Halysaah Page 67 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 67…Khaleesat ta zauna gefen gadon dakin tana kallon screen din wayarta, zata yi picking call din ya katse, it took her almost 2 minutes before returning the call amma har ya katse bai daga ba, ta dinga kallon wayar waiting to see if he will call back amma har bayan minti goma bai kira ba, hakan ya sa ta ajiye wayar a hankali ta mike ta fara gyara dakin, ta sauka downstairs tana dube duben inda zata ga abun shara da goge goge na gidan, har ta fidda rai da samu sai gashi ta gani a under stair storage din gidan, bayan ta gama gyaran dakin da take ciki da Babban corridor din sama sai kuma ta sauko downstairs ta fara gyaran babban parlon hade da goge goge, it took her almost 2 hours kafin ta gama aikin gidan gaba daya, kitchen kuma bata ga abinda zata gyara ba cause it was very neat and tidy alamar yana gyarawa a ko da yaushe, ta maida Household cleaners din da tayi amfani da su a under stair storage din da suke sai gashi yana saukowa downstairs ya canza kayan jikinsa, yi yayi kamar ma bai san me tayi ma gidan ba ya dau makullin motarsa da ta ajiye saman Centre table ya nufi kofa ya fita daga parlon, tabe baki tayi ta tafi sama don ta gaji sosai ba kadan ba, sai da tayi gyaran gidan sannan ta kara tabbatar da girman gidan. Khaleesat na zaune a daki da laptop dinta a gabanta tana studying wani course dinsu da za su yi test dinsa ranan monday, it was a Saturday afternoon, ta juya ta kalli wayarta dake vibrate, sau uku kenan Safiyyah na kiranta taki picking don tasan me zata ce, can dai ta jawo wayar tayi picking ta kai kunne tayi shiru, daga daya side din Safiyyah tace “Haba mana Khaleesat don zaki koya min abu sai kiyi ta min walakanci gashi test za mu yi ranan Monday, is it fail that you want me to fail?” Khaleesat ta sauke wani ajiyar zuciya tace “To ya kike son inyi Sophie? i said u should be coming kin ki” A fusace Safiyyah tace “A’a wallahi bazan zo wannan gidan ba kinji har na rantse, haka kawai in zo ya koreni, shi ba wai kara garesa ba balle ince zai ji kunyan korata, gaskiya bazan zo ba don zan iya zaginsa idan ya koreni” Khaleesat tayi dariyar da bata yi niyya ba tace “Wai ban gane ya kore ki ba, why will he do so bayan yasan wajena ki ka zo” Safiyyah tace “In dai baza ki zo school din ba shikenan kawai i will look for another person to teach me, ni kinsan ba gane lectures nake a aji ba sai in an min bayani dalla dalla gani ga mutum” Khaleesat dai tayi shiru tana jin ta, Safiyyah tace “Sai anjima don Allah….” Khaleesat ta ɗan yi murmushi tace “To let me see if i will be able to come, kin ga karfe biyu da rabi yanxu fa, da tun jiya sai ki gaya min ai, kina school ne?” Safiyyah tace “Eh mana, tun 12 na shigo schl ai” Khaleesat tace “Ohk, i will be coming now” Katse wayar tayi, ta sauka daga kan gadon ta canza kayan jikinta ko rigar sanyi bata sa ba don sanyin ya ragu sosai yanxu, ta dau backpack dinta bayan ta saka laptop ciki ta kashe wutan dakin ta fito, downstairs take leke daga passage way din da take tsaye, ta ga Ajay zaune parlon da wasu turawa biyu alamar frnds dinsa ne ga wine a gabansu, she can’t even remember the last time da suka hadu a cikin gidan da shi, it is more than a month now da take gidan amma zata iya kirga sau nawa suka yi crossing part da shi a gidan, yawanci yana bangarensa take fita school da safe, kuma daya daga ma’aikatan gidan ne ke dropping dinta sannan ta gaya masa sanda zai je ya daukota kamar dai yanda aka basa instruction yayi, in kuma aka dawo da ita gidan bayan ta gama lectures zata ga babu motar Ajay a compound alamar ya fita, tunda a daki take zama bata sanin sanda yake dawowa gidan, the next day kuma the same process will repeat it self, girki kuwa tunda tayi sau uku da shi taga duk bai ci ba don ko kusa da abinda ta dafa baya zuwa kawai sai ta dena sai dai tayi nata ita kadai, but tayi noticing anyi restocking foodstuffs irin na Africa a kitchen din probably because of