Hausa novels

Zakuna Biyar Page 4 By Princess Teema

Wayarsa kirar Infinix hot 12, wayar ta ɗan sha jiki kaɗan, screen ɗinta ta gefe ta ɗan tsage, amma lafiya lou yana kallo. Sauƙowa kasan bed ɗinsa ya yi, a nan ya fahimci Leo bai yi barci ba, wucewa ya yi ya nufi hanyar toilet…A saman WC ya zauna tare da laluɓo wata number da aka yi saving da my Ummie ya danna kira. Yana yi yana duba time. Bugu ɗaya aka ɗaga, sanyayyar muryar mace ce ta karaɗe kunnensa da cewa. “Bloody sai yanzu ka tina da ni ko?”. Da sauri ya hau girgiza mata kai yana faɗin. “A’a Ummie, tin da safe na so kiranki amma ban samu dama ba, mun fita training ne yau”…….. Sanyayyar ajiyar zuciya ta sake sauke kafin ta ce. “ALLAH sarki, ka ce kasha wahala kenan?”…… “A’a Ummie, babu wata wahala, ke dai ki cigaba da tayani da addu’a kawai, in fito da kyakkyawar result, in zama babban soja dan kiji daɗin rayuwarki, zan cika maki burinki matuƙa”. “In Sha ALLAH ina tayaka da addu’a bloody na, ka kara dagewa ka ji? Ina kewarka sosai”………. “Ni ma ina kewarki sosai Ummie na, ki kula da kanki kin ji?”…….. “In Sha ALLAH zan kula, kai ma ka kula, kaga kai kaɗai nike gani in ji daɗi ko? Kai kaɗai ka rage mun a duniya”…… “Haka ne, amma nima ai kin san ke kaɗai ke gareni ko?”. “E haka ne”. Ta bashi amsa a taƙaice, da alamar barci a voice ɗinta.”To shikenan ina yayana?”. Ya faɗa yana gyara zamansa……… “Yayanka yana barci, nima tinaninka ya hanani rintsawa, na damu ina son jin ya ka wuni, na kira layinka sau ba adadi amma baya shiga”. “ALLAH sarki, ai na kashe wayar ne dan in samu damar yin abin da yakamata, yanzu dai ki je kin kwanta, sai da safe zamu yi waya tin da kin ji ina lafiya”……… “To shikenan, kada ka manta da alwalar barci da kuma addu’a, sannan ka dinga cin abinci sosai, ka kuma mai da hankali a kan aikinka, kada ka manta da karatun Alqur’ani da littafan addu’oi”. Tin da ta fara magana yake jinjina mata kai har ta kai karshe, sannan ya amsa da okey In Sha ALLAH zai yi dik abin da ta ce. Albarka ta sanya mashi daga haka suka yi sallama ya katse kiran. Shiru ya ɗan yi tare da kurawa wayar tasa idanu, can kuma ya shiga gallery ɗinsa, ya fito da wani hoto nasa shi da wata kyakkyawar mace, fara tas mai kyan fuska, sai murmushi take yi cikin hoton, ga ta da dimple mai ɗaukar hankali irin nasa. Shiru Zaynash ya yi yana tinanin mafita a garesa, ya so faɗawa Ummie cewa aikin soja akwai matuƙar wahala, amma ya gagara, dan baya son fara bata wani damuwa daga tafiyarsa, idan kuma bai faɗa mata ba ta ya zai dinga samun kwarin gwiwa? Zai iya idan ba’a karfafa shi kuwa?.Waye Zaynash? Mu ɗan ji tarihinsa kaɗan. Zaynash maraya ne da bashi da uwa kuma bashi da uba, sai yar uwarsa guda ɗaya mai suna Ummie, wacce suka yi waya a yanzu kenan! Ummie ita ta reinesa tin yana karami, mahaifansu sun rasu tin yana da shekaru huɗu a duniya, ita kuma tana da shekaru 13 a lokacin, haka ta renesa, daga cikin ƴan uwa babu wanda ya kula da su, saboda mahaifinsu bai mutu ya bar komai ba sai kangon gida da ko kofa babu da kuma gona, haka Ummie ta juri yunwa na cikinta, ta juri dik wata wahala wajen renonsa, ta shiga kalubale da dama saboda shi, sau uku ana ƙoƙarin keta mata haddi dik saboda neman abincin da zata bashi ya ci a lokacin da yake kukan yunwa.Sun rayu cikin kunci da talauci, ba makarantar boko sai ta islamiya, ita ma islamiyar makocinsu ne mai makarantar yasa ya ɗaukesu kyauta. Sun mai da hankali har Ummie ta haddace Alqur’ani mai girma, kakarsu wacce ta haifi babansu ita ma tana gidan nasu ne, amma da yake ta tsufa sosai sai yazamana bata iya taimaka masu da komai sai dai ma su su taimaka mata, dan haka Ummie ke ciyar da su. Shi kuma Kanin babansu ɗaya tilo a duniya yana can wani gari yana rayuwa, tin da ya tafi neman kuɗi bai dawo ba.To a haka dai suka rayu har Ummie ta zama budurwa. Da yake suna da balain kyau kamar ƴaƴan larabawa hakan yasa samari suka fara tururwar zuwa neman aurenta. A lokacin bata yarda ta kula kowa ba, ta cigaba da karatun islamiyarta har ta zama Ameera a islamiyar tasu, malamin ya ɗauketa tana karantarwa a wajen dik wata yana biyanta kamar 5k a kuɗin Naija. Da wannan 5k ɗin take amfani ta haɗa da ɗan aikatau na mutane da wanki a gida da takewa mutane, ta haɗa kuɗin ta sanya Zaynash makarantar boko dake ɗan babban gari kusa da su, ta ce ya yi karatu zai taimaka masu a rayuwa tin da shi namiji ne. Zaynash yana primary 4 a school uncle ɗinsu kanin babansu ya zo garin ganin gida bayan tsawon shekaru. Ya jajanta halin da suke ciki, ya kuma yaba da ƙoƙari irin na Ummie, daga nan ya ce zai tafi da su birni su yi rayuwa a can. Bai yi ƙasa a gwiwa wajen ɗaukarsu su koma can ba, suna zuwa can kuma wani fitina ta tashi ta tsaya na matarsa, ta ce waɗan nan ƴan kauye ba za su zauna mata a gida ba, an yi juyin duniyar nan taki yarda, a na haka kakansu ta faɗi ta rasu, dalilin kenan da yasa matar tasa ta hakura su Ummie suka zauna, imani ya ɗan shigeta ganin mutuwar tsohuwar a gabanta.Su Ummie sun yi zaman shekara ɗaya a gidan amma cikin rashin daɗi da takura, ga kuntatawa da Auntyn tasu matar kawun nasu take masu, dik ta sallami ƴan aikinta su Ummie suka zama masu mata bauta, sun ci kwakwa matuƙa kafin kanin Auntyn tasu da ya dawo daga bautar ƙasa ya ga Ummie ya ce shi fa ya yi mata, yaga tsantsar kyau, Auntyn tasu ta so hana auren amma ALLAH ya yi sai anyi, Ummie ta auri wannan bawan ALLAH. To shi ma dai ba wani kuɗi yake da shi ba, yawon neman aiki yake yi, ɗan makaranta ne. A lokacin Zaynash ya kammala primary, dan zuwansa babban gari ya cigaba da