Halysaah Page 106 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 106Khaleesat na zaune Departure lounge waiting for their flight to America bayan sun sauka garin Abuja, once a while take daga ido ta kalli Ajay da ke ta danna wayarsa don separately suka zauna far away from each other, gashi ko kallon inda take baya yi kamar ma ba tare suke ba, a hankali ta bude handbag dinta ta ciro wayarta dake kashe ta kunna, rabonta da wayar tun bayan da aka daura mata aure da abun duniya ya isheta ganin bata samun Jay a waya, bayan ta kunna taga tana da sauran caji, tasan har Safiyyah ta gaji da yi mata WhatsApp message, kilan in ta ji shiru tayi ma Aunty Farida magana, subscription ta fara yi kafin ta bude WhatsApp dinta, last message din da Sophie tayi mata ta bude tana dubawa taga tana ma online at the moment, hawaye ne ya cika idonta bayan ta karanta message din, kawai tace mata hm, message din na tafiya sai ga WhatsApp call Safiyyah ta doko mata, picking tayi ta kai kunne cikin sanyin murya tace “Sophie” Cikin farin ciki Safiyyah tace “Yau ni naga ikon Allah wajen matar nan, daga yin aure sai kashe waya Coursemate?? wato don ma ki ci amarcin ki cikin lumana babu me takura ki da Housemate, shi dama angon is always not replying messages, wallahi nayi missing dinki sosai Khaleesat you won’t understand, yaushe za ku dawo plss, kinsan fa Monday za mu yi resuming” Khaleesat dake ta sauraron maganganun Safiyyah ta sauke idonta cikin sanyin murya tace “Yau za mu taso in sha Allah Sophie, nan da few minutes za mu yi boarding plane din” Safiyyah ta zaro ido with excitement tace “Don Allah da gaske kike kawata, na zata fa sai nan da sati biyu za ku ce zaku dawo, toh Allah Ubangiji ya kawo min ku lafiya, har girki kuwa zan maku wallahi, i will even meet you people at the airport, Ina Housemate din? Plss ki ce ina gaishesa sosai” Khaleesat ta kasa cewa komai, lokaci daya taji hawayen da ya taru idonta na zubowa, Safiyyah tace “Hello are you der?” Da kyar Khaleesat tace “Za mu yi boarding yanxu, bye” Safiyyah tace “Toh shkkn, pls in layover za ku yi ki min magana a kasar da ku ka sauka, na ma san Layover ne, sai in san sanda za ku iso so that i will be at the airport” Cikin sanyin murya Khaleesat tace “Ohk, bye” Daga haka ta katse wayar ta mayar cikin jakarta ta daga kai tana kallon Ajay fuska daure. After some more minutes Khaleesat suka yi boarding jirgi and they were among the few first to board kasantuwar first class passengers ne su, sake kallon ticket dinta tayi da mamaki don duk tunaninta Business Class ne, this is her first time flying first class and it was strange to her ganin luxury din, Duk da comfort and premium luxury na first class ita kam she wasn’t comfortable bayan tashin su Abuja da few hours saboda Motion sickness da ya taso mata wanda bata fiye yi ba ma a jirgi sai ko in tana cikin damuwa, sau uku tana zuwa lavatory in taji amai ya taho mata, Flight attendant din was trying all possible best to see she is comfortable don da ta tafi zata dawo still to check on her and see if she’s okay, sosai ta bata kulawa Flight attendant din, har daga karshe Khaleesat tayi converting seat dinta into lie flat bed tace mata zata yi bacci sannan ta kwanta ta rufa har kanta da blanket, duk Ajay na kallonsu ko da ba kusa suke ba cause there is enough space separating them, bayan kusan awa daya Khaleesat taji an sauke blanket din da ta rufe har kanta da shi, bude ido tayi suka hada ido da shi, yana duke yana kallonta babu yabo babu fallasa yace “Are you okay?” Da hanci ta amsa masa sannan ta kara jan blanket dinta zuwa kafadanta ta juya masa baya ta rufe idonta, mikewa yayi ya koma seat dinsa ya zauna, har jirgin su ya sauka London for stopover Ajay bai sake ce mata komai ba a