Hausa novels

Ruwan Zuma Page 54 End Hausa Novel

(54) End  Washe gari flight d’in safe suka hau suka koma Kano, a gidan Alhaji Sammani suka fara sauk’a aka ajiye Meenat da Ammi sannan Baba da Haydar suka wuce gidan Laila don ganawa da Abul, Alhaji Abdul shi ma bai bi su ba domin yace baya son k’ara had’uwa da wani mai fushi dashi kamar Madu. Laila da dama Haydar ya fad’a mata yana zuwa da Baba tuni ta shirya gidan ko’ina ya d’auki k’amshi kamar kullum. Mas’ud J kuwa an mishi wanka yayi shiga ta alfarma amma ya koma bacci saboda baya tashi da wuri sai tara ko goma.  Suna isa maigadi ya bud’e musu gate suka shiga, Baba tsayawa yayi a waje Haydar ya fara shiga sannan ya mishi iso suka shiga tare. A falon Haydar suka zauna Laila ta kawowa Baba kunun madara irin wanda Shuwa Arab suke yi kana ta koma k’asa ta zauna suka fara gaisawa. “Amminku tana yawan mini wannan kunun, na yi zaton ita ta fi kowa iyawa ashe Maman Mas’ud ma ba baya ba.” Fad’in Baba cikin yabawa surkarsa.  Laila murmushi ta yi cikin jin dad’i ta ce, “Nagode Baba.” “Ina yaron naku yake? Na ji an ce ya dawo, kira mini shi mana.”  Laila tsoro ne ya kamata tana fatan ba wani abun Abul yayi a bayan idonta ba, bacci ta samu yake yi ta tayar dashi tana tambayarshi me yayi. “Mama ban gane me nayi ba, tun da na dawo nake gidan nan in banda gidan Sabrin babu in da na je. Waya fad’a miki nayi wani abu?” Ya tambayeta cike da damuwa da kuma magagin bacci. “Baban Haydar ne ya zo daga Abuja wai yana son magana da kai. Don Allah in wani abun kayi ka fad’a mini in shirya yanda zan basu hak’uri.” Ta k’arisa maganan tana kallonshi kamar zata yi hawaye. “Wallahi babu abun da nayi. Idan kuma akwai zaki ji sai ki mini duk hukuncin da ya dace dani.”  Wannan magana yasa Laila ta ji sanyi a ranta ta d’aga hannu ta shafa fuskarsa cikin so da k’auna ta ce, “I believe you Abul. Mu je.”   Suna shiga falon shima Abul ya samu guri a k’asa ya zauna kana ya fara gaishe da Baba sai Haydar cikin ladabi, yana mamakin kamannin mutane biyun. Baba ne ya fara magana yana murmushi ga Abul ya ce, “Jikana da fatan ka san waye ni ko?” Gyad’a kai Abul yayi kana ya ce, “Baban mijin Mama.” Amsar tashi ta bawa Baba dariya ya dara kad’an sannan ya ce, “Jiya mun je gidan Senator Gambo Umar mun kar6o maka kayanka da ke can, amma jin yanda shi uban yaron yake bamu hak’uri yasa na gane akwai wani abu da aka maka wanda ya munana. Duk da ban san menene ba raina ya 6aci kuma ina da niyyar tsaya maka har sai na kwato maka hak’k’inka. Kar kasa a ranka kai ba jikana bane na jini, da kai da Mas’ud J duk d’aya kuke a gurina kuma ba zan bari wani ya zalunceku ya zauna lafiya ba.” Tirk’ashi!! Laila zufa ne ya fara taruwa a goshinta duk da sanyin a.c da yake falon, Abul kuma baki ya sake yana kallon yanda Baba ya murtuk’e fuska ranshi babu dad’i. Ashe akwai mutanen da zasu nuna mishi k’auna irin wannan bayan Mamanshi da Mas’ud? Duk irin rashin mutuncin da ya yiwa Haydar ashe tafiya yayi har Abuja ya d’auki babanshi suka je suka kar6o mishi laptop d’inshi? Wani abu yayi musu da ya cancanci wannan alkhairin da jajircewan?  