Mijin Marigayiya Page 30 Hausa Novel
Da kansa ya kula da yanda take mu’amalarta kwana biyu cikin kasala gashi bata ma son magana, don haka ya tasata a gaba ya kaita asibiti. A nan aka tabbatar masa da cewa tana dauke da ciki sati shida. Suna zaune a mota yana tukosu a hanyarsu ta dawowa ya dubeta yace ‘Kin gani ko, kin sami cikin a kwanciyar hankali ba tare da kinje nemansa a asibiti ba ko? Allah ya sa dai ba mai wahaka bane?’Ta dan yi gajeran murmushi tace ‘Smin ya Allah.’Suka yi shiru na dan lokaci, ya dubeta yace ‘Wai ya naga duk kin yi wani shiru ne? kamar ba abin nema ne ya samu ba?’Ta kawar da kai tana murmushin yake tace ‘Bana jin dadi ne, bacci ma nake ji.’Ta kwantar da kanta a jikin kujerar motar ta rufe ido, don haka shima ya kyaleta ya mayar da hankali a wajen tukinsa.……A haka Khadeeja ta dage ta cigaba da mu’amalarta tana yin duk wata hidima da ta saba. Ko a wanne yanayi ta tashi haka take daurewa tayi duk wata hidimarta don bata shirya drama da Mustapha ba. Ta riga ta san idan dai tana numfashi a gidan nan to duk wata hidima da matar gida take yi ba yafe mata zai yi ba; don haka ta daure ta cigaba da dagewa tana yi. Musamman da yake duk wani aiki da ta saba yi a gidan ta riga ta koyawa Rashida kuma ta iya sosai, gashi yarinyar bata da kyashi ko daya, don haka abubuwa suka zo mata da sauki sosai.Sai dai fargabarta daya iyayen Rashida suna maganar ko da wane lokaci za a iya zuwa a dauki Rashida saboda aurenta ya kusa; duk da dai an ce za a kawo mata kanwarta to amma ta san akwai aiki.Haka ta cigaba da rayuwarta tana goyon cikinta.A hankali ta fahimci lokutan da yake zuwa zance wajen naja, kuma da yake shi yake kaita makaranta da ta shiga motar take gane Naja ta fita a motar ko kuma sun fita tare.……..Daidai lokacin da zasu fara jarrabawar karshe a lokacin cikinta ya shiga wata na takwas; ga hidimar gida, ga karatu kuma gashi tana kokarin hada project dinta. A dai-dai lokacin ne kuma Mustapha ya gama gyara gidansa wanda yake fatan da zarar sun koma za ayi bikinsa da Naja. Sau biyu yana kaisu gidan ita da yara, kuma duka zuwa biyun sai ta tambayeshi ko aure zai yi ne yake yin gidan kamar d zubin mata biyu. Amma duk lokacin da ta tambaya sai yace mata ko da zai yi auren to ba yanzu ba; ta rasa gane dalilin da yasa yake son boye mata aurensa da Naja. Don haka ma ta daina tambayarsa gaba daya.Ranar asabar ce kuma tun dare ya sanar da ita da safe yara su shirya zai fita dasu, don haka tun wajen tara na safe ta bayan da suka ci abinci ta sallamesu ta koma ta kwanta. Ya dai ce mata gidan Hajia zasu je kuma suma yaran haka suka gaya mata; amma a ‘yan kwanakin nan yana yawan fita da yaran ranar da babu aiki yace wajen Hajia zai kaisu. Ta riga ta gane wajen Naja yake kaisu, sai dai bata ga dalilin da zai sa tayi masa magana ba tunda ‘yayansa ne sannan kuma gaya musu da yake suce mata gidan Hajia suka je su yake cutarwa ta hanyar koya musu karya.Gaba dayansu suka fice banda Habib, wanda dama ya riga ya saba duk lokacin da za suyi wannan fitar shi baya binsu. A gida yake zama tare da Khadeejan da Rashida.Sai wajen karfe biyar na yamma sannan suka dawo, lokacin ta riga ta gamamabincin dare ta zuba a flask tana kwance a daki. A dakinta yaran suka sameta tana kwance tana hutawa, suka sanar da ita sun dawo. Shukra kuwa sai ta wuce ta haye gadon ta kwanta kusa da ita tana cewa ‘Bacci kike yi Anti?’Ta dan matsa jikinta tana gyara kwanciya, Khadeejan ta dan gyara kwanciyarta tana kawar da Shukran daga cikinta. Tayi dariya tana cewa ‘Na matsa ko Anti, kada na lotsewa kanina hanci.’Tayi dariya saboda itace ta saba gaya mata hakan a duk lokacin da take son kwanciya a jikinta tunda cikin ya fara girma; domin Shukra yarinya ce mai son jikin tsiya kuma ta samu Khadeejna bata tureta. Tace ‘Yauwa, ashe dai kin gane. Kada a dinga ce miki yayar mai lotsttsen hanci.’Suka yi dariya gaba daya; Shukra ta ci gaba da wasa da hannun Khadeejan guda daya yayinda Khadeejan take rike da daya waya a daya hannun tana chatting. Jimawa kadan cike da damuwa tace ‘Anti.’