda tsufan fuskarta ya bayyana tace, “Auren kowa yake so kiyi kuma kinyi, batun a za6a miki wanda zaki aura ba hurumin kowa bane sai naki ke kad’ai. Auren mutumin da bashi da kirki da hali mai kyau babu riba sai fad’uwa, idan bai lalata miki rayuwa ba zai iya lalata ta zuriyar da zaku haifa.�? Duk ‘yan d’akin suka gyad’a kai cikin yarda da maganarta, a nan ta k’ara mayar da hankalinta kan Haydar tace, “Ka kula da ita.�? Da haka Ummii ta tashi ta shige d’akinta bayan ta kira Laila suka shiga tare. Ganin hakan yasa Mas’ud yace su fita su jirata a waje tunda ya lura magana zasu yi. A kusa da motar Mas’ud d’in suka tsaya, kana Mas’ud ya amsa kiransa da ake yi tun a falon Ummii. Bayan ya gama magana da wanda ya kirashi ya shiga motarshi yana cewa Haydar. “Abokaina suna jirana Haydar, once again congratulations.�? Ya mik’a mishi hannu suka yi musabaha suna murmusawa dukkansu. “Nagode Mas’ud, nagode kwarai.�? Ya amsa kana yaja da baya zai cire garen Mas’ud ya dakatar dashi. “Ka barshi a jikinka.�? Yana fad’in hakan ya fice daga gidan ya bar Haydar tsaye jiran Laila. Minti goma da haka Laila ta fito sanye cikin laffaya golden da yayi matuk’ar mata kyau sai walwali take yi, sai dai jikinta a sanyaye yake tamkar wacce bata da lafiya. Wannan karon Haydar tsayawa yayi yana kallonta ba tare da yaji kunya ko fargaba ba saboda ta zama matarsa halalinsa. A take yaji kishi ya shigesa dalilin tun farko baya son yaga ta saka laffaya saboda yana fitar da shape d’in jikinta sosai ba kad’an ba. Lokaci yayi da zai hanata sakawa domin ba zai so kowa ya k’ara kallon manyan cinyoyin matarsa ba. Tana isowa ta mik’a mishi key d’in motarta ya k’ar6a yana had’awa da hannunta wanda tayi saurin janyewa ta zagaya ta shiga baya ta zauna. Karkad’a kai yayi yana murmushi mai bayyana hakwara shima ya shiga motar ya kunna suka fara tafiya. “Amarya babu magana ne?�? Yace da ita yana mai juyowa kada’an yanda zai ganta. “Haydar ka kalli gabanka karka had’u da wata motar.�? “Tunda bakya son in had’u da wata motar meyasa kika shiga baya? Sai ki dawo nan gefena ta yanda zan dinga ganin duk motsinki.�? “Haydar!�? Ta kwa6eshi ganin bai daina juyowa yana kallonta ba. “Idan kina so in daina juyowa tell me you love me.�? Ya k’ara lek’ata da danna masa harara fuskarta babu alamar wasa. Ko kad’an hakan bai damesa yaci gaba da damunta wai sai ta fad’a mishi tana sonshi. Ganin abun nashi bana k’arewa bane yasa ta rufe fuskarta da gyalenta tana tuna maganganun Ummii wanda sune suka hanata yiwa Haydar fad’a.�? “Idan a daa d’an d’akinki ne yanzu kuma ya dawo mijinki kuma shugabanki duk da k’ank’antar shekarunsa. Kamar yanda zaki yiwa mijinki wanda ya fiki biyayya haka shima zaki yi mishi ba tare da kinyi la’akarin kin fishi ba. Ki guji bashi umurni tamkar ke kika ajiyeshi, karki manta miji ko jariri ne shine babba a kanki Laila.�? Shawarwari da fad’an da Ummii tayi mata basu daina yawo a kwakwalwarta ba tana jin zuciyarta a cunkushe tamkar aurenta da Haydar bai kamata ya faru ba. Ta kasa gane farinciki take ciki ko bak’in ciki domin har lokacin bata ji wani sanyi da dad’in da taji a lokacin da aka fad’a mata an d’aura mata aure da Aliyu uban ‘yayanta ba. Ko dai wannan auren is not meant to be? Ko dai tayi gaggawar amsa aurensa ta biyewa zuciyarta da tsoron abunda Mas’ud zai aikata ne? Shin aurenta da Haydar zai zama alkhairi? Wani irin zama zasu yi? Ta yaya zasu fara? Hankalinta bai kwanta da wannan auren ba! Ko dai ta nemi ya saketa? “Mun iso Amaryata.