Halysaah Page 38 By Khaleesat Haydar
Gaisuwa da fatan alkhairi zuwa ga Deejah me sana’ar lamurje da ganja, tare da Aunty Amzaj Maman mara Jidda da Damsalele, Uwata Zeenariya kema an gaisheki da babban murya tare da Hajiya Safiyyah Usman me kantin kayan yara😁 Aneesah Zero zero da Ummi matar mijin uwar gida ku ma na gaisheku da siririn murya, Barrister Inna da ‘ya ta Uwar Annur da Hajiya Sadiya Uwar Hanan kuma duk na gaisheku da fatan alkhairi, Hajiya Sadiya Chamo au banda ke🙄, Mom Asas, Maman Faruk me data, da Sis Aisha Dalhat ga kuma Maman Aisha da Hajiya Bilkisu duk Khaleesat na maku fatan alheri 💖 Sai bayan da aka yi sallan Magrib Umma ta bar gidan Baaba Gaje da yan biyun ta, kuma har ta bar gidan Gaje bata nuna ta taɓa saninta ba don casually ma take amsa mata kamar yanda take ma kowa da ya shigo mata jaje, Umma dai a sanyaye ta baro gidan, tana isa gida taga mutane tsattsaye a kofar gida kowa da abinda ke fitowa bakinsa, sosai taji gabanta ya fadi gashi ta kasa fahimtar akan me ake ta surutu haka, can dai ta dubi wata makociyarsu dake tsaye wajen tace “Munnira me ke faruwa?” Munnira tace “Wallahi Umman su Khaleesah nima fitowa ta kenan da naji hayaniyar tayi yawa, amma wai kamar wasu mutane ne da ba a san ko su waye ba suka shiga gidan naku suka yi aika aika, ance a katuwar mota suka zo….” Umma ta kasa cewa komai tana kallonta, da kyar take jan kafa tana rike da su Islam ta shiga gidan har sannan gabanta bai daina faduwa ba, Su Mama Shatu da Mama Zubaida ta gani tsaye da ‘ya yan su duk sun yi cirko cirko a tsakar gidan da makota ana ta maida magana, tsakar gidan dai cike yake da jama’a kowa na fadin albarkacin bakinsa, Umma ta dake tace “Wai me ke faruwa ne a gidan?” Mama Zubaida ta wani kalleta a walakance tace “Ina kuwa za mu san me ke faruwa tunda mu dai muna zazzaune sai ga wasu kattin gardawa sun kusa goma babu annuri a tare da su sun shigo mana gida da makamai suna tambayar dakin Malam, basu tsaya iya dakin Malam ba hatta sauran dakunan gidan nan sai da suka shiga…” Sai a sannan Umma ta lura da bakin kofar shiga dakin Malam Ali, gaba daya yayi kaca kaca da takardun da ta mayar daxu bayan su Jay sun dau wanda za su dauka, har kayan cikin dakin sai da aka watso su waje har da er katifarsa da akwatin kayan sakawan sa da butar alwalansa, Umma ta juya tana bin tsakar gidan da kallo taga har dakinta an fito da kaya an yi watsi da su waje, da kyar Umma ta karasa kofar dakin Malam Ali ta leka ciki taga basu bar komai ba, dama ba wasu abun kirki ke cikin dakin ba, can ta juya tana kallon Kishiyoyinta amma ta ma rasa me zata ce, Mama Shatu ta kyabe baki tace “Ni takaicina dakunan mu da suka shiga wai ina takardun da Malam ya ba mu ajiya, ni ko nace mu muka san wasu takardu mu da bamu yi karatu ba ta yaya Malam zai bamu takardu mu ajiye ai sai dai ko ya ba er sa da aka kai turai karatu daga karshe tayi ma wanda ya kai ta karatun butulci wai bata son sa kuma, amma ina mu ina ajiyar takardu mu da muke jahilai” Umma bata tanka ta ba ta duka tana tattara takardun dake watse bakin kofar su Islam suka je suna tayata, a haka duk ta maida kayan Malam Ali cikin dakinsa, su Mama Zubaida sai hararanta suke, can Mama Shatu ta kyabe baki tace “Mu dai mun san ko ma wani takarda suke nema bazai wuce yana da alaka da er ki ba kilan kotu za a shiga, tun da kika haifi yarinyar nan muke shiga jarabawa munana a gidan nan, ko kuma muce tunda aka auro ki, mu da bamu san wani talauci ba balle wahalar rayuwa, daga auro ki karayar arzikin da ba a taɓa yin irinsa a tarihi ba ya samu Malam, sannan