Zakuna Biyar Page 9 By Princess Teema
Bayan ta kammala shirya akwatinta, ta rufesa kenan sai ta ji ana sallama a parlo. A natse ta amsa tare da miƙewa ta fito dan ganin wanene?. Cike da mamaki ta zaro idanunta a lokacin da ta ga mai daka mata sallamar. Muryarta har yana ɗan rawa wajen cewa. “Lafiya kika shigo mun parlo yau kuma?”.”Lafiyar ce ta kawo haka”…….. Ɗan zare ido Ummie ta yi, sai kuma ta basar da cewa. “Okey me yake tafe dake?”….. Shiru yarinyar ta ɗan yi, can kuma sai ta ce. “Albishir na zo yi maki, abin da kika kasa bawa mijinmu yau ALLAH ya bashi a jikina”. Ta faɗa tana shafa shafaffen cikin nata. Wata figaggiya da ita kamar kazar mayu, wannan idan babban mota ya zo da gudu iskansa tsab zai kaita ƙasa, ba welcome bare goodbye, tana nan kamar namiji ya ɗaura zani!.Ajiyar zuciya Ummie ta sauke, take murmushi ya bayyana a kan face ɗinta, a sanyayye ta ce. “Kai Alhamdllh, ALLAH mai kyauta mai kari, UBANGIJI ya saukeki lafiya, amma na tayaki murna, banda abinki da rigima ai nima bani na hana kaina ba, ALLAHN da kika ce ya baki shi ɗin ne dai mai bayarwa, kuma shi ne bai bani ba, a haka kuma ina gode mashi ina karawa, amma wlh na yi murna da ALLAH ya bamu ta wajenki, ai dik ɗaya ne!”. Da iya gaskiyarta ta yi maganar, dan ALLAH ya ɗaura mata jaraban son yara, yara makota dik a wajenta suke wuni, dan haka bata bakinciki da wannan ciki, wlh idan aka haifa zata rike tamkar nata In Sha ALLAH baiwar ALLAH.Wani irin ɗaure fuska amaryar ta yi, dan ita ba ta kawo mata labarin dan ta yi murna bane, burinta ta kuntata ma, amma sai ga shi tana murmushi. Cike da takaici ta ce. “To ai ba ɗanki bane, nice uwarsa, kada ki taɓa sa ran zai zo ko da kusa dake ne”……… Sosai Ummie ta ji kirjinta ya buga, sam bata ji daɗin hakan ba, ta zaci ai zasu haɗa kai su reni yaran ne! Ganin fuskanta ya canza yasa amarya jin daɗi, burinta ya cika ta kuntata mata, dan ta kara mata takaici ma sai ta ce. “Idan fitsari banza ne kaza ta yi, ki haifi naki, nawa basu da alaƙa dake juya kawai, almost shekaru 5 kenan yanzu da aurenku ko ɓari baki taɓa yi ba, wai har mazan da kike bi ma babu wanda ya iya yi maki cikin ne? Sai kuɗi kawai suke baki? Ko da yake kece juya, ko zasu dinga kwana a kanki ba samun cikin zaki yi ba”. Ta kai karshen maganar tare da juyawa tana wani hura hanci, ta nufi waje. Tsaye Ummie ta yi, take wasu zafafan hawaye suka wanke mata fuska, da gudun gaske ta shige cikin ɗaki, babu abin da ya fi bata takaici irin ƙazafin zina da suke mata, a dik san da suka ce maza take bi suke bata kuɗi sai ta sha kuka, ga shi yau tsawon wattanni 8 bata samun damar hira da Zaysh, dan tin da suka shiga horo na karshe-karshen nan ba’a basu waya ba, an karɓi wayoyinsu, sai ranar Sunday yake kiranta da wayan securitys officers, kuma mintina biyar ake basu su gaisa da gida su ji idan kowa yana lafiya, baya ga haka basu da wani lokaci ɓatawa, dan a watannin karshen nan horo wuta-wuta ake basu babu kama hannun yaro.Kuka ta ci mai isarta, sannan ta miƙe ta ƙarisa shirinta, wunin ranar haka ta wuni cikin ƙunci, sai can yamma ta nufi shagonta dan su yi lissafi gobe zata yi sammakon tafiya Abuja, daga nan zata hau jirgi zuwa Avaris, ta so zuwa Niger wajen ƴan uwanta na kauye ta kai masu abin arziki tin da ta ɗan samu rufin asiri, amma ba dama, sai ta ce bari ta bari sai ta dawo daga Avaris ta sauƙa ta can!. Ko da ta zo fita sai da amarya ta yaɓa mata magana, wai dan ta ji tana da ciki ne dik ta shiga damuwa har da kuka ido ya kumbura, ita dai bata ce komai ba ta fice abinta. Sai habaice-habaice amarya take yi………. Ita dai bata dawo gidan ba sai dare, a shagonta ta yi sallar mangrib da ishai suka yi lissafi da yaron shagon, sannan ta sayi abinci a restaurant ta dawo da shi. Tin da ta shiga ɗaki ta rufe kofa bata sake fitowa ba, dama mijin ba’a ɗakinta yake ba.A ciki ta ci abincinta ta ƙoshi, daga nan ta kwanta abinta, da assusuba ta tashi ta ja akwatinta, mijin nata kuma yana nuna mata tsantsar so da