Fentin Zina Page 40 End Hausa Novel
FENTIN ZIN🅰️ *PAGE 40.* Ameen yace suka shiga falon ta kofar da take ta waje banda na Cikin main falon ammy, suna dariya.Saida suka kai tsakiyar falon kamin Ammar yace zauna nan barin kirawo ta ta fito ko?, bai jira amsar shi ba ya haura sama ya nufi dakin da yasan tana ciki ya shiga da sallama.Can Kasan makoshi ta amsa mishi ya karaso ciki yana fadin sannu da kadaici amarya ta mai kyawun ado da kyalkyali.Bata ce komai ba domin har yanzu kamar almara take kallon abun wai itace aka daurawa aure da wannan santalelen saurayin da ko a mafarki bata yi tsammanin samun sa ba, hakika Allah mai iko ne akan dukkan komai shi ke tsara al’amura a yadda yaso.Zanso ki danyi hakuri ki taso muje falo ina tare me da babban abokina bai samu halartan daurin aure ba saboda uzuri.Toh tace ta mike dama da akwai hijab a jikin ta.Yana gaba tana biye dashi a baya har inda ya nuna mata mazauni ta zauna.Ahmad kuwa idanunshi na kan wayar shi inda yike chatting da bakuwar da suka making appointment na kwana tare yana shaida mata tayi hakuri yana hanya ya kusa karasowa, ya tsinkayi maganar ammar yana cewa mutumin gafa amarya ta fito kana aikin danna waya focus please.Dagowar shi daidai itama ta dago a lokaci daya idanunsu suka sarkafe dana juna.Wata wawuyar zabura tayi ta mike tsaye tana mai kafe shi da ido tana jifan shi da kallon tsana da kyama, tabbas ko cikin dubbannin mutane ko a wani irin yanayi ta ganshi bazata taba manta wannan fuskar ba, fuskar data zuguza rayuwar ta, fuskar shafa mata tabo mai muni wanda bazai goguba, fuskar data fi tsana fiyeda kowa da komai na rayuwar duniya.Kamar yadda yake a bangarenta haka shima, saidai bambamcin ta da nashi shine, shi yana mata kallon mamaki ne na meya hada ta da abokin shi, lokaci daya nadama ta shige shi ya cigaba da kallonta bai iya cewa komai ba.AMMAR ta kira sunan shi a kausashe wanda ba shi Ammar din ba harda Ahmad din saida ya tsorata da yanayin fitar sautin sunan, shidai ya shiga uku bazai so ya zama sanadin lalacewar auren da ko kwana baiyi ba, bai taba jin cewar abunda yike aikatawa kuskure bane sai yau, take ya tsinci kanshi cikin jin matsanancin kunya da tarin nadama.Ammar tunda ta kira sunan shi ya juya ya kalleta ya tsorata da yanayinta kuma ya kasa amsa mata.Meya kawo wannan fajirin gidana??Jin sunan data kira Ahmad dukkan su saida suka runtse ido.Menene alakar dake tsakaninka da wannan maci amanan mai yaudaran ‘ya’yan mutane mai bata tarbiyyar su, macuci azzalumi mai raba tsakanin ‘ya’ya da mahaifansu, bakin mugu lallai duk inda ya raba bazaiyi alkhairi ba, ka gaggauta fitar mun dashi daga gidana sannan da rayuwar ka matukar kana son na cigaba da kasancewa matar ka, ta karasa tare da fashewa da kuka sosai har jikin ta na kerma, can ta tsagaita tace Allah ne kadai zaiyi maganin shi, lallai idan ka fitar dashi ka sameni sabanin haka kuma kasance dashi bani ba. Tana gama fadan haka ta haura da gudu ta koma dakin da ta fito ta fada gado ta cigaba da kukan ta.A can Kada kuwa Ammar kasa motsi yayi, abubuwan sun daure mai kai amma da yake shidin yana da basira da baiwar