�? Tayi saurin yaye gyalen nata tana gyara zamanta zuciyarta na bugawa. Ganin mutane cirko-cirko da tayi a tsakar gidan yasa tayi saurin bud’e marfin k’ofar ta fita tana tambayar ko lafiya. “D’azu Abul ya dawo hankalinshi a tashe ya shiga d’akinsa yana fasa abubuwa kuma munyi k’ok’arin bud’e k’ofar ya kulleta ta ciki.�? Fad’in Ajidde wacce daga ganinta hankalinta a tashe yake ba kad’an ba. “Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun. Abul yaji labarin auren nan.�? Da haka ta shige cikin gidan da sauri ‘yan uwan nata suka rufa mata baya. A bakin k’ofar d’akin Abul ta samu Sabrin zaune tana buga masa tana kuka tana kiran sunanshi. “Don Allah Yaya Abul ka bud’e kar ka jiwa kanka ciwo.�? Tana ganin mahaifiyarta ta tashi da sauri ta yiwo kanta ta kama hannunta tace, “Mama wai da gaske yaron nan kika aura? Ki fad’awa Yaya Abul k’arya ake masa ya bud’e k’ofar nan kafin ya yiwa kanshi illa.�? Laila bata amsa mata ba ta isa bakin d’akin ta fara kwankwasawa. “Abul ka bud’e k’ofar nan yanzu kar ka bari raina ya 6aci.�? Haydar dake waje ya lura da wani irin mugun kallon da wasu mata ‘yan uwan Laila suke mishi wanda bai ga dalilin hakan ba. Zare key yayi shima ya fita daga motar yabi bayan Laila domin yasan ba lafiya ba. Yana shiga ya sameta a bakin k’ofar Abul tana sauraron abunda yake cewa tana hawaye, “Kin cuceni kuma kin cuci kanki Mama, ki rasa wanda zaki aura kaff mazan duniyan nan sai wannan d’an iskan mai shegen kwad’ayin? Wallahi ji nake yi kamar in kasheshi kuma in kashe kaina. Baki san a wani hali kika jefani a ciki ba. Bazan zauna a gidanki ba duniya zan shiga!�? Yana fad’in hakan ya finciko k’ofar har Laila na buguwa da gini yayi hanyar fita daga gidan Laila da Sabrin suka bishi a baya suna kiran sunanshi amma bai tsaya ba. Yana zuwa bakin k’ofa yayi kici6is da Haydar wanda ke shigowa suka tsaya kallon kallo, zuciyar Abul na tafarfasa tamkar zata k’ona masa k’irji. Laila dake binshi a baya ta iso zata kar6e jakar hannunshi yayi saurin janyeta yayi gaba yana cewa, “Sai kayi dana sanin auren mahaifiyata wallahi.�? Da haka yasa gudu ya fice daga gidan Laila na kwala masa kira tana hawaye. Sabrin ce itama ta fito d’auke da gyalenta da jakarta tana kuka tazo zata fita Laila ta rik’ota, “Sabrin ina zaki je?�? “Mama bazan zauna ina kallon wannan abun kunya da takaicin ba.�? Laila na jin hakan ta sake mata hannu tace, “Ki je.�? Bata kai da fita ba Ajidde ta rik’ota cikin fushi tace, “Ashe kema zaki iya zama butulu ga mahaifiyarki? Wani irin wahala da sadaukarwa ne bata muku ba? Kar ki biyewa Abul ki zama mara hankali kema Sabrin. Karki jawowa kanki fushin Allah akan abunda yake sunna ta ma’aikinsa.�? Rufe idanunta tayi kana ta bud’esu ta sauk’e kan Haydar wanda jikinsa ya gama yin sanyi sosai domin bai ta6a zaton abunda Laila take gudu ya kai haka ba. Wata muguwar harara ta watsa masa kana itama ta fita daga gidan tana share hawayenta. “I’m sorry.�? Laila ta jiyo muryar Haydar a sanyaye. “Ba laifinka bane, laifina ne.