Karfe A Wuta Chapter 65 By Ayshercool
Cikin rashin fahimta, yake bin ta da ido, sai dai tamkar soko, har tayi maganar ta gama, bai iya tofa mata uffan ba, har tayi ta gama ta karɓi wayoyinta da system tayi tafiyarta ɗaki.Ɗakin ta rufe, ta shiga duba call logs ɗin ta, amma kaf ba ta ga kiran Viper ba, wani irin takaci ne ya turnuƙe ta, wato duk siraɗin nan da ta tsallake da kyar, bai kirata ba, balle ya ji a wane hali take ciki.’To idan kuma bai san abun da ya faru ba fa?’ ta tambayi kanta. Ta basar ta ce bari ta jira zuwa gobe, taga ko zai kira wayar.Ƙasan zuciyarta kuma ta din ga hamdala da Allah ya sa bai kira ɗin ba, dan da ya kira Nasir zai ɗaga ne, kuma ba abun da yayi masa zafi, zai iya gaya masa waye, idan ya tambayi waye.***”Naja wai ko ke ki ka saka aka yi wa yarinyar nan wani abu ne?””Wace yarinyar?””Barrister nan? Karofi ya kira ni yana yi mini kashedi, ina tsoron Allah ina tsoron shu’umancin mutumin nan”Naja ta ce “Eh, ni na saka aka yi mata haka, dan so nayi ma ta mutu, na ga kai ka ƙi mayar da hankali ka yi abun da yakamata, ba zai yiwu ta tona mini asiri a banza ba, mutuncina ya zube a idon duniya ba. Ba a taɓa samun wanda ya yi yinƙurin kawo mini tangarɗa ba, ka ƙyale shi ka ke jan ƙafa a kansa ba, sai a kan wannan yarinyar”A fusace Indabo ya ce “wai meyasa ki ke haka ne Naja? Duk iya ƙoƙarin da nake yi a kan lamarin nan? Na gaya miki zata iya zama tarkon da zan kama Viper, kuma ina amfani da ita wurin yi wa yayanta barazana yake yi wa umarnina biyyaya, lokaci ɗaya karofi ya bijiro, yake yi mini gargaɗi a kanta, wai sonta yake yi, wataƙila ma yi yake yi dan kawai ya muzanta ni. Amma gaba gaɗi babu shawara, kin je kin aikata abu, kin saka yana ta kiran wayata yana nema ya tozarta ni””Nifa ban yi danasanin abun da nayi ba, kuma zan cigaba da bibiyarta sai na ga bayanta, ban damu da abun da zai biyo baya ba muddin zan tsira, kar ka manta kai ka koyar da ni hakan” ta kaste wayar tana jan guntun tsaki.***A gurguje Abdul ya yi breakfast a wurin ramma, yayi mata sallama ya fice.Bayan fitarsa ta daɗe tana kuka, kamar zuciyarta ta fashe haka take ji, saboda damuwa da tashin hankali, tun tana lissafin adadin kwanakinta a wurin Abdul, har ta karaya lissafi ya ƙwace mata, tana matuƙar son sanin halin da mahafiyarta ke ciki. Ta sha attempting ta saka wuƙa ta kashe Abdul, amma sai ta kasa, ita kanta ta sha yinƙurin kashe kanta, amma tuna makomarta sai ya sanya ta fasa.Gashi yanzu sam ba ta iya bujirewa buƙatar sa, rayuwa suke yi tamkar ma’aurata, ta yi kuka tayi istigfari amma da ya zo ya kalallameta da zance, sai ta bayar da kai bori ya hau, wasu lokutan idan ta kalli hidimar da take yi masa, ta gyaran gida, kula da abincin sa, yin wani abu da zai saka shi farinciki sai ta yi sai ta ji haushin kanta ya isheta.Abdul kuwa Asibitin su doctor AK ya wuce, ofishin sa ya je suka gaisa ya