karatu, uncle ɗinsu ne yake biya mashi kuɗin makaranta. In taƙaice maku labari har yanzu Ummie tana cikin talauci da kunci ga takurar dangin miji musamman wannan Aunty tasu, dik ta shafe mata bakin fenti a family shi ne yasa basa sonta ko kaɗa. A lokacin da Zaynash ya kammala secondary school sai ya ce shi makarantar sojoji zai tafi, ya zaɓi hakan ne kuma bisa ra’ayin Ummie, tana son ya zama babban soja dan kawo karshen ta’addancin dake faruwa, saboda ƴan bindiga ne suka kashe iyayensu, suka shiga har gida suka yi masu rashin mutunci, sannan suka yi garkuwa da su, da ba kuɗin fansa shi ne suka kashesu suka baiwa karnika gawarwakinsu. In kara takaice maku yanzu auren Ummie da mijinta shekara biyu kenan, bata taɓa haihuwa ba, hakan yasa dangin mijin suka kara sakota a gaba, zagi da cin mutunci kala-kala suke yi mata, kannensa da Auntynsu matar uncle ɗinsu sun hanata shan iska, da ta yi magana ace juya bata haihuwa. Dalilin kenan da yasa Zaynash ya kara mai da hankali dan ya zama babban soja ya ga ya fitar da Ummie daga cikin kuncin da take a ciki, yana balain son ƴar uwarsa kamar yadda take mutuwar son shi. Dama da zai zo GIDA SOJA uncle ɗinsa ne ya yi mashi komai, amma sai da ya sayar da gidansu na kauye da konarsu, sannan ya cika ya kawosa nan, dan AZURE ba dik kai ba, makaranta ce na ɗan wane da wane, uncle ɗinsu ya kashe makudan kuɗaɗɗe kafin Zaynash ya samu wannan makaranta, and da kyar Auntynsu ta bari uncle ɗin nasu ya yi mashi komai ɗin, ita kuma Ummie kuɗi kimanin 50k a kuɗin Naija ta bashi, wannan dalilin yasa ya baya son kawo mata abin da zai ɗaga mata hankali, ya yi alkawarin daurewa dan ya ga ya cinwa narasa. Amma fa bai tsammaci haka GIDAN SOJA yake da wahalar gaske ba. A TAKAICE KENAN RAYUWAR ZAYNASH, DAN HAKA DIK YADDA ZAKU GA YANA GASA DA SAURAN YARA DAN YA ZO NA FARKO KADA KU GA LAIFINSA, BURINSA NE HAKAN DAN TSAMO ƳAR UWARSA DAGA WAHALA, SHIYASA YA DAGE!!. ————————-🔥Ya jima sosai zaune a wajen kafin ya miƙe tare da kashe wayar tasa, sannan ya dawo cikin ɗakin. Still dai idanun Leo biyu yana karance-karance da nazartan makaman da aka koyar da su yau. Ko ɗago kai bai yi ya kalli Zaynash ba, yana cigaba da abin da yake yi. Shi kuma Zaynash sai kallonsa yake yi har ya isa saman bed ɗinsa, ya kwanta tare da jawo bargo zuciyansa cike da tinanin yadda zai rayu a GIDAN SOJA. Ya so ya ɗan yi karatun abin da aka koya masu ɗazun kafin ya yi barci, sai dai ina, gajiyar wahalar da suka yi tasa barci ta yi awon gaba da shi. Shi kuwa Leo ya yi karatu har 1 na dare, kafin ya miƙe ya ɗauro alwala, ya zo ya yi nafilfilinsa, daga karshe ya rufe da shafa’i da witiri kafin ya kwanta dan ɗan rintsawa shi ma!.4:30 ASUBA. Wannan busa ta jiya ita ta tada su, sun sha mamakin ganin yau ma Leo idanunsa biyu yana zaune a tsakiyar gado yana duba waya. Tambayar kansu suka shiga yi wai shi wannan baya barci ne?. Basu san yanayi ba, amma tin 4 yake farkawa, kuma sai 1 yake kwanciya, barcin 3h yake yi.Da wani irin ciwon jiki Vash ya farka, ga in da aka zane shi jiya ya yi ruɗu-ruɗu ya kumbura, idaninsa jajir, jikinsa dik babu kwari. Da kyar ma ya iya tashi, intently ya diro kasan bed ɗinsa, cikin wani irin matsanancin hali ya nufi toilet ba tare da ya yi wa kowa magana ba, shi kaɗai ya san me yake ji. Dirowa ƙasa Zaysh ya yi ya nufi toilet shi ma, jikinsa dik tai tsami. Noor kam komawa ya yi ya kwanta, har da kukan shi jikinsa ciwo yake yi mashi, dan haka wlh ba zai iya tashi ba. Wanka su Zaysh suka yi tare da fitowa suka shirya. Leo already ya yi wanka ya shirya, dan tim 4 ya tashi, yanzu kuma 4:30, wannan 30 mins sun ɗaukesa shiryawa.Bayan sun kammala shiri ne Vash ya ce bari ya tashi Noor. Zaysh dake ƙoƙarin ɗaure jakansa ya ce. “Ka kyalesa ba, zai tashi da kansa ne”……. “No brother, kasan halinsa, bari in tashesa kada a mashi duka”…….. Cigaba da abin da yake yi Zaysh yai bai sake yin magana ba. Slowly Leo yai switch off na wayarsa tare da ajiyeta a saman bed ɗin, ya ɗauko littafin karatun makamansa na jiya ya diro ƙasa da shi, jakansa ya buɗe tare da mai da book ɗin, sannan ya shinfiɗa bed ɗinsa da kyau, ya naɗe bargonsa, ya ɗauko army p-cap sabuwa daga cikin jakan ya sanya a kansa, daga nan ya nufi waje ba tare da ya kalli in da suke ba. Da kallo suka bishi har ya fita. Vash ya ce. “Awww ashe fita ta kofa yake yi, all though ɓacewa yake yi”…….. Harararsa Zaysh yai tare da cewa. “Baka da hankali, dama fita yake yi mana, wani hanya yake bi shi ne abin mamakin”. Ya kai karshe tare da karisa ɗaure jakan nasa, ya ciro biscuit guda ɗaya, sannan ya nufi waje. “Wait for me”. Vash ya faɗa yana nufar bed na Noor. “Yi sauri”. Cewar Zaysh da ya tsaya ta waje a bakin door…… Yana tsaye a wajen sai ga makwaɓcinsu Unays ya dawo zai shiga cikin ɗaki da gudunsa. Binsa da kallo sosai ya yi, a nan ya fahimci dik yadda aka yi daga wajen motsa jiki yake, watau dan ya zo na farko a daren ma baya barci? Fita yake hora kansa? Tab lallai ya fisu zalama wannan, kai kai kai, ya zo da sabon salo fa. Shiru ya yi yana tinani anya shi ma ba zai fara hora kansa ba kuwa? Da daddare idan kowa yai barci. A daidai lokacin Vash ya dafasa tare da cewa. “Let’s go, Noor yaki tashi”……. “I already told you that ba zai tashi ba, just leave him, bodynsa zai faɗa mashi”. Vash yana da tausayi ne sosai, sai ya ɗan yi jim, fuska da alamar tausayi ya ce. “But bai kamata mu kyalesa ba ai”..,…….. “Saboda kai ne ubansa?”