�? Tana fad’in hakan ta shige cikin gidan. Ajidde da take babba a gurin ta yiwa sauran mutanen magana kan su koma ciki, aka barta ita da Haydar wanda yake jin zafi a zuciyarsa ba kad’an ba. Matsawa suka yi gefe ta fara magana kamar haka, “Ba kowa ke murna da wannan auren naku ba, amma hakan bashi zai sa kayi dana sani ko kaji auren ya fita a ranka ba. Ban san labarinku ba amma ka zama garkuwar Laila saboda tana son ‘yayanta bata son abunda zai rabata dasu. Ka zama namiji a gidanka karka bari maganar mutane ya ta6a rayuwar aurenku ko ya lalatashi gabad’aya. Kar ka manta kowanne d’an Adam bai tsira ba, wallahi babu wanda ya tsira daga bakin mutane. Allah ya baku zaman lafiya ya kawar da shaid’an tsakaninku.�? “Ameen, Nagode.�? Kawai yace da ita kana ya fito da key d’in Laila ya mik’a mata ta k’arba. Da haka ya juya ya fita daga gidan jikinshi a sanyaye tamkar bashi ne yake jin kuzari d’azu ba. Ashe haka bak’in ciki yake hana mutum gane jindad’in rayuwa? Acha6a ya tara ya koma gidansu, a tsakar gida ya samu Ammi tana rik’e da radio tana jin labaran rana, rage volume tayi kana ta dubeshi ta kyau tace, “Ali kai kuma daga zuwa d’aurin aure sai kaje kayi zamanka? Tukunna ma rigar waye a jikinka kamar wani sabon ango?�? Ta k’arishe maganan cikin zolaya tana murmushi. “Ammii bani dari da hamsin in akwai a gurinki.�? Yace da ita yana mai kwa6e garen tare da hular. “Ali lafiya dai ko? Ya na ganka haka jiki a sanyaye? Ko don auren da Laila tayi ne? Ta mik’e tsaye ta iso gurinshi. Kad’a kai yayi yace, “Ammi bani kud’in in bawa d’an acha6a.�? Shiga d’aki tayi ta d’auko d’ari biyu ta mik’a mishi kana ya fita ya bawa mai acha6a ya dawo ya zauna akan tabarmar dake shimfid’e a rumfar tasu. “Ali ka sakawa ranka dangana domin Laila ta maka nisa yanzu ta zama matar wani. Allah zai baka wacce ta fita da yardarsa.�? “Ammi an d’aura mini aure da Laila yau bayan ta fasa auren ubangidana Alhaji Abdul.�? Yayi saurin fad’a mata domin kar ta zauna cikin duhu. Dafe k’irji Ammi tayi cikin kad’uwa tace, “Kai Ali!!�? Murmushi yayi wanda akace yafi kuka ciwo kana ya bata labarin duk abunda ya faru zuciyarsa a cunkushe. Shiru tayi na tsawon sakanni tana tunani kuma tana kallonshi tamkar bata gaskata labarin da ya bata ba. Da ya lura da hakan yace, “Ammi baki yarda ba ko?�? Kad’a kai tayi kana sauk’e hannayenta tace, “Ali ina mamakin yanda Allah yake sauya lamarinsa yanda yaso kuma a lokacin da yaga dama.�? Murmusawa tayi irin na jindad’i taci gaba da magana. “Na tayaka murna Ali, Allah ya sa hakan shine alkhairi a gareku baki d’aya. Nayi murna kwarai. Amma dai anyi auren nan babu shiri, yanzu ni d’in uwar ango ce shine nake zaune haka cikin zanin da ya kod’e? Bari in shiga makwabta in sanar dasu wannan labari su zo a yi wunin biki. Zan fasa asusun da nake tarawa ka sayo kayan abinci, tukunna ma a ina zaku zauna?�? Ta dakata da lissafinta ta nemi k’arin bayani. “Ban sani ba Ammi domin yanda kika ji labarin nan a sama nima haka k’aninta yazo ya sameni da maganar auren. A yanda mutane da dama suka tsani auren nan zai yi wuya yayi tsawo Ammi. Zai yi matuk’ar wuya.�? “Me kake so kace?�? Ta dubeshi ranta a 6ace. “Idan har ta buk’aci rabuwa dani zan bata takardarta Ammi domin ita kanta bata cikin farinciki.