kulawa, dan kuwa har tasha ya rakata da sanyin asuba, sai faɗi yake yana nanatawa kan ta kula da kanta. Da motarsu ya zo tashi ma, ya ƙanƙame hannunta yana faɗin zai yi kewanta sosai, ita ma har kwallah ta yi tana faɗin zata yi kewansa, dan tana mugun son shi, kuma tasan yana kula da ita, yana gwada mata kauna, kome yake faruwa ba yin kansa bane, ta sani kuma ta yi mashi uzuri, bata hukunta shi da laifin danginsa ba!. Ko kaɗai bai taɓa yi mata ƙazafin zina ba, masu yi ma idan ya ji ba karamin faɗa suke yi da shi ba, shi ya aminta da ita, danginsa ne dai sai shiru!.A haka suka rabu cike da kaunar juna, ya koma gida ita kuma motarsu ya tashi sai Abuja, daga nan ta hau jirgin Mexico wanda already mijin nata ya wuce gaba wajen shirya mata komai, zata sauƙa a can, gobe ta hau jirgin Avaris kai tsaye, already an shirya jirgin da zasu tafi Avaris ɗin a Mexico, jirgi direct daga nan Naija zuwa Avaris ne babu, sai an yi masu juye a Mexico, shiyasa!. TO UMMIE SAI DAI MU CE SAFE TRAVELS!. ———————-🔥AZURE.BIKIN KARRAMA MATASAN SOJOJI KO ACE PASSING OUT. Barrack ɗin gabaɗaya ya canza, an sake mashi fenti, dik wasu sojojin dake waje sun dawo barrack, hakan yasa barikin ta cika da dubban zaratan sojoji, ta ko’ina su ne ke ta faman shawagi.Ranar passing out, wannan rana ce da za su saka kakin soja da cikakken kima and ƴanci, su tsaya a bainar jama’a a matsayin sabbin sojojin ƙasa, kada ku manta su ba kamar sauran sojoji bane, sun shiga horo na musamman a babi na biyu, kunga dole bikin karramasu ya zama gagarumin biki sosai!.Tin sati biyu da suka wuce aka fara preparation for the ceremony. Yau takama Monday kuma ranar da za su fito daga ɗakin horon da aka shigar dasu bayan shekaru biyu suna gwabzawa da fama. Da safiyar wannan rana, sojojin sun tsananta kai komo a cikin barikin, kowa ka ɗaga ido ka gani sai ka firgita, suna wani muzurai tamkar zasu cinye mutum ɗanye!.Katafaren hall na GIDAN SOJA an ƙawata shi matuƙa, an shirya kujeru da dik abin da za’a buƙata, gefen iyaye da dangi daban, an shirya shi matuƙa, gefen manyan general’s na sojoji an ƙawata shi, gefe guda kuma ga matasan sojojin da suka fara horo tare da su suka yi passing out a zone one, ga wasu sojojin da aka shirya masu rike da bindigu sun kai su 50 a layi, a can ta tsakiyar hall ɗin wasu dakakkun sojoji su 10 ne a tsaye a tsakiyan wajen cikin ƙamewa da nuna kwarewa a kan aiki.A kusa da side nasu General’s an shirya gefen iyalansu, dan suma zasu ziyarci wanna biki. Ga kayan ciye-ciye da aka shirya masu rai da lafiya. Komai yana nan bisa tsari.Basa wasa da lokaci, dan haka karfe 3 na yamma kowa ya hallara a wannan waje, dangin matasan sojojin dik sun hallara, watau tin ana iya kirga motocin dake danno hanci cikin barrack ɗin nan har aka daina, domin kuwa AZURE ta ga manya-manyan ƙusoshi da ake da su a ƙasa da wajen ƙasar, waɗan da ba’a taɓa tunanin ganinsu ba, musamman CEO na STARS BODY LUSH, dayawa sun yi mamakin ganinsa a wajen, sai tambayar kansu suke yi me ya kawo shi nan kuma?.Iyayen Unays sai mamakin ganin daddyn Noor suke yi, dan labarinsa suke ji, yau kuma gasu ga shi, abin like wow. Kyakkyawar waje aka ware mashi shi da family ɗinsa su Aunty Lusi, dikkansu burinsu su ga Noor, rabonsu da shi shekaru biyu da watanni kenan, sun yi kewansa sosai, a lokacin da ya shiga horo na musamman ko sun zo basa samun damar ganinsa, dan a wannan lokaci babu wanda ya isa ya gansa. Shiyasa nima na tsallaka maku wajen, a horonsu na musamman ba’a yarda ko iyaye su ga mutum ba, daga kai sai Captain and Commander! Babu ma wanda yasan duniyar da ake horo na musamman ɗin, amma dai a underground ake yi!. Iyayen Vash ma sun hallara a wajen, da 3 uncles ɗinsa, dan shi shi kaɗai mahaifinsa ya haifa, ba kani ba kanwa!.Kowa ya bayyana, dik sun zauna sun natsu tsit, Ummie ma ta baro hotel da ta sauƙa ta iso barrack cikin shigarta na tsadadden abayarta, da yake sun fito daga horo an basu wayoyinsu, tin da Ummie ɗin ta taso yana waya da ita, shi