Laila kuma tsoro ta ji a ranta don bata son kowa ya ji k’azamar labarin da Abul ya fad’a mata a kanshi, tana son wannan ya zama sirri tsakaninta dashi ba sai duniya sun san ainihin abun da ya faru dashi ba, wanda har tsufanshi wasu baza su daina aibantashi ba. Da kuma ta san cewa Haydar ya tafi Abuja ne don Laptop d’in Abul da ta hanashi saboda sai yanzu ta ji ta gwammace Abul yayi sana’ar ko da kuwa ta sayar da Yalo ne a kan ya koma harkan computer. Dubanshi ta yi wanda hakan yasa shima ya kalleta ya kuma karanci fuskarta ya juya ga Baba ya ce, “Alhaji na gode sosai da wannan d’awainiyar taku a gareni, amma in don ta nine wallahi komai ya wuce a gurina saboda Allah ne ya koya mini darasi a kan halin da na saka kaina a ciki, ai bariki ba kamar gida bane kuma duk wanda ya za6i bariki a sannu duniya zata koya mishi hankali. Lahanin da ya mini kuma karnuka ya sakar mini har suka karya mini k’afa suka ji mini ciwuka bayan mun samu sa6anin ra’ayi ni dashi. Nagode sosai da wannan soyayya Allah ya bar girma ya k’ara tsawon rai.”  Laila tari ta fara babu kyakkyautawa dalilin shak’ewa da tayi ta yawunta da ta ga yanda Abul yake magana cikin nitsuwa da kuma bawa mutane girma kamar bashi ba, ai zata iya rantsewa ko a daa da yake cikin hankalinsa baya kallon mutane da girma kamar yanzu. Lallai gaskiya ne da ake cewa ‘duniya tafi koyawa mutum hankali sama da wanda aka ajiye a aji ake gwada masa’.  Ganin hankali ya dawa kanta ne yasa ta tashi tana cewa zata je ta sha ruwa sannan zata duba Mas’ud J. Tana tafiya Haydar ya kawo jakar Abul ya mik’a mishi shi kuma ya taso ya kar6a yana k’ara musu godiya sannan ya koma ya zauna.  Baba ne yake janshi da hira wanda yawanci akan karatunshi da ake son yaci gaba da yi ne ganin mate d’insa sun wucesa da shekara d’aya. Suna zaune Laila tayi sallama ta shigo da Mas’ud J wanda ya sha kunu ya k’oshi yana zare idanu, Yayansa Abul ya fara hangowa a falon ya fara k’ok’arin sauk’a daga jikin Laila zai tafi gurinsa, ganin haka yasa Laila ta ce, “Gurin Baba na kawoka kana neman zuwa gurin Abul, kalli, ga can Daddy da Baba suna kiranka.”  Bai yarda ya kalli in da take gwada mishi ba sai da ya ga Abul ya rik’eshi sannan ya d’aga ido ya hango Babansa da kuma kakansa da bai cika gani ba. Barin jikin Abul yayi ya rarrafa gurin Babanshi yana gwalantoyi wanda hakan ya bawa ‘yan falon dariya ciki har da Abul da yake jin sanyi da kuma dad’i a ransa wanda ya rasa gane menene dalilin. Baba ya k’ara minti goma a gidan yana wasa da jikansa sannan ya tashi zai tafi yana cewa, “Muna zuba idon ganinka Abul. Idan ka tashi zuwa ka taho mana da wannan mayunwacin.” Ya k’arisa maganan yana nuna Mas’ud J da ya dawo hannun Abul d’in. “Insha Allah zamu zo Alhaji. Mun gode.”  Direba ne ya mayar da Baba gida shi kuma Haydar ya shiga motarshi ya tafi office bayan ya k’ara minti biyar a gidan. “Wow.” Fad’in Abul yana zama a kan kujera shi da Mas’ud J. “Wow kam.” Laila ta amsa itama tana zama a gefenshi har da share imaginary gumi a goshinta. “Haka suke Mama? Haka suke treating d’inki?” “Sabrin bata baka labari bane? Yanda ka san jikarsu haka suka d’auketa dama kasan ita bata samu kulawar Umman babanku ba sai kuwa Ammi ta zame mata Kakar da ta rasa.” “Ta fad’a mini amma sai na d’auka tana fad’in hakan ne don wani manufarta ta daban, yanzu kam nima na gani and I’m happy Mas’ud J have a family like this.” “Kaima family d’inki ne saboda Ammi ‘yar uwarmu ce ta jini.” “Haka ne I’m happy Mama. And I’m happy for you too.” Laila gyara zamanta ta yi ta dubeshi with serious face ta ce, “Yanzu da suka dawo maka da Laptop d’in me kake shirin yi?”  