Gwabnati Jahar bauchi ta Bude shafin bada tallafin karatu (Scholarship) na shekaran 2022.
Gwabnati Jahar bauchi ta Bude shafin bada tallafin karatu (Scholarship) na shekaran 2022.
Assalamualaikum ayau muna tafe da yadda zaku cike Scholarship na Jahar bauchi, wannan Scholarship na iya Yan Jahar ne Wanda suke karatu a makarantar gaba da secondary..
Akwai matakai guda uku Wanda zaku bi domin ku cike.
Na farko: Ku ziyarci daya daga cikin center wacce aka tsara zasu sayarda wannnan form na tallafin karatu, zamu ajiye link a kasa cikin shudin rubutu idan Kun shiga zaku tarar da address na center Sai kuje Mafi kusa da ku ko Kuma zaku iya cikawa ta online idan zaku iya hakan.
Na biyu: Zaku biya adadin kudi kimanin dari shida #600 naira da Kuma 300 naira ga Wanda zaije center su cika Masa Amma ga Wanda zasu iya cikawa online 600 naira kawai zasu biya.
Mataki na karshe: A tabbatar Bayan ancike an fidda acknowledgement slip form domin za’a bukace shi lokacin physical screening.
Dannan shudin rubutun dake kasa domin ganin inda center suke.
Bayan anbude Sai a jaa wayar kasa domin ganin centers.
Domin cikawa da kanku shiga Nan domin cikawa.
Muna muku fatan nasara.