�? Fad’a Ammi ta fara masa yayi shiru yana jinta ba don yana gane me take fad’i ba, domin gaba d’aya hankalinsa na can kan Laila wacce yaga tsantsar nadama da dana sani a idanunta. Tana matuk’ar son ‘yayanta wanda hakan shi ya hanata aure duk tsawon wannan lokaci gudun kar su bar hannunta. A yanzu kuma da ya shigo ya tarwatsa wannan tsari nata yasan aurensu tamkar mutum ne mai tafiya akan kwai. Yana jin an fara kiran sallah Jumm’ah ya tashi yana cewa, “Ammi zanyi wanka in tafi masallaci.�? “Wato maganan da nake fad’a makan ne ba zaka saurara ba?�? “Ba haka bane Ammi, idan na dawo zan zauna mu tattauna.�? Da haka ya shige d’akinsa ya barta a nan tana godewa Allah da yasa Alinta yayi aure ba tare da anyi masa gorin mahaifi ba. Bayan ya gama kimtsawa ya fito zai tafi masallaci Ammi ta tsayar dashi ta mik’a mishi kud’i da yawa a hannunsa. Tace. “Ga kud’in dana fara tarawa don aurenka, tunda har an d’aura babu amfanin cigaba da ajiyeshi. Ka sayo shinkafa da kayan miya zamu yi jollof na biki.�? “Ammi ai kun makara da yin gayya da d’aura tukunya, ni bana so ki fad’awa kowa a unguwan nan har sai naga yanda Allah zai yi. Don Allah ki daina kawo zancen nan.�? Fuskar Ammi ta kwaye alamar bata ji dad’in hakan ba ya kamo hannunta ya zaunar da ita a kan kujeran tsugunno shi kuma ya tsugunna ya fara magana, “Yaushe zaki fita da kanki a tsakar ranar nan kina bin makwabta kina cewa d’anki ya d’aura aure? Yaushe kuma suka yarda da zancenki har suka taso suka zo gidan nan suka tayaki d’aura girki? Karki manta mata na fita ne da izinin mazajensu, a wannan lokacin kuma duk namiji ya tafi masallacin jumma’a, kina son su fito ba tare da izinin mazajensu bane don kawai su tayaki farinciki Ammi?�? “Naji tashi ka bani guri. Amma ko gobe ne sai anyi wannan wunin.�? Murmushi yayi mai sauti yace, “Kud’inki baza su isa a sayi shinkafa da kayan miya ba kuma ni bani da ko sisi, k’arshe ma yanzu ke zaki bani kud’in zuwa masallaci. Da haka ya zari d’ari biyar ya fice a gidan yana mata dariya domin duk cikin kud’in d’ari biyar ce babba. “Ali ka dawo mini da kud’ina.�? Ta fad’i hakan cikin fad’a amma fuskarta ya bada ita saboda murmushin da take yi. “Allah ya kare mini kai daga sharrin masu sharri ya hana mak’iyanmu ganinka har abada.�? Ta bishi da addu’an da ta saba yi masa kullum in ya fita. A can gidan Laila kuwa Ajidde ta fad’awa danginsu kan su koma gidan Madu inda za’a kai amaryar Mas’ud a yi bikin kawai a can. Sauran k’awayen Laila su Hajiya Maryam da Hajiya Shatu da abokan harkokinta kad’ai aka bari a gidan, suma suna cin abincin rana suka musu sallama aka basu souvenirs suka tafi. Kafin la’asar gida ya rage daga Laila sai k’awayenta biyu wanda su suke bata baki tare da kwantar mata da hankali. Ita kuma damuwarta kaff na kan Abul wanda take kiran wayarsa amma tana jinshi a kashe. Tasan ba zai bar wayar a kunne ba kuma k’arshenta wannan karon ma da kyar su sameshi da kansu har sai ya bayyana don kanshi. Tana son kiran Mas’ud ta fad’a mishi halin da ake ciki amma kuma ta fasa domin yau ne ranar farin cikinsa bai kamata ta 6ata mishi ba. Da yake tun farko tare suka ajiye lokacin da za’a d’auko amaryarsa, ai kuwa lokacin yana yi ta d’auko laffayanta ta saka zata fita Hajiya Shatu ta tambayeta ina zata je. “Zamu je d’auko matar Mas’ud ne, ko kun manta?