Bayan karatun Qur’ani mai tsarki da tayi,Sabarimala Jayakanthan wata ‘yar kasar Indiya mai fafutukar kare hakkin bil’adama ta yi rabo ta musulunta. Sabarimala ta kasance sananniya ce a Kudancin Indiya.
Ta sami damar aikin umarah a watan Ramadan bana.
Ta sami damar ziyartar kasar Saudiyya a wannan wata na Ramadan domin yin aikin Umrah saboda samun damar shiga musulunci da tayi. A cikin wani faifan bidiyo da ya yadu a shafukan sada zumunta, an hangeta tana karanta kalimatu Shahada yayin da take tsaye a cikin harabar masallacin Makkah.Yanzu haka ta chanza Sunanta zuwa Fatima Sabarimala.
Ta bayyana makasudin shigar ta musulunci
A wani faifan bidiyo, Sabrimala ta bayyana dalilin da ya sa ta shiga musulunci. A cikin faifan bidiyon, an ji tana cewa “A Yanzu ina son Musulunci fiye da yadda nake son kaina.”
Sannan ta sake tambayan kanta dalilin da yasa ake nunawa al’ummar musulmi kiyayya, tare da rera karatun Al-Qur’ani cikin murya mai ban sha’awa.