jirgin. A cikin airport din ma ko kusa da inda take bai zauna ba suna jiran connecting flight dinsu to Baltimore, ita dai taki zama sai Safa da marwa take a Departure Lounge, she looks so uncomfortable, lokaci lokaci take satan kallonsa duk da yaki ma kallon inda take kamar bai san Allah yayi ruwanta ba, can dai ta dake ta nufi inda yake zaune ta tsaya amma kuma taki kallonsa tana wasa da veil din jikinta, daga kai yayi ya kalleta dai dai sanda ta saci kallonsa, tana ganin sun hada ido ta ɗan turo baki ta sauke idonta a hankali tace “I am having issues” Kallonta kawai yake jin abinda tace, Tayi kasa da murya tace “I need sanitary pad” Ajay ya dauke idonsa yayi shiru kamar me nazarin abinda ta fada, after almost a minute ya daga kai ya sake kallonta yace “Do I look like a pad vendor?” Ita dai taki kallonsa har sannan kuma bata fasa wasa da gefen gyalenta ba, bai sake ce mata komai ba tsabar mamaki ya tallabi chin dinsa yana girgiza kafa, can dai ya kuma kallonta yace “So as the lady you are you don’t even know ur Cycle to prepare ahead?” Nan ma dai Khaleesat taki kallonsa taki cewa komai, Gyara zamansa yayi yace “Thank God is ur self you are going to disgrace here not me, nayi maki kama da me siyar da sanitary pad da zaki ce min you need sanitary pad, ko kuma amfani nake da sanitary pad?” Kamar zata yi kuka tace “Ni dai don Allah ka duba min kafin a fara boarding….” Jin yayi banza da ita kuma babu alamar zai tanka mata don wayarsa ma ya hau dannawa, tana ta tsaye for almost 5 minutes a wajen, a hankali ta juya kawai ta bar kusa da shi ta koma can inda take tsaye ta ci gaba da tsayuwarta tana kallonsa, after some minutes ta ga ya mike, daya daga Lounge staff din dake wajen Ajay ya nufa for assistance or even a concierge service request if possible don bazai iya fita daga Departure lounge din just like that ba, not too long after sai ga shi an kawo masa sakon da ya bukata, tun da Khaleesat taga Ajay ya nufota rike da ledan Sanitary pad tayi saurin dauke kai kamar bata san yana zuwa ba, yana isa gabanta ya mika mata ledan, bata yarda ta hada ido da shi ba ta amshi ledan a hankali tace “Nagode” Kamar jira yake yace “Kazamar mace ce kawai bata san when her period is going to be due ba…” Yana fadin haka ya juya ya bar wajen, ta bi sa da wani harara tana turo baki, daga karshe dai suka yi boarding jirgin da zai kai su Maryland wajen karfe takwas saura na safe, after 8 hours trip kuma suka sauka airport din Baltimore, sosai Khaleesat tayi farin cikin ganin Safiyyah da ta zo tarbanta a airport har da tsadadden bouquet of flowers dinta, Khaleesat ta rungumeta tare da flowers din looking so happy, Safiyyah ta bi Ajay da ya wuce su da kallo baki bude, can ta kalli Khaleesat tayi kasa da murya tace “Shi kuma wannan fa? Har da shi ku ka dawo dama?” Sai kuma ta fara kalle kallen inda zata hango Housemate shi kuma, ganin bata ga alamar sa ba tace “Ina Housemate din?” Khaleesat ta kasa ce mata komai tana kallonta, lokaci daya hawaye suka cika idonta, da mamaki sosai Safiyyah tace “Kuka kuma? Me ya faru? What’s happening?” Khaleesat ta rungumeta hawaye masu zafi na zuba idonta ta fara shesshekan kuka, Safiyyah was speechless at first ta ma rasa ta ina zata fara magana don duk zurfin tunaninta bata kawo dalilin kukan Khaleesat a ranta ba a wannan lokacin, ta dago kanta tana kallonta tace “Tell me what is happening mana pls Khaleesat? Ina Housemate din? Ko dai ba ayi auren bane tukunna? but ke kika ce min an daura ai, and that was the last time we chatted, da naga baki online since after then nayi chatting Aunty Farida tace min ai har an kai ki Bauchi” Khaleesat ta fara goge hawayen da ya ki tsaya mata, ganin ba magana zata yi ba kawai Safiyyah ta kama hannunta suka bar wajen, suna