‘Umm.’ Ta amsa ba tare da ta bar abinda take yi ba.Tace ‘Gaskiya ni ba zan koma wajen Anti Naja ba, a wajenki zan zauna ko?’Ta ajiye wayar tace ‘To wa yace zaki koma wajen Anti Naja kuma? Ai muna nan tare, ko ba gamu ba a gidanmu.’Cike da damuwa tace ‘Ai itama tace aurota Abbanmu zai yi ta dawo gidanmu. Amma sai mun koma sabon gida. Shine yau da muka je wajenta take cewa Yaya Afaf idan ta tare duk wajenta zamu koma. Gaskiya ni dai ba zan koma ba ko?’Ta dan yi shiru tunani yana nema ya birkita kwakwalwarta; duk da bai gaya mata ba ta san yana kai yaransa wajen Naja, amma maganganun da Najan take gayawa yaran basa kama da maganganun da ya dace a gaya musu a daidai wannan lokacin. Sai dai ta san babu yanda zata yi tunda shi ya bata dama.‘Anti.’ Muryar Shukra ta katseta tana kiran sunanta.Bayan ta amsa Shukran ta cigaba cikin damuwa ‘Tace saura wata biyu ta tare, gaskiya idan ta zo ki gaya mata ni a wajenki zan zauna ba a wajenta ba. Kuma ma na ji tana gayawa Yaya Afaf idan an koma sabongida sama take so kece a kasa, na gayawa Yaya Afaf mune a sama mu dake tace min wai daAllah can. Gaskiya kia gaya musu mune a sama.’‘Hmm! Zan fada musu Shukra, ai mune a sama kada ki damu.’Ta cigaba da surututa tana bawa Khadeeja labarin irin abubuwan da suke yi idan suka je gidan Naja.Duk da Khadeeja bata yi mamakin jin cewa Naja ta san da sabon gida ba amma ta yi mamaki da ta ji cewa har Naja ta zabi part din da take so yainda ita kuma har yanzu bai ma gaya mata ita da wata matar zasu zauna a gidan ba. Ta kasa gane dabarar da Mustapha yake jin yayi da yaki gaya mata zai yi aure; amma dai zata cigaba da binsa taga karshen wulakancinsa. Ko da yake a ‘yan kwanakin nan ma yanda yake kara tubure mata ta tabbatar da tana biye masa da kullum sai sun yi fada. To sai dai bata da wannan lokacin tunda ga project dinta wanda take so ta gama kafin su fara jarrabawa wanda tana fatan Allah ya sa kada haihuwa ta zo mata har sai tayi final paper.Haka ta ajiye wannan ma a ranta tana jiran ranar da zata titsiye Mustapha tunda haka ya zaba.……..Tun kafin su fara jarabawa ya sanar da ita idan ta haihu aka yi suna aka gama zuwa barka zasu koma sabon gida, saboda baya so aje a bata masa gida. Itama tsarin yayi mata don haka ba tare da wata matsala ba ta amsa. Kuma kamar yanda ya bata umarni ta fara hada kayanta da zata tafi da su duk da cewa ya gaya mata ya saka sabbin furniture a gidan.Ranar da zata yi jarrabawar karshe ya kama yara suna hutun makaranta, kuma sai 2pm zasu shiga paper. Don haka yace idan babu matsala yanaso ta shirya da wuri su tsaya a sabon gida taga furniture din da ya siyo in ya so sai ya ajiyeta a makaranta shi da yara su wuce wajen Hajia. Ta riga ta gama karatunta don haka tun wajen sha daya ta shirya suka shiga mota gaba dayansu suka kama hanya.Saman gidan yana dauke da parlor guda biyu karami da babba da kuma dakuna guda uku sannan da kitchen, daki daya da parlor suna tare da juna wanda dama ya sanar da ita nan ne nashi part din. Kasan kuma parlor ne guda daya, sai dakuna guda biyu wadanda suke kusa da juna sai kuma wani dakin guda daya wanda yake gafe, sannan kuma da kitchen. Parlor din kasan duk a nan aka sauke furniture din; duk da kusan kowanne yana cikin kwalinsa.Suna shiga suka dan yayyage kwalin ita da yara suka gani.Ya dubeta yana nuna dakunan kasan yana cewa ‘Sai ki zabi a wane dakin za a saka miki gadon, in ya so daya dakin kuma sai a dauko gadonki na tsohon gida a saka.’Ta kama hanyar sama tana cewa ‘Eh hakan ma yayi; dakin wanda yake jikin nakan sai saka min sabon gadon a nan in ya so na kusa da shi sai a gyarwa ‘yan mata na ko? Shi kuma Yaya Habib sai a bashi wannan na kasan.’Shukrace kawai ta biyota shi yana tsaye a inda yake. Ta dan juyo tana cewa ‘To kazo muje mana ka gani…