gashi sanadin er da kika haifo ga abinda ya samu Malam a karo na biyu, daga ke har ‘ya yanki babu wani abun alkhairi a tare da ku sai masifa, ina ma Malam zai yada kwallon mangwaro ya huta mu ma mu huta ki tattara ki koma can kasar ku ki auri buzu ɗan uwanki” Sha’awa dake tsakar gidan wanda tana daga cikin mutanen farko da suka shigo bayan Mama Zubaida da Mama Shatu sun kurma ihu, amma fa sai da gardawan suka fita sannan suka samu bakin ihun neman agaji su da yaransu, Sha’awa tace “Haba Mama Shatu, wannan wani irin magana ce kike yi haka don kin ga Ummansu Khaleesah bata tanka ku a gidan nan, wannan ai cin fuska ne, kar fa wataran ku kureta ayi dauki ba dadi a gidan nan, don mai hakuri bai iya fushi ba wallahi” Wani zagi Mama Shatu ta kundumo mata a fusace, Sha’awa ta rama tace “Wallahi ba dai ubana ba, sai ko in naki uban me gyaran keke dake kabari” Ganin fada na kokarin kaurewa a tsakar gidan Umma da wasu mata suka fitar da sha’awa dake kunduma ma Mama Shatu zagi ta uwa ta uba, ga su Labeebah na kokarin dambe da Sha’awa dake zagar masu uwa su ma duk aka rirrike su, a haka dai aka fitar da Sha’awa dake gyara daurin zaninta da ya kusa faduwa gashi babu komai kasan zanin, tana huci take cewa “Shegu en kutumar uba masu bin bokaye, ko jiya sai da aka bani labarin kun je wajen wani boka na kuma san warce ta raka ku, kun ga kuwa Umman Khaleesah ta fi ku ko a wajen Allah tunda bata san hanyar zuwa gun Malamai ba” A haka dai aka fitar da Sha’awa daga gidan, Umma dai jiki a sanyaye ta tafi kofar dakinta ta tarar su Islam suna ta maida kayan cikin dakin da aka watso waje bayan sun kunna er fitilar dake ba dakin hasken, Noor na kallon Umma tace “Umma kinga babu kayan abincin a inda suke” Umma ta kalli inda Maman Salame ta ajiye mata kayayyakin abincin da su Jay suka kawo taga wayam, tsayawa tayi tana kallon wajen babu ko kiftawa tsabar mamaki yasa ta kasa cewa komai, muryar Nenne taji a tsakar gidan cikin fushi tana cewa “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, meye haka aka cika gidan nan kamar ana taron farin ciki? Ku yan unguwan nan tsabar munafurci da gulma bakwa tashi shigowa sai iftila’i ya faru sannan ku bi ku cika ma mutane gida ko wacce da warin jikinta, farin cikin iftila’in ku ke ko menene haka? Doo Allah duk ku fita ku ba mutane waje mu ji da daya, ai ba kanmu farau ba, en iska kawai magulmata” Rai bace ta nufi dakin Umma hannunta rike da jarkar manja daya hannun kuma rike da tocilan ta, ta tsaya daga bakin kofa tace “Zahra’u me suka dauka a dakin Alin da suka zo?” Umma da ta zauna gefen katifar ta tace “Shigowa ta kenan nima Nenne, na je gidan Baaba Gaje an sakota daxu da yamma” Nenne ta kalli kayan da su Islam ke shigarwa daki tace “Har dakin naki suka shiga ne? To ni Usama ce min yayi iya dakin Ali suka shiga suka watso kayan ciki, ke kuma wa ya watso naki tsummokaran waje?” Mama Shatu tace “To shi da ya sulale ya gudu ya bar gidan ta yaya zai ce iya dakin Malam suka shiga? Ai babu dakin da basu shiga ba a gidan nan yau, mu ma duk mayar da namu kayan mu ka yi, hatta babban jarkan mangyada da na siya jiya sun dauke, iya shi suka dauka a dakina, Ita kuwa Zubaida kwashin adashin da aka kawo mata suka dauke” Nenne ta fara matsar kwalla cikin rawan murya tace “Lallai na ga abinda ya isheni bai ishi Ubangijina ba, to yan fashi Awdul din ya aiko mana wannan karan? Don dai duk mun san yafi karfin wani kudin adashin da bai taka kara ya karya ba balle wata jarkan mangyada, Allah mun gode maka da wannan rantsattsiyar jarabawan da mu ke ciki mun gode