tafiya a hankali cikin sanyin murya Khaleesat tace “Sophie, Housemate isn’t my husband!” Safiyyah ta tsaya ta juya tana kallon Khaleesat da sauri babu ko kiftawa tace “I don’t understand” Khaleesat ta sauke idonta wasu hawayen na sauka idonta da kyar tace “Yes, he isn’t” Safiyyah that was so confuse tace “Then who is the Husband? Don Allah ki gaya min Khaleesat….” Khaleesat ta kasa cewa komai hawaye sai kai kawo suke a idonta taki dago kanta, A hankali Safiyyah dake gwalo ido tace “Ajay?” Khaleesat ta daga idanuwanta ta kalleta with more tears rolling down her cheek ta gyada mata kai trying not to burst into cry, kallonta kawai Safiyyah take babu ko kiftawa kana ganinta kasan ba karamin girgiza tayi ba a inda take tsaye kamar warce ruwa ya cinye, they stood there for more than 3 minutes babu wanda yace komai cikinsu, Safiyyah was just staring at her kamar gunki don ko kwakkwaran motsi bata yi, ita kuwa Khaleesat sai share hawayen da yaki tsaya mata kawai take, daga karshe Safiyyah ta kama hannunta a hankali suka ci gaba da tafiya slowly, kana ganin Safiyyah kasan she is more than shock and speechless at the same time, tsaye suka samu Ajay jikin motar da zai kai su gida ya rungume hannu fuskarsa babu yabo babu fallasa alamar su yake ta jira, driver din da ya zo daukansu daga gida har ya gama saka traveling luggages dinsu gaba daya a bayan mota, Safiyyah na kallonsa with calmness tace “Ina yini, ya hanya?” Ajay yace “Alhamdulillah” Ta juya ta kalli Khaleesat da idanuwanta har sun yi jajir saboda kuka tana ɗan murmushin karfin hali tace “Kawata zan koma can gida in dauko abincin da na girka, i will call you to know where to bring the food for you” Kai kawai Khaleesat ta gyada mata, Safiyyah ta kalli Ajay tace “To sai anjima, zan je in dauko mata abinci a gidanmu” Ba tare da Ajay ya kalleta ba yace “Ohk, you can get in the car and tell the driver ur Address” Daga haka ya zaga ya shiga front seat, Safiyyah ta ɗan yi jim, can kuma dai ta bude bayan motar, sai da Khaleesat ta fara shiga sannan ita ma ta shiga ta kulle motar, a haka suka bar airport din, dai dai gidansu Safiyyah Drivern yayi parking bayan ta nuna masa sannan ta kalli Khaleesat tace “Ina zuwa” Bude motar tayi ta sauka ta nufi apartment dinsu, few minutes later sai ga ta ta fito da warmers din abinci biyu Khaleesat ta bude mata door din motar ta amshi warmers din ta ajiye su tana kallon Safiyyah a hankali tace “To ki shigo” Safiyyah ta ɗan kirki murmushi bayan ta saci kallon Ajay ta gefen ido tace “A’a ki dai je gida ki huta, ko gobe sai in zo in sha Allah” Nan da nan hawaye ya cika idon Khaleesat tana kallonta pleadingly alamar ta shigo motar, Shi dai Ajay ko kallonsu bai yi ba, Safiyyah ta sauke boyayyen ajiyar zuciya ganin hawayen idon Khaleesat ta kara satan kallon Ajay, sai kuma ta zaga ta daya side din motar ta bude ta shiga ta kulle sannan driver ya ja motar suka bar unguwan, wajen karfe biyar suka isa gidansu Ajay, bayan driver yayi parking a parking lot Ajay ya bude motar ya nufi entrance din gidan, Safiyyah ta bi sa da kallo sai kuma ta taɓe baki tana gyada kai murya can kasa tace “Tabɗijam” Bude motar tayi ta sauka rike da warmer daya na abinci, Khaleesat ma ta sauka tana rike da handbag dinta da dayan warmer din, a haka suka nufi cikin gidan driver na biye da su da traveling boxes dinsu, suna shiga babban parlorn suka tarar da babu kowa ciki, but everywhere was sparkling clean ga wani daddadan kamshi da parlon ke yi, Safiyyah ta zauna kan kujera tana kallon Khaleesat tayi kasa da murya tace “Khaleesat how did you agree to this? Menene ya faru har haka ta kasance? Dama ana switching aure all of a sudden just like that? Bar masa ke Jay din yace yayi kenan? Kuma me ya janyo hakan? Cewa yayi yana son