Uncategorized

Macijine Page 63-64 Hausa Novel

Elegant online writers📚📚

Free book 

Page 63/64

_______________Jikin nanny ne yayi sanyi sosai,ganin Adeeb atsaye,kuma ya gansu tare da amma,tasan yanzu kam kome zata faɗa masa ,bazai taba yarda da ita ba.ahankali take takawa zuwa gareshi,gaba ɗaya jikinta ba kwari,

Shikuwa Adeeb yana tsaye ya kafeta da Mayun idanunsa ,masu sanya mutum yaji shi cikin tsoro da fargaba.

Nanny Tana karasowa tace “magajin fada ,fushi kake dani ko”?

Ta fada cikin sanyi murya  da mutuwar jiki.

Lumshe ido Adeeb yayi ,zuciyarsa na masa zafi yana mamakin abinda nanny tayi masa,ace wai nanny ta hada kai da maƙiyarsa tana tayata ƙoƙarin cutar dashi,matar daya ɗauka matsayin uwa ?mutum kenan.

“Ko kaɗan nanny bana fushi dake,kawai ina godiya ga Allah ne ,daya nunamin gaskiya ,na gane irin mutanen da nake tare dasu,na daukeki tamkar mahaifiyata nanny,Amma bansan nayi babban kuskuren yin hakan ba,dan Allah kiyi haƙuri”ya faɗa yana mai haɗe hannayensa guri ɗaya alamun neman afuwa.

Sosai nanny kejin ciwo cikin ranta ,damuwa da taraddadi sun cika mata zuciya,dama tayi wannan tunanin,tasan idan har Adeeb ya gansu  tare da amma ,to shikenan,kuma kome zata faɗa masa bazai yarda da ita ba,amma Allah shine shaida bata da nufin cutar da Adeeb ko kaɗan.

“Magajin fada wllh abinda kake zargi ba haka bane ,kada ganina tare da amma yasa maka kokwanto akaina, wllh nima Ina jinka tamkar tareeƙ bazan taɓa cutar dakaiba magajin fada.

Nanny ta faɗa cike da damuwa aranta.

Girgiza kai kawai Adeeb yayi tare da barin gurin,zuciyarsa kamar zata fashe tsabar damuwa .

Kallonsa kawai nanny keyi,tana fatan Allah yasa ya gane gaskiya cikin sauri kafin komai ya daɗa lalacewa.

Ba kowa cikin falon ammi,sai ƙamshi dake tashi ta ko’ina ,dan ammi akwai son kamshi,kai tsaye ya nufi dakin kwananta, nocking yayi amma shiru,hakan yasa shi shiga cikin dakin kai tsaye.saidai nan ma ba kowa cikin dakin.

Download>>> The Governor Wife Book 3 Complete Document

Harya juya  zai fice ,sai kuma zuciyarsa ta raya masa ya duba wanann akwatin da yaji ammi na  magana akanta.

Dan haka juyowa yayi yana karewa dakin kallo.

Ahankali yake duba dakin dan neman wannan akwatin,amma yayi iyakar dubansa bai ganta ba.

Harya hakura sai kuma ya hango wata akwati mai kyau da ɗaukar ido,yasan akwatin Dan acikinta ammi ke ajiye kwalakwalanta ,dan haka sai yayi tunanin ba komai cikinta,  har ya juya  da nufin barin dakin,sai kuma zuciyarsa ta kwadaitu da son duba akwatin . 

Dan haka ahankali ya zauna tare da ɗauko akwatin, danna lanbobin bude akwatin yayi,dan kuwa tuni yasansu, aikuwa saiga akwati ta bude,gwalagwalai ne acikinta iya ganin ka ,masu kyau da ɗaukar hankali,kallo ɗaya zaka musu kasan an zubar da maƙudan kudade wajen mallakar sarkokin.

Dubawa yayi tayi amma baiga  komai aciki ba,sai wani dan karamin akwati mai kyau da ya gani,kallon akwatin yake da mamakin meye acikinsa aka wareshi ?lallai yana son ganin abinda ke ciki.dan haka hannu Ya mika tare da ɗauko akwatin ya bude.

