Halysaah Page 66 By Khaleesat Haydar
Khaleesat tsabar yanda ta zama shock kasa cewa komai tayi a inda take zaune kamar ruwa ya cinye ta, ta shiga uku ita kam ga kuma wani da yafi Abdul tashanci, Safiyyah na huci tace “Ta shi mu je, don dai ban san yanda ake yi bane a kasar nan, da Nigeria ne ai daga nan police station na nufa in je in kai report, to su nan ban san ko ana haka ba” Ita dai Khaleesat ta kasa tashi don duk jikinta yayi sanyi kamar an watsa mata kankara, Ganin Khaleesat taki tashi Safiyyah tace “Ki tashi mu tafi don Allah kar ya sake dawowa” Khaleesat ta kalleta tace “In tafi ina? Am not going anywhere Safiyyah, haka kawai in koma apartment dina ya bi ni can?” Safiyyah na huci tace “Kuma fa haka ne” Khaleesat ta dafe kanta da yayi mata nauyi tace “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” Safiyyah tace “Wannan fa kamar ya fi Abdul zama ɗan daba, ni wallahi ban san haka yake ba da ko hanyar da ya bi a makarantar nan ma bazan dinga bi ba, in ba dai in danna 911 yanxu su taho ba gaskiya” Khaleesat ta wani kalleta tace “Su taho su yi maki me? Kar kiyi dialing ki bari sai na bar nan tukunna” Safiyyah ta koma ta zauna tayi tagumi, Khaleesat ta bude handbag dinta duk jiki a sanyaye ta ciro wayarta, ta fi second talatin ta kasa dialing number Ajay don ta tsani masifarsa ita kam, but did she have a choice? Haka kawai ta koma Apartment dinta Aymaan ya bi ta ko kofar a kulle yake ya balle ya shigo mata ta shiga uku, ita sai yau ma ta kare masa kallo kana ganinsa kaga someone on drug shi yasa idonsa suka zama kamar me sexy eyes ashe tsabar shan kwaya ne, Safiyyah ta kalleta tace “Dole dai wancan mara mutuncin za ki kira, don ni wallahi bana son Ajayn nan gwara Housemate sau miliyan, ki ji fa ranan har da korata saboda kawai zai maki magana sai kace bai san yanda muke da ke ba, ya maida ni kamar wata bare ranan, abinda Housemate dinki bazai taɓa yi ba kenan yace in tashi wai zai maki magana, tun daga ranan na kullacesa a raina wallahi, ashe haka yake da baƙin hali ban sani ba, nace masa good afternoon wai ya amsa da evening tsabar rainin hankali, pls i don’t like him” Khaleesat tace “To ina da wanda zan kira bayan shi ne?” Safiyyah tace “Yaushe Housemate din naki zai dawo ne? Gaskiya we are missing him yayi maza ya dawo” Khaleesat tace “Oho” Daga haka tayi dialing number Ajay, sai da ya katse ta sake kira sannan ya daga, taji yace “What again Madam?” Hurriedly yayi tambayar as if in a haste to cut the call, ta sauke idonta a hankali tace “Zuwa yayi ya same mu a department ni da Safiyyah” Ajay yayi shiru, sai kuma yace “Sai aka yi yaya?” A sanyaye Khaleesat ta gaya masa abubuwan da ya zo ya fada da kuma yanda suka yi da Safiyyah daga karshe, Ajay dake ta sauraronta yace “Kin ga wannan kawar taki me shegen rawan kai sai ta ja maki bala’in da baki yi tunani ba a rayuwarki, who sent her to exchange words with him? Duk ba ita ta kai ki inda kika hadu da gayen ba? And meye kike son in maki da kika kirani yanxu?” Khaleesat ta katse wayarta ta ajiye, Safiyyah dake ta kallonta tace “What is he saying?” Khaleesat dai tayi shiru bata ce komai ba, sai ga wayarta ya fara ring ta duba taga shi ke kiranta, Safiyyah ta taɓe baki tace “Allah sarki Housemate gaskiya yana kokari da wannan Ajay din ashe haka yake? Wallahi yanda kika san Malamin islamiyya haka nake ganinsa ni dai yanxu, kullum a fusace yake, ki