. Zaysh ya faɗa. Da sauri Vash ya girgiza kai. “No, amma a nan we’re brothers, mun zama ƴan uwa tin da babu iyaye”. Gaba Zaysh ya yi tare da cewa. “Ai sai ka tsaya kada ka tafi tin da Noor bai farka ba, kai waye ma ya ce maka a gidan soja lokacin horo ana taimako ne? Ko da yake kai sabon zuwa ne, bari ka fara gogewa a nan ne ina ga in ka taimaki wani aka baka horon da sai ka kwanci mutuwa zaka gane me nike nufi”. Yana tafiya yake wannan magana. Da sauri Vash ya rufa mashi baya zuciyansa cike da tausayin Noor. Kai tsaye masallaci suka nufa, a lokacin har an kira sallah, ana shirin tada kabbara ma. Bayan sun yi sallah sun fito, kowannensu sai miƙa yake yi, saboda wahalar da aka sha jiya, jiki dik tsami, daga masu cewa wash, sai masu cewa ash, sai kuma masu cewa bayana, abinku da farin shiga.A gabansu Captain ya tsaya cikin tsantsar jarumta da nuna dakan jiya ne shi, cikin kakkaifar murya ya ce. “1, 2, 3 start!” Cikin ɗaga murya.Yana cewa start suka buɗi baki game da ɗaga murya suka fara rera taken GIDAN SOJA…… “We march through fire, through storm and rain, with steel in heart, we bear the pain, for land and honor, we stand so tall, United as one, well never fall. Oh, we rise, we fight, we stand as one, through darkest nights, til battle’s won. With fearless hearts, our banners wave, We are the strong, we are the brave! Our boots leave echoes on the ground, A thunderous beat, a mighty sound. No chains can break the will we hold, Our spirit fierce, our hearts like gold. Through blood and dust, through fire and war, we march ahead, forevermore. For freedom’s call, for justice true, Our oath is strong, we’ll see it through. Oh, we rise, we fight, we stand as one, through darkest nights, til battle’s won, with fearless hearts, our banners wave, we are the strong, we are the brave!”. Suna kai ƙarce ba tare da ɓata lokaci ba ya ce.”Yau ce ranarku ta biyu a GIDAN SOJA, yau ma zaku sake maimaita horon jiya ne har na tsawon sati biyu, amma na yau za’a fara karfafa maku horon ne domin juriya da jajircewa wahalarku ta karu, horon yau ba kamar ta jiya bace ba, da ɗan banbanci, a yau dole zaku yi gudun kilo mita biyar ne saɓanin na jiya biyu, kuma a yau akwai lokaci, lokacinku zai fara kirgawa ne daga yanzu, dan haka ku bada himma, ku ɗauki waje, ku shirya!!!”. Ya faɗa da karfi alamar su karfafa zuƙatansu, sannan ya ɗan dakata da maganar yana bin fuskokinsu da kallo. Can ya tsayar da kallonsa a kan Noor dake tsaye a karshen line ɗin jikinsa jike da ruwa, yanzu ya iso wajen sai haki yake yi, irin ta jiya aka sake maimaitawa, yaki tashi, da Commander ya taka shi kuma ya firgita ya sume masu a wajen, aikuwa Commander yasa aka kaisa wajen tap aka mashi wanka da ruwan sanyi, irin dai jiya. Ga shi bawan ALLAH dik ya yi tsuru-tsuru kamar anwa akuya wanka da ruwan ƙanƙara, gwanin ban tausayi wlh.Shiru Captain ya ɗan yi, ya kalli Noor ya kuma saci kallon Leo dake gefensa ya zura hannaye a aljihu kamar mai tinanin wani abin ya yi shiru. “Na sake maimaitawa. Yau ba kamar jiya ba, yau zaku yi gudu na tsawon kilomita biyar ba tare da tsayawa ba, dan kuna da lokacin dake kirgawa wanda in ya cika baku kai madakata ba, to dik wanda ya rage a baya, sai ya sake farawa daga farko kuma a wannan adadin lokacin ba karawa, ya sake gagara iyawa zai sake farawa, dole sai ya yi a wannan lokaci da aka ɗeba mashi ko kwana zai yi a nan, kuma babu juyawa!”…….. Ya sake maimaita jawabinsa ne saboda Noor, saboda ya kalli gabaɗaya yaron hankalinsa baya a kansu, yana firgice sosai. “Ready!”. Ya sake faɗa in a hash way.A take suka kara kamewa suna ɗaukar harama. “Go!!”. Cikin ɗaga murya ya faɗa, cikin zafin nama suka bazama da gudu suka nufi hanya. Da farko-farko su Noor an zage sosai, dan yana sahun ƴan gaba-gaba. Da gudu ta yi gudu kamar kilo mitna uku haka, sai ga shi ya fara baya-baya.Ba shi kaɗai ba, dayawan sojojin sun ja da baya daga wannan gudu, bayan kamar mintuna 10 suna gudun, gwiwowinsu sun fara kerma, amma ba wanda ke da damar tsayawa, dole su yi gudu in ba haka ba su faro daga farko, a wannan waje ne ake cewa BA SANI BA SABO!. A daidai wannan lokaci matasa uku suka zube gwiwowinsu a kasa, sun gaji ba zasu iya cigaba da gudu ba! Cikin waɗan da suka zube gwiwowinsu har da Noor, saboda bai taɓa yin gudu haka ba, ba zai iya jura ba, jiya ai tafiya ce ba gudu ba!.Suna faɗuwa Captain dake biye da su a baya yana isowa yasa wasu zaratan sojoji su ɗaukesu aka mayar da su can farko su fara. Da farko Noor ya ɗauka wasa ake yi da ake cewa in suka faɗi zasu faro, bai san a GIDAN SOJA babu wannan wasa ba! Magana ɗaya ake yi babu ƙari! Lallai shi ma a yau ya shaida cewa babu tausayi a GIDAN SOJA, nan ya fara kuka da hawayensa yana faɗin a barsu su cigaba kada su fara daga farko! Sai dai babu wanda ya saurare shi, suma sojojin da aka sanya su ɗaukesa ba imani ne da su ba, suka ɗaukesu suka mai da su farko, kuma suka tilasta masu gudun dole ko su sha zabga-zabgan bulalu. Kafafun Noor tamkar zasu ɓalle, jikinsa har yana wani irin kerma! Su Zaynash har sun kai in da madakata yake su kuma Noor yanzu suka sake farowa. TO MU BI BAYAN SU ZAYNASH MU GA NI, KAFIN DAGA BAYA MU DAWO BAYAN NOOR.Suna isa madakata kowannensu ya dakata, masu kwara amai a gefe suka fara kwararawa, masu zubewa ƙasa dik suka zube suna nishi sama-sama. Shi da kansa Leo yau sai da ya durkusa ƙasa, saboda ya ci wahala. Captain yana zuwa ya ce ya basu mintina uku da su miƙe su sha ruwa sannan su yi readyn cigaba da gudu dan komawa in da suka fito. BABBAN MAGANA!.Take wasu zuƙatasu ta fara karaya da aikin soja, wasu suke jin tamkar su koma gida, ba zasu iya jurar wahalar nan ba, wai ba’a barinsu su huta. Basu san idan har za’a barsu suna