Hausa novels

Matar Damisa Book 1 Chapter 17 Complete Novel

🐅 MATAR DAMISA 🐅
(The Wife Of Tiger)

 

*MALLAKIN*
*ASMEETAH* ✍️✍️

https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt

Wannan page ɗin sadaukarwa ne wa masoyana masu mun comments da kuma sharing 🥰😘😍

*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
___________________________________

https://www.facebook.com/103637491942644/

💫💫 *{{N W A}}* 💫💫

بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم

*BOOK* *ONE*
*PAGE* ➡️51 & 52⬅️

Zaman sarauta tayi ta ɗora ƙafar ta ɗaya akan ɗaya ta ƙura wa Junaid ido sai murmushi take ta zubawa, shi kuwa duk abunda take yana kallonta ta cikin mirror,
Bayan ya kammala shiryawar sa cikin sleeping dress juyowa yayi yana taku cikin nutsuwa yayo kan Ayush yana faɗin “idan kin gama koke-² nakin inaso zan kwanta bacci..

Ɗaga kanta tayi tana kallon fuskar sa cikin rashin fahimta ta miƙe tsaye murya ciki-² tace “mommy tana nan ne?”
Shi sai lokacin ma ya tuna shin ta dawo ne daga asibitin ko kuma tana can har yanzu, yasan halin mom yanzu sai tace zata zauna a gurin Dr. Hasheem!

Bin ta gefen Ayush yayi yana faɗin “let me check her..”
Itama bin bayansa tayi da kallo har ya fice daga ɗakin, zuciyarta fari sol ita kaɗai sai murmushi take yau jin kanta take kamar ba ita ba!
a ranta take faɗin “yanzu zan samu damar aiwatar da aiki na akan Junaid, zan cika burin mahaifiyata, haba yanzu ka fi kyau wallahi amma mutum koda yaushe fuska a ɗaure kamar wanda aka aiko wa sakon mutuwa.”
Maganar zuci take kamar wanda take magana a gabansa!
Gaban mirror taje ta tsaya tana kallon kanta a ciki, ga light ɗin ɗakin green colour, fuskar nan sai sheƙi yake…

“Ɓingel! Ɓingel!! Ɓingel!!! kada ki wahalar da zuciyarki akan abun hari na kuma maƙiyina,
Junaid ba mijin Aure bane domin bazamu taɓa barinsa yayi Aure ba indai yana raye!
Ke sarauniya ce, kuma gimbiya, kada ki ƙasƙantar da kanki akan ɗan masaƙina wato shalelen damusa na,
Hahaha! Hahahah!! Hahahaha!!! ”

Ayush tayi matuƙar tsorata da jin waɗannan maganganun a ta cikin madubi,
Bayan ya kammala wani irin dariya yake yi har saida glass ɗin madubin ya tsage….

Jaa da baya tayi tana furta “Innalillahi wa inna ilaihi raju’un, wanene kai”
Ji tayi an ƙara tintsirewa da dariya sannan yace “yau zan sanar miki ko ni waye ne, amma inaso ki fita daga cikin rayuwar Junaid domin kina hanani rawar gaban hantsi, idan kina tare da shi damusa na jinya yake baya samun lafiya har sai kin bar gurin da Junaid yake..”

Jin hakan yasa Ayush ƙara matsowa dab da jikin madubin a hankali ta furta “Abbah!”.