ce “Kai ne zaka yi morning kenan?”Ak ya ce “Eh ni ne your excellency kai fa zuwa yanzu ya ci ace ka ajiye Lab coat, tun da ana ta ƙishin-ƙishin kai ne zaka zama lamba biyun garin nan, zaka koma field ɗin dadynka”Abdul ya ce “Nifa Ak ko lamba ɗayan ƙasar nan na zama, ba zan iya daina aikin likita ba, ina gudanar da office ina consultation” suka tafa tare da kwashewa da dariya tare.Ak ya ce “Sannu doctor excellency, ina ƙanwar ka da kuka zo tare kuwa? Baka wani tsaya mun gaisa da ita ba, ko dan kar na ƙyasa ka bani ita, ai ban taɓa sanin kana da ƙanwa ba, na zata kai ne ƙarami”Abdul ya tsuke fuska ya ce “A wane room patient ɗin take ne?””Ai ta uzzura sai da aka sallameta, amma Alhamdilillah jikinta yayi kyau sosai, sai dai ka yi mana ward round idan da abun da za a taimaka mana ayi mana” ya jinjina kai ya juya ya fice daga office ɗin.***Tun bayan da ɗan mama ya tabattarwa Viper an sallami Nabila daga asibiti, yake kallon wayarsa yake jiran kiran wayarta, amma shiru ba ta kira shi ba, har ya fara tunanin ko ƙarya ɗan maman ya yi masa da ya ce ta warke an sallame ta.Shigowar Walid ce ta dawo da shi hayyacinsa, ya ɗaga kai ya kalle shi, Walid ya ciro wuƙarsa ya zareta daga cikin gidanta, ya kalli Viper ya ce “Lakwari da gaske yake, na iske madaki, ƙafarsa ba ta takuwa, raunin da ka yi masa ya zama gyambo a ƙafarsa, ga shaida harafin sunanka na zana masa a gadon bayansa, yadda shi ma ba za a kammala na sa labarin ba, dole sai an ambaceka”Viper yayi kamar zai yi murmushi ya ce “Mai laya”Walid ya ce “Na kiyayi mai zamani, Allah ya kiyaye mini kai ɗan amanata”Viper ya ce “Ina kewar wancan kwanakin, kwanakin da aka yi rashin ji da gaske, yanzu girma ya fara zuwa duk an daina wasu abubuwan”Walid ya yi murmushi ya ce “Rashin jin ai duk ba na daɗi bane ɗan uwa, duk da kai ƴar madara ta fara saita mana kai, Allah ya karɓi kayarsa, amma duk da haka ba zan gushe ba ina jinjinawa Nabila, dan ita tayi abun da muka kasa, albarkacinta mun sake ganin walwala a tare da kai, duk da ba ta kai ta wancan lokacin ba””That angry bird, masifaffiya” ya furta yana kallon liti ya ji me zai ce.Aikuwa kamar mai jiran ƙiris hya e “Ba wata tsiya da ta tsinana masa, sai shegen naci da taurin kan tsiya, mara kunya da ita sai kayan ƙaton kai kamar injin markaɗe da ƙwala-ƙwalan idanuwa kamar an soya aya, ai wallahi ‘yar madara duniya ce, ga kunya da girmama mutane, wannan tsagerar kuwa, tana zazzarewa mutane ido, ni har mamakin mai zamani nake yi wallahi”.Walid ya ce “Ai ita ce daidai da ku, daga kai har mai zamanin, mu da muka kasa iya masa, ita ai gata nan yana saurarenta””Ba wani nan, ni haryanzu ba gama yarda nayi da ita ba, yar leƙen asiri ce”Walid ya ce “To tayi leƙen asirin, ai ba asirinka ta leƙa ba ko?””Ware, ban da naga kuna ta tata, da sai na saka tsumagiya na jiƙa mata jikinta, sai na yi mata mazinacin dukan da ba zata iya tashi ba, na rama muguntar da yayanta yayi mini a station”Viper yana gefe yana jin su, wasu lokutan faɗan Walid da liti nishaɗi yake saka shi, kamar sako da sako.Nabila wuni tayi da waya a hannu, amma shiru babu kiran Viper, shi ma haka ne, wuni yayi yana kallon wayar ta sa yana sauraren kiran wayarta, amma ba ta kira ba.