hutawa to ba amfanin training ɗin ba, saboda jikinsu ba zai saba da wahalar har ya bada juriya ba, wannan hutu da zasu dinga yi zai rinƙa haifarwa da garkuwar jikinsu ƙasala da rauni! Shiyasa ba hutawa, daga wannan sai wannan har sai jikinsu ya karɓi azaban sosai!. ————————-🔥A gaggauce suka sha ruwan da aka shirya masu a wajen tin kan su iso, Sannan suka dasa daga in da suka tsaya, a hanyarsu ta komawa kilomita 3 daga farkon farawa suka ci karo da su Noor suna yi, yana kuka tamkar ransa zai fita, baya ganin gabansa, gudu kawai yake yi, da alama ya sake faɗuwa aka mayar da shi daga farko, dan da ya ci ace sun wuce kilo mita 4 yanzu.Zaynash da Vash sun yi mugun tausayawa Noor, suna jin tamkar su je su karɓa mashi, amma ba dama, Vash har idanunsa suka ciko da kwallah sosai. Bayan sun koma sai kuma me? Crawling under fire simulation, watau rarrafe karkashin igiyar da suke wa laƙabi da igiyar wuta. Ba kamar jiya normal igiya ba! TASHIN SENSE!.Cikin wani fili suka nufa, inda aka shimfiɗa igiyoyi masu ƙarfin gaske, inda dole su rarrafa a ƙarƙashinsu cikin ƙasar laka. Ga wasu zaratan sojoji a both side dake watsa masu ruwan kamar na sama dan ƙara wahalar rarrafen. Sannan dole su yi wannan rarrafe na tsawon mita 30 ba tare da tashi ba, suna tashi waɗan ban igiyoyin ƙayoyi ne a jikinsu, irin karafunan nan ne masu ƙayoyi, dik zai cake masu jiki, shiyasa ake danganta wajen da fire, saboda wahalarsa, idan ka yi kuskure waɗan nan kifiyoyin suka cake maka hannu da sassan jiki ka zub da jini, ko ka ji ciwo kuma dole ne ka cigaba da yin horo.Haka suka afka wannan waje suka fara yi, a wannan lokaci matasa dayawa sun yi kuka, kuka sosai tamkar ba maza ba! Sun ji azaban da basu taɓa zata ba!. Sai dai kuma har suka kammala babu wanda aka samu ya tashi, sun jajirce, dik da suna kuka sun jure sun cinwa in da ake so!.Bayan nan kuma sai aka ɗaukesu zuwa wani katafaren waje, aka tsaitsai da su shiru, sannan wasu sojojin suka zo suka hau ɗaɗɗaure masu idanu da hankey na sojoji. Zasu aiwatar da blindfolded navigation horon laluɓe ne a cikin duhu, saɓanin jiya na sallaƙa tsaunika ƙanana.Bayan an ɗaure masu idanu babu damar kallo ko kaɗan, sai aka kwashesu a motar sojoji zuwa cikin daji mai ɗan duhu saboda cikar dogayen bishiyoyi da manyan itatuwa masu ganye, dik a cikin Barrack ɗin wajen yake, dama waje ne na musamman domin horar da matasan sojoji.A nan Captain ya umarcesu da kowa ya tsallaka duwatsun dake gabansa, ya yi dik mai yiwuwa domin fitar da kansa daga cikin wannan waje. Ya kara da cewa, akwai duwatsu, sannan akwai itatuwa, akwai ramuka, wasu ramukan da ruwa, wasu kuma babu, dan haka su fitar da kansu daga wannan daji.Bayin ALLAH, ba gani da ido, ga shi kwata-kwata bama su san filin ba, bare ace sun san ya yake zasu iya kwatar kansu, yanzu fa sai dai su dogara ga jin sautin umarni Captain, da kuma jin sautin nunfashi ƴan uwansu da laluɓe cikin duhu. Kuma idan suka tafka kuskure, za a mayar da su su sake farawa ne.Sun tsorata sosai, dayawa daga cikinsu sun karaya. Da Captain ya ga haka sai ya ɗan yi gyaran murya tare da cewa. “Wannan horo yana koyar da ku amincewa da kai, zaku iya yakin sunkuru ta hanyar shaƙar numfashin mutum, zaku iya yaki a daji ba tare da tsoro ko fargaba ba, koya maku yadda ake yakin sunkuru ne wannan, zai zamana da numfashin abokin gaba zaku iya farmakarsa, zaku koyi yaki da ji da motsi ne kawai, dan haka get ready!!”. Jin kalamansa yasa sun karfafa zuƙatansu, sun jajirce sosai, sun kuwa kara ɗaura ɗamara, take suka sauke ajiyar zuciya. Nan Captain ya umarcesu da su fara. Laluɓe suka fara yi, wasu na capko wasu, wasu kuwa tin ba’a je ko’ina ba sun fara faɗuwa ƙasa, wasu sun fara buguwa da jikin itace.30 mins kawai garesu su fita daga cikin wannan daji, hakan yasa suka kara mai da hankali sosai, amma sun jijji ciwo ta hanyar faɗuwa, buguwa da dutse, buguwa da itace, dik sun fita hayyacinsu kafin su fito daga wannan waje.Suna fita aka kwance masu idanu, kowannensu da sauri ya fara bin in da yake da kallo, suna nishi sama-sama. Ruwa aka basu kowa ya sha, sannan aka ce 5 mins garesu. Izuwa yanzu sun fara sabawa, dan haka basu ji wani tsoro ba da aka ce 5 mins garesu. Wasu ma irinsu Leo, Zaynash, da Unays sun yi gaggawar riga kowa miƙewa domin cigaba da karɓar horon. Matasan sojoji da dama sun ji ciwo a hannun da gaban goshi, amma Captain bai nuna kamar ya gani ba dik da ya ganin, ya umarcesu kawai da su tashi su koma cikin motocin da aka kawosu bari su koma.Da kyar wasu suka iya tashi, amma ko kaɗan babu alamar tausayinsu a idanun manyansu, kamar ma basu san suna yi ba! Kuma da dik wani motsinsu a idanun Generals na sojojin ne. Sun yi matuƙar mamakin ganin yadda aka ɗaukesu zuwa wajen wani bene mai bala’in tsawon da ya fi na jiya, ya fi dik benayen dake GIDAN SOJA tsawo sosai. Kallon-kallo suka fara yi a tsakaninsu kafin su mai da kallonsu a kan Captain dake tsaye ya rungume hannaye a kirji. Ganin suna kallonsa yasa ya yi masu nuni da benen a kan su haura. Dole suka fara haurawa da gudun gaske, dan ba wasa ake yi a nan ba, dik jigatar da suka yi ɗazun basu bi ta kansa ba.A nan ana koya musu yadda za su shawo kan tsoro ne. Dole su hau kan bene mai tsayi su tsaya ba tare da motsi ba, sannan su tsallaka wani igiya daga gefe zuwa gefe, ma’ana daga wannan bene zuwa wani bene. Wanda ya nuna tsoro, sai a barshi a can sama har sai ya cire tsoron gabaɗaya. Dayawa daga cikinsu jikinsu ya yi kermar tsoro, amma dole suka jajirce, dayawa daga cikinsu daga kan wannan horo zuƙatansu ta fara bushewa, take suka daina