Wani irin haske ne ya bayyana a jikin madubin ya soma sheƙi ga taurarin da suka bayyano suma ta cikin madubin,
Ita ma Ayush haske ne ya bayyana a jikinta sai wal-wali take, wannan hasken ne ya janyeta cikin madubin ta ɓace ɓatt…

Tsintar kanta tayi a cikin wani sansani wanda ko bishiya babu a waran balle ɗan adam ko tsuntsu babu, ƙasar gurin fari sol sai feshin ƙanƙaran da ake yi!
gurin ya yi matuƙar burgeta sanyi ne yake ratsa duk ilahiriin jikinta, weather yayi matuƙar yi mata daɗi sosai,
Duba kanta tayi taga abun mamaki an canza mata kayan jikinta zuwa gown doguwar riga fara sol, daga saman rigar ya matse ta zuwa kunkumin ta kuwa rigar ya baje sosai ta bayan har jan ƙasa take, rigar dogon hannu ne na net ga wani irin takalmi a ƙafar ta mai shegen tsini shima farin ne tas, sai gyaran gashi data sha an tuttuƙe gashin sannan aka sanya mata hular sarauta na gold mai sheƙin bala’i,
Anyi mata makeup sosai wanda duk wanda ya ganta sai ya suma tsabar kyan data yi!
Ga wasu zobina na gold suma yanda aka jera mata su a duk yatsun hannun ta, sai warwaraye suma na gold sai sheƙi suke,
Sai kuma sarƙar wuyanta mai ɗaukar ido ya kame wuyanta gam shima sai bada kalar hasken sa yake,
Hatta ƙafarta sai da aka jera mata sarƙoƙi wanda tana tafiya suna bada kalar sauti…
*MASHA* *ALLAH* Ayusher fa ta fito sai wanda ya ganta zai bada labari kamar dai Asmeetah domin har musabaha mukayi 😁😁

Kallon kanta take yi da gasken gaske fa itace abun ya yi matuƙar bata mamaki, kanta ne ya ɗaure tana cigaba da kallon wajen da take
“Wai aina nake nam? ko dai mutuwa nayi ne aka kawoni nam! Ga kuma feshin ƙanƙarar da akeyi ba ruwa kuma, ƙasar gurin laushi ga kuma fari tass….”
Magana take a fili tana ta waige-² ..

Ƙarar gudun doki taji daga nesa ana nufan gurin da take tsaye, idonta akan yanda zataga ɓillowar mai tafo wa!

Wani mutumi ne fari tas dogo ne sosai ga ƙiran jiki kamar basamude duk jikinsa a murmurɗe gashi da ƙirar ƙarfi,
Ba riga a jikinsa sai wasu tarukucan sarƙoƙi a wuyansa da kuma dantsen sa duk sarƙoƙi yanda ya ɗaɗɗaure su a ƙatoton dantsen sa!
Suman gashin sa kuwa har gadon bayan sa ga laushi, sai wandon buzaye dake jikinsa,
Yana gudu da doki wanda shima yasha kwalliya, ta ƙasan sa kuma wani ƙaton damusa ne shima yake ta tiƙar gudu shima har da sarƙar sa a wuya…

Sai da yazo daf da Ayush sannan ya tsaya tare da sauƙowa akan dokin,
Tsayawa yayi a gaban Ayush yana kallon ta da murmushi a saman fuskar sa.
Yace
“Ɓingel na gaisheki gimbiya mai sarauta a hannu” sai da ya sunkuyar da kansa ƙasi alamar girmamawa sannan ya miƙa mata takobi mai shegen masifar kyau ga sheƙin da yake yana wal-wal, hannu tasa ta karɓa idonta akan mutumin mayar da tokobin tayi cikin gidansa
Tana faɗin “godiya nake….”

Shima damusan durƙusawa yayi ya gaishe da Ayush sannan ya miƙe,
Sake baki Ayush tayi tana kallon ikon Allah, a cikin ranta tace “ni kuwa a duniya nake?”

Kamar wanda yaji abunda tace sai ji tayi ya katseta da cewa
“Haƙiƙa keɗin gimbiya ce, kuma a duniya kike nan ɗin bayan masarauta ta ce! ba mai zuwa nan sai ni da kuma shalele na ya nuna damusar sa da hannu….”

Ayush baki na motsi kaɗan-² tace “waye ne kai?”
Murmushi yayi yana kallon ta yace “ɓingel, ni mahaifinki ne wanda kika daɗe kina son gani amma hakan baiyu ba sai yanzu gani ga ki ɓingel”

Zaro ido waje tayi cike da mamaki take kallonsa bata san lokacin da wani irin farin ciki ya ziyarce ta ba tana faɗin “yau ni ce a gaban mahaifina” lokaci guda kuwa ta fashe da kuka….