her, don ita duk wani ciman turawa ba damunta yayi ba, may be yayi noticing hakan ne yasa ya siyo mata irin wanda take so, gyaran gida kuma tunda workers din are around iya dakin da take ciki kawai take gyarawa, tana saukowa downstairs ta gaida friends dinsa sannan ta kallesa shi ma ta gaishesa, bai amsa gaisuwan ba without looking at her yace “Ina za ki je?” Ta sauke idonta tace “Zan shiga school” Still not looking at her yace “Ki yi me a school on a Saturday?” Ta ɗan kallesa, sai kuma tace “Tutorial zan ma Safiyyah” Sai a nan ya juya ya kalleta yace “As per the lecturer you are in John Hopkins ko? to baza ki je ba” Tayi shiru tana kallonsa, ya hade rai yace “Ko baki ji me nace ba?” Bata fuska tayi tana kallonsa, ya ci gaba da maganar da yake da friends dinsa, tana jan veil din jikinta tace “To zata iya zuwa nan?” A takaice Ajay yace “Baza ta zo, leave this parlor Madam” Ta wani tura baki ta juya ta koma sama, tana komawa daki ta kira Safiyyah, a hankali tace “Sophie i met the door locked kuma no one is around….” Safiyyah ta katse ta tace “Har workers din gidan?” Khaleesat tace “Kawai ki nemi wanda zai maki Tutorial din Sophie, ranan Monday before the test zan sake yi maki” Safiyyah tace “Ai shikenan, dama ban saka ran za ki zo ba, in ma Ajayn ne ya hanaki shi ya sani don ko a jikina wallahi, dama tun ranan farko da muka je duba Housemate dinki da na fara ganinsa sam bai kwanta min a rai ba naji tsoronsa, wai don Allah yaushe Housemate din ki zai dawo ne abu almost 2 months yanxu, ko dai anyi awarding dinsa doctorate Degree dinsa ne shi ne ya tafi yayi wasu abubuwan a Nigeria? shi kuma wancan uztaz din ko anyi cancelling work dinsa ne yake sakewa daga farko?” Ita dai Khaleesat tayi shiru bata ce komai ba, magana Housemate din nata yake mata balle tasan sanda zai dawo? Kuma kullum da damuwan hakan take kwana take tashi a ranta, ta rasa gane me yasa communicating din da baya yi da ita ya tsaya mata sosai a rai har yake damunta, well… may be he have his reasons, she is not even judging him, but deep down she knows she misses him so much, she misses everything about him, wani lkcn in ta kasa hakuri takan dake zuciyarta tayi masa magana ta WhatsApp, zai kuma yi mata reply amma casually, in yayi mata haka kuma bata iya daurewa sai tayi kuka, last maganar da tayi da shi almost a week ago ta tambayesa yaushe zai dawo, kawai yace mata soon and that was how the conversation ended, after that basu sake magana ba har yau, dama kuma ita ke yi masa, Safiyyah tace “Ni dai sai anjima, ina ta maki magana zaki min shiru katina na tafiya” Daga haka ta katse wayarta, a hankali Khaleesat ta ajiye wayar hannunta a gefen gado. Few weeks later Khaleesat na zaune ranan friday ita kadai a haraban department dinsu, Voice call suka gama da Aunty Farida ta WhatsApp bayan ta turo mata wasu videos da ta kasa fahimta sai kawai ta kira Aunty Faridan don tana online, tunda suka gama wayar Khaleesat ta kasa kwakkwaran motsi a inda take zaune, she looks so confuse and shock at the same time, kamar ance ta daga kai ta ga Aymaan da wata yarinya suna tafiya, yarinyar na ta masa labari da turanci, bata yi kama da er Nigeria ba duk da kana ganinta kasan er Africa ce yarinyar, Khaleesat ta sauke idonta tana kallon wayar hannunta har suka wuce ta, sai ga Safiyyah ta fito daga Hall din karatu da Backpack dinta a hannu, tana isowa kusa da Khaleesat ta zauna tace “Ke baki ga Aymaan ya wuce ba yanxu?” Khaleesat dai tayi shiru don har sannan bata yi recovering daga shock din da take ciki ba, Safiyyah ta kyalkyale da dariya tace “Ni wallahi naji haushi da ya Musty ya neme sa wai har da basa hakuri akan abinda muka masa, me muka masa in ba cowardliness irin na Musty ba? Abinda ma shi ne ya nuna mana halin jakanta, tunda uwata ta haifeni ban taɓa ganin matsoraci kamar Ya Musty ba, ni da nake mace ma na fi sa dakakken zuciya, wai ka samu namiji kamar ka kana basa hakuri, wallahi ban so ace case din nan ya mutu da wuri ba na so ayi