sanin abu sai ya hango abunda yake faruwa.Ahmad ne yayi karfin halin dukan kafadar shi ya dawo hayyacin shi sannan yace cikin sanyin jiki: ni zan tafiyanzu dan Allah ka samu ka lallashe ta komai zatace ko ta maka ka mata uzuri, daga haka yayi kokarin barin falon sai dai bai kaiga cimma hakan ba don ko taku biyu lafiyayyu baiyi ba yaji an jawo rigar shi ta baya da karfin gaske, juyowa yayi abunda ya bashi tsoro sosai ganin yadda fuskar Ammar ta sauya farad daya sakamakon kololuwar bacin rai daya shiga na sabon rainin wayon da Ahmad din ke kokari zuwa mai dashi.Kara pincikar shi yayi ya zaunar dashi kan kujera inda ya zauna tun farkon shigowar su, ya nuna shi da yatsa yana huci yace cikin daga murya. Bayan duk wannan wasan kwaikwayon ina kake tsammanin zaka tafi? Babu inda zaka je sai ka sanar dani abunda yake faruwa sai ka mun bayani game da abunda idanuwa na suka gani da kuma abunda kunnuwa na suka ji, bazan bari kayi koda taku daya ne da nufin barin gidan nan ba har sai ka warware mun wannan kullin. Ya karasa kamar wadda yayi tsere.Kasa hada ido dashi ahmad din yayi amma cikin sigar lallashi da kwantar da murya yace, kayi hakuri dan Allah kada ka tuhume ni akan son sanin ya al’amarin yake, ka tambayi matar ka zata fada maka kuma duk ma abunda tace din ka yarda haka din ne domin na tabbata Ameena bazata maka karya ba.Kallon shi kawai Ammar keyi yama rasa me zaice amma batu na gaskiya ji yake ina ma da zai iya da ya shakeshi sai ya sumar dashi.Kai nafi sani! Na san wanene kai da kuma dukkan abunda zaka iya aikatawa shiyasa nike tambayan ka tun wuri ka fada mun abunda ya kamata in sani.Ganin da gaske dai fa bazai bari ya fita daga gidan ba sai yaso yi masa dabara yace naji! Naji zan fada maka komai amma yanzu kam zuciyata ba a daidai take harbawa ba ina cikin tashin hankali ka bari zuwa gobe nayi alkawarin zan fada maka komai. Ya fada yana zare ido kamar sabon kamun hauka.Murmushin gefen baki yayi yace saboda ka raina wayona ko? Saboda ka maida ni shaka tafi ina mai tabbatar maka tare zamu kwana sai ka fada mun abunda ke faruwa wanda ni kaina ban sani ba.Ameena kuwa kukan ta tasha sosai a hankali kukan ya lafa har tayi shiru gaba daya ta hau ajiyan zuciya bayan ta goge hawayenta.Zuciyarta ce ta hau raya mata bata kyautawa Ammar ba data yi fushi ta baro shi a falo tunda shi baida masaniyar komai gameda rayuwarta ta baya toh akan me zata yi fushi dashi? Take taji bata ji dadin abunda ta aikata mai ba sai ta mike dama bata cire hijab dinta ba ta fice a dakin zuwa falo.Ammar zai sake magana kenan yaji alamun tafiya hakan ya sakashi dakatawa da abunda yayi niyyar fada din sai ya juya yana kallonta dukda hijabin ya dan rufe fuskarta hakan bai hanashi ganin yadda idanunta suka kumbura ba alamun tasha kuka sosai.Karasowa ciki tayi ba tare da ta kalli gefen da suke ba saboda bata son ganin wannan Ahmad din don ji take kamar ta shake shi ya mutu kowa ma ya huta.Zama tayi a kujerar nesa dasu ta soma fadin, kayi hakuri mijina hakika nayi kuskuren biyewa zuciya na kokarin hukunta ka a bisa laifin da baka aikata ba, ina mai baka hakuri wannan bai wuce