Gargadar So Chapter 73 By M Shakur
Wajajen 7:30 aka gama kamun su hafsa kanninta da Khadija wanda sune suka dawo best ladyn Hawwa suka kaita jeep ganin Khaleel na cikin jeep din yasa tahade fuska ta shiga ta zauna suka rufe kofa suka wuce tasu motar, Driver yaja motan Khaleel yakai hannunshi zai kama hannunta dayasha lalle ta dauke hannun dasauri maida hannunshi yayi back sai kawai yaciro wayanshi yataho inda take yawani jawota zuwa jikinshi yamusu hoto tana turomai baki sannan yasaketa yace “lemme post it on insta all those girls Susan I’ve been taking ga yar sandan data kwance musu ni” hararanshi tayi shima bai kulata ba ganin kumbure kumbure takeyi kiris take jira so he’s going to be patient daga gobe ne on Saturday ware haka an kawomai ita gidanshi har gida sukaje da kanshi ya sauko yabude mata mota yamika mata hannu danta rikeshi ta sauko sabida gown nata ta kabar da hannunshi ta sauko ahankali abinta tawuce shi tai cikin gida yabita da kallo dakinta tawuce Ammi kadai ne tana kwasan some jakan gifts ganinta yasa tace “kun dawo Amaryana” adan kunyace ta sauke kanta kasa tace “Ammi zip” ijiye bags din tayi tazo tashiga jamata zip tana kwance mata head tace “Hawwa Khaleel na miki matsanancin so kinga hakan kuwa?” Shiru Hawwa tayi tashiga cire kayan tana mamaki inasu Noor dasu Ramla da Miemie, Ammi tace “suna gidan Malam Sama’ila wajen yammatan gidan wai harsunyi kawaye, bari na sallami baki na” Gyadamata kai Hawwa tayi tana mamakin duk inasu Hafsa wannan da dakinta is empty.A uwardaka duka suka zagaye mahaifiyar tasu dake zaunw abinta tana duba wani azkar, daga Aminu har Hafsa, Kadija da Rahama Mimie ce kawai babu wajen suma sabida yarane. Anatse Aminu yace “Umma this is your last chance akanme zaki rike Hawwa aranki kan abinda ba itane tamiki ba? Bata duniya akayi? Ni aganina koma menene mahaifiyarta tamiki base on abinda yarinyar nan tamana yaci kin hakura kin yafemata, Umma school dina kap zuwa yau dana gama Hawwa ce babu kwandalan Baba, gasu Khadija, Hafsa da Rahama su basuyi university ba amman Hawwa ce ta aurar dasu Baba baida ko sisi kudaden Hawwa ne akayan dakinsu, banda haka akai akai take turamanakudi takirasu ta tambayesu yaransu, Mama kinga makarantan masu kudi da Miemie keyi Hawwa ce Umma menene wannan abun wannan wani irin tsana ne eh Umma” ahankali Hafsa tace “Umma dukanmu yaranki mun hadu yau muna miki fada muna nuna miki gaskiya bazaki dauka ba?” Khadija da duk tafisu zuciya tace “kai wlh Umma Allah karya bani bakar zuciya irin taki” dasauri Umma ta kalleta saikuma tafashe da kuka tace “ohh nice mai bakar zuciya ba Mahaufitae Hawwa data rabani da baban ku ba, nakasa auruwa sai bayan tarasu yadawo yawani aureni kuna cemin kaza kaza, ina mahaifiyarku baku sona kin fison Hawwa shikenan na barkı da Hawwa gaku ga ita kufitarmini daga daki” shiru Aminu yayi saikuma yace “shikenan Umma bazamu tursasaki kiyi abinda bakiso ba, kituna Allah yana tareda masu hakuri, sannan Allah baya kama laifin wani da wani, banda haka Umma shi Allah yanada adalci” yawuce yafita, su Hafasat suka bishi abaya dakin Aminu duk suka shiga.Hawwa na zaune kan dadduma tareda Noor sun idar tana koyama Noor azkar yarinyar is 4 amman wai bata zuwa islamiyya sannan babu mai koya mata agida, Baba kuma na hira da Ammi da Dado da Anty Lami Miemie da Ramla basa dakin sallama akayi Aminu ya bude kofan dakin yashigo dawata katuwar kwali na LG washing machine saiga su Hafsat duka biye dashi Hawwa tabisu da kallo Ammi tace “a’ah wannan kuma menene Aminu haka”? Dan murmushi yayi yakalli Hawwa dake kallonsu yace “Ammi hada kudi mukayi muka saiwa Ya Hawwa washing machine na tambayi Hafsa tace shine kadai baku sayo ba dakukaje sayayyan kayan daki” yadanyi shiru yakalli Hawwa ahankali yace “Ya Hawwa I wish nafara aiki and I wish I can afford more than this wlh Ya Hawwa zan iya baki duka duniyan nan kin chanchanci haka”dakin kowa yayi tsit yana kallonsu, Ahankali Hafsa tashare hawayen daya zubomata tace “Ya Hawwa baki taba kallonmu kaman yaran kishiya ba, ko ki kallemu da abinda Umma take miki, Ya