***Nasir ne zaune a ɗakinsa, yayi zurfi sosai a cikin tunani, yana ta tuna wasu abubuwan da suka faru a ‘yan kwanakin nan sosai yake jin yana zargin Arfa tana aikata wani rashin gaskiya, da take ɓoyewa, mussman da ya ji ta ambaci viper lokacin da ta farfaɗo, ba zai yiwu a ce magagi ne kawai ba, kuma a yan kwanakin nan tayi watsi da lamarin cewa zata taimaka masa a kan nemansa balle ya ce tsananin saka abun a ranta ne ya sanya ta farko da sunansa, amma haryanzu yana son sanin dalilin da ya sanya Indabo ya ce zai yi tarko da Nabila ya kama Viper, menene haɗinta da shi?.Nabila tana zaune a kan gado, tana waya da Alhaji Wada, sai kashe murya take yi, wai ita haryanzu ba ta warke ba, ya biye mata sai sangarta take yi, kamar ba babban mutum ba yana lallaɓata, tun da ya ce zai kuma zuwa gida dubiya ta ce masa ai ta warke ba sai ya zo ba.Sallamar baba magajiya ce ta sanya tayi masa sallama, ta ɗago ta kalleta da murmushi.”Yauwwa yar gari, ai dama zuwa nayi na tashe ki, ki samu ki karya ki sanya wani abun a cikinki, ashe ma kin tashi “”Eh hajjaju, ina kwana””Lafiya lau, ya ƙarfin jiki kuma?”Nabila ta ce “Alhamdilillah da sauƙi””To Allah ya ƙara kiyayewa, ki cigaba da addu’a Allah ya ƙara tsarewa, dama mu ma addu’a cikin yin ta muke babu dare babu rana, Hasbunallahu wa ni’imal wakil, ki yawata faɗarta babu adadi, da yardar Allah ba dai mutum ba sai dai Allah”Nabila ta yi murmushi ta ce “Kin faɗa kin nanata mini, na daɗe da haddacewa ai””Kya ci ƙaniyarki da kin daɗe da haddacewa, zamanin nan na yanzu waya ce miki ana zama haka? Kana da ido ba na ganin gari ba, Addu’a kake tuƙuru iya yinka, baka san waye maƙiyin fili da na ɓoye ba”Sosai Nabila take dariya ta ce “Aikuwa maƙiyina yana ruwa, dan ni kaina ba wani cikakken saiti ne da ni ba in ji Abba””Ke ki yi addu’a kawai yar nan, tashi ki je ki samu abun da zaki ci” ta saukko daga kan gadon, ta fice falo tana miƙa, wayarta take kallo lokaci lokaci, duk kiran Viper take jira, amma shiru.Sauda ta kalleta ta ce “‘yar asara an fito”Nabila ta ce “Wallahi kuwa, Allah ya nufa barka da safiya, bazawara uwar son banza ga gadonki ga na asara””Arfa, me ki ka ce?””Sauda kin sani sarai bana shiru idan aka gaya mini babu daɗi, ni yanzu a kan tsini nake, magana ɗaya mara daɗi ki ka yaɓa mini, sai na yi miki goma mai zafi, ba girmata ba Allah ya sa haifata ki ka yi” Sauda za ta yi magana, ta jiyo takun Abba yana saukkowa daga kan bene, dan haka ta haɗiye maganar ta, tana kallon Nabila.