ajizanci bane na dan Adam sannan nasan abunda ya faru a gaban idon ka zasu isa dasa maka zargin wani abu.Ta dakata kadan ta numfasa kana ta ci gaba, babu bukatar wani dogon bayani wannan da kake gani.Ta nuna Ahmad da yatsa amma bata bari ta kalle shi domin tuna mata yake da sakarcin data aikata.Shine mahaifin shureim…..Ai kafin ta karasa ma jiri ya debeshi Allah ya taimaka akwai kujera a kusa da shi sai ya fadi a kanta, kirjinshi na bugu, sam baya ma duniyar na wucin gadi.Motsa baki yake yi yana son furta wata kalma, sai dakyar ya saita kanshi ya pointing direction din Ahmad ya soma magana cikin karyewar zuciya da in ina yace.Amma ka cuce ni Ahmad! Lallai nasha yi maka nasiha da kaji tsoron Allah ka daina wannan mummunar dabi’ar da kake yi ina kuma kyamatar halinka nasha fada maka hakan amma ban taba tsanar wannan halin naka ba sai yau, duk duniya babu wanda ya taba yimun cuta da cin mutumci kamar yadda ka mun, a halin da zuciyata take ciki idan naci gaba da ganinka zuciyata zata buga dan Allah ka nisance ni kada ka sake nuna fuskarka a gareni, abunda kayi kuma sakamakon naga Allah don’t haka ka tashi ka barmun gida ka fice mun da gani.Babu inda zaije,,,, ammy ta fada lokacinda take shigowa falon bayan ta gama sauraren dukkan abunda suke cewa.A razane dukkan suka waiga suna kallonta harta karaso ta zauna a daya daga cikin kujerun tana aunawa Ameena wani irin kallo kana ta maida idonta kan Ahmad.Kai Ammar tsabar tsaurin ido abokin naka kake ciwa zarafi akan mace? Har kake fadin ya bar maka gida? Toh barima kaji infada maka idan bacci ma kakeyi toh ka farka domin wannan amincin naku daya samo asali tun daga yaranta bazan iya kallo yana rushewa a gaba na ba kuma inyi shiru in zuba ido.Lumshe ido Ammar din yayi kana ya ware su a hankali yanajin zuciyar shi kamar zata buga, yana jin kanshi na sara masa, ya dafe kan cikin karfin hali yace, amma ammy kinsan meya aikata babu adalci a ciki, kin sani cewa bai kyauta mun ba sam kumaya zalunce ni. Ya diga aya yana yi kamar zai yi kuka.Eh lallai dole ka fadi haka! Waima meyasa kake ta kokarin dorawa abokinka laifin ne shi kadai, meyasa? Ta tambaya tana tsare shi da ido.Ameena ta dan zamo daga saman kujera tace ammy ina yini.Hannu ta daga mata tana fadin ina zuwa kanki ki dan rike gaisuwar ki kadan zan juyo in amsa.Kasa komawa saman kujerar tayi ta zauna a kasa tare da sunkuyar da kanta yayinda taji jikinta yayi sanyi soaai game da lamarin ammy, ya matar da takewa kallon mutuniyar kirki mai mutumci da mutumta mutane amma bisa wani dalili nata take maltreating dinta harma take hadawa da dan da take ikirarin tafi so fiye da komai, sai dai ta mata uzuri dole idan tayi la’akari da irin soyayyar da uwa kewa danta.Ganin babu wanda yace komai sai ta kuma juyawa kan Ammar da yayi mutuwar zaune kanshi a kasa yana jiran jin hukuncin ammyn sa da yake ganin kamar an sauya masa ita ne.Nace meyasa kake ganin duk wannan laifukan da kusa kuran Ahmad ne kadai yayi su? Ince dai ba fyade ya mata ba da hadin kanta komai ya faru? Meyasa bazaka ga nata laifin na biyewa dadin bakin na miji wurin bashi hadin kai a aikata