ya shige mata gaba wajen samu ta iso lafiya, ya roki Captain alfarmar da a kama mata hotel, da yake yanzu Captain ya zama abokinsu sai ya aminta, ya tura yaransa biyu aka ɗaukota a airport, aka kaita hotel, da zata zo barrack ta kira Zaysh a waya, ya sanya ta ɗauki abin hawa ta ce a kawota AZURE kowa yasan wajen! Kun ji yadda aka yi ta zo.Waje ya yi tsit kowa sai rarraba ido yake yi suna jiran bayyanar sojojin. Su V da suka sha kwalliya na wucewa tsara, tamkar zasu tafi gasar kyau, suna zaune a side na family ɗin senior staff, su passing out ɗinsu sai next week, ba tare za’ayi da na su Leo ba, saboda abin zai yi yawa!. Wani kafurin Italian gown mai tsantsan kyau da ya bi shape ɗinsu, ya fito da su tamkar ka sace su ka gudu da su, ga ash hair ɗin nan nasu da ya sha gyara, waɗan nan gajeru na gaban goshin sun ƙara fito da tsananin kyansu!.Dik wasu manya a Avaris yau sun bayyana a AZURE, president, vice president, governors, ministers, kai kowa ya hallara, shiyasa tsaro ya yawaita, helicopter sai shawagi suke yi sama, ga su eagle and jet dake kewaye dan tabbatar da tsaro.Wani irin bit ne ya karaɗe gabaɗaya hall ɗin, ga take GIDAN SOJA ɗin dake tashi ya bi tare da bit ɗin, wanda ya sanya gabaɗaya hall ɗin aka ƙara natsuwa tsit. A jere matasan sojojin nan suka fara shigowa, suna taku cikin tsantsar jarumta, gabaɗayansu sanye suke da sabbin kakin soja da ya kara masu kwarjini na musamma, kakin soja firgita makiya kenan!.Cikin zafin jini suka tako har izuwa saman stage in da aka tanada masu dan tsayuwa kowa ya gansu!……. Ni da kaina na ce ya ilahil alamina, watau dik wanda ya sansu a shekaru biyu baya a yanzu ba zai taɓa ganesu ba, zun zama wasu irin dakakkun maza, lafiyayyun cikakkun maza majiya karfi! Dik da a cikin kaki suke idan kuka gansu ku kun san ba horon wasa suka karɓa ba, fuskokinsu tamkar waɗan da aka aikowa da saƙon cewa wuta zasu shiga, babu wasa ko alamar fara’a a kan fuskokinsu.Daddyn Noor ai bai san lokacin da ya mike tsaye yana kallon ɗansa ba, a tsaye yake, babu wasa a kan fuskansa, dik yadda suke zaton ganinsu sun zarce hakan, tin daga kan tsayuwan Noor daddynsa yasan namiji ne wannan a tsaye, dik wani sauran tausayinsu horo bar two ɗin nan ya kwashe masu shi.Dikkansu hannunsu ɗaure da tambarin lambobin yabo da jarumta a jikinsu. Ga wani tsantsar natsuwa da kwarjini a tattare da su. Wasu sojoji su 4 ne suka zo da fareti suka fesa masu wani haɗaɗɗen perfume mai bala’in kamshi dan karramawa ta farko a garesu.Wani irin busa ne mai karfi ya karaɗe hall ɗin wanda yasa kowa ya kara natsuwa tsit, wannan busa alama ce ta karramawa a garesu, kuma alama ce ta sun yi nasara.Dikkan jama’a idanunsu na kan waɗan nan matasan sojojin ne, musamman family ɗinsu da suka canza masu, sun ga sun zama dakakkun maza, murɗewar jikinsu ya razana zuƙata, ga fuskokinsu kana gani kasan maza ne a wajen! SOJA MARMARI DAGA NESA!.Bayan busar wannan ƙaho sai recap of their struggle, wani dakakken soja mai zubin rashin imani ne ya tako izuwa tsakiyar hall ɗin, a gabansu ya tsaya tare da miƙawa GAT sd card dake hannunsa cikin girmamawa tare da sara mashi. Karɓa ya yi ya sanya aka kunna makeken tvn dake wajen, sannan ya bada sd card ɗin aka sanya a tvn. Take video ɗinsu a lokacin horo na biyu ya bayyana, irin gwagwarmayar da suka sha, bakar azaban da suka sha. Wajen da ya fi komai ɗaukar hankalin jama’a shi ne in da suke gwabza faɗa da junansu dan kwarewa a faɗar hannu, ya ilahi, duka sosai suke yi wa juna tamkar ba jikinsu ba, a wani waje tayar mota ce take bi ta kansu, suna kwance flat a ƙasa motar take bin ta tsakiyar cikinsu, kuma basa jin komai, saboda jikinsu ya rigada ya kame, babu abin da zai yi masu.Da aka hasko wani waje in da Vash ke kaiwa Noor naushi a ciki sai da dayawa daga cikin jama’a suka ɗan datse idanun, slowly suka sake buɗewa, sai suka ga Noor a tsaye tamkar saƙago, bai ji komai ba a kan wannan naushi. Wani waje suna kwasan manyan kayayyaki a gadan bayansu su yi ta