�? “Sai ki tambayi mijinki idan ya barki sai ki fita.�? Fad’in Hajiya Maryam tana gyara zamanta domin bata da niyyan fita. Sake baki Laila tayi tana kallonsu cikin mamaki da kuma haushi, “Yanzu fitan da zan yi sai na kira Haydar ya bani izini?�? Gyad’a kai Hajiya Shatu tayi kana tace, “Kin jima baki yi aure bane amma ba’a canja wannan tsarin ba har yanzu, kuma kinsan hukuncinki idan kika fita babu izininshi. Karki nemawa kanki tsinuwar Allah tun ba’a je ko’ina ba.�? D’aga musu hannu tayi alamar surrender tace, “Naji, naji.�? Kana ta shige d’akinta ranta a 6ace tana tunanin yanda zata kashe wannan aure ba tare da ran kowa ya 6aci ba. Su Ajidde ne suka d’auko Naana amaryar Mas’ud aka kawota gidan Madu aka yi bud’an kai da yamma, ana sallan magriba aka kaita gidan da Mas’ud ya gina shi da kanshi shima a cikin Jakara wanda tafiyar minti uku zai kawoka gidan Laila. Bayan isha kowa ya watse aka bar amarya da kawayenta kafin angwaye su shigo. Daga masallacin jumma’a Haydar yaje gurin aikin Nasir wanda tun bayan abunda ya faru da Laila ya ja baya dashi, wai yana tsoron kar a kulleshi. Yana ganinshi suka yi musabaha cikin d’okin ganin juna kana ya gaisa da sauran mutanen gurin suka zauna. “Kana nan abunka?�? Fad’in Nasir yana mik’a mishi coke mai sanyi. Haydar ya k’arba tare da yin godiya yace, “Ina nan. Yau aka d’aura aurena da Laila.�? Nasir da ya kur6i Coke d’inshi ya shak’e ya fara tari Haydar kuma yaci gaba da sipping nashi a hankali tamkar bai ga Nasir ba. “Kai mugu ne d’an iska.�? Nasir ya fad’a tsakanin tari. “Maganin mai gudun abokinsa don tsoro. Wallahi kaji kunya! Yaushe rabon da kazo gidanmu? Tunda Ammi ta dawo gida baka k’ara zuwa duba jikinta ba.�? “Ba ina maka waya ba?�? Ya amsa masa bayan tarin ya tsagaita. “Waya bai isa ba.�? “Sue me.�? Haydar ya ajiye goran coke d’in a saman counter yace, “Wallahi ba wasa nake maka ba. An d’aura mini aure da Laila yau.�? A nan ya bashi labarin abunda yaga zai iya fad’a masa ba tare da ya fad’i abunda ‘yayan Laila suka yi ba, saboda 6oye sirrin ‘yayanta. “Kai Haydar!�? “Baka yarda bane?�? “To uban me kake yi a nan kana Ango d’anye shataf?�? “Ina kake son in je?�? Ya tambayeshi yana tsura mishi ido. “I don’t know, amma dai ba nan ba kuma ba cikin tsofaffin kaya ba.�? “Sue me.�? Bai bar gurin ba sai bayan isha bayan ya nacewa Nasir ya rok’i ubangidansu ya dawo dashi aiki a kantin tunda ya daina aiki a Lu’a Ventures. Yana isa unguwarsu yaga motar Mas’ud a k’ofar gidansu yayi saurin shiga don jin meya kawoshi. Samu yayi Mas’ud na zaune a kan tabarma shi da wani abokinsa d’aya suna hira da Ammi cikin yaren Shuwa wanda har yau shi bai iya ba. Sallamar da yayi yasa suka dakata da maganan da suke yi kana suka amsa ya samu guri ya zauna yana mik’a musu hannu suka yi musabaha. “Ali ina kaje tun d’azu ana ta nemanka? Mas’ud bana fad’a maka ana yin isha zai dawo gida ba?�? Mas’ud ya gyad’a kai yana kallon Haydar yace, “Ai kuwa Ammi.�? Haydar dai shiru yayi yana jiran da wacce suka zo domin har cikin ranshi ya raya cewa Laila ce ta aikosu ya bata takardarta tun kafin auren ya kwana. “Ka had’a kayanka ku tafi.�? Cewar Ammi tana mik’ewa ta shige d’akin Haydar don tayashi had’a kayansa. “What? Ammi ban gane in had’a kayana ba sai kace wata mace.