FATALWAR DELU 🤡
Part 2
Kingboy Isah 👑
Short story
ZAMANI WRITERS ASSOCIATION
Nan take zuciyata ta fara sake-sake ina tunanin dalilin da zai kawo yarinya karama kamar wannan bayan gari da tsakar dare haka, ba ma ita kadai ba kuma harda jariri. Wata zuciyar ta ce min hala dai tare da uwarsu suke ko ta fito yin bayan gida ne domin bisa ga dukkan alamu a kauyen nan ba ko wane gida bane za’a samu masai a bandakinsu. Can kuma sai na tuno maganganun Bukar na cewa bayan karfe 9 na dare ba mai kara fitowa waje a garin. Na dubi yarinyar da ke bina da kwala-kwalan idanunta da na haske da fitilar wayata hade da cewa “Ke ina mamanki me ya fito daku daji da tsakar daren nan? Kuma kina ji kaninki na kuka ba zaki daukkeshi ba?”.
Ina magana tana bina da kallo har nayi shiru banga alamar bakinta ya motsa ba balle inyi zaton zatayi magana. “Ke dake nake magana ko ke kurma ce?”. A zuciyata na fara tunanin yarinyar nan kurma ce, don haka na fara mata nuni da hannu ina zancen kurame duk da ba iyawa nayi ba. Duk yadda nake lankwasa hannu ina nuna jariri da yake ta kwala kuka da alamar ta daukeshi amma yarinyar nan da shegen taurin kai ta tsareni da ido ko kiftawa bata yi. Dan haka raina ya fara baci na daina zancen kuramen kai tsaye naje da nufin daukar jariri, amma da na haska fuskar tashi sai na tsaya ina kallonshi, sunyi kama sosai da waccan yarinyar bayan kwala-kwalan idanu har da farin abu mai kamar gari irin na fuskar yarinyar shima a fuskarsa.
Bayan na sa hannu na tallabo shi ina daukarshi sai ji nayi yayi shiru ya daina kukan da yake, kai tsaye naje na dungurawa yarinyar hade da cewa, “Karbeshi”. Bisa mamaki sai naga taki motsa hannu tana dai nufin ba zata karbeshi ba. A fusace na ce “Yau ga yar iskar yarinya, karbeshi ko na faffala miki mari”. Aa maimakon yarinyar ta ji tsoro amma ko gezau bata yi ba, bayan kallona da take bata wani yunkuri na karbar yaron. Don haka na dungura mata shi na dora shi kan cinyarta, hade da cewa “Gashi nan maza kiyi masa wasa kafin sakaran uwar taku da ta barku nan ta dawo ta karbeshi”. Ita dai bata ce komai ba haka kuma bata rike yaron ba, wanda shi kuma yana barin hannuna ya sake tsala sabon kuka. Ban damu ba na mike tsaye sai da na kara has-haskawa ina magana a zatona ko uwar ta su zata ji ta fito su nufi gida amma naji shiru. Dan haka na juya na tafi ina tsaki ni kadai ina wa uwar yaran nan masifa.
Na fara tafiya kenan naji kamar kukan yaron a bayana, don haka na juya hade da haskawa. Yarinyar na gani dauke da jaririn ta nufo inda nake, “Ke ina kuma zakije ba zaki jira mamanki ba, ko kina nufin dama ke kadai ce ba tare da mamanki kuke ba?” Nayi maganar ina kare mata kallo duk da sanin cewa ba lalai ta tanka mini ba. Jin tayi shiru na ce, “Kuma dan iskanci shine zaki daukko mata jariri, maza muje ki wuce gida”. Na fada a zuciya ina kara jaddada jin haushinta kamar na kamata in zane. Jiranta nake ta shiga gaba mu wuce in kaita gida amma yarinyar nan tayi tsaye tana kallona. Dan haka kamar dazun na kara mata irin zancen kurame na nuna mata hanya da nufin ta wuce. Yanzun ma dai kafeni tayi da ido ko motsawa ba tayi ba, dan haka na fusata na dauki wani guntun kara na nufeta, a zatona zata ruga amma har na karasa gurinta bata ma motsa ba.