gudu iya kurewar gudu, horo na gaske suka yi ba kamar bar one ba, Noor tin da ɗan sauran murmushi a kan face ɗinsa har komai ya kau, ya fuskanci reality, ya zama tsayayyen namiji wanda bashi da wasa kuma baya ɗaukar wasa!.Wai a haka wurare masu sauki aka nunawa iyayensu, ba’a nuna masu ainahin azaban ba, dan wlh dik wanda ya ga ainahin azaban da suke sha a bar two ba zai yarda ya turo yaransa aikin ba, sai ma da suke lallankwashe kasusuwan juna, kaga tamkar zasu karyesa ne, abin dai ba’a magana sai shiru.Captain ne ya kashe video ɗin tare da cewa. “A yau kuna tsaye a gabanmu ne a matsayin jarumai masu ƴanci, kun sha wahala, kun sha horo, kun sha yunwa, amma kun tsaya tsayin daka! Kun cancanci wannan rana ta karramawa!”.Har cikin ransu sun ji mugun daɗin kalamansa, kuma a yanzu mugun kaunar Captain suke yi, dan ya tsaya masu, shi ya mayar da su cikakkun maza, saboda jajircewarsa yasa suka yi nasara a yau!. Time for oath of allegiance ya yi, a nan ne aka umarcesu da su tsaya a gaban mic dake saman stage ɗin, sannan su fuskanci dunban jama’ar dake wajen dan yin rantsuwa ga wannan aiki. Ba musu suka kaddamar da abin da aka ce. Hannayensu suka ɗaga sama suna masu dunƙulesa alamar karfafawa, haɗe baki suka yi wajen cewa. “A yau muna tsaye a kan kafafunmu gaban dubban jama’a, muna rantsuwa da sunan wanda ranmu ke hannunsa cewa zamu kare ƙasarmu, rayuka da dukiyata, ba zamu taɓa bari abokan gaba su yi mana ƙawanya ba, dik wasu dattin dake a kan kasarmu zamu kawar da shi!”. Gabaɗaya sojojin nan voice ɗinsu ya zama Lion voice mai kaifin da babu wasa a cikinta, musamman Leo and Noor, zai Zaysh and Vash, then Juraiz and Units then saura.Suna kai karshe aka harba bindigu uku a jere, daddyn Noor daɗi ya sanya ya gagara yin magana gabaɗaya, yaga ɗansa ya zama dakakken namiji jarumin gaske, tamkar ba shi ba!Cikin wani irin kamewa da takun jarumta Captain ya matsa gaban GAT, sara mashi da karfi ya yi haɗe da gwada zarrar jarumta!. Miƙewa GAT ya yi, a daidai lokacin dakakken soja mai kama da saƙagon dake bayansu ya miƙo mashi ƴar kyakkyawar akwatin dake hannunsa, karɓa GAT ya yi, ya miƙawa Captain. A wani irin kame Captain ya karɓi akwatin ya juya ya koma gaban sojojin nan. Iyaye sai farinciki suke yi. Buɗe akwatin ya yi, wasu gold stamp ne guda shidda a ciki. Cirosu ya yi tare da miƙawa sojan dake bayansa akwatin, kowani kambu yana ɗauke da sunan wanda za’a sanyawa. Daga ƙasa ya fara, wanda ya zo na shidda a horon bar two shi ne Juraiz na ɗakinsu Unays. Matsawa Captain ya yi, a wuya ya sanyawa Juraiz kambunsa, take aka yi harbi guda biyu a sama na girmamawa garesa. Sake matsawa zuwa mutum na biyar ya yi, watau Unays, sanya mashi ya yi shi ma aka harba two bullets a sama. Ya matsa na huɗu Vash, yaro ya zama shirgegen soja mai rai da lafiya. Sanya mashi kambunsa ya yi, ya sake matsala ya sanyawa Zaysh dake na uku kafin ya matsa ya sanyawa Noor dake matsayin na biyu, watau Leo ya tsaya tsayin daka sai da ya mayar da Noor dakakken namiji, dik in da ya sanya kafa Noor sai ya sanya, bai mashi ta daɗi ba amma a karshe yasa ya yi nasara!.Lokacin da Captain ya zo sanyawa Noor wannan kambu shi da kansa yasan Noor namiji ne a yanzu, sai da ya kare mashi kallo kafin ya sanya mashi kambun, sannan sai da ya sanya hannu ya buga shoulder ɗinsa da karfi alamar jajircewa kafin ya wuce wajen oga Leo dake tsaye tamkar wanda aka sassaƙa! Ya kafe kallonsa a waje guda, wanda da na juya dan ganin wa yake kallo sai da na firgita. Ya ilahi ya lillahi, wani bawan ALLAH yake kallah wanda dik da yana sanye da Dr nose mask hakan ba zai hana ka san cewa ALLAH ya yi halitta a wannan waje ba, kamanninsa da Leo tamkar an tsaga kara ne, still shi ma kitso ce a kansa na kalba, kitson ma zara-zara kuwa, zanensu ya fito sosai, ya tara kitson a tsakiyan kai ya ɗaure, hannunsa rike da p-cap da ya cire daga kansa. Dik da yana zaune kai daga ganinsa kasan mazajene a wajen, eyes ɗinsa kalar sanyi, irin jade eyes ɗin nan, in kuka gansa zaku zaci yana jin barci, ga idanun very sharp, har sun fi na Leo rikitarwa, dan shi zaku zaci yasa kwalli a idon ne, kuma haka halittarsu yake, kunga ɗan round mouth lips ɗinsa kuwa? Gasu pink color kamar na mata, maza da ja aka sansu, su kuma nasu pink color ne sosai. ALLAH ya yi halitta a wannan waje jama’a!.Slowly ya mayar da p-cap dake kansa, gabaɗaya ya kafe Leo da kallo shi ma. Zayra’an Muhammad Haizaan kenan, Big Bro na Leo, the same father the same mother, su biyu ne rak wajen iyayensu, Zayra’an zai kai kimanin 32 years a yanzu, tsayayyen namiji ne wanda ya samu horo a AZURE shekarun baya da suka wuce, zakaran da a lokacinsa babu wanda ya iya bugesa, yaki yarda aiki a AZURE shiyasa ya koma Us military, mutumin da yadda kuka ga Leo haka yake, har ma ya fi Leo wasu dabi’u masu gindayar da mutane, zaka iya zaman shekara da shi bai ce maka kala ba, in ma kai ka mashi magana ba lallai ya amsa ba, kaifi ɗaya ne, wlh in ya ce e to fa e ɗin nan ne babu wanda ya isa ya sanya shi canzawa, idan kuma ya ce a’a fa ita ma ta zauna, yana da nuna iko da isa a waje, a cewarsa dik in da ya je shi ne sarki, dole kowa ya yi ƙasa da kai dan girmanawa a garesa. A lokacin da ya karɓi horo a hannun GAT ne, lokacin GAT yana matsayin Commander kafin ya samu karin girma. Dik wata izza da isa a barwa Zayra’an kayansa, bakinsa bata buɗewa ta yi magana sai dai ido ya cika aiki. Idan ya zuba maka ido sai ka tsargu ka yi abin da ba shikenan ba, idan ya zare maka ido da alamar tuhuma in baka yi saa ba sai ka saki fitsari a wando, idan ya yi maka magana cikin tausasawa sai ka rikice saboda daɗin muryansa, idan kuma ya daka maka tsawa in har baka da kwarin zuciya kana iya sumewa! Kyansa yana haukata dayawa, yana rikita maza da mata, shiyasa baya shiga taro, baya zuwa ko’ina saboda idanun jama’a, kada ku manta sun fito ne daga ƙabilun da suka fi kowani ƙabilu kyau a duniya! Kunga kuwa batun kyau ma sai dai ayi shiru, amma suna rikita kwakwalen mata da maza, ko namiji ya gansu sai ya sake juyawa ya gansu bare mace.Sanya mashi kambun Captain ya yi tare da buga shoulder ɗinsa alamar kwararawa. Daga nan Captain ya karɓo kambun karmawa mataki na biyu, a nan aka sanyawa Ameer da sauran matansan room ɗin nasu dana room 3.Daga nan ne GAT ya tashi tsaye, cikin takun jarunta ya isa gaban mic da aka tanada dan jawabinsa. Take dik wani soja dake wajen ya ƙara kamewa da alamar girmamawa. Da kaifaffar harshe ya ce. “Ina yi wa sojojin da suka yi nasara murnar tsallake wannan babban aiki, hakika sun cancanci jinjina ta musamman, jaruman gaske ne, kuma dikkansu sun fito da sakamako mai kyau, sai dai a bisa doka wannan horon bar two da aka basu lallai ba za su karɓi sakamakon horonsu ba har sai sun ƙaddamar da Mission guda biyar, bayan sun kammala shi sun dawo, a nan ne zasu samu sakamakonsu na farko da na biyu, misali idan ace yanzu sun fita da muƙamin lieutenant, idan suka gama wannan Mission ɗin, suka yi shi da kyau, kuma suka yi nasara, suna iya fita da muƙamin General, Major General, har izuwa muƙamina, dan wannan Mission da zasu yi shi zai tabbatar da jarumta da kwarewarsu a aiki, dan haka yau ba rana ce ta yaye ɗaliban soja ba, yau rana ce ta shiga sabon babi, za’a basu hutun sati biyu, zasu je gida suga dangi da iyaye, dik abin da zasu yi zasu yi shi ne a cikin wannan sati biyun, daga nan za su dawo bakin aiki dan shiryawa wannan mission ɗin!”