ta gwabzawa, na tsani in ga an shashantar da Case me zafi irin haka, bayan hakurin da Ya Musty ya basa naga kamar yana shakkar Ajay ma, kinsan na gaya maki frnd dina Sulaiman ya gaya min ashe narka masa duka Ajay ya so yayi aka maza aka shiga tsakaninsu, amma duk da haka ya sha kulli wajen Ajay, to duk har da hakan ya tsoratasa ya kama kansa da mu, amma nasan zai fake da cewa Ya Musty ne ya basa hakuri, kuma yaga Ajay ya daukeki daga apartment din ki ya maida ki gidansu, kinga ai dole ya tsorata da lamarin, Allah ya sa dai Housemate din ki ma bai ba Aymaan din hakuri ba don daga yanda ya sameni yayi min magana ta WhatsApp sanda abun ya faru har da bani lefi wai me yasa zan yi ma Aymaan rashin kunya wallahi babu tantama shi ma Housemate din naki ya basa hakuri, ni fa na tsani in ga maza suna baya baya da case din tashin hankali kamar wasu mata, shi yasa Ajay ya burgeni da ya nuna masa hauka, wo koma yaya ne dai can ta matse masa shege, ai kinga bai sake bi ta kanmu ba a school din nan, kaiii mun ga jalala ashe lafiyarsa qlau mutumin, sannan bai taɓa aure ba sai yawon iskanci…” Shiru Safiyyah tayi ganin hankalin Khaleesat gaba daya baya jikinta, Safiyyah tayi kasa da murya ta kamo hannunta tace “Me ya faru kawata? Is anything the matter? Naga lafiya na bar ki naje dauko Backpack dina, why the sudden change of mood? Ko Aymaan din yace maki wani abu ne?” Khaleesat ta kasa ce ma Safiyyah komai, sai ga hawaye cike idonta, Safiyyah ta dire jakar hannunta a kasa tace “Subhanallahi, don Allah me ya faru? Me Aymaan din yace maki mu kira Ajay yanxu” Khaleesat na goge idonta cike da karfin hali tace “I spoke with Aunty Farida now” Safiyyah ta zaro ido tace “Me ya faru?” Khaleesat ta sauke idonta a hankali tace “Kawai ce min tayi Housemate dina yaje can gidanmu jiya” Safiyyah ta wani kalleta, can tace “Don Allah ji yanda kika sa gabana ya fadi na zata mutuwa aka yi a gidan naku, to don ya je gidanku sai ki fara kuka? Ko dai dama akwai abinda ke damunki kike son kiyi kukan amma sai yanxu kika samu sarari?” Khaleesat ta girgiza mata kai, wasu hawayen na taruwa idonta tace “Gida wai ya siya ma Abbana” Safiyyah ta bude baki da mamaki tana kallon Khaleesat, can ta dafe kirji tace “Gida fa Khaleesat?” Khaleesat ta kasa cewa komai wasu hawayen na sauka idonta, ta bude wayarta ta shiga chat dinsu da Aunty Farida ta tsaya dai dai wajen videos din ta mika ma Safiyyah wayar, Safiyyah was speechless for almost 2 minutes bayan ta gama kallon videos din gidan, wato gida ne har gida irin na zamani that is well furnished, a hankali Safiyyah tace “I am short of words too Khaleesat, wallahi ban san me zan ce ba, but just know that ur Housemate is one in a million Khaleesat….” Khaleesat ta fashe da kuka, Safiyyah ta rungumeta soothingly tace “It’s something to be happy about ba kuka za ki yi ba, yanda ya saka iyayenki farin ciki Allah Ubangiji ya dawwamar da shi cikin farin ciki na har abada, Allah ya saka masa da mafificin alkhairi, ya biya masa duk bukatansa na alkhairi, yanxu kina komawa gida sai ki nutsu ki kirasa” Cikin kuka Khaleesat tace “Ko na kirasa baya picking” Safiyyah tayi shiru, can tace “May be he have his reasons Khaleesat, just compose a text for him sai ki tura masa ta WhatsApp, and i will also thank him via WhatsApp on ur behalf, duk wani abun farin cikin ki nawa ne nima….” Ita dai Khaleesat ta kasa cewa komai but she is soo emotional, ta kasa daina kukan da take, a haka driver ya zo daukanta, Safiyyah ta rakata har inda yake parking ta bude mata back seat tace “Don Allah kar ki je gida kina wannan kukan, wannan ai abun farin ciki ne ba na bakin ciki ba da zaki yi ta kuka har haka” Khaleesat ta gyada mata kai kawai tana share hawayenta, Safiyyah ta daga mata hannu tace “Anjima zan kira ki in sha Allah” Nan ma dai kawai kai Khaleesat ta gyada mata a haka drivern ya ja motar suka bar wajen. Bayan sun isa gida Khaleesat ta bude kofar parlor ta shiga da sallama can kasa, kanta a kasa ta gaida