daga kar ya katse, ni yanxu na gaya ma Mustapha wannan magana ai zai gano na tafi Party bayan ce masa nayi baki da lafiya zan je apartment din ki daga schl ranan” Khaleesat tayi picking call din ta kai kunne taki cewa komai, yace “Kashe min waya kika yi?” Tace “To me zan yi idan ban kashe ba, kawai kayi ta ma mutum masifa kullum” Yace “Sai ki je kiyi sorting self din ki out” Daga haka ya katse wayarsa, Safiyyah tace “Tirrr, anya wannan zai iya zama da mace kuwa? Ina ga a world din da ya tashi iya maza ne kawai suka yi surrounding dinsa, amma sam bashi da sympathy wa mace, kawai tashi zaki yi mu tafi gidan Yaya Mustapha don nima ban baki goyon bayan zuwa apartment din ki ba, Aymaan drugs din da yake sha basa gaya masa gaskiya” Ita dai Khaleesat bata ce komai ba, gaba daya taji zaman America din ma ya fita kanta har ma da karatun, shikenan ita daga wannan sai wannan a rayuwarta, hawaye taji ya cika idonta, Safiyyah tace “Ke kuma matsalata dake kenan, komai sai kice kuka kamar wata er yaye, Meye abun kuka kuma? Ni fa ina da strong mind yanda bakya zato” Ita dai Khaleesat goge hawayen idonta kawai take don ta gaji kuma haka, Safiyyah ta tabe baki ta koma gefe, haka suka zauna for almost 10 minutes a wajen kowa da tunanin da yake a ransa, murya can kasa Safiyyah tace “Kin ga kuma gashi can zuwa, wannan mutumi dai bashi da alkibla” Khaleesat ta daga kai tana kallon inda Safiyyah ke kallo, lkci daya ta dauke kai fuskarta a daure, A hankali Safiyyah tace “Ni dai kinga tafiyata….” Daga haka ta dau handbag dinta kamar munafuka ta bar wajen kan Ajay ya karaso, har Ajay ya iso wajen Khaleesat bata sake kallon direction dinsa ba, Yana kallonta yace “Rashin kunyan ki har ya kai ki dinga katse ma mutane waya yanxu?” Ta wani kallesa amma taki cewa komai, sai kuma ta kauda kai, yace “Ba magana nake maki ba?” Bata fuska tayi tana shirin kukan da ya tokare mata a makogwaro yace “Sai dai kiyi ma kanki kuka ba ni ba, and in case u don’t know…. work load dake kaina yafi karfin duk wani kananun issues din ki, Jay ne yake iya combining both ni kam bazan iya ba, i will be taking you home ki zauna can har sanda Jay zai dawo ku ci gaba daga inda ku ka tsaya, i don’t have much time to be fighting with a tout because of you” Ita dai bata ce komai ba, ya hade rai yace “Baza ki tashi ba?” Mikewa tayi without looking at him, ya juya ya bar wajen ta fara bin bayansa tana hararansa, can apartment dinta ya fara kai ta, bayan yayi parking yace “Kar ki bata min lkci ki shiga ki dauko duk abinda zaki bukata for now, don’t waste my time” Bude motar tayi ta sauka ta nufi apartment din, sai da ta ɓata kusan minti ashirin a cikin gidan bata fito ba, patient dinsa ya kare ya dau waya zai kirata kenan ya ga motar da ya tsaya dai dai apartment din, kallon motar ya dinga yi don ya gane motar waye, wanda ke cikin motar na ganin motarsa sai yayi gaba ya wuce apartment din yana driving slowly, Ajay ya dinga kallon motar da mamaki, wato uban fist din da yayi masa banda frnds dinsu sun shiga tsakani bai ishesa ba kenan, few a cikin abokan Aymaan are also his frnds shi yasa matter din ma bai yi escalating ba har suka shiga tsakaninsu suna ba Ajay hakuri, amma fa Aymaan ya sha kulli kafin abokan su yi intervening, haushin hakan yasa yaje ya samu su Khaleesat a department dinsu, sai kuma yanxu gashi ya sake biyota gida, Ajay ya gyada kai, ya ci sa’a