�? Yabi bayanta yana mata magana amma har ta fara jawo kayanshi masu dotti da wankakku tana ajiyewa a gefe bata ce mishi kanzil ba. Dariya Mas’ud yayi amma yayi saurin k’unsheta yana kasa kunne shi da Hamidu abokinsa. “Mu da aka kai mana mata shi kuma shi za’a d’auka a kaiwa matarsa. Bari mu ga ko zai yi kuka in yazo rabuwa da Maman nashi.�? Mas’ud ya k’ara fashewa da dariya yana sauraron draman Ammi da Haydar. “Ammi don Allah karki ta6a mini gajerun wandunana masu dotti, ki bari zan had’a kayan da kaina. Ammi!.�? Ya fad’i hakan yana kwacewa daga hannunta cike da kunya. “Ammi nifa babu inda zan je in barki ki kwana ke kad’ai.�? Ya fad’i hakan bayan sun gama had’a kayan. “Yau na saba kwana ni d’aya? Lokacin da ka tafi bautar k’asa a can kudu da waye nake kwana? D’auki jakanka ku tafi karka 6ata musu lokaci.�? Fad’in Ammi kenan tana turashi gaba. “Ammi ki bari gobe zan je da kaina muyi maganan inda zata zauna, zan nema mana gidan haya.�? “Mas’ud yace ya baka gefenshi ka zauna a gidan tare da matarka har Allah ya hore maka kayi naka.�? “Amma kuma bai yi shawara dani ba ina matsayin namiji sai ke yake fad’awa hakan?�? “Tun bayan magriba suke gidan nan, yana son maganan da kai amma baka nan wayarka ma bata shiga, shiyasa suka zauna zaman jiranka.�? K’arshe dai haka suka fito daga d’akin Mas’ud na k’unshe dariyarsa domin hakan ba k’aramin dad’i ya masa ba, kuma ya samu abun tsokanan Haydar kenan. “Haydar kar kayi kuka fa, kasan rabo da iyaye akwai zafi, amma kullum zaka dinga zuwa kana ganinta ai. Ko Ammi?�? Ammi ta shafa kanshi tamkar k’aramin yaro tace, “Kwarai kuwa. Ai bamu yi nisa ba.�? Haydar ya rufe idanunsa na sakanni goma yana danne 6acin ransa domin yasan da gayya Mas’ud ke mishi haka. Tun kafin suyi bankwana da Ammi ya figi jakarsa yayi waje yana cewa, “Sai da safe Ammi.�? “To ka tsaya kuyi bankwana da kyau mana, ko baka son a ga kukan da kake yi ne?�? Fad’in Mas’ud yana zura takalmansa yana kecewa da dariya. Ammi da har lokacin bata gane gayya ake yiwa d’anta ba jikinta yayi sanyi tace, “Kuka yake yi ko? Allah sarki Ali.�? “Babu komai zamu rarrasheshi. Ai kamar kunya yake ji ma.�? Haydar da yake waje duk yaji maganganunsu ya cije le6e cikin takaici. Har waje Ammi ta biyosu ta musu bankwana kana ta koma gidanta ta rufe cike da kewan d’anta tilo data fi so a duniya. A hanya Mas’ud ne ke tsokanan Haydar amma ko kad’an bai nuna yasan yana yi ba, k’arshe wayarsa ya d’auka ya fara danne-danne gudun kar ya mayar masa da martani domin bai mance halaccin daya masa yau ba na bashi auren Laila. A Pharmacy d’insu suka yi parking suka fito Haydar na mamakin me ya kawosu gurin. Sai da suka shiga Mas’ud ya sallami duk masu aikin gurin akan sai gobe su zo su bud’e shagon. Shagon ya rage daga Mas’ud, Hamidu da Haydar wanda tun shigowarsu ya samu guri ya zauna. “Angon Laila.�? Mas’ud ya kirashi cikin tsokana yana zama kusa dashi da syringe a hannunsa. “Mallam me zaka yi da wannan d’in?�? Haydar ya tambayeshi yana matsar da fuskarsa baya. “Zamu gwada jininka ne ko kana da STDs, bazan kaiwa Laila kai haka ba tare da an maka gwaji ba. Domin kafin a d’aura auren ma an buk’aci ganin takardunka na asibiti nace duk na sani.�? “I’m clean man, bani da ko malaria balle HIV.