***Abbu ne zaune a gefen gadonsa, fuskarsa sanye da farin glashi, ya zubawa hoton hannunsa ido. Shi da Zahra’u ne, da sadik, shi kuma hannunsa riƙe da Al’amin, bai fi shekaru biyu ba a lokacin, sai dai fuskar nan ta sa tamau, babu alamar fara’a.Murmushi Abbu yayi, tun Al’amin yana yaro baya son wargi, ba shi da faa’a, ya tuna yanzu a jikin hoton ba kowa sai Al’amin, shi ma ga yadda ya zama, rabon da ya saka shi a idonsa, tun fitowarsa daga prsion da ya zo masa nan, kusan shekara guda kenan.”Wai meyafaru ne kamar kuka fa kake yi?”Ya ɗaga kai ya kalli rahila ya ce “Kuka kuma?”Ta leƙa ta kalli hannunsa, ta kwaɓe baki ta ce “Kai ta wani abu kamar ƙaramin yaro, ka ɗauki hoto ka saka a gaba kana kuka, haba kai kuwa?” Yayi mata shiru bai ce komai ba.”Abbu, dan Allah magana nake so mu yi da kai””Ina jinki””Dan Allah ka yi haƙuri ka yafewa Abba, ya koma kasuwa, sai raragefe yake yi a gari da shi da Nazifi, ina tsoron kar su faɗa wani mummunan halin, rashin sana’a ga matashi babbar matsala ce”.Ya ƙare mata kallo ya ce “Rahila, nawa ɗan ma da ya kangare, sallama shi nayi, ba zai yiwu in cigaba da jan ɓarayi a jikina suna zalunta ta ba, su yi ta yawo babu sana’ar, ai uban su yana raye, ya nemi abun yi ya ba su””Ni kake kallon idona ka ke cewa yarana ɓarayi?””Na faɗa rahila, ba ɓarayin bane ba? Wane irin gata ne ban yi musu ba, ƙarshe rashin lafiya na kwanta aka rasa wanda zai zauna da ni a cikin su a asibiti, ƙarshe cewa ki ka yi kar na ga laifin su, ba hakkinsu bane ba, amma ni na riƙe su na ciyar da su, na kula da su, ni nawa hakkin ne? Yanzu nake ƙara danasanin biye miki, na wofantar da nawa ɗan, kuma ki tattatara su gaba ɗaya su bar mini gida, dan ba hakkina bane ba riƙon su”Cikin takaici ta ce “Wallahi ba zan rabu da ‘ya’yana ba, sai dai na tattara da ni da su mu bar maka gidan””Allah ya raka taki gona, ya tsare hanya”Cikin fargaba ta kalleshi ta ce “Au babu ruwanka kenan in tafi baka damu ba?” Tashi yayi, ya ja tsaki ya mayar da takardun gabansa ya bar ɗakin.***Nabila ta kasa jurewa, hankalinta ya fara tashi, ko wani abun ne ya samu Viper, duk da bai fiye kiranta ba, sai da ƙwaƙwƙwaran dalili, amma shirun yayi yawa. Yau take shirye-shiryen komawa wurin aiki, Barrister Habib ya tabattar mata da an gyara office ɗin ta, an canza mata wani.Har ta shirya ta tsaya, ta kira lambar Viper.Yana kwance idanunsa a lumshe, yana ɗan kaɗa ƙafa, ya ji ringing ɗin wayarsa.Ganin lambarta sai da ya yi ajiyar zuciya, amma ya zubawa wayar ido, sai da ta kusa katsewa, sannan ya ɗaga kuma yayi shiru.”Hello Viper””Salamu alaikum” ya faɗa a nutse.”Wa’alaikum Salam, kana lafiya?””