Mamaki ,al’ajabi ruɗu da kuma faduwar gaba sune suka ziyarci zuciyar Adeeb,sakamakon ganin sarƙar nan ta Hulwa data bace ,cikin wannan akwatin,

Me yakawo sarkar Hulwa cikin kayan ammi?har akayi mata adana ta musamman?me hakan ke nufi,shidai yasan ammi tana da sarkokin da suka ninka kudin wannan bare yayi tunanin ta daukene dan bata da mai tsada kamar wannan ,to me hakan ke nufi kenan?innalillahi meke faruwa ne acikin gidan nan?kodai akwai Abinda ammin nashi ke kullawa da gaske ? Wayyo ina zaisa kansa ?dawa ya kamata ya yarda ne cikin fadar nan? Dauko sarƙar yayi cikin sauri ya maida komai inda yake sannan yayi saurin barin dakin na ammi ya koma part dinsa. Zuciyarsa na zafi kamar zata kama da wuta .

Lokacin daya koma part din nasa fattu ta farka,tana zaune tana kuka,tsoro takeji,har lokacin barin ma dataga ita kadaice cikin dakin,ina Hamma ya tafi ya barta?karfa wannan Rashad din ya dawo mata? Gashi wannan innar ma bata dawo ba,wannan tunanin yasata ƙanƙame jikinta tana kuka.

Adeeb kuwa cikin wani irin yanayi na sarewar zuciya ya shigo cikin dakin,abubuwa sunyi masa yawa cikin zuciyarsa,jinsa yake kamar bashiba, kansa banda ciwo ba abinda yake ,wai meke shirin faruwa da rayuwarsa ne ?me hakan ke nufi ?me amminsa ke nufi da ɗauke sarƙar Hulwa?

Kukan hulwar da yaji Yone yasani saurin ƙarasawa cikin dakin.

Karanta Littafin : Macijine Shi Complete Novel

Tana jin motsi sa ta zabura atsorace tana mai kallon ƙofar dakin.ganin Adeeb ne ya shigo yasata saurin yunkurawa ta mike da gyar tana kuka tare da kallonsa.

Da saurinsa ya ƙaraso inda take ,yana zuwa ya kamo hannunta tare da shafa gefen fuskarta yace “menene kike kuka?inane yake miki ciwo ?ya faɗa cikin mugun sanyin murya ,wanda har saida fattu ta ɗago kanta ta kalleshi,

Idanunsa sunyi jajur sosai jijiyoyin kansa sun fito rudurudu,fuskarsa tayi jajur ,kana gani kasan yana cikin damuwa da tashin hankali.

Cikin kuka fattu ta faɗa ƙirjinsa ta rungumeshi, tana faɗin “tsoro nakeji Hamma ,ko ina ganin ƙaninka nake yana min gizo Hamma” ta fada cikin kuka tana ƙanƙame Adeeb.

Cike da tarin damuwar da baisan menene mafitarta ba shima ya ƙanƙame fattun ajikinsa yana mai lumshe ido da sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi,

Ahankali yake faɗin”kiyi haƙuri Hulwa , dagani harke muna cikin damuwa, Hulwa komai bayamin dadi na kasa gane dawa ya kamata in amince cikin fadar nan,Hulwa kowa na fadar nan so yake yaga bayana bansan me na tsare musu ba” Adeeb ya faɗa cikin murya mai tattare da karaya da sarewa.

Shiru fattu tayi tana sauraron abinda yake fadi,ita fa sam bata fahimci inda zancen sa ya nufa ba,ahankali tace “Hamma ,su waye ke son kamin bayanka”?

“Shiru yayi yana mai kara rungume fattu ajikinsa,dan sosai yake jin nutsuwa na samunsa sakamakon rungumeta da yayi,zuciyarsa tana yi masa sanyi .shafa gashin kanta kawai yake bai ce komai ba.

Kusan minti biyar suna rungume da juna ,kafin Adeeb yayi karfin halin zareta daga jikinsa ya zaunar da ita abakin gado,kallonta yake ,har zuwa lokacin idanunta basu koma yadda suke ba,akwai kumburi da kuma dan jaa kadan acikinsu.

 Hannunta ya kamo cikin nashi ya rike gam-gam yana kallonta.ji yake kamar ita kadai ta rage masa wacce zai fadawa damuwarsa,saidai fattu yarinyace,idan ma ya faɗa mata damuwarsa bazata fahimci me yake nufiba.

Kallonsa fattu tayi itama,tabbas akwai Abinda ke damun hamman nata,ko menene oho.”Hamma meke danunka?baka da lafiya ne ?ta fada cikin muryar marasa lafiya ,wadanda suka sha  kuka.