Abul saukar da Mas’ud J yayi a k’asa sannan ya jawo jakar ya ciro komai da yake ciki, suturunsa ne da wasu k’ananan abubuwansa wanda ciki har kayan mayen da ya saya bai gama sha ba da kud’ad’en da ya sata a shagon Mas’ud.  Laila saurin d’aukan kayan mayen ta yi kana ta shiga kitchen ta kwararar a sink sannan ta saka ruwa ya wuce dashi. Tana dawowa ta samu Abul ya jona laptop d’in a charge ya kunnata tana booting. “Baka ce mini komai ba Abul.” “Kiyi hak’uri ina son nuna miki abun da zan yin ne.”  Murmusawa Laila ta yi kana ta gyara zamanta tana kallon duk abun da yake yi har computer ta bud’e aka nuna hoton Abul da Sabrin a matsayin screen saver. Arrow ya kai kan wani folder ya ce, “Duk wani information, videos, pictures da kuma links da nake samu daga dark web a wannan folder nake ajiyewa kuma nayi deleting d’inshi.” Ya danna ‘delete’ kana ya shiga cikin trash ya k’ara gogewa.  A haka ya dinga shiga da fice yana nuna mata duk abu mara kyau da yake ciki yana gogewa sannan ya shiga ainihin site d’insu na members d’in k’ungiyar ya fitar da kanshi bayan ya canja sahu ta in da baza su sake turo mishi invite ba har abada. “Na goge komai Mama, na bar wannan rayuwar har abada saboda ina son na zama kyakkyawan misali ga Mas’ud J ya tashi yana alfahari da kasancewata yayansa.” “I’m so proud of you habibi. Allah ya maka albarka Abul ya kuma yafe maka kurakuranka.” “Ameen Mamana.” Bayan Haydar ya dawo gida da dare yaci abinci ya huta sannan Laila ta sanar dashi duk abun da ya faru da Abul, da kuma shawarar data yanke a kan bata son kowa ya ji wannan labarin sai shi da Mas’ud, hatta Sabrin bata son ta sani. Haydar ya so ya tayar da k’ayar baya da yaji zaluncin da Faruk ya yiwa Abul amma Laila ta tausasheshi tana cewa, “Ka d’auki hakan a cikin k’addararsa da kuma kamashi da Allah yayi akan laifukansa masu tarin yawa. Sannan kayi duba da Rahamar da Allah ya mishi ya shiryashi, amma shi wanda za’a kai k’arar ina yake? Wa yasan in da ya shiga? Mu godewa Allah da yasa abun bai yi tsanani haka ba sannan mu manta da komai tamkar bai faru ba. A k’arshe kuma ina gode maka bisa jajircewarka a gareni da iyalina sannan ina son maka albishir da cewa ina d’auke da juna biyu na wata d’aya da sati biyu.” Fad’in irin murnar da Haydar yayi 6ata lokaci ne don har kyauta ya yiwa Laila ta dalleliyar mota da kuma albishir da cewa Baba ya basu babban fili shi da Mas’ud a Tudun Yola zasu gina part uku su dawo ciki har da Ummii da ta mak’ale a Maiduguri. A daren ranar Baby k’anin Mas’ud J ya ji yayyafi har sai da ya gaji.   Kwana d’aya da haka Haydar, Mas’ud da Ammi suka dawo da Meenat gida sannan mazan suka nemawa Alhaji Abdul aurenta gurin Babanta. Baban Meenat ya so ya hana da ya ji cewa Alhaji Abdul bai ta6a aure ba, to a ina yake kawar da k’ishinsa na d’ayan jinsin? Haydar bai 6oye masa halin da Alhaji Abdul d’in yayi na neman mata ba a kwanakin baya ba amma bai sanar dashi tarihinsu da kuma cakwakiyar da suka fuskanta ba wanda hakan yasa ya gwammace kar a yi tone-tone. “Duk halin shi na daa wallahi ya daina saboda ni shaida ne a kan hakan, ina bibiyar rayuwarsa ba tare da ya sani ba saboda bana son ya koma rayuwarsa ta baya. Sannan Meenat kamar k’anwa take a gurina ba zan ta6a cutar da ita ba haka Ammi ma tana goyan bayan wannan had’in, idan har kuma tasan Alhaji Abdul bai canja halinsa ba ba zata amince ba. Don Allah ka bawa Yayana auren ‘Yarka Insha Allahu ba da kayi dana sani ba.” “Shikenan ya fara zuwa in ganshi tukun, sannan idan yarinya ta nuna bata so ni bazan mata dole ba. Allah ya shige mana gaba ya za6a mana mafi alkhairi.” “Amin.” Mas’ud ya amsa yana fatan wannan aure ya tabbata don shima ya gaji da kallon Alhaji Abdul babu mata.  