ba a Nigeria suke ba, wayarsa ne ya fara ring ganin Jay ke kiransa ya daga, daga daya bangaren Jay yace “Yarima me yasa baza kayi respecting title din da kake holding ba pls, why are you like this? menene ya kai ka fada da Aymaan? A America ku ke fa ba Nigeria ba Bruh” Ajay dake sauraronsa yace “Ai ba mu yi fada ba, kilan dai nan gaba za mu yi, don sai na karya masa hannu in bai yi hankali ba, dama naga ba shi da Stamina bugu daya ya tafi kasa don haka karyasa ba wahala zai min ba…” Jay ya ja tsaki yace “Can you hear ur self plss? I will report you to Abba in dai baza ka dena wannan abun da kake yi ba, kai bini bini ka kai fist kamar wani ɗan dambe? who does that pls, haba wannan zubar da class dinka kake wallahi” Ajay yace “To wa ya jawo? Ba kai da wannan brat din bane ku ka ja har nake fada? Da baka bar ni da ita ba hakan zai faru ne?” Jay yace “A’a dama can hannunka kaikayi yake, stop using us to cover ur foolishness, sannan ni ban bar ka da ita ba because i know she is old enough to care for her self with no supervision kai ne dai ka maida care dinta hannunka voluntarily for reasons best known to you, Kuma ni ba gashi nayi ma Aymaan din magana ba kuma ya fahimce ni, amma kai komai sai ka sako hargagi ciki kamar jira kake ka fara dambe” Shiru Ajay yayi, kawai sai yayi ignoring wasu daga maganganun Jay yace “Ohk, kayi masa magana shi yasa naga motarsa yanxu a kofar apartment dinta ko?” Jay yayi shiru, sai kuma yace “Kai me ya kai ka apartment dinta?” Ajay ya katse wayarsa ya ajiye, sosai yaji Jay ya bata masa rai, and he was boiling from inside, ji yayi kamar ya ja motarsa yayi tafiyarsa ya bar ta da faith dinta a gidan tunda dama ba idea dinsa bane dawowarta America, har ya fara reverse amma kuma sai ya kasa tafiya, ya sake kallon direction din da Aymaan ya bi yaga babu motarsa alamar ya tafi, Jay ya dade bai ɓata masa rai kamar haka ba, kawai ya dau wayarsa ya shiga contact dinsa ya danna masa block sannan ya ajiye wayar, sai ga Khaleesat ta fito daga apartment dinta, ko kallonta Ajay bai yi ba har ta gama saka duk abubuwan da ta dauko a back seat don taga bai bude booth ba babu kuma alamar zai bude, bayan ta kulle seat din ta bude front seat ta shiga motar ta kullo kofar a hankali, ita ma bata kallesa ba kamar yanda shi ma bai ko kalleta ba ya fara reverse din motar. Har suka isa gidan ba abinda yace mata ita ma haka, yayi wucewarsa ciki ya bar ta da kayanta, haka nan ta dauka kayan bit by bit tana shiga da su gidan, har sannan yana tsaye parlor waiting for her to finish, sai da ta gama shigo da kayan babu yabo babu fallasa yace “Meet me in the kitchen” Daga haka ya nufi kitchen din ta bi bayansa, Utensils da aka kebe a kitchen din ya nuna mata wajen da suke a takaice yace “That is a no go area, duk ma me zaki taɓa a kitchen din nan banda su” Yana kai wannan ya fice daga kitchen din ta dinga kallon Utensils din ba ma sae an gaya mata ba ta gane iya shi ke amfani da su, can ta tabe baki ta juya ta fita, bayan ta kai duk abubuwan ta dakin da ta sauka jiya taji wayarta dake jaka na vibrate, ta dau jakan ta bude ta ciro wayar, sosai gabanta ya fadi ganin number Housemate dinta, duk da tayi deleting number amma tsaf yana kanta don special digits ne bbu wahalan haddacewa….*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788 👈🏻, it’s better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*