ba daidai ba? Inda ace ta nuna bata so ta kuma dage baza’ayi lalatar da ita ba na tabbata abunda ya faru din da bai faru ba, alokacin giyar soyayya ta debeta ta manta da duk wani mutumci da kima ta ‘ya mace da Allah ya mata tayi abunda ranta keso daga baya kuma tana dana sani, don haka ina so ka sani kuma ina gargadin ka da babbar murya, wannan ya zama darasi a garemu duka dama ‘yan baya masu zuwa, amma dai abunda ya faru kada ya taba zumuncin ku ina so ku maida komai tamkar bai faru ba ina fatan kun fahimta.Dukkansu suka hau gyada kai kamar kadangaru.Numfashi ta dan sauke a ranta tana hamdala da samun damar data samu a yanzu kuma a kansu, hakan ya faranta mata sosai, sai ta juya ta fuskanci Ameena tace yauwa na dawo kanki.Ban taba kin ki ba duk tsayin wannan lokutan hasalima ina yin duk wadannan abubuwan ne domin ki kara fahimtar irin girman kuskuren da kika aikata a rayuwar ki saboda na lura har yanzu akwai wauta a tare dake, don haka ina mai roko a gare ki ki girma kisan me kike yi, girma a yanzu ya soma kamaki tunda har kin ajiye da mai tasanma shekaru bakwai dole kisan abunda kike yi, na yarda da tarbiyyarki na kuma san bisa tsautayi ne abunda ya faru din ya faru amma harda sakacin ki da kuma biyewa son rai Allah ya Kara kiyayemu da zuri’ahr mu daga fadawa halaka.Ameen ammy nagode da fahimtata da kikayi nagode da matsayin da kika bani a zuciyar ki da ahalinki nayi alkawarin insha Allahu zan kara kusanta kaina ga ubangijina da neman gafara da kaskantar da kai a gare shi zan muku biyayya iya iyawata ni na daukeki ne tamkar mahaifiya wacce ta tsuguna ta haife ni dan Allah ki dauke ni tamkar ‘yar da kika haifa wallahi zan miki biyayya daidai gwargwado.Dafa kafadarta ammy tayi tana dan bubbugawa alamar gamsuwa da kalaman Ameena.Juyawa tayi kan Ahmad da duk yaji ya muzanta kunyar duniya duk ta dabaibaye shi tace kaji tsoron Allah ka sani yadda kake lalata diyoyin wasu ba wayewa bace kuma Allah na sane da hakan, a tsammaninka zaka nemi nutsatstsiyar yarinya ka aura ta haifa maka ‘ya’ya kuyi rayuwar farin ciki alhalin ka hanama wasu iyayen da ‘ya’yansu farin ciki? A’a! Allah baya zalunci kuma baya so ayi, ina jiye maka kamun Allah shiyasa nike maka fatan shiriya kafin lokaci ya kure maka, yanzu ina amfanin ka haifi ‘ya’ya ba tare da aure ba, ‘ya’yan su kasance cikin kunci kana ganin zasu so su nuna ka a matsayin mahaifin su ne? Kana ganin zasu yi alfahari da kai? Ko daya dukkan ‘ya’ya suna so ace uba na gari ne ya haife su kuma ta hanyar data dace, Allah ya ganar damu ya kubuto mu daga halaka.Cikin sanyin jiki ga hawayen da suka soma sintiri a kumatunshi tun lokacin da ammy ta soma magana ya daga hannayen shi biyu sama yace Allah na tuba ka yafe mun, sannan ya kalli ammy yace nagode kwarai ammy hakika ke uwa ta garice da ko wani da zaiyi fatan samu insha Allah daga rana irin ta yau bazan sake aikata wani zunubi alhalin ina sane ba.Alhamdulillah Allah ya yafe mana gaba daya, nagode da Allah ya nuna mun wannan ranar da abokina ya shiryu. Cewar Ammar.Ahmad ne ya mike yaje gaban Ameena yasa gwiwowinsa a kasa yace nasan na cutar dake sosai