jin tsoron mutuwa, ace ka hau bene can sama, sannan ka bi ta kan igiya ka tsallaka daga wannan bene zuwa wani? Ai dole zuƙata su fara bushewa daga tausayi da tsoro!. ————————-🔥Bayan dik wahalar da suka sha, sai aka koya musu rikon ƙananan bindigogi wanda aka karantar da su jiya, su za’a sanyasu rikewa da yadda ake sauya harsasai cikin minti biyu kacal. Idan mutum ya kasa cika wannan lokaci, sai a hukunta shi da ƙarin horo hawa bene ko rarrafawa cikin ƙasa or taɓo. Wanda ya fi kwarewa, shi ake ba damar jagorantar abokan horonsa, hakan yasa suka zage dantse.Captain ya kura masu ido sosai yana kallon motsin kowa, tin daga kan yadda ya ga Leo yake canza bullet na bindigarsa ya gane ba yau guy ɗin nan ya fara rike bindiga ba, lallai dole yasanta sosai, saboda a ƙasa da minti ɗaya ya canza bullet ɗinsa, ba Captain kawai ba, harta manyan jami’an dake kula da dik motsin matasan sojojin sun razana da ganin abin da Leo ya yi, har ya sanya masu shakku a kansa, suka fara jin anya kuwa ba wata a ƙasa kuwa? Dan shi ba ɗan kasansu bane, saboda GIDAN SOJAN AVARIS da ya fita daban a duniya ne yasa ya ce zai yi appley a nan, zai zo ya karɓi horonsu da kyau, a gida ma sun ki, amma ya kafe shi fa lallai sai ya zo, da suka ga ya kafe kawai suka sake mashi.In takaice maku labari haka ranansu ta biyu ma ta kasance a GIDAN SOJ, suka karɓi horo kamar jiya. Bayan horo, kamar jiya sai karfe 8:30 bayan sallar isha’i suka koma ɗakunansu. Suna shiga suka yi wanka suka hau shirin kwanciya. Sai dai da suka shigo basu ga Noor ba, kuma basu tambayi ina yake ba. Suka hau shirin kwanciyarsu, suna cikin shiri ne ya shigo ɗakin tare da rakiyar wasu sojoji guda biyu, ya ji ciwo ne a kafa sosai a dajin da aka kaisu aka ɗaure masu ido, ya taka wani karfe ta fasa mashi kafa, ciwo ne da ba za’a iya kyalesa ba, dole suka ɗaukesa zuwa military hospital ɗinsu aka wanke kafar aka gyara mashi kada wata cuta ta shiga.Sojojin suna rakosa suka juya suka fita, shi kuma ya kariso ciki, da sauri Vash and Zaysh suka yi kansa, rirrikesa suka yi suna tambayansa me yake faruwa. Idanunsa a kumbure saboda uban kukan da ya ci, kyawawan pink lips ɗinsa irin na mata sun ciza sosai, saboda ya yi ta ciccizasu a lokacin da yake jin azaba, har gefen lips ɗin nasa ta fashe saboda damketa da hakori da yake yi. Kama shi suka yi zuwa saman bed, suka kwantar da shi tare da cigaba da tambayansa me yake faruwa. Idanunsa ya rufe kafin ya kwashi dik irin azaban da ya sha ya faɗa masu. Gudun farko kawai ya maimaita sau biyar, rarrafawa cikin kasar laka ya yi sau uku, a wannan daji sai da ya ya dinga sakewa har sai shidda, a nan ne ya taka wani karfe mai kaifin gaske ta fasa mashi kafa ta jefe wajen idon sahu ba ta wajen takalma ba. Tin da ya fara basu labari suka yi mugun tausaya mashi, sai sorry suke ce mashi. A tare suka haɗa kai, suka shirya mashi ruwan wanka, sannan suka tallafa mashi ya shiga toilet dan yin wanka. Dik abin da suke yi Leo yana zaune yana nazarin makaman da aka kara koya masu yau, na jiya ne aka sake maimaita masu da kyau dan ya shiga kansu yadda yakamata. Bai ko ɗago ido ya kallesu ba, dan shi ba abota ya zo yi GIDAN SOJA ba! Horo ya zo karɓa.Bayan Noor ya kammala wanka da shirinsa tsab, kowannensu ya haye saman bed ɗinsa, sannan suka fito da wayoyinsu kamar jita. Noor ne ya fara kunna wayansa, dan kafin a basu wayoyin sai da aka shar’anta masu cewa da daddare ne kawai aka lamunce masu su kunna waya, dan haka in zasu kwanta suka kashe wayar basa sake kunnanta sai sun dawo ɗakin bayan horo.Shi dai Zaynash yaki fito da wayansa, dan yana jin kunyarsu, dikkansu wayoyinsu manya-manya na ƴaƴan manya, nasa ce kawai matacciya, sai yake jin kunyar fitarwa. Noor yana kunna wayar ya kunna data, nan sakonni suka hau shigowa kamar ruwa, dik kuma na ƴan uwansa mata ne dake ta turo mashi saƙon kukan sun yi kewansa. Bai bi ta kan kowannen saƙo ba, kai tsaye ya shiga kan number da aka sanya my dad. Video call ya dannawa wannan number yana ɗan gyara kwanciyarsa da kyau, sai ciza laɓɓa yake saboda zafin da jikinsa take yi mashi. Bugu ɗaya aka ɗauka, dik da ɗakinsu da haske amma fuskan Noor bata fita sosai a call ɗin ba, hakan yasa ya kunna hasken wayar ta gaba. Yana sauke idanunsa a kan wani kyakkyawan mutum mai ɗan matsakaicin jiki, suna kama sosai, fari tas da shi, ga idanu dara-dara farare tas, da alama mutumin ma a kwance yake, kyakkyawan gaske sosai. Harara ya dallawa mutumin kafin ya ce. “My dad baka yi barci ba?”……. Wani irin cool smiling ya saki kafin ya amsa da. “I’m waiting for your call, how can I sleep?”………. Sake hararansa Noor ya yi. “Daddy gidan Soja akwai wahala, ba zan iya jura ba, ka zo ka ɗaukeni”. Ya kai karshen maganar cikin raunin murya. “Pleasure very soon zaka saba”…. Zai yi magana daddy yai sauri sake cewa. “No, kawai ka faɗa mun success da ka samu a yau?”. Yana turo baki ya amsa da. “Alot my hero”. Wani irin ƙayataccen murmushi dad ya saki kafin ya ce….. “Thats is my son, I know you will succeed, try to bring us a good result”….. “I will try my best dad, where’s my Auntys?”