Ƙalau”Cikin marairaicewa ta ce “Wai baka san abun ya same ni bane ba? Kwana nawa baka ga kiran wayata ba baka neme ni ba, wrong connection na wearing aka yi a office ɗina, wuta ta shi, aka rufe ni ta waje fa””Na sani””Ka sani?”Ya ce “Eh”Cike da takaici ta ce “Kuma ka kasa nemana a waya, da mutuwa na yi fa””Allah ya jiƙanki, zahra ma da mutu haƙuri nayi, balle ke. Sai ki ƙara taka tsantsan da abubuwan da ki ke yi”Wani ƙululun takaici, ya tokare mata wuya, sosai ta ji zafin abun da ya ce mata, kawai ta katse wayar.Walid ya ce “Viper, kamar baka kyauta ba fa” yayi masa shiru, hakan ya sa shi ma yayi shirun bai kuma cewa komai ba.Baƙin ciki da ɓacin rai ya sanya, babu wanda ta yi wa sallama a gidan ma, tayi tafiyarta.Tana tafe a hanya ta din ga jin wani abu mai kama da kishi, da ɓacin rai yana taso mata, har ga Allah ba ta san jauhar ba, amma tana son ta saboda Allah, amma abun da yayi mata yau, ya sanya ta ji ranta ya sosu.”Meyake damuna ne? Wai son bawan Allah nan nake yi? Na shiga uku me yake shirin faruwa da ni ne? Idan ta tabatta son shi nake yi, na yi wauta, to yaya ma za ayi hakan ya yiwu abu daga wasa?” Har ta ƙarasa wurin aiki, tunani take a zuciyarta. Tayi shiru tana sauraren zuciyarta dan ta tabattar da abun da take tunani gaskiya ne ko akasin haka, amma bata kai ga hakan ba, aka ƙwanƙwasa glashin motarta, masu gadi ne suke yi mata barka da dawowa, tare da yi mata sannu da jiki”.Ta saukko daga motar, suka gaggaisa, sannan ta shiga ciki, a cikin ma murnar ganinta suka din ga yi suna yi mata sannu.Ko mintuna talatin ba ta yi a sabon office ɗin ba, barrister Habib ya ƙaraso.”Autar lauyoyi, ƙaramar su babbar su, aminiyar sumy, ƙaramar sauro ka da ƙatuwar giwa, ba giwar ba hatta toron ma kayarwa ki ke yi”Nabila ta yi murmushin yaƙe ta ce “Ni har ka bani kunya ma””To yaya jikin naki?””Alhamdilillah yayi sauƙi sosai”Ya ce “Masha Allah, yanzu ya ake ciki da batun shari’ar nan? Zamu je prison ɗin ne wurin mutumin?””Za a bari mu ganshi kuwa?”Habib ya ce “Za’a bari mana ba dole ba, ai na je lokacin kina gadon asibiti, ba na son abun da zai kawo tsaiko a harkar shari’ar gaba ɗaya” “Kai amma na gode sosai yaya habib “”Kar ki damu Nabila, ba ke ba, hatta ni na ji haushin yadda shari’ar nan ta gudana, kuma cin mutuncin harkar shari’a ne, a wannan karon zamu yi nasara in sha Allah “”Allah ya sa yaya Habib” suka fito suka hau motar barrister Habib suka fita.Nasir da yake bin Nabila a wata motar, ya ga fitar Barrister Habib da Nabila, ya sake rufa musu baya, sannu a hankali ba tare da sun san yana bin su ba, sai dai azabar kishi ya sanya ya ji har wani dishi-dishi yake gani.A wannan karon Nabila tayi mamakin yadda aka basu damar ganin baba maigadi, ba tare da an raina mata hankali kamar yadda aka saba ba.Suka gaisa cikin mutuntawa, duk ya rame yayi wani iri.”Baba, ina mai sake baka haƙuri, amma ban karaya ba, in sha Allah zamu ɗaukaka ƙara ne”Jiki a sanyaye Baban ya ce “Kina ta ɗawainiya, ni idan babu hali, kawai a bar maganar nan, na bar wa Allah”Barrister Habib ya ce “No ba zai yiwu ba, ka manta yadda muka yi da kai wancan zuwan da nayi muka haɗu?”Yayi shiru ya sunkuyar da kai.”Ka yi