ina fatan zaki yafe mun.Girgiza kai tayi itama cikin kuka tace Allah ma muna masa laifi kuma ya yafe mana idan muka nemi yafiyarsa don haka ni wacece da bazan yafe maka ba, Allah ya yafe mana gaba daya.Nagode Ameena Allah ya saka da alkhairi.Ammy ce ta katse su bayan ta mike tsaye, toh ni dai zanje in kwanta sai da safe.Toh said da safe ammy suka amsa bakunan su a hade, shima Ahmad said da safe ya musu ya wuce.Bayan fitarsa ne Ammar ya dawo kusa da matar shi yace Allah ya miki albarka my wife you are queen, ina son ki sosai fa, kinga ma tashi mu shige don so nike nanda wata tara mu samawa shureim kanin da zasu yi wasa don rage masa zaman kadaici.Rufe fuskarta tayi da tafukan hannayenta…BAYAN SHEKARU UKU.Zuwa lokacin abubuwa da yawa sun faru ciki harda rasuwar Abdul tsohon mijin Ameena bayan dogon jinya da yayi, al’amarin daya tashi hankulan ahalin shi.Maryam kuwa cuta take fama da ita sosai na cancer na mahaifa da kuma cuta mai karya garkuwar jiki wato (H.I.V) a halin yanzu tana kwance ne rai a hannun Allah sai dai fatan Allah ya bata lafiya Ameena taso zuwa dubata amma fir Ammar ya hana saidai tayi musu aike, kuma sunji dadi sosai don kudade sosai masu kauri ta aika musu.Rayuwa suke mai cike da jin dadi da walwala, Ameena fa hankali ya kwanta sosai sai wani kiba data yi da haske da cikinta na haihuwa yau ko gobe, sun gama siyayyan kayan baby murna kuwa a gun ammar baki baya rufuwa, lokacin data fara ciwon nakuda sosai hankalin Ammar ya tashi yayi kiran ammy.Cikin gaggawa ammy ta dawo gida dama ta tafi gun aiki, note(basu fi sati kwana uku da dawowa ba don tare da ita ya koma abuja bisa umurnin ammy).Da nurses guda biyu ta dawo suka karbi haihuwar Ameena inda ta haifi ‘yan biyu na miji da mace, tun a gurin ammy ta fuskanci alkibla tayi Sujudush-shukur kana ta kira Ammar ta sanar mishi bayan sun gama gyara mai jego, ai ko ba’a jima ba suka shigo gidan tare da Ahmad da a yanzu ya zama wani ustazu harda gemu ya tara kana ganin shi kaga kamilallen mutum.Anyi suna yara sunci sunan namijin yaci sunan baban Ammar Abdulkadeer, macen kuma sunan inna Rukayya, ana ce musu Rafeeq da Rafee’ah.Taro yayi taro anci ansha anyi bidiri fateema ma tazo da karamin cikinta tana laulayi dakyar ma Anas ya bari tazo da yace ta bari har ta samu sauki kamin tazo sai ta saka masa kuka don haka sai ya barta tazo din.Haka rayuwa taci gaba da tafiya wa wadannan masoya guda biyu cikin soyayya da begen juna, su inna da baba malam sun samu natsuwa da kwanciyar hankali sosai a yanzu kam, Ammar ya sauya musu gida ya kuma budewa baba malam katafaren shago makil da kaya ya fara sana’a. Ameena bata taba tsammanin a rayuwarta zata samu irin wannan farin cikin ba amma sai gashi ta samu sai dai tace Alhamdulillah. *ALHAMDULILLAH* ! _Anan na kawo karshen wannan labari nawa ina matukar godiya ga masoya mabiya wannan littafin bisa jajircewar su da kaunar da suka nuna a gare ni da kuma addu’o’inku da fatan Alkhairi, ina godiya sosai kuma nima ina kaunar ku fiye da misali._ Zaku iya tuntubar HAUSA novels BOOKS Ta wannan number 07060897227 *EESHERT ADAMU* *MATAR MAJEEDADI* ✍️:



