Story & Written By
Mommyn Fareesa
*Godiya*…. Alhmdllh ala kully halin”tsira da amincin Allah sutabbata ga shugabammu annabi muhammad (S A W)yah Allah yadda nafara lafiya Allah kasa na gama lafiya”Allah yabamu ikon anfana da abinda yake daidai🤲
Gargad’i
Wannan book d’in k’irk’irarran labarine”banyi shi dan wani /wata ba”banyarda acanzamun book ta kowace sigaba”sbd mallakata ne.
Dedicate to all my paid grps 🥰🥰ina yinku totally guys💃🏼💃🏼
*Idan kin karanta kiyi comment, kokuwa bbu zancen cigaba”idan anji shiru karma Ayi jaje*😉😉
BISSIMILAHIR RAHAMANIR RAHIM
🅿️1&2
*Key stone bank Kaduna state*
……da misalin k’arfe 10:35 am”zaune suke kan kujeru, kowa na harkan gabansa”masu bin layin bud’e acc da wad’anda za’a yiwa gyara a acc nasu”duk suna zaune wasu atsaye”yarinyace y’ar kimanin shekara 15 zuwa 16″aduniya”sanye take da hijab har k’asa da wasu takalmi fashion a k’afarta”tana d’auke da wata baby girl”da zatayi shekara guda aduniya”agefenta wata yarinyar mace ce “shekarunta basu wuce 35″tana sanye da fararen kaya na nurses ajikinta…..
Duba agogon dake d’aure atsintsiyar hannunta tayi ta yatsina fuska tace”.gsky Aysha nagaji da jira wlh”
nima haka anty”kusan awarmu 2 fa”kodai muje waje da zainab kartayi kuka?”
kafin matar tayi mgn”wani sanyayyan k’amshi yadaki hancinsu”yacika wajen”Aysha ta d’ago kanta da sauri”idanuwanta suka hasko mata wani had’add’an hand some guy”
Dr sadeeq kenan!yana sanye da suit bak’ak’e ajikinsa”sunyi matuk’ar haska chacoolet colour d’insa”fuskarsa ad’aure bbu annuri yadad’e da bak’in glass”directly k’ofar dake bud’e ta glass suka shiga,shida wasu mutum biyu dake binsa abaya”suka nufi inda ma’aikatan bank d’in suke…
da mamaki Aysha ta kalli anty murja tace”.dubifa anty zaman awa nawa mukayi?”shi dg zuwa zai wani kama shiga ciki”tanata wani shan k’amshi.
Allah yakyauta kawai tace”.sbd a asibitin dr sadeeq anty murja ke aiki”tasan halinsa sarai.
hangowa Aysha tayi ta glass yama zauna suna mgn da ma’ai katan.azuciye ta tashi da zainab ahannunta ta kutsa kai ciki”
gaban anty murja na fad’uwa tadinga kiranta”amma ta mata banza”da hanzari tabi bayanta.
babu ko sallama Aysha ta kutsa kai ciki”waye kai mlm dazakazo kamana cin layi?”wannan adalcine ku kuma kukeyi ko zalunci?”tafad’a tana murgud’a d’an bakinta…..tana kallon su”tunda tafara mgn dr sadeeq beko kalli gefen datakeba”wani cikin ma’aikatan yace”.kiyi hak’uri yarinya zakishigo amiki komai yanzun”
tab’e baki Aysha tayi tace”.to gsky saidai wannan yafita idan angama damu saiya shigo”tafad’a tana kallon dr sadeeq”
Kallonta kawai P’A d’insa keyi”azuciyar sa yace”. Lallai yarinya na tausaya miki bakisan waye both ba”
Ke Aysha !zo mana”cewar anty murja dg bakin k’ofar”
gsky anty bazanzoba” kishigo muyi abinda yakawomu kawai”shi wannan nakeso yafita yawani share mutane.
yatsina fuska dr sadeeq yayi kamar yaga kashi yace”. you are very stupid! yafad’a cikin cool voice”fuskarsa amatukar d’aure yajawo face mask yarufe hancinsa”
se wani mazurai kakeyi bayan kaci mana layi….ke Aysha banace kizo ba?sa’an kine?dan Allah dr kayi hak’uri”tacika shirme da k’uruciya”anty murja tafad’a cikin fad’uwar gaba”sbd tana gudun kar yakoreta a asibitin sa.
