Mejo Najeeb Page 29 By Autar Alheri
“Amsa sallamar dasu dady keyi sukayi, bayan sun shigo Perlor sunzauna ne najeeb yashigo riƙeda hannun maryama…gaba ɗaya daga Hajiya Umma har Hajiya mama da kallo sukabi hannun najeeb dake cikin na wannan kyakkyawar budurwar dabasusan ko wacece ba…shikuwa becewa kowa komaiba yasamu wuri yazaunarda ita tukunnah Shima yazauna kuma alokacinne su general aliyu suka shigo Perlor….sudai su Hajiya Umma da kallo kawai sukebinsu sunajiran suji mikefaruwane sukagansu ahakan kowa fuska ba walwala….duddacewar suma dasu ƙurjin arai amma Zasu danneshi har se sunji nasu tukunnahAlhaji Abubakar ne yayi gyaran murya kana yace “najeeb. “Na’am Abba ya’amsa mishi kanshi aƙasa..gyara zama yayi kamin yace “najeeb Mike faruwane? Kagaya muna gaskiyar abinda ke faruwa tsakanin ka da wannan yarinyar? Domin ka ɗaure muna kai dazantukanka dudda cewar muma nemanka mukeyi sabida wani al’amari megirma daya faru…arazane yaɗago yana kallon Alhaji Abubakar kafin yabuɗe bakinshi murya na rawa sabida sauri yace “wani abunne yafaru Abba? Miyake faruwane? Yatambaya cikin damuwa. “Dakata najeeb baka bani amsar tambayar danayimaba kaima kanayimun wata tambayar.”Abba bazan iya amsawa bane ayanzu please kafara gayamin abinda yafaru konasamu nutsuwar amsama taka tambayar Abba wani abin yafaru dawani agidannan? Umma ina ƙannena? Kosune wani abin yasama kugayamin please? Yayi maganar aruɗe…..ganin duk yadda yaruɗe ne yasa Alhaji Abubakar cewa “bafa wanda wani abin yasama najeeb kowa yana lafiya al’amarin danacema yafaru kuwa bakomaibane face aurenda muka daurama kwanakin baya kuma ayaune amaryar zata tare gidanka batareda kasaniba dama shine abinda muke nemanka agayama sekuma gaya kazo muna dawani zance mekamada almara akan wannan yarinyar shin minene gaskiyar lamarin?? Yaƙarasa zancen yana kafeshi da ido.Wani irin ajiyar zuciya najeeb yasauke wadda tabawa su dady da su Hajiya Umma mugun mamaki domin kosu dasuke iyayenshi mata wannan zancen yadaki zukatansu balleshi da’akace an ɗaurawa Auren…amma gayanayin yadda yayi kamar wanda yasamu wani abun dayake nema yaɓace mishi ayanzu kuma yasamu.”Kainake saurare najeeb kaji zancen danakeyi kuma kayi shiru….Alhaji Abubakar yaƙara tambayarshi….ajiyar zuciya yaƙara saukewa kana yabuɗe baki ahankali yace “tabbas Abba abinda kaji nafaɗa gaskiya ne wannan yarinyar matatace kuma kune dakanku kuka Daura Auren….ido suka zaro atare kamin dady yace “wannan wanne irin shirmen banzane najeeb? Waikaga munyima Kamada ƙananun yarane kokuma sa’anninka? Yakana neman maidamu mahaukatane? Dady yafaɗa cikin hasala domin duk jiyakeyi kamar yashaƙoshi dagashi har Alhaji Abubakar yahuta datakaicin wannan abin…..shikuwa mejo najeeb cikin tabbatar da kalamanshi yace “wlh Allah Abba matata ce kuma kune dakanku kuka karɓa min aurenta, Abba yarinyar dakuke faɗar kun auramin kuntaɓa ganinta ne? Kallon Alhaji Abubakar dady yayi domin yaji mizece….cikin sauri Abba yace aa bamu taɓa ganintaba. “To kagani Abba wannan itace yarinyarda kuka auramin bawai wata bace. “Kamarya to idan itace wadda muka aurama ita kuwa wannan da’akawo wacece? Ko itace aka zoda ita yau?? Dady yaƙara jefo wannan tambayar….tunkamin yarufe bakinshi Hajiya mama tace “sam ba ita bace domin kuwa waƴannan baƙin da’amarya sukazo shiyasama kukaganmu anan zaune munasan sanin yadda abin yake duddacewar ajiya kace akwai wani al’amari megirma daze faru agidannan amma sam bamu ɗauka aurene kayiwa najeeb ba batareda munsaniba, taƙarasa zancen cikin takaicin wannan al’amarin ayiwa yaro aure sekace maraya🙄”Towai mike shirin faruwane nifa nakasa fahimtar wannan abin Alhaji Abubakar Mike shirin faruwane? Cewar alhaji Khamis, domin gabaki ɗaya ayanzu kanshi yaɗaure…..ajiyar zuciya alhaji Abubakar yasauke kamin yace “tsaya alhaji Khamis aide doline komi yawarware amma akwai abinda nake tunani kai najeeb yasunan wannan yarinyar? “Maryam, yabashi amsa atakyaice…iKon Allah kenan “to awane gari kaɗaukota? Yakoma jeho mishi tambayar..”gombe State Shima yaƙara bashi amsa.Kai Alhaji Abubakar yagirgiza kana yace “tabbas matarshice Alhaji domin idan baka mantaba alokacinda mukadawo har mukazo da dangin yarinyar sukaga