�? “Bani hannunka domin bazai d’auki minti goma ba.�? Haydar ya mik’a hannunshi ba tare da tsoro ba aka ja jininshi. Minti sha biyar da haka Mas’ud ya fito daga d’an k’aramin Lab d’insu dake cikin shagon yana cewa, “You are clean.�? Daga nan shagon aski suka wuce, shi dai Haydar na kallon ikon Allah yana kuma binsu ne kawai. A can aka masa aski da gyaran fuska wanda Mas’ud yaso a kwashe sajenshi Haydar yace in aka cire masa shima sai ya cire na Mas’ud. Da dariya suka fito daga gurin tamkar wasu abokai kana suka wuce gurin sayan kazar Amarci. “In ba don kai ba da yanzu na jima a d’akin matata wallahi.�? Fad’in Mas’ud yana biya musu kud’in kajin da drinks d’in da suka sayo. Bayan sun dawo cikin mota ne Hamidu ya mik’awa Mas’ud wani kullin magani a takarda yace, “Goga kar ka manta da ita fa.�? Mas’ud yayi saurin k’ar6a ya barbad’a a bakinsa ya shanye haka ba tare da yasha ruwa ba. Haydar ya kallesu cikin rashin yarda yace, “Wannan d’in menene?�? “Maganin zaman lafiya ake bawa angwaye a daren farko. Ko zaka sha?�? Hamidu ya mik’a mishi wata takardar Haydar ya girgiza kai yace, “Nagode.�? “Ka bada maza wallahi, tsoro kake ji?�? Fad’in Mas’ud yana k’ara barbad’a wani garin a bakinshi. Jin wannan kalma ta ‘tsoro�? da ya tsana yasa ya wafci uku daga hannun Hamidu ya had’iyesu duk a lokaci d’aya suka dubeshi suna zare ido. “D’aya ko biyu ake sha ba uku ba.�? Fad’in Hamidu cikin kad’uwa yana maida sauran cikin aljihunsa. “I challenge you Mas’ud ka k’ara d’aya in ba tsoro kake yi ba.�? Haydar yayi challenging Mas’ud. D’an zaro ido kad’an yayi ya dubi Hamidu wanda yayi saurin girgiza masa kai tare da masa alamar yanke kai, kana ya kalli Haydar yace, “You won.�? Haydar yayi dariya yana jin kanshi suka cigaba da hira irin tasu ta maza. Sai da suka iso gidan Laila sannan ya dawo hayyacinshi ya fara tunanin yaya Laila zata kar6eshi da auren nasu gabad’aya. Hamidu da dama shi yake driving aka barshi a mota, Mas’ud kuma ya rako Haydar har cikin falon Laila ya zauna. Mas’ud ya shiga part d’inshi na daa ya kulle kana ya dawo ya kulle d’akin Sabrin dana Abul ya jefa keys d’in a aljihunsa ya shiga d’akin Laila. A bakin gado ya sameta rik’e da waya tana danne-danne. Ganin Mas’ud da tayi yasa ta ajiye wayar a gefe da k’ak’alo murmushi tace, “Ango me kake yi a nan? Na d’auka tuni ka shiga gidanka.�? “Na kawo miki naki Angon ne tunda na lura kunya kike yi baki tambayeshi ba.�? “No karka mini haka, kace mini wasa kake yi.�? Ta fad’i hakan tana dafe k’irjinta. “Yana can falo. Sai da safe don bacci nake ji sosai.�? Ya fad’i hakan yana gyara garenshi kana yayi saurin fita daga d’akin. Haydar ne ya rakashi har bakin mota kana Mas’ud ya lek’o ta window yace, “Abunda kasha d’in nan yayi maka yawa, ka tabbata ka rage zafi idan ba haka ba wallahi gobe zaka kasa fitowa cikin jama’a, kaji na rantse maka.�? Yana fad’in hakan Hamidu yaja motar suka fita daga gidan suna kyakyatawa da dariya. Haydar da sai a lokacin ya gane me yasha yayi saurin dafe kanshi cikin dana sani. Yafi minti biyar tsaye a gurin yana tunanin me zai yi amma kwata-kwata hankalinshi bai bashi idea d’aya kwakkwara ba. K’arshe juyawa yayi ya koma cikin falon ya samu Laila zaune a kan kujera ta dafe kanta hawaye na tsiyaya a idanunta.

Mum Fateey 👌

Back to top button