maka Allah, Alhamdulillahi ya Allah, Ina ga in ba tattarawa muka yi muka hakura da zaman birni mu koma kauye gaba daya ba muna cikin mummunan hatsari a Mariri gashi ba mu da gata, kar wataran cikin dare mun saki baki muna bacci su babbake mu, su babbake banza tunda babu me tsaya mana” Ita dai Umma tayi shiru bata ce komai ba, Nenne na kallonta tace “Su kuma samarin da suka sha uban fararen kaya suka zo mana nan suna kwambo dama yaudarar mu suka zo yi bamu sani ba, sun zo nan sun gama cika mana baki sai gashi tunda suka karkade wandonsu suka fita bamu sake ganin keyar su ba, to ina amfanin karya? har da ce min za a saki Ali kwanan nan ashe duk yan iskan gari ne makaryata bamu sani ba” Umma dai kallon Nenne kawai take, Nenne ta mika ma Islam jarkan manjan hannunta tace “Ba ruwana, wahalan da nake ta sha kan Ali ko shi ya halittoni duniya ai sai haka, kai kenan kullum ayi ta garkame ka kamar kasungumin barawo, sai kace wanda yayi ma Allah wani saɓon da bamu sani ba, saura kadan kwale kwalen da na hau jiya zan je nema masa taimako ya kife da mu banda Allah ya tsare, to ina dalili bayan ba shi kadai na haifa ba, in ya kasheni sauran su yi yaya? ke ungo amsa ki mika ma uwarki ta tsiyaya min manja, nawa ya kare” Islam tace “To ai an kwashe kayan abincin gaba daya Nenne” Nenne ta gwalo ido tana kallon direction din da aka ajiye kayan abincin taga wayam, bude baki tayi tana kallon Umma tace “Zahra’u ina kayan abincin? Ko kasuwa ki ka kai kika siyar? Fatarar taki ta kai haka Zahra’u?” Umma tace “Saboda me zan kai kayan abinci kasuwa in siyar Nenne, daga zuwa gidan Baaba Gaje in dawo nima na tarar an kwashe kayan abincin” Nenne ta ajiye jarkan hannunta a kidime ta saki salati tana tafe hannu tace “Baki kulle dakin bane Zahra’u?” Umma tace “In zan fita ai ina sa ma dakina kwado, to fasa kwadon aka yi, ga makullin ma a jakata” Nenne ta juya ta fita daga dakin dai dai shigowar Usama wani almajirin Malam Ali dake tare da shi tun yana da arzikinsa, kuma har yanxu dai yana tare da shi, Nenne na haska sa da tocila tace “Yauwa Usama kace iya wani daki mutanen suka shiga a gidan nan?” Usama yace “Iya dakin Alhaji kawai suka shiga” Nenne bata sake cewa komai ba ta nufi dakin Mama Zubaida don yafi kusa da ita, tana dage labulen dakin ta fara haske hasken tocila, sai kuma ta duka karkashin gadon karfen dake dakin ta hango carton din indomie biyu an tura su can ciki, ta kwalo ma Usama kira ya karaso da sauri tana haska masa karkashin gadon tace “shiga ka jawo min kwalayen taliyar yaran can” Ai ko ya shiga ya kwaso su ya fito da su, Nenne ta shiga cikin dakin tana duba bayan kyaure nan ma taga Babban jarkan man gyada ta sa Usama ya fiddo waje, ta gama duba dubenta a dakin bata ga wani kayan abincin ba sannan ta nufi dakin Mama Shatu, a bayan kyaure taga buhun shinkafa daya da quarter an lullube da zani, ta kwalo ma Usama kira shi ma ta saka ya kinkimo su ya fitar waje, a dakin Mama Shatu still taga kwalayen taliya da na maggi da jarkan manja duk ta sa Usama ya fiddo su waje, Nenne na kallonsa tace “Kwashe su ka mayar dakin Zahra’u Usama” Yace “To Nenne” Sai a sannan Nenne ta juya tana kallon su Mama Shatu da suka yi wuki wuki da ido ko wacce na kokarin diban ruwan alwala a buta, Nenne tace “An dai yi asara duniya da lahira, barayin banza barayin wofi, tirrr da halin ku, wato ga sabon jarin kayan abinci kun samu ko, tunda Zahra’un ta maida kanta er wahala warce bata san ciwon kanta ba, da ban ce a tsam min manja ba shiru zata yi maganar ta bi rariya ta bar ku da haram, ko zama da ku kadai