Tallafo kanta yayi yana faɗin “gimbiya bata kuka amma kin mayar da kuka abun sana’ar ki, hakan yana ƙona mun rai ɓingel,
Inaso ki zama jaruma, idan ana riƙe da takobi kuka ƙaiƙashewa yake!!!
Goge mata hawayen da ya zubo mata yayi da hannayensa masu laushin gaske…

(ikon Allah! A tunani na zanga wani dattijon tsohon boka sai kuma naga akasin haka,
Kyakykyawan mutum mai siffar jaruman bahindiye,
A tunani na zanga ƙazamin boka amma sai naga fashion man, a ƙalla shekarun sa bazasu wuce 45 ba, Ayushh kuma tana da 20years a duniya….)

“Ɓingel nasan kin tsaneni a cikin zuciyarki, sakamakon labarin da mahaifiyarki ta baki akaina, wanda hakan ba gaskiya bane,
Mahaifiyarki bata san komai a kaina ba, ni ba mungu bane, ni ba azzalumi bane, ni kaina nasan dalilin daya sa nake wahalar da Junaid wanda sirri ne a gareni, zaki san wannan sirrin amma ba yanzu ba akwai lokaci!
Ɓingel ki daina ɗaukar kanki cewa ke bakida ƴanci,
Ke ƴa ce kamar kowa ni mahaifinki ne, kuma ta hanyar Aure aka sameki, amma sai dai mahaifiyar ki bata san da hakan ba,
Ni na sanar miki ne domin ki sakawa ranki nutsuwa, ki kwantar da hankalin ki a matsayinki na ƴer masarauta gimbiya *MAYUSHERT* asalin sunanki kenam!!!
Sannan mahaifiyarki tana nan da ranta bata mutu ba, akwai lokacin da zakii ganta ba yanzu ba…
Kece AYANAR JUNAID hakan yasa damusa na baya iya motsi idan kina tare da Junaid domin duk wani motsin sa yana a tattare da Junaid,
Rashin motsawarsa kuma illa ne hakan yasa banaso kina kusantar shi saboda damusa yana cutuwa motsinsa kuma zaisa Junaid cutuwa,
Makaryar wannan tsafin kuma yana tattare da ke, hakan bazai yuba saboda zaki iya cutuwa, kuma zan iya rasa duk wani ƙarfin ikona….”

Ajiyar zuciya yajaa yana kallon ɓingel ɗinsa wacce itama kallon mahaifin natan take..

Leɓenta ne yake motsi da ƙer ta iya cewa “meye abun dake jikina na makaryin tsafin?..”

Dariya yayi short har sai da dimple ɗinsa ya lotsa yace “bazan sanar miki ba ɓingel, saboda nasan idan soyayya tayi nisa zaki iya cutar da ni,
Amma inaso ki sani cewa bazaku taɓa yin Aure ba a tsakaninku ke da Junaid,
Har sai an karya wannan tsafin jikinsa, idan kuma ba haka ba
*DAMUSA* *BAZAI* *AURI* *GIMBIYA* *MAYUSHERT* *BA*…

Kafin ta furta wani abu ya kuma katseta da cewa “ga wannan duk wani ƙundin tarihi na yana ciki, kada ki bari wani ya gani”
Wani ƙatoton littafi ne ya miƙa mata a bayan littafin an zana masarauta…..
Ya kuma cewa “duk wanda ya ɗauki littafin nan bazai taɓa buɗe shi ba, sai wanda yake da alaƙa da masarautar kamar ke…
Na barki lafiya Ɓingel..”

Juyawa yayi yahau saman dokin sa,
Ayush kuwa tana riƙe da takobi da kuma littafin da aka bata
Baki na rawa tace “shin menene sunanka?”