……. “They’re not here, they’re in their room, but Lisa bata nan”……. Shiru ya ɗan yi, sai kuma ya ce. “Dad here is my friends da na haɗu da su a nan, they help me and they’re so king and perfect”. Ya faɗa tare da juyar da wayansa ya nunawa daddy bed ɗin su Zaynash dake kwance shiru.”Zaynash this is my dad, ku gaisa”. Ya faɗa yana sauƙiwa kasan bed ɗin intently, ya zo ya miƙawa Zaysh wayar. Karɓa ya yi, a mutunce suka gaisa, daga nan ya karɓa ya miƙawa Vash ma suka gaisa. Dik da basu magana da Nirash sai ya ji yana son kai mashi wayar su gaisa da daddynsa, wata zuciya ta ce a’a kada ya je, wani kuma ya ce ya je Nirash zai amsa. Daurewa yai tare da nufar bed ɗin Leo. Sallama ya yi mashi tamkar wanda zai shiga wani ɗakin saɓanin yadda ya je wajensu Vash ba sallama. Ai cikin zafa su Vash suka ɗago kai suna kallonsa, suna jiran su ga Leo zai karɓi wayar ne ko kuwa.A gaban bed ɗin ya tsaya tare da cewa. “Here is my dad, ku gaisa”…… Leo yana kwance shiru, ya kifa littafin tasa a fuska kamar yana barci, kuma idanunsa biyu, amma babu alamar zai amsa Noor. Shiru ya tsaya zuciyansa sam babu daɗi na abin da Leo yake yi masu, amma ya zasu yi? Dole sai hakuri. Ko sunan Leo ɗin fa basu sani ba, kuma wai suna ɗaki guda.Jin shiru yasa dad ya ce. “Are you okay pleasure?”. Da sauri ya amsa da. “Yes dad”. Ya faɗa yana juyawa ya bar wajen.”Is there any problem?”. Dad ya tambaya, da sauri ya girgiza kai alamar a’a, sai ya haye bed ɗinsa ya kwanta zuciya babu daɗi. Haka suka cigaba da hira da daddyn nasa har barci ya ɗauke su Zaynash, sun shafe 2 hours suna hira, da alamar shakuwa da kaunar juna matuƙa a tsakaninsu. Sai can suka yi sallama, ya katse kiran tare da kashe wayar bakiɗaya, daga nan ya hau barci shi ma. Ɗakin ta yi tsit alamar dik sun yi barci harta Leo ɗin ma. ————————–🔥NEW YORK. CRYSTAL PALACE.Ayi hakuri da zaman da zan yi wajen bayanin inane CRYSTAL PALACE, zan yi hakan ce dan ba zan sake bayani a kanta ba, kuma zan yi hakance dan na tabbata ba kowa yasan irin ginin da nike nufi ba har sai na yi bayani, bugu da kari CRYSTAL PALACE tana da alaƙa da kusan kowa dake a cikin wannan littafi, dik wata rikici daga cikinta yake fitowa, shiyasa dole zan daure in sha wahalar typing dan fayyace maku tsarinta dallah-dallah!.CRYSTAL PALACE. Watau duniyar glass masu bala’in kyau da kyalli game da ɗaukar hankali, duniya ce guda mai zaman kanta, cikin CRYSTAL zaku rantse da ALLAH kasa ce or gari mai zaman kanta, wajen da ke haskakawa kamar rana, amma mu shiga cikin domin ku ganewa idanunku. Katafaren yankin da na tabbata baku taɓa cin karo da irinsa ba. Wasu irin jiga-jigan hyper glass skyscrapers a wajen, gine-gine masu hawa 30 zuwa 50, dik na glasses masu canza launi bisa yanayi gari, suna ƙyalli kamar lu’u-lu’u, tare da golden edges. Akwai manya-manyan solar gardens, lambunan zamani masu amfani da hasken rana, sannan suke canza launi da dare su bada sky blue light mai ƙara ƙawata wajen da ɗaukar hankali. CRYSTAL PALACE gamayyan gidaje ne masu hawa 30 zuwa 50 da a ƙallah zasu kai 20 a wajen, dikka ƴan haya ne cike a cikin, idan har aka kama maku kuɗin da suke biyan hayan kowani hawa ɗaya a shekara ya isa sayen katafaren gida na alfarma a Abuja Naija, sannan dik kuɗaɗɗen suna tafiya ne wani asusu guda ɗaya, haka na nufin mallakin mutum ɗaya ne. Akwai infinity sky villas, wasu box masu zubin gidaje ne masu shawagi a iska, haɗe da smart levitation technology, ba kamar gidajen zama bane, a’a, su na yawon shaƙatawa ne a sararin samaniya, idan kun gaji da zaman cikin gida kuna da damar fita ki yanki ticket ku shiga wannan karamun box zai yi sama daku kamar ƙaramin jirgi, sai dai a iya sararin samaniyar CRYSTAL yake tsayawa baya zuwa wani wajen.Ga watsu rantsasstsun neon quantum roads, titunan da ke haske bisa tafiyar mutane da motocin zamani. Ga wasu magnetic highways, hanyoyin mota da ba sa buƙatar taya, sai fasahar levitation. A saman waɗan nan tituna akwai wasu jiga-jigan Guards madaka ƙarti dake kai komo suna shawagi dan tabbatar da tsaro, kuɗin da ake biyan waɗan nan Guards ɗin kawai arzikin wani kamshaƙi ne a Naija.Sannan akwai hanyoyi a sama, sky walkways, hanya ce da ta fita daga wannan gini izuwa wannan amma ta sama, kowani hawa akwai hanyoyin da suka sada gine-ginen, ba sai ka sauƙo kasa ka sake hayewa sama idan zaka je wajen mutum ba. Akwai ƙayatattun wuraren hutawa a ciki irinsu ethereal beach, wani nau’in teku da ke canza launi a bisa lokacin dare ko rana, ba kato sosai bane, an yisa ne dan mazauna CRYSTAL ɗin su mori kuɗin hayansu da kyau. Ba iya su aka tsaya ba, akwai cloud nine resort, wurin hutawa mai shawagi a saman gajimare! Amma shi ma a iya sararin samaniyar CRYSTAL ɗin ne. Lunar reflection park, wani kaɗaɗɗen lambun da ke hasken launin wata, saman lambun wasu kyawawan taurari ne aka yi kwalliya da su dake ƙarawa wajen kyau.Akwai Crystal sphere arena, wajen taruka, wasanni, kallon cinima dan kallon film ko wani abin, da wajen nishaɗi da aka yi amfani da fasahar hologram.Irin solar da ake amfani da shi a CRYSTAL yana bada wutar lantarki ba irin solar da aka sani bane, domin kuwa su haɗe yake da views ɗinsu, idan rana ta daki glasses na windows ɗin sai wutar lantarki ta samu, batiransu na chanji wanda yasa ko dare ce wuta bata taɓa ɗauke masu.Babu ƴan aiki a CRYSTAL PALACE, domin kowani gida akwai robot dake aiki bisa umarnin mazauna wannan gida. Akwai SOLARIS CORE, wani katafaren gini ne wanda ya kasance cibiyar kasuwanci, a nan kasuwansu yake, super market kala daban-daban a ciki dan yin shopping ba sai sun fita waje ba. Dan a kara ƙawata CRYSTAL PALACE kawai sai aka yi wasu floating luxury malls a saman, idan kana so zaka iya zuwa can ka yi shopping ɗinka hankali kwance. KAI TURAWA FA SUN CI GABA, YANZU NASAN WASU SUNA NAN SUNA TINANIN ANYA AKWAI DIK ABIN DA NA KIRGAN NAN A GASKE KUWA? TO DIK AKWAISU SARAI, IN BAKU JE IN DA SUKE BA KUN KARANTA A NOVEL ƊINA, SHIYASA NA DAURE NIKE MAKU BAYANINSU DALLAH-DALLAH DAN KU GANE, NAIJA MA MUKE DA KANANAN GINE-GINE IRIN ESTATE BARE SU? AI