. Ya dakata yana kallon iyayen sojojin.Irinsu Ummie da basu san me Mission yake nufi ba sai daɗi take ji, ita dai ƙaninta ya zama soja tin da ta gansa da kaki. Sauran iyaye kowa fuskarsa ta sauya, musamman daddyn Noor dake da mallakin ɗa namiji ɗaya tilo a duniya, kunga kuwa ba zai so a tura shi wani Mission da manyan ƴan ta’adda a duniya ba. Basu gama dawowa daga tinanin da suke yi ba suka ji GAT na kirga irin mission da zasu yi, ciki har da kirgo kungiyar IRON FIRST wanda jiga-jigan jami’an Amurka sun ƙasa damkesu, amma wai ake kiransu matsayin mission na biyar da su Ko za su yi. BABBAR MAGANA, DA MATSALA KUWA!Kai wasa ma ake yi. A cewar daddyn Noor, domin shi bai yarda IRON FIRST mutane bane, yadda duniya take maganarsu, an gagara kamasu ɗin ne za’a ce wai su Noor zasu yi mission a kansu, very funny thing. Amma fa a cewar daddyn Noor, dan yana ɗauka Noor da ya sani ne, kunsan sanin da ka yi wa mutum a farko ko me zai zama a haka zaka dinga kallonsa, shi daddy kawai yana kallon Noor a ɗan shagwaɓa rago mai kukan da ya sani yake yi!.GAT ya kammala jawabinsa da kiran sunayen manyan ƴan ta’adda da zasu yi mission a kansu, daga nan ya ce Leo shi ne shugaban da zai jagoranci wannan runduna tasu, su 12 ne kenan a tawagar, from room 1 to room 3, kunga mutane 4 ne a kowani ɗaki, su 12 kenan. GAT ya naɗa Leo a matsayin Commander wannan runduna, dole su yi mashi biyayya da karrama shi, Noor assistant, daga nan ya umarci da a kawo stars ɗinsu, kowa iyayensa su sanya mashi star ɗinsa a gaban riga.Yana gama magana aka saki bindigu uku sama da karfi. Sannan Captain ya ɗauko stars ɗin a cikin box, iyaye one after the other aka fara kiransu suna zuwa dan sanyawa yaransu. A room 1 iyayen Vash aka fara kira. Wani kyakkyawan matashi ne ya taso ya kariso wajen, dik in da ake neman namiji wannan ya kai. Dr Aryan Muhammad Khaiza’an kenan, babba likita kuma natsastsen matashi mai jini a jika. (Ku lura, sunan mahaifin Vash da mahaifin Leo kusan iri ɗaya ne, amma ba ɗaya ba, na Leo Haiza’an, na su Vash Khaiza’an)A gabansa ya tsaya tare da karɓar star ɗin, ya sanyawa Vash a gaban riga, da karfi Vash ya sara mashi kafin su rungumi juna cike da kauna da kewar juna. Daga nan Vash ya bisa suna sauƙa ƙasa dan kara ganin juna. Iyayen Zaysh aka kira a mataki na gaba da su zo. A natse Ummie ta tashi ta nufi wajen, jikinta sai rawa yake yi, dan har ga ALLAH a tsananin tsorace take da sojojin dake wajen, kun san su ko kakinsu mugun kwarjini ne da shi. Tana zuwa ta karɓi star ɗin, da kyar ta iya jurewa, Captain ya nuna mata in da zata sanya mashi! Sakawa ta yi tana ta kallon fuskansa, gabaɗaya yanzu tsoronsa take ji, kwarjininsa ya firgitata, dik ya canza kamar bashi ba. Sara mata ya yi kafin su rungumi juna kirjinta kamar zai fashe saboda tsoro da faɗuwar gaba, take ta fara ruwan hawayen tsantsan farinciki, yau ALLAH ya cika masu burinsu ya zama soja. Daga nan ya bita suka sauƙa ƙasa dan su gana da kyau. Sai daddyn Noor da aka kira, cike da farinciki da alfahari ya taso, wasu jiga-jigan guards suka take mashi baya har zuwa in da Noor yake a tsaye, aka bashi star ya sanya mashi, sannan suka rungumi juna, sai da daddy ya girgiza jin jikin Noor a jikinsa, ya ji namijin gaske, ai a take ya ji zuciyansa ta wastsake, ya ji lallai Noor zai iya wannan Mission ɗin!. Da sauri daddy ya ja shi suka nufi wajensu Aunty Lusi da tin shigowarsu GAT yake ta kallonta, ya ga ƴar kyakkyawa, da alama su Arya zasu samu second mother idan da rabo!Lokacin da aka kira family ɗin Leo Big Bro ɗinsa ya miƙe ya fito sai da kowa ya kallesa ya sake kallah, dan ma dai yana sanye da winter jacket mai ɗan tsawo zuwa gwiwa da ta rufe kakkarfa kuma kyakkyawan surar jikinsa, amma dik da haka an kafesa da idanu. A gaban Leo ya tsaya a dake tare da karɓar star ɗin ya sanya mashi sannan suka rungumi juna. Dik wanda ɗan uwansa ya sanyawa star ɗin nan sai an buga bindiga sama alamar girmamawa!.Kama hannun Leo ya yi suka koma gefe dan ganawa, saboda an gama dik wasu important abin da za’a ayi saura ci da sha, suna da damar ganawa da ƴan uwansu.To mu koma baya kaɗan, tin da su Leo suka shigo hall ɗin nan su V suka rikice. Tana sauke idanunta a kan Noor bata san time da ta miƙe tana faɗa masu su tayata ganin shin da gaske na jikin robar mansu take gani ne ko bashi bane. Arya ce ta jata ta zaunar da ita dan kada ta tara masu jama’a, sannan ta ce shi ne mana, amma ta natsu taga jama’a a nan ai. Da kyar ta natsu, ba ita kaɗai ba har su Angelina da kyar suka natsu saboda gigicewa da