ya isa ya dinga jefa Ali a masifa iri iri, ai ba kyau zama da jahilai shine kawai bai gane ba” Daga haka ta juya ta koma dakin Umma. Khaleesat na bakin pampon dake compound din Aunty Farida tana wanke wanke, ita kadai ce a gidan gaba daya don duk sauran tenant dake gidan sun fita aiki, Aunty Farida kuma ta tafi kasuwa, juyawa Khaleesat tayi jin an bude gate, ta mike tsaye tana kallonsa, murmushi ya sakar mata ya rufe gate din ya karaso cikin compound din shi ma yana kallonta, ta sauke idonta a hankali tace “Sannu da zuwa” Yace “Good morning Halysaah” Ɗan murmushi tayi ta sunkuyar da kai ta gaishesa sannan ta juya ta tafi ta bude masa kofar shiga parlon Aunty Farida tana kallonsa, yace “Aunty fa? ina ta kiran wayarta no response” Khaleesat tace “Eh ta bar wayar a gida ne ta tafi kasuwa” Ya kalli plastic chair dake veranda din Aunty Farida yace “Let me seat here ba sai na shiga ba, i just came to check on you” Khaleesat ta sauke idonta a hankali tace “I really appreciate Housemate” Yace “To ki zauna mana” Ta kalli second chair din dake wajen sannan ta zauna, sake gaishesa tayi da ladabi tana kallonsa, yace “Lafiya lau Halysaah, how is ur body?” Tana wasa da gefen karamin veil din jikinta tace “Naji sauki” Yace “To amma naga kin rame, baki cin abinci ne?” Tayi shiru, yace “Baki ci ko?” Ta ɗan yi murmushi tace “Ina ɗan ci kadan” shiru ne ya biyo baya for almost 30 seconds, ta ɗan daga kai ta kallesa taga kansa a kasa, ajiyar zuciya ya sauke calmly yace “Everything will be alright soon in sha Allah Housemate” Nan da nan hawaye ya cika idonta, da kyar tace “But i don’t know my mom’s condition, i am really worried” Jay yace “Don’t worry, Umma tasan kina nan, mun je can gidanku da Ajay, i assure you everything is fine back home do not worry ur self pls, yanxu dai we are working on clearing ur dad first before anything, soon in sha Allah he will be free from the debt” Hawaye na sauka idonta tace “To amma ni bazan iya zama da Abdul ba tsoron sa nake wallahi, kawai torturing dina zai yi yayi revenging abinda nayi masa, i am afraid” Jay yace “Do not be Housemate, we won’t allow that happen in sha Allah, we will go to any extent na ganin hakan bai faru ba” Khaleesat dai tayi shiru tana share hawayen idonta, after some seconds yace “Baki tambayi Ajay ba?” Ta daga kai tace “Na zata tare ku ke yana waje” Jay yace “Not at all yana kano, bai ma san nayi tafiya ba, i took an early morning flight, zuwa 12 noon kuma zan koma kano in sha Allah, i just came to check on you” Khaleesat na kallonsa cikin sanyin murya tace “Nagode sosai, kuma naji dadi” Ya kalli agogon wrist dinsa dake nuna karfe sha daya saura yace “I will be leaving for the airport now kar inyi missing flight dina, kafin Ajay yayi noticing i am not home ya fara damuna da kira” Khaleesat tace “Ko ruwa baka sha ba, ko in kawo maka shayi? Kilan ma baka yi breakfast ba ko?” Da damuwa tayi tambayar tana kallonsa, Yace “No i am okay Housemate” Wayarsa ne ya fara ring ya ciro yana kallon screen din yayi murmushi sannan ya nuna mata screen din taga Ajayn ne ke kiransa, mayar da wayar yayi aljihunsa sannan ya fiddo 100k ya mika mata yace “In case you need anything Halysaah” ta girgiza masa kai tace “A’a Nagode, bana bukatar komai wallahi” Mikewa yayi ya ajiye mata kudin a kafarta ya fita daga balcony din yace “Take care of ur self Housemate, idan na sake samun lkci ko zuwa nan da few days ne zan dawo in sha Allah, my regards to Aunty Farida” Khaleesat ta mike tana kallonsa ta kasa ce masa komai wasu sabbin hawayen suka cika idonta, ya