SUN SHAHARA A GINE-GINE SHIGEN CRYSTAL PALACE TIN TINI.Ga wani katafaren elysium cloud lounge, wajen cin abinci ne a sama mai balain kyau da ɗaukar hankalin wanda aka tsara shi sosai. Yanayin tsarin tsaron wajen, akwai irin drone security ɗin nan, ƙananan jirage dake kula da tsaro dare da rana, da zarar sun ga wani motsin da basu yarda da shi ba zasu hau kara take Guards su ɗauki matakin gano meke gudana ko wace barazana ke zuwa. Ga irin bio scanning entryways, babu wanda zai shiga yankin ba tare da kowa dake cikin gidansa ya gane waye ya shigo CRYSTAL PALACE a yau ba! Dan akwai tv da aka haɗa da bio scanning ɗin a kowani gida dake wajen.Dik da haka akwai quantum shielding system, tsarin wall da aka kewaye wajen mai amfani ne da wutar lantarki dan kare yankin daga barazana ta waje, ko jingina daga waje ka yi da jikin bango sai ka ji shocking, kuma bulletproof ne wall ɗin, ga wani katafaren CRYSTAL PALACE HOSPITAL a takaice mu ce CHP, hospital ne dan kula da lafiyarsu, asibiti ne wanda shi ne na huɗu a duniya wajen karfi da kayan aiki game da manyan jiga-jigan likitoci. Gate guda biyar ne na shigowa CRYSTAL, wanda kuma dikka gate ɗin suna da mahaukatan tsaro na ban mamaki, ba sai na faɗa maku haɗuwar gidajen dake cikin CRYSTAL ba, saboda makurar haɗuwa ne, dik wanda kuka gani cikin CRYSTAL babban kai ne, ya kai yadda ba’a tinani, wane karamin kai da iya kama haya a cikinsa.To a duniya gabaɗaya irin CRYSTAL PALACE guda huɗu ne kawai, kun taɓa jin labarin THE LINE NA SAUDIYA AND THE CIRCLE NA DUBAI? to su ne guda biyun CRYSTAL cikon na uku sai kuma wani a nan cikin US ɗin shi ne na huɗu, sai dai THE LINE AND THE CIRCLE kunga mallakin gwamnatin kasashen ne, kuma bama a fiddasu ba, shi kuma CRYSTAL mallakin wani mutum ne wanda su kansu mazauna wajen basu san ainahin mai wajen ba, dan an ce ya fi shekaru 10 da mutuwa, wasu sun ce yana prison and ɗauresa life in prison, dan haka yanzu wajen tana karkashin kulawar wani ne daban, to koma dai menene mu je zuwa dan abin dayawa. A takaice yadda Crystal yake kenan. Gidajen cikin CRYSTAL ɗin nan dikka an kama hayansu, babu empty, kada ku manta gidaje ne guda 20, kuma dikkansu benaye ne masu hawa 30 zuwa 50, amma dik wasu manya dake jin kansu a ƙasar sun kama haya suna ciki da family ɗinsu, dan yanayin tsaruwar wajen da kuma karfin tsaronsu, dan ko tsuntsuwa bata isa wucewa ta sararin samaniyarsu ba na’ura zata harbota ko ta kaɗata wani waje, zallar basira da technology aka zuba wajen tsara wannan gini, shiyasa ya fita daban……… Wannan ma na takaita maku haɗuwar CRYSTAL PALACE wlh. ———————–Kai tsaye mu wuce Crystal Palace Hospital, watau CPH. A hankali ta fara ƙoƙarin buɗe idanunta da suka yi mata mugun nauyi, tana son motsa jikinta amma ta gagara, da kyar ta yi karfin halin waro idanunta waje. Ya subhanallah, idanun nata sun yi jajir sun kumbura matuƙa, sun zama abin tsoro. Zazzarosu sosai ta yi tana bin in da take da kallo, ganin bata gane ko’ina bane wajen yasa ta ɗan motsa lips ɗinta da suka yi mata nauyin tsiya, tongue ɗinta tamkar an ɗaɗɗauresa, da kyar ta iya cewa. “Mammy, mammy where are you?”. Shiru babu wanda ya amsa mata, hakan yasa ta yunkura zata miƙe, sai ta ƙasa, a nan ta ji alamar jikinta a ɗaure yake, ƙoƙarin sauƙo da kallonta izuwa jikin nata ta yi, a daidai lokacin aka turo kofar room ɗin wanda hakan yasa ta wurga eyes ɗinta can. Wani mutum ne ya shigo hannunsa rike da wasu ledojin drip guda biyu. Sanye yake da tail coat, kafafunsa na cikin wasu haɗaɗun cover shoes masu tsadar gaske, fuskansa a sanye da nose mark, kansa sanye da hat, gabaɗaya kayan jikinsa bakake ne harta socks dake kafafunsa.Yana shigowa ya sauƙe kyawawan dara-daran eyes ɗinsa a kanta, while ita ma shi take kallo, dik da yana sanye da nose mask hakan ba zai hana ka gane cewa haɗaɗɗe bane. Yana da tsawo sosai, ga cikar halittar, dik in da ake neman namiji wannan ya kai.Ganin idanunta biyu yasa intently ya iso gaban bed ɗin, a gefe ya ajiye drip ɗin kafin ya mai da kallonsa a kanta da kyau. Can ƙasa ya ce. “Had luck”. Ya faɗa yana kai hannu zai riko nata hannun. Da sauri ta janye baya, da kyar ta iya sake cewa. “Who are you and where is my mammy?”.A maimakon ya amsa mata sai ya kai hannu ya kama nata, a natse ya zare mata drip da ya kare yana faman jan jininta. Bayan ya cire ne ya zauna saman sofar dake kusa da ita, bai sake yi mata magana ba, da ganin haka ita ma bata sake yi mashi magana ba, ta yi shiru tana tinanin ina mahaifiyarta take?!. Daga karshe ta yunkura, a hankali ta miƙe zaune a tsakiyar haɗaɗɗen bed ɗin da ba zaka taɓa cewa na majinyata bane.Ƴan kafafunta ta yi ƙoƙarin zurowa ƙasa, sai dai ina, gadon yana da tudu bata iya taɓo ƙasa ba, ɗan shagwaɓe fuska ta ɗan yi, kamar zata yi kuka, kai kallonta a kansa ta yi, ya sunkuyar da kai shiru tamkar ba mutum a cikin ɗakin. Turo baki ta yi tare da gyarawa ta matsa bakin bed ɗin sosai. Dirowa ƙasa da karfi ta yi a in da ta tafi gabaɗaya zata faɗi ya miƙe kafansa ɗaya ya tareta, ashe dama yana kallonta, da ta faɗo forehead ɗinta zai bugu da tiles ɗin ne, sai ya tare kan nata ya bugu da kafarsa.Slowly ya ɗago da kallonsa a kan face ɗinta, bai yi magana ba yasa hannu ya kama nata hannun, da hannu ɗaya ya ɗagata tare da miƙewa tsaye ya jefata kan gadon. A kan face ɗinta ya tsayar da idanunsa, still dai babu alamar zai yi magana. Yanayinsa yadda kuka san wani shahararren gangster haka. Komawa ya yi ya zauna tare da ciro wayansa daga aljihu, intently ya fara latsa wayar yana typing message. Ɗan zuba mashi idanu ta yi, sai kuma ta turo baki, take dara-dara violet eyes ɗinta suka cika tab da kwallah, a fili ta ce. “Where are you mammy? I’m so scared here, come and take me away from here”. Cikin kwararriyar turancinta ta yi maganar, voice ɗinta ba dai daɗi da sanyi ba, ga zallar madarar shagwaɓa.Yana jinta sarai, amma ko motsi bai yi ba, yana cigaba da latsa wayarsa. Ganin babu mai kulata ne yasa ta lallaɓa ta koma ta kwanta shiru. Kyakkyawar yarinyar karshen haɗuwa, gashin kanta light ash very silky haka, ga wani irin sheki da yake yi, violet eyes ɗinta dara-dara farare tas da su.