Murmushi yayi sannan yace ” *SARKI* *RAAMAD*..

Ya kamata ki rage tsoro domin ke jinin Jarumi ne….
Sannan ni ba Boka bane sai dai na kasance ni matsafi ne, kuma ni musulmi ne! kada kuyi mun mummunan fassara…”

Yana kaiwa nan yayi tafiyarsa.
Ita kuwa Hasken daya kawota shine ya kuma ɗaukar ta….
Sai tsintar kanta tayi a cikin toilet ga ruwan shower yanata zuba..
Jikinta ta duba taga jallabiyan Junaid aka maido mata dashi, ga kuma hannunta riƙe da littafin tarihin mahaifinta da kuma takobin da ya bata…

Bata ankara ba taji ance “Yushert wai mekike a toilet haka since.”
Muryar Junaid ta jiyo yana magana..
Wanda tin ɗazu shigowar sa room ɗin bai ganta ba sai zubar ruwa yake ji,
A tunaninsa wanka take sake yi, bai yi tunanin babu kowa a ciki ba…

Rasa yanda zatayi da abubuwan da suke hannunta ta yi, da sauri ta buɗe drower cikin toilet ta a jiye su a ciki sannan ta rufe..
Ta kashe ruwan dake zuba sannan ta fito,
Zuba mata eyes yayi yace “daman ba wanka kike yi ba tin ɗazun? to me kikayi kenan?”

kiɗimewa tayi ta soma ƙinƙina tana faɗin “daman daman da daman nayi ne”
Kallon ta yake cike da mamaki yace “kinyi mai?”
Gaba ɗaya ta rasa mai zata ce, sai kawai zuba masa ido tayi…

Tashi yayi daga zaunen ya nufi toilet ya buɗe ya gama dube-dubensa
Yakai idonsa kan drower yasa hannu zai buɗe da gudu Ayush tayo kansa tana faɗin “na wanke toilet ne kar ka ɓata shi,” ta kuma riƙe hannunsa wanda yakai zai buɗe gurin ma’ajiyin ta.

“Mtsw kuma shine ina tambayarki kika yi shuru?..”
Sunkuyar da kanta tayi ƙasa ta kasa ɗagowa,
Jan hannunta yayi suka fita daga cikin toilet,
Kai tsaye haurawa saman bed ɗinsa yayi
Ya kwanta tare da janyo mayafi ya rufe jikinsa
Tsayawa tayi Ayush, yace “ke bazaki kwanta bane?”

Murya ciki-ciki tace “ni bazan iya kwanciya a tareda kai ba”
“For what?”
Ya tambaya a takaice.
“Saboda bazan iya juran yanayin da zan shiga ba!”
“Ban ganeba? What do you means?”
Yayi tambayar yana kallon fuskar ta.
Sunkuyar da kai tayi ta kasa cewa komai…

Tashi yayi daga kan gadon
Yace “toh kwanta na bar miki gadon tinda bakyason kwanciya da ni”
Ɗaukar pillow yayi yaje saman sofar ɗakin ya kwanta…
Itama bin kan gadon tayi ta mimmiƙe tareda rufe kanta da mayafi..

Maganganun mahaifinta ne suka soma dawo mata kwakwalwar ta,
Tayi matuƙar yin farin cikin jin abu biyu daga gare shi
Mahaifiyarta tana raye, da kuma ita ba ta hanyar fasiƙanci aka sameta ba,
Wannan abun yayi mata daɗi a ranta
Bugu da ƙari kuma taga mahaifinta face to face tinda aka haifeta bata taɓa ganinsa ba…..

A ranar da farin ciki ta kwana…….!