Da yammacin ranar Alhaji Abdul ya zo shi da Haydar k’ofar gidansu Meenat amma shi Haydar d’in zama yayi a mota ya bar Baban Meenat yana yiwa Yayansa bincike shi kuma yana amsawa cikin nuna girma da mutunci, duk da cewa zasu iya sa’anni da juna. Sai da Baban Meenat ya gamsu sannan ya shiga ciki ya turo Meenat wacce ta fito cike da kunya ta kasa had’a idanu dashi.  Alhaji Abdul bayan gaisuwarta da ya amsa sai ya rasa abun fad’a saboda wannan ba matar banza bace da za’a nuna mata jikinta ake so ba, wannan matar mutunci ce da ake son aurenta don ta zama Uwa ga ‘yayansa. “Na san kinsan dalilin zuwana ina fatan zan samu masauk’i a zuciyarki kamar yanda kema kika samu a tawa zuciyar?”  Shiru Meenat ta yi amma murmushi ne a fuskarta wanda hakan yasa Alhaji Abdul yaji sanyi a ranshi don da alama tafiyar zata yi kyau. Bai k’ara minti biyar a gurin ba ya dawo cikin mota yana saving d’in numbernta a wayarsa.  Haydar ne ya kunna mota suka fara tafiya yana tambayarsa yanda suka yi. Alhaji Abdul ya sanar dashi komai Haydar ya kwashe da dariya ya ce, “Da gaske cewa kayi da fatan zaka samu masauk’i a zuciyarta kamar yanda itama ta samu a naka? Zamanin ya canja brother, idan ana magana ana had’awa da turanci ya fi jan hankali. Wai masauk’i a zuciyarta?” Haydar ya k’ara kwashewa da dariya yana nuna Alhaji Abdul da yatsa, a maimakon Alhaji Abdul ya 6ata rai sai farin ciki ne ya lullu6eshi wai gashi shi da k’aninsa Haydar suna wasa da dariya.  Cikin wata d’aya aka d’aura auren Alhaji Abdul da Meenat in da Amarya ta tare a gidanshi da yake zama bayan ya canja furnitures da fentin gidan saboda yace baya son ya k’ara ganin abunda zai tuna mishi rayuwarsa ta baya. A ranar da Amarya ta tare sai da ya kusan kaita asibiti saboda shigan saurin da yayi mata ya d’auka irin matan da ya saba huld’a dasu ne kuma abunka da an dad’e ba’a had’u ba. Farin cikin samun budurcinta da yayi yasa sai da yayi hawaye yana cewa, “Ban yi tsammanin zan sameki a matsayin budurwa ba, ba wai don ban yarda da tarbiyyar da iyayenki suka baki ba, a’a sai don ina ganin girman laifukana zasu hana Allah ya bani salihar mace kamar ki.”  Meenat da tasan kad’an daga cikin labarin mijin nata ta nemi kar ya sake tayar mata da zancen rayuwarsa ta baya. “Me kike so in baki don in nuna miki farin cikina Meenat?” “Ka soni, kar ka cuceni.” “Wallahi ina sonki kuma ba zan ta6a cutar da ke ba, ke amanar Allah ne a gurina.”  Abul ya koma school inda ya nisanta kanshi da duk wani aboki 6ata gari, sannan tsakaninshi da Haydar mutunci ne da girmamawa yana kiransa da suna Baban Mas’ud. Banney ya zo Kano ya sauk’a a gidansu, shi ya raka Abul yayi registration sannan Abul ya zaga dashi ciki da wajen Kano wani lokacin har Mas’ud J suke d’auka su je yawo.  