Ina zuwa na zafga mata kara a baya hade da cewa “Wuce muje ko in ci ubanki a dajin nan”. Wannan karon ma bata motsa ba dan haka na kara zafga mata kara, a karon farko sai gani nayi ta daga kai sama ta fashe da kuka, da faruwar haka sai ta tsugunna ta ajiye jaririn a kasa cikin tsumma, ni dai ina binta da ido na daga kara ina nufin kara doka mata. “Yi mun shiru ubanwa kika ajiyewa yaron, kaji yarinya da rashin hankali. Maza ki daukeshi muje”. Na fada ina zare mata ido. Ganin taki daukar yaron da sai kuka yake na sake tsula mata kara a baya. Ba zato sai gani nayi ta juya baya a guje tana kuka mai kama da ihu. Ni kuwa na saki baki ina kallonta, a tunanina ai ko guduwa zatayi cikin gari ya kamata ta nufa, amma sai naga tayi hanyar jeji. A zuciyata na ce, watakil wajen uwarta zata koma halan. Don haka na dauki jaririn na bi bayanta a guje.
Na danyi gudu kadan na nemi yarinyar nan sama ko kasa na rasa, a iya hasashena dai dan lokacin nan in ba gudun haske ne da ita ba, bai kamata ace ta bace min ba. Dan haka na shiga has-haskawa bayan kabobi a zatona ko boyewa tayi a gun, amma banganta ba. Tsaye nayi cik da jaririn a hannu ina ta haske-haske cikin daji ina kwala kira amma na ji shiru ba yarinyar nan ba alamarta. Jaririn na haska da fitilar waya, wanda tunda na dauke shi naji yayi shiru. Kara karewa fuskarsa kallo nayi da kyau, idonsa biyu kyar a kaina, ba wannan ba ni fa gani nayi ma yana hararata. Na kara gyara fuskar tashi da kyau daga cikin tsumman zani, tabbas hararata jaririn yake yi. “Ka ga dan iskan jariri uban me nayi maka kai kuma da kake hararata”. Na fada a fili sai kace jaririn yana jina.
A zuciya na fara tunanin ko dai haka idanunsa suke shiyasa da yake kallona nake ga kamar harara ce. Ba wannan ba, sake daga kai nayi ina duban dajin tare da haskawa, na tabbata in da yarinyar nan uwarta ta tafi kira yanzu ya ci ace ta dawo amma gashi shiru har yanzu bata dawo ba gashi ta barni da jariri a hannu. A zuciya na fara nazarin yadda zanyi da jaririn nan, ni ba abin in yadda shi a nan ba ko ba komai mutum ne kuma jariri da baisan komai ba. In na ajiye shi a nan bansan halin da zai shiga ba, watakil ma wani mugun abun ko maciji suna iya cutar da shi. Don haka na yanke shawarar tafiya da jaririn can shagon Bukar in ya so da safe in bashi labarin abinda ya faru a nemo uwar yaron a bata danta.
Da haka na juya da nufin komawa har na kusan isa cikin gari sai naji kamar mutum na biye da ni a baya, na juya hade da haska hanyar sai kuwa na ga wannan yarinyar ashe ita ce ke biye da ni, a wannan karon bayan kallo kuma sai hararata take. Fuska a daure na ce, “Ke! da gidan uwar wa kika tafi kika bar kaninki a hannuna, zo ki karbe shi”. Na nufeta amma bisa mamaki sai gani nayi ta sake juyawa ta ruga. Ba karamin fusata nayi ba dan haka na ce, “Lalai yarinya baki san halina ba ne, bari na ajiye shi a wajen nan idan kin ga dama ki zo ki dauke shi idan baki ga dama ba ki barshi a wajen”. Ina gama fadin haka na ajiye jaririn na juya na cigaba da tafiya. Ina ji kamar ana bina a baya amma ban juya ba, haka ban damu ba har na karasa shagon Bukar na shiga na kwanta bayan na kulle dakin daga ciki. Har bacci ya fara daukata naji ana kwankwasa kofa. Don haka na tashi na bude kofar ina fadin waye, da bude kofar naji kamar karan gudun mutum ya tsere, Amma bayan na bude sai banga kowa ba bisa mamaki sai na ga jaririn nan a ajiye bakin kofa, ina haskashi kuwa ya fashe da kuka…………………..
Zan cigaba