Uffan dr sadeeq beceba”saima yayi kamar badashi takeba”anty murja ta fisgo hannun Aysha suka baro gurin”
Dr habib(aminin dr sadeeq)yadaiyi shiru yana ganin k’arfin halin y’ar tatsitsiyar yarinyar datake son shiga gonar abokinsa.
zuciyar dr sadeeq na zafi ya kalli dr habib da P’A d’insa ya mik’e tsaye”
basuce komaiba suka bishi abaya”yanajin dole yatuhumi murja wacece wannan k’aramar marar kunyar yarinyar ?”da har zata nemi tashigar masa hanci yabarta”
suna fitowa suka shige mota”jefi jefi dr sadeeq yayi tsaki”dama dalilinsa na zuwa”acc nasa baya transfer”dukda acc 2 garesa”to na nan” shine keda manyan kud’ad’ensa ne aciki”gaba d’aya damuwa tamasa yawa” ga wannan yarinyar marar tarbiyya zata k’ara masa da wata”
ringing d’in wayar dr habib yakatse masa tunani”dr. Habib na murmushi yace”.mutuniyar ce takirafa abokina”
Tsaki dr sadeeq yaja yace”.kaga mlm tun muna girma da arzik’i dakaj karabu dani da zancenta”
wane irin nacine wannan haka?”meyasa matan yanzun bbu tarbiyya wai?”
karkaga laifin sady abokina “kasan tana son….. earpiece dr sadeeq yasaka yatoshe kunnansa”
Dr habib yagirgiza kansa yana dariya yana mamakin tsaurin ra’ayi irin na abokinsa”
gida zaka ajiyeni”saika ajiyesa asibiti”yafad’a batare daya kalli driver d’in ba .
yaya jikin ammin wai?”da sauk’i sosai”muje naduba jikin nata”
Kai tsaye anguwar sarki suka nufa”,abakin get d’in wani katafaren babban gida”P’A d’in dr sadeeq yayi horn”
bayan anbude musu get, yadanna hancin motar aciki”suna fitowa suka wuce ciki”
masu aikine kawai a main parlou sunata goge goge”kasancewar time d’in be wuce 11am”
sashen ammi suka wuce”honorable lawal da ammi na kan kujera”ita tana kwance kamar gawa”shikuma yana zaune”yadda dai take tun samun lalurarta tsawon wata 3 kenan”sai hindatu (k’anwar dr sadeeq)tana zaune kan carpet tana matsawa ammin k’afafuwanta”
Kallo d’aya dr sadeeq yayi wa honorable lawal yad’auke kansa”fuskarsa bbu wata walwala”
yaya sannunku da zuwa”bece komaiba dr sadeeq ya zauna”sbd haushin hindatu yakeji”sbd ta zab’i aure akan ta zauna tayi jinyar mahaifiyarsu. dr habib kawai ya amsa mata”yamata yamai jiki”sannan ya gaisheda honorable lawal daketa wani cin magani….
Dr sadeeq yakalli ammi ya matso yakama hannun ta”k’wallah tacika idonsa”ammi yaya jikin naki?”yafad’a yana kallon ta”idanuwanta ta bud’e”ta kalli dr sadeeq ta kalli honorable lawal”
Atake dr sadeeq yahad’a rai”sbd yafahimci nuni take masa yagaishesa”
shifa harga Allah tunda daddynsa yarasu amminsa ta auri mutumin can hankalinsa be kwanta dashi ba….
Tashi tsaye honorable lawal yayi beyi mgn ba yabar parlourn”
Ammi ta rufe idanuwanta”duk maganar da dr sadeeq kemata tak’i bud’e ido.
Dan Allah yaya sadeeq kayi hak’uri kadena fushi dani”cewar hindatu”
Kallo bata isheshiba yatashi tsaye yashige wani d’aki”bbu jumawa yadawo ya d’auki ammi yashiga ciki da ita”
Dr habib yayiwa hindatu sallama yafita,da nufin yajira dr sadeeq a mota…..
*wanene dr sadeeq*?