Ajay da ta gani zaune parlor da Salem, sannan ta wuce sama, sau daya Ajay ya bi ta da kallo sai kuma ya dauke kansa, after some minutes yana kallon Salem yace “I am going up to get some rest, will you still be around?” Salem yace “Ohk i will wait har ka sakko” Mikewa Ajay yayi ya dau wayarsa sannan ya saka House Slippers dinsa ya wuce sama, kofar dakin da take ciki ya tsaya yayi knocking, Khaleesat da ta kwanta gefen gado ta dora kanta saman pillow feeling so emotional ta mike zaune tana kallon kofar, yana bude kofar ta fara goge sauran hawayen idonta, ya shigo closing the door behind him yana kallonta yace “What happened?” Sauke idonta tayi bata ce komai ba, yace “Ba kya ji na ne?” Girgiza masa kai tayi a hankali tace “Ba komai” Yace “Bakomai zaki shigo ma mutane gida kina kuka?” Ita dai tayi shiru bata ce komai ba, yace “Sake kula ki yayi a school din ne?” Ta daga kai ta kallesa ta girgiza masa kai cikin sanyin murya tace “A’a, kawai kaina ne ke min ciwo” Daga sama har kasa ya kalleta sannan yace “Kukan ya baki magani” Daga haka ya juya ya fita daga dakin…. Wajen karfe biyar Khaleesat ta farka daga baccin da ya dauketa tun bayan da Ajay ya bar dakin, da yake ba sallah take ba, mikewa zaune tayi ta jawo handbag dinta a hankali ta bude ta ciro wayarta, number Housemate dinta da bata kara saving ba har sannan tayi dialing hoping he will pick her call today, amma har ya katse bai daga ba, ta sake kiransa nan ma bai daga ba, to yanxu me ma zata ce masa ta WhatsApp, words failing dinta kawai za su yi in ma tace tayi masa magana ta can, bata ma san ta yaya zata fara ba, ɗaga kai tayi ta kalli kofar dakin jin ana knocking, sai da aka sake knocking din sannan ta sauka daga kan gadon tana tafiya a hankali ta tafi ta bude kofar, daya daga workers din gidan ne rike da tray din abinci, mamaki tayi don tun zuwanta gidan babu worker din da ya kawo mata abinci har daki, infact ita ce ma ke girka abinda take ci a gidan, ta dai amshi tray din cikin sanyin murya tace “Thank you” Sannan ta juya ta koma daki, bayan ta ajiye tray din ta bude plate din dake rufe a kai taga Jollof rice ne yana tiriri alamar yanxu aka gama girkin, ga wani aroma me dadi na tashi, ta bude wani plate din taga full chicken laps biyu anyi grilling dinsu, sai kuma bowl din veggies da dressing dinsu a gefe, with 2 bottles of water and a glass cup da can drink, still a kan tray din taga maganin ciwon kai, a hankali ta dau spoon ta goge sa da tissue din da aka yi wrapping dinsa sannan ta fara cin abincin, kuma sosai abincin yayi dadi, ya kuma yi yaji kamar a Nigeria aka yi, ta dai ci abinda zata ci ta ajiye sauran for dinner. Washegari still haka aka kawo mata breakfast har daki, bacci ma take tunda ba school zata je ba ta sauka kan gadon ta saka hijab sannan ta bude kofar, bayan ta amshi tray din ta kulle kofar dakin ta tafi ta ajiye breakfast din don sai ta fara wanka…. Wajen karfe biyar din yammacin ranan Ajay na parlor tare da Salem aka bude kofar parlon, tun da ta shigo Ajay ke kallonta da wa enda ke biye da ita a baya, wato jakadiyarta da aminiyarta Hajiya Usaina, sai er aminiyarta da bazata wuce 25 years ba, Salem ya mike tsaye yana welcoming dinta da ladabi, ta amsa masa sama sama without looking at him, sai da ta zauna parlon bayan jakadiyarta tayi saurin gyara mata throw pillow sannan Ajay ya gaisheta, ta amsa cike da isa tace “Daga Massachusetts Boston mu ke, mun je convocation din Afrah a Havard University, we will be passing the night here before leaving for Nigeria tomorrow” Ajay dai bai tanka ta ba, ya gaida aminiyarta warce convocation din er ta suka je a Havard din, Afrah dake ta kallonsa ta gaishesa, ya amsa without looking at her sannan ya mike ya nufi sama, shi dai Salem ya juya ya fita daga parlon, Ajay na haurawa sama direct dakin da Khaleesat take yayi knocking sannan ya bude kofar.*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788 👈🏻, it’s better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*