magana mana, mun yi magana da kai fa sosai baba, ka bata haɗin kai dan Allah, a wannan karon muna fatan ayi nasara, ka yi mata bayani, saboda ƙoƙarin kamanta gaskiya har nema aka yi a sabauta rayuwarta, ka yi magana baba, ka yi mata bayanin komai.Nabila let’s record it Incase”Ta jinjina kai ta ɗaukko wayarta, ta danna recording ta ajiye.Cikin tsoro ya ce “Dan Allah to kar ku gaya wa kowa, kun ga yarana duka mata ne, na aurar da wasu, ina da biyu ƴan mata, an ce muddin na yi magana abun da ya samu ramma zai same su, koma su rasa rayukansu gaba ɗaya tsoro nake ji” mamaki ya cika Nabila, dan ita duk bai yi mata wannan maganar ba.”Baba, ni na baka tabbacin nan, babu abun da zai samu iyalanka, ka ba ta cikakken haɗin kai, idan ka bari ta sake faɗuwa a shari’ar nan, kaga magauta sun yi galaba a kanta, kuma yayan da ka ke yi wa, ka ɓata musu suna”Ya jinjina kai ya ce “Ana saura kwana biyu uwar ɗakin hajiya jidda, tayi waya ta ce aje garin su ramma, ta dawo su haɗu da ɗaya mai aikin, ayi mata gyaran gida, saboda tana ji da Ramma sosai, tana da biyayya, kuma bata yi mata sata.Ranar an ɗaukko ramma, suna ta aiki, zulai ta tafi kasuwa, ɗan yayar matar gidan ya zo, sunansa Abdul, ban daɗe da fara aiki a gidan ba, dan babban mutum ne sosai mutumin, in da suka baro, jami’an tsaro ne suke yi masa gadi. Unguwar nan da suke ne, jami’an tsaro layuka suke gadi, ni kuma aka samo mini buɗe ƙofa da rufewa a gidan.Bayan yayi mata, ya tafi zulai ta fito tana kururuwa, bayan ta dawo daga wurin sayen kayan miya. Bayan mun kai ta Asibiti, magana ta bazu, aka ce an sallame ni daga aiki, amma za a neme ni, daga baya yan sanda suka je gidana suka tafi da ni, wai zan ba da bayanin abun da na sani, muna zuwa aka rufe ni aka ce ni ake zargi, kuma aka yi mini barazana da muddin na ce bani bane ba yarana na cikin haɗari”Nabila ta ƙulu ta ce “Amma meyasa baka yi mini wannan bayanin ba ni, na san ta ina zamu ɓullowa lamarin? Nayi ta wahalar neman shaida ka kuma ƙi bayani a kotu”Barrister Habib ya ce “Kwantar da hankalinki, ki yi haƙuri kin san uba da ‘ya’ya””Ki yi haƙuri na san nayi kuskure amma a tsorace nake ne nima”Ta kalleshi ta ce “Ya sunan mai gidan?”Ya girgiza kai ya ce “Ban sani ba””Ya za ayi ka yi aiki a gidan wanda ba ka san sunansa ba?” Yayi shiru ya sunkuyar da kai.Barrister Habib ya ce “Tashi muje, ma ƙarasa sauran aikin” haka suka fito Nabila tana mita, barrister Habib yana bata haƙuri.Law firm ɗin suka koma, suka fara arranging ɗin yadda zasu yi appeal, sun gama ta fito suka haɗu da barrister Kabir, yayi mata sannu, tare da yi mata kashedi, a kan ta raba kanta da aikata duk wani abu da zai sanya ta shiga matsala, ta bishi da to, ta fita ta shiga motarta ta nufi gida.Nasir bai ga wani abu ba a bibiyar Nabila da ya yi yau ba, amma bai ji zuciyarsa ta gamsu ba, ya sakawa ransa zai yi assigning wani wanda zai din ga bibiyar masa ita lokaci zuwa lokaci.