suka yi a ganin Noor and Leo, ita kanta Arya ta gigice da ganin Leo, ya kara kwarjini da zarra, da ta kalli face ɗinsa sai da ta sha jinin jikinta, sai da gabanta ya faɗi.Ita kuwa V matsawa jikin Angelina ta yi tana ta faman santin kyan Noor, wai a hoto ma ashe an rage mashi kyau, tuni ta manta da tana son Leo, to taga first love, wanda ta fara so a rayuwanta tin buta wuci 8 years ba, kuma kun san so ba ruwansa da kyau, dik da Leo ya fi Noor kyau ita dai Noor ne ya fara shiga ranta, dama saboda tinanin ba zata samu ganinsa bane yasa ta bada kofar Leo ya shiga zuciyanta.Angelina ɗin ma sai tayata santin kyansa take yi, dik sun rikice, Arya dai tana zaune a natse, tamkar babu abin dake damunta, daga karshe ma ta ɗan yi ƙasa da kai ta daina kallon Leo saboda tsananin sara mata da kan nata yake yi idan tana kallonsa.Bayan an gama karramasu sun koma gefe da ƴan uwansu, manyan baki sun fara cin abinci ne V ta ce. “Angelie ni zan je in gana da love ɗina, ALLAH zan je in yi mashi magana”. Riketa Angelie ta yi tare da cewa. “Baki da hankali ko? Bari daddy ya kamaki zaki sani ne, ai kin san ya hana boys ɗinsa su kulamu, kuma muma ya hanamu kulasu ko?”. Tana turo baki ta ce. “Wannan ba boy ɗin daddy bane, baki ji me aka ce bane? Kwararrun jami’an ESS ne, emagemcy secret service. Dan haka shi ba boy ɗin dad bane”. …….. “Amma ai kin san kowani kaki yana karkashin GAT ne ko?!”. A cewar Arya dake jinsu, ta yi maganar a natse sosai cikin dakewa ga class. Marairace murya ta yi tamkar zata yi kuka, a shagwaɓe ta ce. “Please bloody, ku barni in je in gansa, in ba haka ba zan yi ciwo, ko kuna son in kamu da ciwo ne?”…….. Da sauri suka girgiza kai, har suna haɗa baki wajen cewa a’a basu son ta kamu da ciwo. “To please ku kare mun wajen daddy bari in je in gansa in dawo, two mins kawai”. Da yake suna bala’in son juna sai suka aminta, har da cewa zasu ce da daddy ta je toilet ne, kuma ta yi sauri ya dawo, da okey ta amsa tare da lallaɓawa ta zame jiki ta fice. A lokacin Noor yana tare da Auntys ɗinsa a can waje gefe da hall ɗin, daddynsa kuma ya nemi zama da GAT dan ya ga yadda za’ayi a cire Noor a wannan mission kawai ya koma da ɗansa gida, gara mashi ya je ya yi aiki cikin Us army kusa da gida!.Tin daga nesa ta hangosa kewaye da mata, haba take ta ji ranta ya ɓaci tin ma bata san me alaƙarsu ba, bai ma san da ita ba wai tana kishinsa, har da yin sauri ta kariso wajen. Excuse ta yi mashi a natse. Da sauri su Luna suka kai kallonsu a kanta, shi kuwa Noor yana rike da Auntynsa da yake bi wajen haihuwa watau Aunty Lisa, ya rike hannunta sai hira suke yi, ya yi kewansu sosai, so bai ɗago ya kalli V ba!.Aunty Lisa ta fi kowa saukin kai, da sauri ta ce. “Like wow, fine girl, pleasure look at this beautiful lady, wajenka ta zo ko?”. …… Sai a lokacin ya ɗago ido, kallo ɗaya ya yi mata ya ɗauke kai tare da girgizawa Aunty Lisa kai game da cewa. “No Aunty, I don’t even know her, this is my first time seeing her”. Da sauri Lisa ta saki hannunsa tare da riko hannun V, tana yaba kyanta musamman ash hair ɗinta dake ta faman kyalli, ga wannan na gaban goshi da ya kara fito da kyanta, cike da kulawa ta ce. “Fine girl lafiya?”…… Mamaki ne ya kama Noor ganin har da sake hannunsa ta kama wata, sai ya ja baya tare da komawa kusa da Aunty Luna yana hararar Lisa ta kasan ido, irin like zamu haɗu dake ne, amma bai to magana ba. Ta gansa sarai, amma ta share kamar bata gani ba, saboda ita dai V ta tafi da imaninta….. Jin ya kira su da Aunty yasa V ta ce. “Good evening aunty”…… “Evening my love, kema a nan barrack ɗin kike? Wajen pleasure ɗinmu kika zo ko? Ya sanki ko?”