———– silent for almost 40 mins ne ya biyo baya kafin wasu nurses guda biyu suka katse masu shirun ta hanyar shigowa. Ɗaya hannunta rike da wata ƴar CPH-note-b, ɗayar kuma hannunta rike da babban leda mai shaƙe da magunguna. A gaban bed ɗin suka tsaya, mai rike da magungunan ne ta miƙawa guy ɗin tana faɗin. “Here’s her drugs, make sure she’s taking it on time”.Hannu yasa ya karɓi magungunan ba tare da ya kalli in da suke ba, ita kuma ɗayar nurse ɗin miƙa mashi note-b ɗin ta yi, saƙon sallama ne, takarda ce mai ɗauke da sunan CRYSTAL PALACE HOSPITAL da sauran bayanan yarinyar, me dalilin kwanciyarta, kwananta nawa, kuɗin da aka cajesu, kai komai dai, a karshe time da date da aka sallameta. Sannan takardan nashi ne, dan idan ba mazauna CRYSTAL ba babu wanda yake da irin takardan, din in zaka kwanta jinya sai ka zo da notebook ɗin, a nan za’a cigaba da yi maka rubuce-rubuce har ranar sallama!.Nan ma karɓa ya yi, ba tare da ya yi magana ba ya miƙe tsaye, gentle ya tako zuwa gaban bed ɗin. Hannu ɗaya yasa ya ɗauki yarinyar sai saman shoulder ɗinsa, bai bi ta kansu ba ya nufi waje. Yana fitowa wasu jiga-jigan guards masu zubin gangsters su uku suka take mashi baya da gudu. Kai tsaye wajen wani dankareren mota ya nufa, tin kafin ya iso wasu guards madaka karti dake kusa da motar suka ɓalle mashi back door. Ciki ya jefa yarinyar kamar yaki, sannan ya shiga gidan bayan shi ma. Da sauri suka mayar da door ɗin suka rufe, da wani irin gudun karti suka nufi sauran motocin dake wajen, da gudun gaske suka ja motocin suka kutsa cikin C-P (CRYSTAL PALACE) Ita dai taga ikon God, sai kawai ta hau binsu da kallo, tam daina magana tin da har yanzu ba’a samu mai iya amsa mata ba.Ɗaya daga cikin shahararrun ginin da ya fi ƙawatuwa a wajen suka nufa, shi hawa 10 ne kawai, sannan shi gabaɗaya glass nasa sky blue ne babu mix. A parking lot na gidan suka paka motocin, da gudu wasu kartin guards dake shawagi a gidan suka nufo motocin. Nasa suka fara ɓuɗewa kafin na kowa. Fitowa ya yi cikin zafin nama, yasa hannu ya ɗauketa sai saman shoulder ɗinsa, hannunsa ɗaya rike da drugs ɗinta. Ita dai shiru kawai ta yi tana kallon ikon God. Kai tsaye elevator ya nufa, daga kan yadda yake tafiya zaku san lallai wannan shahararren gangster ne, tafiyarsa babu wasa ko sanyin jiki. Hawa na biyar ya haye. A wani katafaren parlo mai tsananin kyau ya dakata. Shiru ya ɗan tsaya kamar na 1 minute, sai kuma ya nufi wani door dake fuskantosa. Yana zuwa ya ɗan taɓa handle na door ɗin sai ga shi ya buɗe kansa. Wani katafaren sleeping door ne, katon bed ne kawai a ciki, yana shinfiɗe da wani haɗaɗɗen bedsheet na alfarma white kala, da one side sofa. Sai kofar toilet and balcony wanda dik da glass aka yi su kun sani.A saman bed ɗin ya direta tare da ɗaura drugs ɗinta a gefenta, daga haka ya juya bai sake kallon in da take ba. Parlo ya fito, kai tsaye ya nufi wani madaidaicin door dake fuskantar ɗakin da ya fito.Wani haɗaɗɗen dry kitchen ne a wajen, da alama babu kowa a gidan sai shi kaɗai. Kyakkyawan pot ya ɗauko daga cikin pot set ɗinsa, ruwa ya zuba a ciki tare da buɗe drawers na sama ya ɗauko wani ɗan karamain bottle, wani green leaf ya ɗebo daga ciki, ya zuba cikin ruwan pot ɗin, sannan ya ɗauko wani bottle na honey. Kaɗan ya zuba zuman a ciki, ya kunna gas, a kai ya ɗaura tare da nufo waje.Yana fitowa ita ma ta fito daga room ɗin da ɗan gudunta tana faɗin. “Mammy I don’t want to stay here, please come and take me away from here”. Tana kuka sosai da hawayenta. Kallo ɗaya ya yi mata ya ɗauke kansa, sai ya nufi wani siririn hanya dake kusa da glass wall dining room dake cikin parlon.Da kallo ta bisa, a ranta ta ce ko dai baya magana ne?. A fili kuwa hawaye na cigaba da tsere a kan fuskanta sosai. Tana ganinsa ya yi amfani da remote wajen sauƙo da staircase daga sama, sannan ya haura sama abinsa ya kyaleta tsaye kamar wata doluwa.Zaman dirshan ta yi a ƙasa tare da sanya hannayenta dikka biyu ta fara watsa kyakkyawan ash hair ɗinta tana cigaba da kuka. Lokaci guda kuma ta ɗan kwaɓe fuska tana ɗage hanci sama wai jikinta na tsamin datti, dan yau kwanakinta uku a asibiti bata yi wanka ba, kuma babu wanda ya yi mata, tin da suka kawota ma shi sai jita ya je, tana sume aka kaita, daren jiya ta farfaɗo tana kuka kenan aka yi mata alluran barci, bata tashi ba sai ɗazun. Farfaɗowarta jiya yasa aka kirasa a waya ya zo, tin kuma da ya fita wajenta jiyan sai yanzu ya koma ya ɗaukota da likitocin suka sanar da shi ta samu lafiya zai iya tafiya da ita. Abin da ya sumar da ita kuma shi ne hayakin wutar da su Eagle suka kunna a gidansu. Wannan yarinya ba kowa bace face ƴar Dr Hushaima ALLAH jiƙan rai, da alama kuma wannan mutumi shi ne bahagon murɗaɗɗen mutumin da Dr ta taimaka dik da ban sani ba, hasashe nake yi, naga halinsu na rashin magana iri ɗaya ne da wancan, to wai ma su waye su ne?. To yanzu dai mu ɗan koma baya kaɗan dan mu ji ya aka yi yarinyar Dr ta tsira?.

STAR LADY TAKU CE TA AMANA.🔥

Back to top button