Hawwa da Baby Minal na ciwo bataci abinci ance a asibiti she is under weight Babanta baida kudin soyamata abinci” tai dan shiru saikuma tafashe da kuka sosai tace “Ya Hawwa kadaice tafito da kudi tadinga siyanma Minal abincin yara daban daban, kala kala, wlh babu wanda bata siyamana ba, cerelac su gaber rice babu kalan abincin yara da bata soyama Minal ba har yarinyar tazo tafara ci tanata kumari” ahankali Hawwa ta tashi dagakan dadduma idanunta yayi ja kanninta are making her emotional, Hafsa tace “I wish kowa aduniya zai sami big sister kaman Ya Hawwa, she takes care of dukanmu zuciyan Ya Hawwa daban ne, she’s too good” hannu Hawwa tabude mata dasauri Hafsa ta rungumeta tsamtsam a jikinta su Khadija ma haka, Aminu Hawwa ta kalla tace “come here big head” zuwa yayi tabashi side hug tareda shafa kanshi hawaye na zubowa daga idanunta she wish this was real marraige, all this farin cikin da yan uwanta keyi she wished for mutum better than Khaleel sukemawa, su Ammi kowa saida ya goge kwalla ganin Hawwa dasu Aminu, ahankali Hawwa tace “zan dinga amfani da washing machine din nan kullum kobanda wanki ma” dariya duk sukahau yi su da ke kuka daidai nan akai sallama ana bude kofan dakin duk suka dago Umma ce sanye da Hijabi kowa ya tsaya turus yana kallonta Umma bata taba shigowa dakin ba, Hawwa ta kalla daga bakin kofan tace “nashigo?” Gyadamata kai Hawwa tayi da sauri shigowa Umma tayi tazo gaban Hawwa ga mamakin kowa kawai saitai kasa zata duka dasauri Hawwa tariketa tace “Umma mehaka”? Fashewa tayi da kuka kawai tace “Hawwa ki yafeni ki gafarceni duk abinda na miki na dauramiki tsana akan abinda baki duniya akayi, na dinga miki mugun fata kema ki dade baki aure ba kaman yanda mahaifinki yamini, nayi kuskure amman yarana sun ganar dani, sun nunamin hanyar gaskiya Hawwa kiyakuri dan girman Allah” Dasauri Hawwa tace “Umma wlh bakımın komiba kiyakuri ki yafeba both Babana da Mamana abinda suka miki kinji” Gyadamata kai tayi tace “na yafe musu har abada” ta rungume Hawwa tace “Allah yamiki albarka, Allah ya albarkaci aurenki yabaku zaman lafiya da yara masu albarka” kowa na dakin harda Baba sukace Ameen, Umma tadauko tadauki ledan data taho dashi tabude atampa mai kyau ne ciganvi na gold irin na 15k dinnan tace “ga gudunmawa kinji” cikeda farin ciki Hawwa tace “Umma wayyooo Allah na nagode Umma tayi kyau ina sonta wlh saida salla zan dinga nasaka” Umma ta washe baki she loves yanda Hawwa ta nuna tanaso itadakeda atampopin millions a akwati Hawwa tawuce takaima Baba dasu Ammi tace “Baba Ammi kallo abinda Umma na tabani” Baba da Ammi tace akashe lafiya zuwa wajen dash Baba suke Umma tayi tace “Zainab Malam kuma kuyafemin” Ammi tace “Zainab komi yawuce amanta da baya” Baba yace “nayafe miki Zainabu nima kiyafeni” ahankali tace “nayafe Allah ya yafemana duka yahadamu a Aljanna” kowa yace Ameen, tace “Zainabu meya rage ba’ayiba? Mezanyi?” Ahankali Ammi tace “jere za’aje gobe agidanta inaso ke zaki jagoranci abin Umma, ga Lami kuma” Umma tace “ba matsala Allah yakaimu gobe da rai da lafiya” kawai suka shiga hira ana planning biki gobe dan akwai dinner da daddare karfe takwas Hawwa sai kallon kowa take adakin one big happy family all this farin cikin da planning bikinta hala nan da wata daya, ko sati daya, ko sati biyu yasaketa fa ko? Gashi mashayi, dan party, dazata gayamusu bazasu yarda ba, babu mai daukar bad magana akan Khaleel, lallen hannunta dayayi fitinannen kyau ta kalla wai itane zatai aure yanzu, kiranta Munawwarah tayi hakan yasa ta tashi ta kwantar da Noor datai bacci agado tawuce taje ganin magani zata bata yasa tace “ba Ammi tace adakata ba Anty” Munnawara ta dungure mata kai tace “wannan ba maganin mata bane, maganin cicciko da naman gaba ne taciki, batace kar abaki wannan ba ai, shanye nidai kibani kitafi” kama hanci Hawwa tayi tasha da kyar tanayi kaman satai amai Munawwarah tace “za’asha daga kafin afasa” Dasauri Hawwa tace “meza’a fasa”? Dan bata gane maganan ba Munawwarah tace “tashi kije nidai bacci zanyi” tashi Hawwa tayi tafice abinta taje ta kwanta.