_____________ washe gari Mommy tana zaune akan kujerar ɗakin da aka kwantar da Dr. Hasheem,
sai gani tayi ya miƙe zaune yana faɗin “Allah ku ceceni daga hannun wannan mungun mutumin, wayyo zai kashe ni”. yana ta waige-² idonsa ne suka sauƙa akan mommy wacce ta riƙe shi tana cewa “Dr ka kwantar da hankalin ka babu abunda zai sameka, insha Allahu zaka samu sauƙi.”
Sama-² yake jan numfashin sa gaba ɗaya ya rasa sukuninsa, duk jikinsa sai ciwo yake!

Kansa ya sha bandeji ga hannayensa waɗanda suma suka sha ƙarfuna, ya samu karaya sosai.
A yanzu ba mutumin daya tsana a rayuwarsa inba Junaid ba
Yana maganar zuci “wai ni Junaid zai rufe ido yamun wannan aika-²? insha Allahu zan ɗau fansa bazai ci bulus ba, nima zan nuna masa nii ba kawwan lasa bane, nima inada gata…”

Yayi tagumi sai hawayen dake tsiyaya daga idanuwansa,
Mom ce ta dafa kafaɗarsa tace “Dr Hasheem kayi hakuri dan Allah, nasan Junaid ya aikata babban kuskure, amma inaso ka sani cewa yayi maka hakane ba tareda saninsa ba, baya cikin hayyacinsa kaima kasan da hakan, ka kuma san halin abokin nakan, nima a hankali nake binsa saboda abu kaɗan ne yake ɓata masa rai….”
Hmmm! Jan zuciya tayi sai hawayen daya zubo saman fuskar ta, zuciyar ta ne yake mata raɗaɗi ta rasa yanda zatayi ta magance matsalar Junaid…

Shuru Dr yayi baice komai ba, shi kaɗai yasan kalar raɗaɗin da yake ji shima..

*****

Asuban farko Ayush ta farka daga bacci tana miƙa tashi tayi tanason shiga toilet domin ɗaurowa alwala sai da ta kunna light ɗin ɗakin before ta shige cikin toilet tama manta da Junaid acikin ɗakin,
Har saida ta tsuguna kafin ta tuno ashe dai tana period, turɓune fuska tayi tana faɗin “kashh! na manta” ta nufi hanyar fita kenam ta tuno da ajiyar datayi cikin drower, da sauri ta nufi gurin ta buɗe ciki, ajiyar zuciya tayi ta dafe saman ƙirjinta,
Ɗaukar su tayi ta fice daga toilet
Tana fita kuwa idonta suka sauƙa akan Junaid gaban ta ne yayi wani irin bugawa sauran kaɗan tasau littafin a ƙasi, hannunta ne yahau ɓari!
Shi kuwa yana kwance sai shan baccinsa yake cikin nutsuwa.

Da sauri ta tusa littafin da takobin ƙarƙashin gado.
Ta taso tana tafowa gurin da Junaid yake a kwance saman sofa, durƙusawa tayi tana fuskantarsa idonta akan sa tana ji yanda yake jan numfashi a hankali idonsa a rufe ba ƙaramin kyau yayi mata ba,
Ta kai idonta kan maroon lips ɗinsa gashi ɗan ƙarami
tana matuƙar jin sha’awarsa amma shi ko kaɗan baya wannan tunanin a ransa
Ji take kamar ta rungumeshi tsabar tsananin so da ƙauna,

Red lips ɗinta take matso dashi saitin nasa tana ƙoƙarin manna masa kiss
Jin yanda numfashin su yake gaurayuwa yasa Junaid buɗe eyes ɗinsa daiden lokacin ta ɗan zura tongue ɗinta cikin bakinsa,
Ita kuwa kasa control kanta tayi yasa har ta aikata hakan ba tare da saninta ba,
Cikin sa’a kuwa ta kamo harshensa ta fara masa tsotsar lollipop tana lumshe ido.

(To fah Ayush ta tafi sararin samaniya 🫢,
Yooo lips ɗin Junaid ne jan hankali gareshi 🙈🙈🙈 )..

Shi kuwa kamar wanda aka ɗauke masa wuta, ido ya lumshe yana jin duk tsotsar da take masa amma ya kasa dakatar da ita,
Shi ko kaɗan baya wani jin feeling sai zaƙin harshenta da yake ji, harshenta kamar zuma.