Laila kuma cikinta ya fara girma har ta yaye Mas’ud J an kaishi gurin Ammi a Abuja yana hutu, da zai dawo ne aka sha gwagwarmaya tsakanin Haydar da Ammi kan cewa shi yayi mata alk’awarin bata d’ansa, amma shi kuma ya ce ya fad’i hakan ne cikin wasa. K’arshe dai Baba ne ya raba wannan arangamar akan cewa Mas’ud J zai dinga zuwa hutu gurin Ammi a kai a kai. Sabrin ma ta samu ciki wanda ake tsammanin zata riga mamanta haihuwa da wata biyu, sai dai hakan sun d’aukeshi a matsayin abun murna ba abun kunya ko 6oyewa ba saboda haihuwa ta Allah ne sannan ‘yaya Rahama ne, wani nema yake yi amma ya rasa, sannan a cikin ‘yayan mutum bai san waye zai ji k’anshi idan ya tsufa ba. BAYAN SHEKARA HUD’U aka yi bikin gama makarantar Abul da Sabrin, Abul ya zama rik’ekken computer scientist da kowanne ma’aikata ke fatan aiki dashi amma bai za6i kowanne ba sai kamfanin Lu’a Ventures k’ark’ashin mijin mamansa wato Haydar. Laila ta sake haihuwa hud’u bayan Mas’ud J yanzu ‘yayanta 5 tare da Haydar, mata uku Maza biyu. Ganin tana wahala sosai yasa Haydar ya ce ya yafe mata haihuwar yara biyar sun isheshi Allah ya musu albarka, daga nan ne Laila ta daina haihuwa ta cigaba da kula da ‘yayanta wanda tsakaninsu baya wuce shekara d’aya. A wannan lokacin ne kuma suka gama ginin gidansu suka k’aura ciki tare da Ummii wacce ta yarda da kyar da rarrashi.  Mutuncin da ke tsakanin Alhaji Abdul, Haydar da Mas’ud kuwa k’ara gaba ta yi suka cigaba da rayuwa cikin mutunta juna da kuma yafiya ga ‘yan uwansu. Madu ma ba’a barshi a baya ba domin ya ajiye zuciya da mugunta a gefe ya rungumi k’annensa ana zumunci babu sukar juna. Ummii ma yanzu ta sake da Laila tana hira da ita ta cire tunanin ‘yarta zata iya fad’awa rayuwar da take tsoritar mata. Baffa Nazifi yana ziyartar ‘yayan d’an uwan nashi lokaci-lokaci don har zuwa gidan Sabrin yake yi ya duba lafiyarta watarana har kud’i yake bata daidai k’arfin aljihunshi ta k’ar6a tana godiya cikin farin ciki. Abul da Umma har yanzu suna manne domin ita bata canja ba sai zaman hak’uri da kowa yake yi da ita, kuma har gobe Abul ne kad’ai jikanta bata son harkar Sabrin ko kad’an. Sannan tsakanin Abul da Alhaji Abdul har yau an kasa had’asu a inuwa d’aya, don Abul ya ce zai iya yafewa kowa amma banda Alhaji Abdul, haka tsakanin Madu da Alhaji Abdul d’in sai dai a yi gaisuwa a wuce amma Madu na jin haushinsa har yanzu bai daina ba, dalilin da yasa yake yarda su gaisa kuwa saboda taimakonshi da yayi ne lokacin da ake k’ok’arin kulleshi a prison. Hajiya Maryam ta cire implant tana jiran ta samu ciki kamar yanda take buri yayin da Hajiya Shatu kuma ta auri wannan abokin mijin Hajiya Maryam d’in da ta ce tumbinsa ya shanye sunnar auren.  Wata ranar asabar Laila ce zaune a cikin d’akinta tana tsefewa yarinyarta ‘yar shekara hud’u mai suna Aslamiyya gashinta (daga Mas’ud J sai ita kuma takwarar Ammi ce), Mas’ud J mai shekara biyar da watanni ya biyo k’anwarsa ta biyu Khadijah mai shekara uku da gudu zai daketa ta 6uya a bayan mamanta tana haki kamar ranta zai fita. “Me ta maka ka biyota haka? Don Allah yaushe zaka gane ka girma ne ka daina fad’a da k’annenka Mas’ud?” “Ina drawing ta buge mini hannuna na 6ata kuma I can’t erase it because da paint nake yi.”  Laila juyawa ta yi tana kallon Khadija da tayi tsuru-tsuru da ido tana neman yin kuka, “Ke kika yi tsokana amma tun kafin a miki fad’a kike kuka? Baza ku saka mini ciwon kai da sassafen nan ba. Abul, Abul.” Laila ta kwala kiranshi ya shigo hannunsa d’auke da yara biyu da za’a iya cewa shekarunsu d’aya amma namijin me shakera biyu Muhammad (takwaran Alhaji Sammani) yafi girma kad’an sai k’anwarsa kuma autarsu Malak wacce take da shekara d’aya tal a duniya. “Mama ya dai?” Abul ya fad’a yana sauk’e Muhammad daga hannunsa amma Malak ta mak’ale mishi alamar baza ta sauk’a ba. “Ka je kayi shari’a tsakanin Mas’ud J da Khadija, yarinyar nan ta raineshi kullum idan yana drawing sai ta 6ata mishi.”  