***Su liti suna karyawa, Viper kuwa yana zaune yana yanke farcensa da nail cutter.Wayar liti aka kira, ya karɓa ya ɗaga ya ce “Ya ne?””Normal, kwana biyu ba ku shigo gada ba fa””Eh ka san yanayin ne, sai muna bayyana muna ɓacewa, meye labari?””Baban Viper ne ya zo rumfa, ya na neman ka, ko kai ko walid” liti ya kalli walid ya kalli Viper.”Meyafaru yake nemanmu?”Ya ce “Ban sani ba, ya dai tambaye mu, ko Viper yana zuwa wurin, muka sanar masa rabonmu da shi, tun kafin a kama shi, shekara shida kenan”Liti ya ce “Normal ne, zan faso fatan rumfa komai lafiya?””Lafiya ƙalau tana ta garawa”Ya jinjina kai ya ajjye wayar.Liti ya cigaba da kallon Viper, Viper bai kalle shi ba ya ce “Ko dai ka yi magana, ko kuma ka daina kallona””Allah ya baka haƙuri, na daina kallonka” kamar ya gaya wa Viper, zuwan mahaifinsa rumfar shayinsu, sai kuma ya fasa ya haɗiye maganar.***Abdul ne yayi sallama a falon, ya shigo a gajiye, ta amsa sallamar tana tashi zaune daga kwancen da take.Ya ajiye jakarsa, ya kwanta a jikinta ya ce “Wash”Ta ce “Sannu””Yauwwa sweetheart” ta kama hannunsa, ta cire masa agogon hannunsa.”Tashi a cire safar””Ki bari na huta na gaji”Ramma ta ce “Ƙato da kai kana shagwaɓa, wataƙila ma ba wani aiki ka yi ba kake wani wash”Ya ce “Kaii, baby kin san mutum nawa na yi wa tiyata kuwa? Ga kusan asibiti uku naje na ga marasa lafiya””To tashi ka yi wanka, ka ci abinci” ya kalleta ya yi murmushi ya tashi zaune, ya shafa kanta ya ce “Allah ya yi miki albarka babyna, i so much love you” yayi maganar yana sumbatar goshinta.Kallonsa take yi, tana son jin matsananciyar tsanarsa a zuciyarta, amma abu ya gagara, sai wani ma kyau da ta ga yayi mata.Ya tashi ya tafi bedroom, yayi wanka, Ramma ta goge hawayenta tana fatan Allah kar ya jarrabeta da son Abdul.Yayi salla ya fito, ta bashi abinci.”Beb, in sha Allah komai ya kusa zuwa ƙarshe, zan bayyanawa duniya ke, ina daf da gayawa babana maganarki, a san yadda za a gyara lamarin mu cigaba da rayuwarmu, am ready na ɗauki kowane risk mu zauna tare in sha Allah my rahama”Tayi ajiyar zuciya tare da murmushi.”Dan Allah ko sau ɗaya ki ce kina so na mana””A’a ni ban iya ƙarya ba”Ya ce “Zaki yi bayani ne”***”Hello masoyiyyata”Nabila ta ce “Na’am sumy kalar kyau””Albishirinki?””Kuɗi dubu goma”Sumayya ta ce “Mayyar kuɗi, ba za a bayar ba”Tayi dariya ta ce “Fesa mini””Arfa ranar monday in Allah ya kaimu, zan fara aiki, ni da yaya murtala zamu buɗe gidan radion”Nabila ta miƙe ta ce “Dan Allah masoyiyya””Wallahi da gaske, ke Allah ne ya kawo mana mafita, an bani damar ƙirƙirar programs, har na sami program ɗin da zamu din ga yi tare, mu ci karenmu babu babbaka, babu mai yi mana barazana da daka tsawa”.”Ke gani nan zuwa gidan naku ma, tare da ni za a buɗe gidan rediyon nan in sha Allah”Duk wannan abubuwan da Nabila take yi, ƙarfin hali