ki shi ma shine Jay ya hakura? Da wani bakin ya iya budewa ya fadi hakan? Bai ji kunya ba? Budurwar brother dinsa fa? Does this look normal at all? Ke da wani ido kike kallon Jay yanxu? Shkkn wannan ne makomar azababben soyayyar da ku ka yi da Jay kenan? Is this how everything ended? Ko dai kuskure aka yi gun daurin auren aka daura da shi cikin rashin sani sai kawai aka ce ayi hakuri aje a haka tunda aure ya dauru? Don Allah ni dai ki fahimtar da ni wallahi kaina bai taɓa kullewa irin yau ba, i am so confuse Khaleesat, Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un” Khaleesat dai ta sunkuyar da kanta duk tana jin abubuwan da Safiyyah ke cewa tayi shiru hawaye na zuba idonta, Safiyyah ta kalli sama da sauri jin Footsteps, shiru tayi ganin Ajay ne ke saukowa downstairs, yana isowa cikin parlon ya kalli Khaleesat yace “Ai kinsan dakin da kike zama a gidan nan, so you can go accommodate your self there” Yana fadin haka ya nufi inda zai yi leading dinsa to the kitchen of the house, Safiyyah ta bi sa da wani kallo, can ta taɓe baki ta mike ta dau abincin Khaleesat tayi kasa da murya tace “Tashi mu je ki bani amsar tambayoyina, ta yaya kika yarda da auren nan” Daga haka ta kama hannun Khaleesat dake goge hawayen da ke zuba idonta suka wuce sama zuwa Bedroom din da take zama idan tana gidan, suna shiga dakin wanda shi ma was sparkling clean Khaleesat ta ajiye handbag dinta kan gado cikin sanyin murya tace “Wanka zan yi Sophie, na gaji sosai” Safiyyah tace “To je kiyi bari in shigo maki da sauran kayan ki, amma wanne ne akwatin ki a kayan kar in taɓo ma kaina masifa?” A hankali Khaleesat tace “Duk nawa ne kayan” Safiyyah tace “Atoh” Sannan ta fita daga dakin, Khaleesat ta cire kayanta ta shiga bandaki, ko da tayi wanka ta fito har Safiyyah ta ciro mata kaya mara nauyi a tsadadden akwatin lefenta, da kayan shafanta, Khaleesat ta gama shiryawa sannan ta kwanta gefen gado tana kallon abincin da Safiyyah ta zuba mata, Safiyyah tace “To ki yi sallah mana sai ki ci abincin kafin ki kwanta” Khaleesat ta girgiza mata kai tace “I am not praying” Sai kuma ta sauko daga kan gadon ta zauna kan lallausan milk carpet din parlon ta jawo plate din abincin da Safiyyah ta dibar mata a hankali ta fara ci, ko da ta ci sake komawa tayi ta kwanta, ganin she looks so tired sai Safiyyah bata bukaci amsar tambayoyin da ta tula mata ba daxu ta kyaleta kawai, after some minutes bacci ya dauke Khaleesat. A hankali Khaleesat ta bude idonta ta fara kalle kallen dakin da take ciki, ita kadai ce a dakin bata ga Safiyyah ba, wuta mara haske sosai ne kunne a dakin which made her realize it’s already dark, ta jawo handbag dinta a hankali ta ciro wayarta don ganin karfe nawa, ta ɗan bude ido ganin karfe goma saura few minutes, ajiye wayar tayi dai dai sanda aka bude kofar dakin, juya fuskarta tayi zuwa daya side din duk da bata san who open the door ba, after some seconds taga an kunna wutan dakin zuwa me haske tarr, zagawa yayi zuwa ta inda take facing a dakin suka hada ido, dauke idonta tayi, taji yace “Daki kike jiran a kawo maki dinner?” Without looking at him tace “Did I even say I am hungry?” Bai tanka ta ba ya juya ya nufi kofa ya fita daga dakin closing the door, mikewa tayi zaune tayi tagumi, ta fi minti talatin a haka sai kuma ta jawo wayarta ta bude WhatsApp, DM dinta da Jay ta shiga ta dinga kallon last message da ta ajiye masa da bai yi reply ba har yau, hawaye ta ji ya cika idonta, jiki a sanyaye tayi typing din sunan da take kiransa wato Housemate tayi masa sending, after a while ta kashe data dinta ta ajiye wayar don bata ga alamar yana online ba, komawa tayi ta kwanta tana goge hawayen dake sauka idonta.*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah ur evidence 07087865788*