A hankali yake motsa tongue ɗinsa yana juya shi a cikin nata
Wani irin salo yake bada wa hakan ya ƙara jefa ta cikin duniyar taurari,
Bata san lokacin data haura saman sa ba ta rungume shi sosai,
Hot kiss suka shiga aikawa juna, a cikin tana nishi ciki-² har ya fito fili, duk abunda take kuwa yana jinta!
Amma duk da hakan bai sa yaji sha’awa ba sai dai nutsuwar da yake samu a tattare da ita,

Ganin bata da niyar barinsa yasa ya tallafo kanta ya raba bakin ta da nasa,
Yana faɗin “it’s okay, kin samu nutsuwa koh?..”

Wani irin kallo take binsa da shi,
Idonta kamar wacce tayi shaye-shaye, a hankali take lumshe su tana maida numfashi sama-²
Kallon ta yake sosai ya fahimci halin da take ciki hakan yasa ya ƙwantar da kanta saman ƙirjinsa yana shafa sumar kanta,
Abu ne yake yawo masa a rai
“Meyasa bana shiga yanayin da kowa yake shiga ne! bansan ya ake ji a sex ba, ban san sha’awa ba, ban san ya ake ji a romance ba, ban taɓa mafarkin sex ba, ban taɓa fitar da spam a jikina ba,
Innalillahi wa inna’ilaihi raju’un Allah ka magance mun matsala ta….”
Haka yaketa maganar zuci,
Shi kaɗai yasan takaicin da yake ji a ransa,

Yana cikin wannan zancen zucin yaji har an shiga sallah a masallatu,
Ita kuwa Ayush bacci ne ya ɗauketa mai nauyi, a hankali ya tashi ya ɗagota a hankali
Ɗaukar ta yayi ya kwantar da ita akan gado,
Kafin shima ya shiga toilet ya ɗauro alwala
ya gabatar da sallar sa yayi addu’o’insa yana zaune akan sallaya da carbi a hannunsa yana lazumi…..

 

Domin sauke CikakkenLittafin Sai Ku Danna bulun Rubutun dake kasa 👇👇

Matar Damisa Book 1 Complete Novel Document 

Some of related Hausa Novels

*MASHA* *ALLAH*
Love much my fans😘
Ina matuƙar ƙaunar ku, kuna ƙarfafa mun gwiwa akan littafina mai suna
*MATAR* *DAMUSA*
(the wife of tiger)

Ku sani yawan comments ɗinku shine yawan typing ɗinku,
Kuma comments ɗinku shine yake ƙarfafa mun gwiwa,
A taimaka ayi mun *SHARING* 🙏🙏🙏

*🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝*
*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦350
2GB = ₦600. 2GB = ₦700
3GB = ₦900. 3GB = ₦1000
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1300
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1600

*GLO* . *9MOBILE*
1GB = ₦350. 500Mb ₦250
2GB = ₦700. 1GB ₦500
3GB = ₦1050. 2GB ₦1000
4GB = ₦1400. 3GB ₦1500
5GB = ₦1750. 4GB ₦2000

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
*🪀08066268951*

*SAFNA* *GRAPHICS* *DESIGNER*
Kina kasuwanci bakida logo?kina kasuwanci da wani abu wanda idan aka kallah xa’ace eh lallai wannan yar kasuwa ce,tom indai wannan ne matsalan ki maganin ta yaxo,domin SAFNA GRAPHICS DESIGNER tashirya tsaf domin shirya maku xafafan kuma qayatattun GRAPHICS kala kala kuma a parashi dai dai da aljihun ku,kedai kaidai kada kataba bari wannan daman yawuceku,ina maraba da kowa da kowa domin parincikin ku shine nawa,call, texts or WhatsApp 08148318396

 

*ASMEETAH* *CE* ✍️✍️✍️

Back to top button