daga mata hannu kawai ya nufi gate don bai ma son ganin hawayen nata, tana kallonsa har ya fita sannan ya rufo gate din, parlon Aunty Farida ta shiga ta zauna kan kujera ta rufe fuskarta tana rera kuka tana shessheka….. Bayan few weeks na zirga zirga a cikin garin kano, da kuma zuwa court lauyan su Jay yayi Succeeding na amsan Bail din Malam Ali, afterward suna sa ran kotu tayi dismissing claim din Alhaji Musa saboda previous debt forgiveness dake kasa, a kuma yi masa imposing monetary sactions for abuse of process, all this weeks Jay da Ajay where so cautious of der movement in kano and they were at alert In case of necessity ko kadan basu ba Abdul chance din yi masu ba zata ba cause sun san bazai rasa informant a unguwan ba, ranan da suka yi dropping din Malam Ali a gida bayan kotu ta bada bail dinsa farin ciki gun iyalinsa da wasu yan unguwan ba a cewa komai barin ma Umma, sai shigowa gidan ake ana taya sa farin ciki, shi ko Malam Ali har kasa ya duka cikin ladabi yana gode ma Jay da Ajay, shi dai Ajay ya juya ya koma jikin motarsa ya tsaya ya rungume hannu, ga motar escort dinsu a bayan motar tasa, Jay har ya gaji da ce ma Malam Ali ya dena masu godiya, Calmly yace “Don Allah Baba ka dena mana godiya, mu saboda Allah muka yi…” Malam Ali na gyada kai yace “To… to…to wannan gaskiya ne, Allah Ubangiji ya maku albarka, Allah ya saka da alkhairi, Allah ya kara daukaka, Nagode Nagode” Duk a birkice yake godiyan, Mama Shatu ta dauko tabarma ta shimfida tace “Taho ka zauna ka huta ko zaka dawo seti Malam, naga duk a firgice kake” Nenne ce ta shigo unguwan bayan wani almajiri yaje har gidanta ya sanar mata Malam Ali ya dawo, mayafin nata ma a baibai ta yafa ga dankwali da ta kima a kan mayafin tana hade hanya ta taho gidan ɗan nata, bata kula da Ajay a kofar gidan ba ta shige ciki da sauri, Ajay ya ciro wayarsa dake vibrate a aljihunsa yana duba me kiran sa, gyara tsayuwarsa yayi yana kallon screen din wayar babu ko kiftawa ganin Aunty Farida ke kiransa, haka kawai yaji zuciyarsa ta harba don Aunty Farida bata kiransa all this while, in ma da wani abu shi ne ke kiranta, ya kalli Jay da ya fito daga cikin gidansu Khaleesat, har sannan ya kasa daga kiran Aunty Farida.*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788 👈🏻, it’s better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*Akwai wani abu da yake iya faɗakar da tunani tun daga nesa…Wani ƙamshi da yake sa zuciya bugawa da sauri…Wani ɗanɗano mai narkar da zuciyar masoyi…Wannan shi ne ƙamshin *Scent Palace**Scent Palace*, da ke cikin birnin Gombe, shine gidan turaruka na musamman da ke kawo muku turaruka masu inganci daga cikin gida da waje masu ɗorewa, masu daɗin shaƙa, kuma masu burgewaIdan kina son turare da zai saka masoyinki ya ƙara zurfafa soyayyarsa gare ki ko kuma turare da zai sanya ki zama abar misali a wajen jama’a to *Scent Palace* shine mafita.Abubuwan da muke da su sun haɗa da:Turaren jiki (body spray/perfume) na mata da mazaTuraren gida da ɗakiTuraren motaTuraren wuta na gargajiya da zamaniEid Gift Boxes an tanada musamman domin ku da masoyankuMe yasa *Scent Palace*?✔ Ingantattun turaruka daga ƙasashen waje✔ Farashi mai sauƙi da rangwamen Sallah✔ Kyaututtuka da aka shirya cikin kwali na alfarma✔ Nationwide delivery *Scent Palace* ba kawai turare ba ne ƙamshi ne da ke ƙarfafa soyayya, daɗi, da kimaTuntube mu yau don odar ki:📍 Gombe📞 08038888936 Instagram/Facebook/WhatsApp:08038888936,08154812224*Scent Palace* Ƙamshin da ke bayyanar da ƙima! Ƙamshi ba wai kawai ƙamshi ba magana ce ta zuciya