Abul kallon Khadija yayi yarinyar kyakkyawa chocolate color kamar mamansu ya fara magana ta yaren Shuwa yana cewa, “Meyasa kike 6ata mishi abun shi?”  D’an muskutawa ta yi kad’an tana wasa da yatsun hannunta ta ce, “Ina son koya but he wouldn’t let me.” “Nikam ku fita falo can ka yi shari’ar zan yi waya da Sabrin na ji d’azu tace bata jin dad’in jikinta watakila haihuwar ce.” “Babana ya kusa samun k’ani kenan? (D’anta d’aya mai suna Aliyu suna kiranshi Saif sa’an Aslamiyya ne, kuma takwaran Babansu Marigayi Aliyu.) “Ya kusa kam, d’an kaniya ina yake tun d’azu ban ji d’uriyarsa ba.” Fad’in Laila tana waige-waige don yaran har sun mata yawa. “Yana d’akin Banney yana koyan Likitanci kinsan yace irin Uncle Banney zai zama.” “To Allah yasa hakan alkhairi ne.”  Da haka Abul ya ja Mas’ud J da Khadija zuwa falo don yin shari’ar da Laila ta sakashi. Laila kuma sai da ta k’arisawa Aslamiyya tsifan sannan ta d’auko wayarta ta kira Sabrin wanda magana kad’ai ta yi Laila ta gane nak’udan take yi bil hak’k’i har sun isa asibiti yanzu ita da Salman. Hijabinta ta d’auka ta sanya kana ta dubi Aslamiyya yarinya mai sauk’in kai da hak’uri ta ce, “Ki tattara k’annenki ku tafi sashen Ummii ko Aunty Naana zan je asibiti, don Allah kar wani ya tsaya a nan sashen.” “To Mama.” Ta fad’i hakan tana fita daga d’akin. Laila kuma waya ta d’auka ta kira Banney ta ce, “Likita idan motarka akwai mai zaka kaini asibiti Sabrin tana nak’uda.” “Akwai mai Mama, ki fito mu tafi.”  Abul ta samu a falo yana ganin yanda Mas’ud J ke koyawa Khadija drawing bayan ta bashi hak’uri tare da alk’awarin baza ta sake 6ata mishi ba, shi kuma akan cewa zai dinga koya mata. “Abul kana nan ne ko zaka fita?” Fad’in Laila bayan ta iso gurinsu. “Zan fita anjima kad’an, ke kika fad’awa Aslamiyya ta kwashi yaran zuwa side d’in Aunty Naana? Ta zo tana musu magana suka k’i kulata sai ta yi tafiyarta.” Ya k’arisa maganan yana dariya. “Wai a hakan na jaddada mata kar ta bar kowa, yarinyar nan bata son ciwon kai ko kad’an.” Laila ta murmusa har hakwaranta na bayyana. “Sanyin ta yayi yawa.” “To zan bar maka aikin nata, ka tattara yaran ka kaisu can side d’in Aunty Naanan ko Ummii su zauna a can kafin in dawo.” “To Mama.” Banney shi ya kai Laila asibiti wanda awa biyu da haka Sabrin ta haihu d’anta namiji a karo na biyu. Bayan an sallamesu Safa ta iso asibitin suka wuce gidan Sabrin d’in dama ita ta mata zaman jego a haihuwar Saif, Laila kuma gida ta dawo cikin murna da farin cikin samun jika a karo na biyu.   A daren ranar Haydar ya dawo daga Abuja Laila ta tar6eshi cikin murnar ganinshi wanda satinsa d’aya kenan baya gida. Sai da ya gama wasa da yaransa tare da bawa kowa tsarabarsa ciki har da Abul da Banney sannan kowa ya nemi makwancinsa shi kuma ya shiga wanka. Yana fitowa ya jiyo muryar Laila da Mas’ud a falonsa suna magana, sai da ya saka kaya sannan ya fito ya samesu a falo suna kallo. “Ina dana sanin had’a gida da kai wallahi, mutum ya dawo daga tafiya yau sati d’aya kenan rabonsa da iyalinsa shine zaka zo ka takuramu.” Fad’in Haydar yana zama a