. Cikin rawan jiki take tambayarta, dan tana ganin kamar Noor ya santa kawai kunyansu yasa ya ce bai santa ba. V da tsiya sai ta ce. “Yeah Aunty, he knows me, kuma shi ne ya ce in zo in gaisa da Aunty’s ɗinsa, amma kada na nuna kaman nasan shi, wai yana kunyanku ne”……… Ai a miliyan Noor ya juyo da kallonsa a kanta, ɗan turo baki ta yi, bata ma san time da ta ɗan hararesa ba, sai da ta ga ya waro idanunsa sosai a kanta, da sauri ta yi ƙasa da nata idon kirjinta na bugawa da kari, gabaɗaya kwarjininsa ya rikitata. Wani irin fara’a ne ya bayyana a kan fuskokin Aunty’s ɗin nasa gabaɗaya, dan su suna tsananin son abin da yake so, a tinaninsu yana son V tin da ya ce ta zo ta gaisa da su……… Cike da so da kauna suka jawota jikinsu, Aunty babba watau Aunty Luna ce ta ce. “Pleasure ɓoye mana ita da kake son yi ko?”. …Lisa ta amsa da. “Baka son mu ganta ko?”…… Lusi ta ce. “Gata makurar haɗuwa, zo mu je wajen daddy mu kaita ya ganta shi ma”……… Luna ta sake cewa. “Pleasure gaskiya na yi matuƙar farinciki, gata natsastsiya, a ina ka samota?”……… “Dik ba wannan ba, mu kaita wajen daddy kafin mu dawo mu ji daga in da ya samo ta”. Cewar Lisa. Na’am da hakan suka yi, da sauri suka ja hannun V zasu wuce.Noor da mamakinsu ya hanasa yin magana ne ya yi saurin riko hannun V ɗin dan ya dakatar da su. Sun goge mashi hadda, shi da bai taɓa kallon yarinya ba wai za’a kaita ta gaisa da daddy. Muryansa a sanyaye ga shi yanzu voice ɗinsa ta fashe ta zama lion voice, in a cool way ya ce. “Aunty please stop it, ni fa ban san wannan yarinya ba”. Da sauri Lusi ta ce. “Idan baka son mu kaita wajen daddy ne ma to mun hakura ba zamu kaita ba, amma batun baka santa ba bai ta so ba!”……… Saboda ya dakatar da zancen yasa ya ce. “Okey na ji na santa, ba sai kun kaita wajen daddy ba to”. Fara’arsu ta ninku, fuska cike da murmushi suka dinga yabawa V suna yi masu addu’a kasancewa tare har abada, da ya ga abin nasu ba mai karewa bane sai ya ce. “Ni bari in je wajen daddy”…. Da sauri Aunty Lisa ta rikisa tare da cewa. “Ya za’ayi bakuwarka ta zo kuma ka tafi ka barta, ku tsaya a nan mu bari my je wajen daddy muna zuwa”. Basu jira amsar shi ba, suka wuce gaba. Har sun ɗan fara tafiya Lisa ta dawo da sauri, a kunne ta fara yi wa V raɗa kamar haka. “Kinga ɗan autanmu ne shi, muna ji da shi, ki kula da shi sosai, nasan tin da ya zaɓoki har ya ce ki zo ki gaisa da mu to kin ciri tuta kuma kin fita daban, please kada ki bari ransa yana ɓaci, dan muna son shi fiye da kanmu, anjuma zamu dawo kuma zamu zo har gidanku kin ji?”…… Kai kawai V ta gyaɗa alamar to. Juyawa Lisa ta yi zata tafi Noor ya yi saurin damko gashin kanta, da yake saƙo ne su akwai wasa sosai a tsakaninsu, kuma yanzu ji yake ma shi ne babba tin da ya zama namijin gaske, dama can ya rainata. Buge mashi hannu ta yi tana hararansa kafin ta ce. “Sai ka fara yin budurwa baka faɗa mun ba, bayan ka ce nice zan zaɓa maka mata, zamu haɗu ne, zaka zo ka sameni, ba dan ka yi sa’a yarinyar ma makurar haɗuwa bace ai da na rusa wannan soyayyar, kuma ka kula da ita na faɗa maka”. Ta faɗa tana dallah mashi harara cike da kauna da zolaya kafin ta wuce da ɗan gudunta saboda ya kawo mata damka!.Shiru wajen ya ɗan yi, shi yana kallon ƙasa ita kuma tana kallonsa irin kallon huce haushin tsawon shekaru tana dakon begen ganinsa……. Katse masu shirun ta yi da cewa. “Good evening sir”. Cikin girmamawa ta yi maganar…… Shiru kamar bashi a wajen, hakan yasa ta sake faɗe dan tana zaton bai jita ba. Nan ma shiru bai amsa ba, take jikinta ya yi sanyi, ta ji bahu daɗi, muryanta na rawa, a shagwaɓe sosai ta ce. “Ka yi hakuri da abin da ya faru”. Sai a lokacin ya ɗago kai, kallon tsab yai mata kafin in a cool way can ƙasa ya ce. “Meyasa kika mun karyar cewa na sanki?”……….. Baya kaɗan ta ɗan ja saboda yadda idanunsa suka firgitata, a ƙoƙarinta na ja da bayan ne wayar dake hannunta ta suɓuce ta faɗo ƙasa. Bata kai ƙasa ba yasa kafa ya tareta.Dafe kirji V ta yi, ganin ya tare yasa ta sauke ajiyar zuciya. Tamkar ball haka ya yi jifa sama da wayar sai ya capke da hannunsa, akwaisu da saiti ne sosai. Dawo da kallonsa a kanta ya yi, a dake ya ce. “Answer me, a yaushe na sanki? Meyasa zaki yi wa Auntys ɗina karya har kina ƙoƙarin sanyasu ɓata rai dan na ce ban sanki ba? Wacece ke? A ina kika sanni?”. STAR LADY TAKU CE TA AMANA.🔥