ne kawai, zuciyarta na tare da Viper, tunaninsa kawai take yi, tama rasa wane irin tunani take yi a kansa, ga zuciyarta da take ta azalzalarta da son ganinsa.Tare da Nabila aka yi bikin buɗe sabon gidan radio, mutane suka din ga kiran wayar suna yi wa Sumayya fatan alkhairi, tare da tabattar mata da duk in da ta tafi suna tare da ita.A program ɗin farko da suka fara yi da sumayya, suka sanya masa suna ƙeƙe da ƙeƙe.Tun da sumayya ta gabatar da Nabila, kasancewar masu saurare sun santa a bakin sumayya, suke ta tura saƙonnin gaisuwa, wasu kuma suna tambayarta dalilinta na ƙalubalantar bunkure foundation, duk da irin gudunmawar da take bawa al’umma.Sumayya ta ce “Masoyiyya, kin ji tambayoyin masu sauraro mai zaki ce?”Nabila ta yi murmushi ta ce “Babu abun da zan ce, sai su kasance da mu a sabon shirinmu, na ƙeƙe da ƙeƙe. Ba wai bunkure foundation ba, duk wani abu da ake kitimurmura a cikin sa, ko rashin adalci zamu yi bajekolinsa a wannan shiri, kuma program zai iya bi ta kan kowa, duk wanda ya ga kuma an yi masa ba dai-dai ba ya ƙalubalance ni a gaban shari’a.Manyan shari’oi da aka yi bita da ƙulli a ciki, yadda ake danne hakkin mara galihu ake tsayawa yaran masu kuɗi, yadda ake wasa da hankalin talaka, da tauye masa hakki, shi fa wannan program ɗin, kai har da shari’ar wani gawurtaccen matashi da ya shahara, jami’an tsaro suna nemansa, sai dai abun mamaki shi ne sai da ya shafe shekaru biyar ba ayi masa shari’a, a shekara ta shida aka sake shi, kuma yanzu an ce ba bisa ƙa’ida aka sake shi ba wai nemansa ake yi.Akwai tarin kwamacla a harkar shari’a a ƙasar nan, a shirin ƙeƙe da ƙeƙe zamu fayyace abubuwa da dama, na ban mamamki” suka ƙarƙare program ɗin cikin wasa da barkwanci.***Alhaji wada hankali kwance yake zaune yana shan lemo a kofi, yana kallon indabo da yake ta haƙilo yana magana.”Karofi, ka shiga gonata da yawa, ka kiyayeni, muddin kana son yarinyar nan ta rayu, ya zama dole ka takawa shirin nan da zasu fara gabatarwa burki”Karofi ya ce “Sabod me? Kai da kake ɗaukar nauyin gidan radion ka ake abun da ka ke so waye ya hana ka? Ni na ɗauki nauyin program ɗin dan haka babu ruwanka da abun da ake yi””Karofi, ka san na fi ƙarfin kafi ga bayana ko?””Ai ka san shi ƙarfen cikin wuta sai da ɗan uwansa ƙarfe, babban mutum mai kima a ƙasar nan, bai kyautu ace ka na ɓata lokacinka a kan wata ƙaramar alhaki kamar wannan yarinyar ba.Auuu ashe fa ta sako wani zance a maganarta, mai kama da maganar Al’amin Viper, wato mai zamani. Kana tsoron ta tona maka asiri cewa kai ne ka saka aka kashe matar Viper ko? Ka kwantar da hankalinka ba ta san wannan labarin ba, idan har ba tana haɗuwa da Viper ba ya gaya mata da kansa”Wani irin shock indabo yayi, ya sandare a tsaye, jin yadda Alhaji mu’azzam wada kankarofi yake farke sirrin da bai taɓa tunanin wani mahaluki ya sani ba.
Ayshercool 08081012143