gefen Laila. “Sai dana fad’a maka this is a bad idea ka nuna kafi son hakan.” Laila ta k’ara ruruta abun tana k’unshe dariyarta. “Ba zan yi zuciya in tafi ba tun da naga alamar hakan kuke so, Maman Naana ne bata da lafiya yau da yamma aka kirata ta je gida ganinta, sai d’azu ta mini waya wai in barta ta kwana zuwa gobe ta ga yaya jikin zai kasance. So yau ni gauro ne, Kalti mik’o abincin da kika girkawa mijin naki mu ci ni dashi.” “To Allah ya bata lafiya, gobe sai ki shirya ki je ki dubosu. Laila kawo mana abincin nan.” Haydar ya fad’awa matarsa uwar ‘yayansa.  Laila tashi ta yi ta kawo musu duk abun da ta girka ta ajiye a gabansu suka sauk’a k’asa suna ci suna hira gwanin ban sha’awa domin k’arfi da yaji Haydar ya zama abokin Mas’ud na k’ut da k’ut. Tsokanan juna da suke yi kuwa kai in baka sansu ba sai naka ran ya 6aci su kuma suna dariya cikin annushuwa da kwanciyar hankali. Har sha d’aya da rabi Mas’ud yana nan ya k’i tafiya, Haydar kuma gaba d’aya ya matsu ya ke6ance da matarsa don satin da yayi baya tare da ita jinshi yake yi kamar shekara.  Ganin da gangan Mas’ud ya tsaya ya k’i tafiya yasa Haydar ya tashi tsaye ya kamo hannun Laila suka yi hanyar d’akinsu yana cewa, “Ban haifeka don ka hanani sukuni da matata ba, su yaran ma sun yi hak’uri sun barmu. Idan ka gama hiran ka fita Allah ya tashemu lafiya.” Suka shiga cikin d’akin Haydar ya rufe k’ofar har da saka key. Laila dai girgiza kanta kawai take yi tana murmushi don draman Haydar da Mas’ud ba k’aramin nishad’i yake sakata ba. Mas’ud bai k’ara minti d’aya ba ya kwashi snacks ya fita yana mita wai sun wulakantashi fuskarsa d’auke da murmushi, a zuciyarsa kuma godewa Allah yake yi da ya had’a Kaltinsa aure da Haydar.  Suna jin ya rufe k’ofa Haydar ya jawo Laila jikinshi yana ture had’edd’en d’aurin da tayi da kallabinta, gashinta da ta yarfawa kitso k’anana suka zuba a bayanta ya kama gashin yana shinshina yana lumshe ido ya ce, “Tun da nake da ke ban ta6a jin akasin k’amshi daga jikinki ba, kullum cikin k’amshi da kwalliya kike bakya gajiya da faranta mini Laila, har gobe ina godewa Allah da ya bani ke a matsayin matata uwar ‘yayana. Allah ya k’ara miki hak’urin zama da Gerontophile mijinki.” “As I said earlier, ina farin ciki da ka kasance hakan saboda na daina saka tsoron tsufa a raina yanzu. I love you Ruwan Zuman Laila.” Ta fad’a tana had’e goshinsu guri guda tana lumshe idanunta. “Bahaushe yayi gaskiya da yake cewa; “SOYAYYA RUWAN ZUMA CE” I love you more Ruwan Zuman Haydar.” Da haka ya kashe musu wutan d’akin Laila na dariya a hankali.ALHAMDULILLAH A nan muka kawo k’arshen wannan littafi na mai suna Ruwan Zuma wanda ya koyar da darussa kala daban-daban kamar haka, 1-Tazarar shekaru tsakanin mata da miji wajen aure ba abun kaico ko abun dariya bane. Aure suka yi wanda sunnah ne na Manzon Allah SAW, amma sai a samu masu kushewa suna baza labarinsu da hotunansu ana musu dariya ana zaginsu. Kai mai kushe wannan aure kana cewa an yi abun kunya idan a yau aka tsayar da kai gaban Manzon Allah SAW gefenshi kuma matarsa Nana Khadija shin zaka zagi aurensu bisa dalilinka na cewa mace mai yawan shekaru ba za ta auri namiji k’asa da shekarunta ba? Idan har baza ka iya ba so kar ka yiwa wanda suka kwaikwayeshi, idan kuma kayi ka jira hukuncinka daga Allah wanda ya yarda da wannan auren da kake kushewa kake zagi. 2-Girman