Dr sadeeq kenan!matashin saurayi mai jini ajika”d’an kimanin shekara 38 zuwa 40 aduniya”
Mai tashe da wayewa da ilimin da Allah yabashi”shiba fari bane” bakuma bak’i bane”wankan tarwad’a ne”(chacoolet colour) colour me wahalar samu”cikakken bafulatanin uzuli ne gaba da baya.suman nan tasa tasha gyara ,tayi bak’i k’irin tanata k’yalli”hakama sajen daya zagaye fuskarsa yyi luf gwanin sha’awa”dr sadeeq yahad’u ta ko ina”dogone bai cika jiki sosai ba”amma k’arfaffa ne”jikinsa amurde yake”irinsu dr sadeeq akema lak’abi da 1 in 1000….lolx”miskiline nabugawa ajarida guy d’in”yakammala karatunsa na likitanci ak’asar Cairo”
Dr sadeeq mutum ne shi me kaffiya da ka’ida”yanada tsatstsauran ra’ayi”beda surutu,kuma bayason surutu”ko mutum mai mgn”da yawan jama’a nacewa basusan dariyarsa ko murmushin saba.any time fuskarsa ad’aure take”saidai yanada tausayi da taimako”mutum ne shi wanda yasan darajar iyayensa”yana matuk’ar k’aunar amminsa da tsananin kyautata mata da yimata biyayya….
Abubakar Aliyu !shine sunansa”mahaifinsa Alh Aliyu d’an asalin jihar yola ne da mahaifiyarsa hjy Aysha”neman kud’i yakawosu anan Kaduna da zama”kowa nasu na yola”amma mahaifiyar Alh Aliyu tarasu”
Sadeeq shine d’ansa na fari”sai ibrahim”wand a befi 2 yrs ba da haihuwa yarasu”sannan auta hindatu”suna son juna sosai Alh Aliyu da family nasa”shahararren me kud’i ne Alh Aliyu”yanada gidajen man fetur da companinnika”bayan sadeeq yakammala karatunsa na likita” yagina masa asibitin sa”ayanzun shekara 1da wata 5 kenan da gina asibitin”Alh Aliyu kuwa shekararsa guda cif da rasuwa”wanda bbu abinda yasameshi”kawai da safe aka ga gawarsa.sannan kuma amininsa honorable lawal ya aure matarsa hjy Aysha “wata 2 da auren takamu da cutar paralise”ayanzun wata 3 kenan….. fad’in tashin hankalin da dr sadeeq yashiga b’ata bakine”akan abu 2″mutuwar daddynsa ,da rashin lafiyar ammi”sannan kuma saida ammi tace”.idan be amince ta auri honorable lawal ba zata tsine masa”sannan ya yarda”amma ko kad’an be k’aunar auren”hakan yasa ko ganinsa sadeeq besonyi….sannan yahad’a duk wani dukiyarsu ya adana yana ankare da komai nasu”yasaka mutane da ya yadda dasu su kula da komai”shikuma yana asibitinsa.ko yanzun ammi ce keso yatura wa honorable lawal million 5 ta acc”shine yaje bank sbd acc d’in baya transfer.
Allah yayiwa dr sadeeq farin jinin y’an mata”akwai course mates nasa, da y’ay’an dangi, da k’annan abokansa,duk da suke cewa suna sonsa”amma be amsawa”hasalima shi yatsani soyayya”acewarsa b’ata bakine da lokaci”balle ayanzun damuwarsa ciwon mahaifiyarsa”,har India sunje last 3 weeks amma bbu sauk’i”saidai kashe kud’ad’e da akeyi”dukda matsayin dr sadeeq na likitan mata”amma yakasa gane matsalar amminsa”
Da yawan wasu matan lafiyarsu qlau suke zuwa asibitinsa sbd kawai suganshi suke zuwa.
Dr sadeeq beda amini daya wuce dr Habib”sai kuma dr Abbas”duk acikin asibitin sa suke aiki”amma sunfi abota da dr habib”sbd shi tun primary skul suke tare dashi”dr habib yanada mata”amma dr Abbas beda mata”kamar dr sadeeq”har daddynsa yabar duniya yanaso yaga yayi aure”shi kuwa aganinsa bbu wacce tamakai aji ko matsayin dazai sota da zancen soyayya”wacce yakema kallon b’ata time……
Ab’angaren Aysha da…✍️
Comment kawai guys yazo da sabon salo🤣
Idan banga zazafafan sharhi ba bbu nadare karma Ayi jaje😎😎🏃🏼♀️🏃🏼♀️
Dr sadeeq book 1 free ne🤙
Mom fareesa🖊️