gidannan nagayama abinda yafaru? Yayi maganar yana kallo Alhaji Khamis ɗin…”eh Hakane kagayamin….”yawwa to wannan ɗin itace aka fara ɗaura Auren da ita itace maryama daga baya aka Ɗaura da wannan ɗin da’azo da ita yanzu itakuwa itace hawwa’u sedai abinda bansaniba anan shine yadda akayi harshi najeeb yasanda Auren harya ɗauko yarinyar.”to ai shine zemuna wannan bayanin ta yadda aka yi yasanda Auren harsuka haɗu shida ita, cewar dady….general aliyu dayayi shiru kawai yana kallonsu se ayanzu yayi magana, tahanyar faɗar “dady kubari ni zangaya muku yadda aka yi suka haɗu haryazo nan da ita domin agabana akayi komai..”to shikenan munajinka Aliyu gaya muna. Zama general aliyu yagyara yashiga basu labarin haduwarsu da Isseta har izuwa lokacinda maah tabawa najeeb amanarta har korarda Abba yayi mata sedai yaɓoye musu cewar Maah aljana ce ba mutinba abinda yace musu wata dattijawace wadda suma basu santaba maybe sunada wata alaƙa da Isseta ɗin shiyasa harta yanke hukuncin bawa najeeb ita…..yaƙarasa zancen yana duƙarda kanshi ƙasa..Mukoma baya kaɗan masu karatu idan baku mantaba alokacinda maah tabawa najeeb amanar Isseta tace musu akwai abinda yadace tagaya musu kuma zata gaya musu tunda sun aminta Zasu zauna inuwa ɗaya tace dabasu amintaba tabbas bazata gaya musu ba daganan tashiga gaya musu wani rikitaccen al’amari wanda yagirgizasu gaba ɗayansu kuma alokacin bamu faɗi abinda suka tattauna ba, to wannan rikitaccen al’amarin shine aurenda aka ɗaurawa Isseta da mejo najeeb ɗin shine tagaya musu wanda ko alokacinda aka Ɗaura Auren bamu faɗi Sunan wanda aka Ɗaura Auren dashiba abinda kawai mukace yaron wannan alhajin dayazo neman auren to bakowa bane face najeeb kuma ita tasanda komai tunda Allah yabasu baiwar sanin abinda bamu saniba shine babban dalilinta nahaɗa najeeb da Isseta domin daga farko Nigar taso maidata hannun mahaifiyarta shine wurinda tace acan yadace ace Isseta tanacan amma ƙaddarar rayuwa takawota nan garin gombe, to dawannan Auren na barazata yashigo seta yanke hukunci bawa mijinta ita batareda waƴanda suka ɗaura auren suntashi haɗa suba, acewarta mijinta shine mafi dacewa daya kulada ita yanzu…..kunji abinda yafaru abaya ga wanda yamanta ze iya komawa baya page na 25 & 26 zegane minake nufi domin zega zancen maah alokacinda tahaɗa su kafin umaima takawosu garin Lagos..Cigaban labarinAjiyar zuciya duk wanda ke perlor yashiga saukewa domin kuwa wannan abun baƙaramin mamaki yabasuba musamman haduwar ma’auranta dakuma mamakin wannan matar data haɗasu kowacece ita ? Tunda batasan najeeb ba balle harta gane dashi aka Ɗaura Auren….dukkansu tambayar dake ransu kenan sedai kafin wani yasamu damaryinta tuni umaima tashafe musu ita azukatan su akaci gaba da abinda yatarasu.”Ajiyar zuciya alhaji Abubakar yasauke kamin yace “to yanzu dai tun da duk mefaruwa tafaru abinda zamuyi Ayanzu shine neman mafita domin kawo sauƙin abin, mafitar kuwa itace kazaɓi ɗaya acikinsu domin bazeyu kazauna dasu su biyu ba doline ɗaya zaka saka kazauna da ɗaya tunda ubansu ɗaya kamar yadda megarinsu yagaya muna…..”gaskiya kam Hakan za’ayi zaka saki wannan daba iyayenta ne suka kawotaba kuma dama can ahakan aka tsara zaka saki ƙaramar kazauna da yayar, cewar dady…wani irin waro ido mejo Nejeeb yayi cikin tashin hankalinda ya bayyana ƙarara akan fuskarshi…kamin yayi magana alhaji Abubakar yace “ah’ah alhaji baza’ayi Hakanba ita wannan sun daɗe tare bakasan tun wani lokaci suke tareba kuma shi najeeb ɗin bakasan ra’ayinshiba abinda za’ayi za’abashi zaɓi ne yaɗauki ɗaya acikinsu idan kuwa wani abin na auratayya yataɓa shiga tsakaninsu da wannan ɗin tofa babu zancen yazauna da waccan doline ita ɗin zeɗauka se ahaƙura da hawwa’u tunda dukkansu abu ɗaya ne. “Hakane kam dady yafaɗa kafin yamaida dubanshi akan Najeeb yace “kagaya muna gaskiya kataɓa kwanciyar aure da wannan yarinyar??? Gaban general aliyu ne yafaɗi jin wannan tambayar menauyin gaske da akeyiwa aminin nashi domin yanada tabbacin baze amsataba, sedai begama zancen zucinshiba yaji cool voice ɗinshi yana faɗar “yes I have sex her time by time,,mun rigada mun zama Abu ɗaya nida ita, Hakan kawai yatsinci kanshi da fadar Hakan….!