mace, yawan shekarunta ko kuma wai  ‘yayanta na haihuwa itama tana haihuwa bashi zai hanata haihuwa ba idan har tana da lafiyar d’aukan cikin, masu aibata matar da take haihuwa da yawan shekarunta shin kuna da tabbacin wanda ta haifa a k’uruciyarta ne zasu kula da ita ko kuma su zasu yi mata addu’a idan ta mutu? 3- Iyaye ku daina gudun 6acin ran ‘yayanku akan abun da Allah ya halatta muku, sannan ku kula da ‘yayanku ku basu tarbiyya kuma ku wadatasu idan kuna da wadata amma ba’a ce ku sangartasu su dinga juyaku son ransu ba, idan kuma kuka aikata hakan ku zaku fara yin kuka da irin yanda zasu mu’amalance kafin kowa. Iyaye ku saka ido akan harkokin ‘yayanku sannan kar ku ji tsoron musu fad’a da hukunci idan har buk’atar hakan ta taso, ku kuka haifesu basu suka haifeku ba. Sannan kar ku manta bayan duniya Allah zai tambayeku yanda kuka basu tarbiyya Ya kuma hukuntaku in kuka zama sanadin lalacewar su. 3- Mai mugunta da munafurci a kullum baya cin riba a k’arshe, a farko Allah zai iya bashi sa’a ya cuci bayinsa sai dai a k’arshe Allah zai kamashi a ranar da bai yi zato ba balle tsammani, sannan kuma zai yi nadama mai matuk’ar yawa.  4- Duk abun da mutum zai yi a rayuwarsa in har yana kan gaskiya ne kar yaji tsoron bakin mutane saboda Allah da ya halatta masa wannan abun shi zai dafa masa ya kuma karesa. Shin akwai wani bawa da zai iya cin nasara a kan wanda Allah ya dafa masa alhali shi kanshi halittar Allah ne? Kar ka bari mutane su tsara maka rayuwarka saboda duk abun da kayi wasu sai sun zageka baza ka ta6a tsira ba. 5- Mu ji tsoron Allah a kan mu’amalarmu da mutane don bamu san me gaba zata haifar ba. Zaka iya wulakanta mutum amma a k’arshe shi zai zama gatanka haka kuma zaka iya bautawa mutum k’arshe shi ya zama dalilin kukan ka, wannan darasi ne babba a cikin littafin Ruwan Zuma. 6- Bahaushe yace yaron da ya hana uwarsa bacci shima ba zai yi bacci ba. Kuyi duba ga yanda Abul ya d’agawa Laila hankali amma da yake a kan gaskiya take sai duniya ta koya mishi hankali ya wahala iya wahala har shiryuwa ta riskeshi. Iyaye ba abun wasa bane ko abun wulak’antawa, duk wanda ya raina nashi ya jira yanda rayuwarsa zata k’are kafin ma a je lahira. 7- Idan kuka yi duba da rayuwar mutanen cikin Ruwan zuma kama daga kan Ammi, Alhaji Sammani, Ummii, Madu, Alhaji Abdul, Laila, Haydar da kuma Abul babu wanda bai ga k’alubale a rayuwarsa ba, wasu laifinsu ne ya bibiyesu suka wahala yayin da wasu kuma laifi kad’an ne ne suka yi amma suka yi dana sani mai tarin yawa a gaba. A littafin Ruwan Zuma nobody is perfect kowa da aibunshi kamar yanda a hak’ik’anin rayuwa kowa yake tara bai cika goma ba. 8- Sannan mu koyi yafiya ga ‘yan uwanmu mu kuma guji rik’o, ban ce ka manta ba saboda zuciya bata iya manta sharrin da aka mata amma ka yafewa wanda ya maka sharri sai ka ga Allah ya d’aukaka ka fiye da shi. Sannan yafiya na sanyaya ruhi yana kuma jawo Rahamar Allah kan bayinsa.I   Zan tsaya a nan ba don darussan sun k’are ba sai don na san ku da kuka karanta baku manta su ba suna cikin kwakwalenku. 

Zaku iya samun sauran littafaina Matar Kabila da kuma Fatu a Birni a wannan number 09023713064, kamar yanda kuka nishad’antu da RZ suma ina da alhinin zasu nishad’antar daku. Sannan zaku iya samuna a wattpad ta wannan link d’in  https://my.w.tt/IKR4zCOYfbb Nagode.

Taku a kullum Mum Fateey 👌

Back to top button