Ahankali ya koma kusa da ita ya zauna ,kallonta yayi yace “Hulwa abinda ke damuna yana da yawa,ina cikin wata sarkakiya wacce Allah ne kawai zai fitar dani,bani da wanda zan fadawa damuwata ahalin yanzu,bana son sanar da abie na komai,dan gudun ɓacin ransa,saboda tsoron kar ciwonsa ya tashi,kiyi ta min addu’a kinji hulwatee” Adeeb ya faɗa yana mai riƙe habar fattu tare da zuba mata gajiyayyun idanunsa.

Cike da tausayawa fattu ke kallon Adeeb,kafin itama ta sanya hannunta akan fuskarsa tana shafa gefen fuskar tashi, kamar yadda yake mata .sannan tace “Hamma zanyi ta maka addu’a Allah ya yaye maka damuwarka, kuma kaima kayi ta addu’a Allah maji rokon bawansa ne ,Allah ya bawa abie lafiya Hamma,amma me zai hana ka sanar da innarka itama ta tayaka addu’a” fattu ta faɗa bayan ta cire hannunta daga kan fuskar Adeeb.

Karanta Littafin>>> Duk Tsanani Hausa Novel Complete Document

Wata sassanyar ajiyar zuciya Adeeb ya sauke lokacin da fattu ke shafa gefen fuskarsa ,ahankali ya lumshe idanunsa yana jin wani irin sanyi yana Ratsa zuciyarsa.

Ahankali ya bude idonsa lokacin da yaji ta cire hannunta daga kan fuskarsa.kafin yace “Hulwa ammina tana daga cikin mutanen da nake son boyewa damuwata ,ahalin yanzu bazan iya sanar da ita komai daya danganci lamarinaba,ke dai kiyi ta min addu’a kinji”ya faɗa cikin murya mai cike da ban tausayi.

Sosai fattu kejin tausayin hamman nata yana Ratsa zuciyarta.ahankali ta ɗora kanta gafen kafadunsa tare da rungumoshi ta gefe.tayi shiru cike da tunanin meke damun hamman nata.

Ahankali shima ya dora kansa akan nata kan yana jinsa tamkar marayan da bai da kowa.

“Hamma wannan innar bazata dawo ba ko?” Ta fada ahankali idanunta alumshe.

Shima idonsa alumshe yake yana shafa kan fattu ,yace “kina so ganinta ne?

“Daga kai tayi alamun eh sannan tace ” eh Hamma ina son ganinta ,ina kaunar ta har cikin raina ,kuma tace daga yau itace inna ta”

Ajiyar zuciya Adeeb yayi kafin yace ” Hulwa  ita kadai kike kauna ? Ni baki kaunata?ya faɗa ba tare da yasan ya fadi hakan ba .saida ya faɗa sannan ya fahimce me yace .

“A’a  Hamma ina ƙaunarka sosai mana,ina sonka,kaidin kamar baffana kake ,bani da kowa saikai, Hamma bana son wani abu ya tab aka ma” ta fada tana ɗago kai tare da kallon Adeeb.

Cikin wani irin farin ciki da jin dadi Adeeb ke kallon fattu,zuciyarsa cike da  jin dadi yace “da gaske kike Hulwa?” Ya faɗa cikin murmushi yana kallonta.

Jinjina kai tayi itama cikin murmushi tana kallonsa.

Ahankali ya janyota jikinsa ya rungumeta  gamm yana mai lumshe ido , sosai yake jin wani irin. Daɗi da Nutsuwa cikin zuciyarsa.

Karanta Littafin>>> Gidan Uncle Complete Novel

“Kina son ɓata min shiri ko ?,kisani wllh idan kikayi wani kuskuren dana rasa damata,kema zaki karbi naki hukuncin ,kin sanni kinsan halina,kuma kinsan abinda zan iya aikatawa ,dan haka ki kula da kanki,komai yana ƙoƙarin lalacewa saboda sakacinki,to bazan laminci wannan abinda kike yiba.wllh zan aikaki gurin da duk wanda zai zamenin matsala nake aikawa.akan wannan karagar zan iya batar da kowa”

Wani mutum ne daya lulluɓe ilahirin fuskarsa ke fadin wannan maganar cikin ɓacin rai  yana kallon ammi,wacce ke tsaye cikin tsantsar tsoro ,jikinta sai rawa yake cikin tashin hankali tace “dan Allah kayi hakuri ,wllh ina yin iyakar ƙoƙarina akan wannan abun ,kuma aKwai shirin da nake yi ,karka damu ka kara hakuri “ta fada cikin rawar murya,tana kallon mutumin da baka ganin komai bace kwayar idanunsa.

Cikin fushi mutumin ya damƙi wuyan ammi ya hadata da jikin bango yana faɗin”bana son jin komai  daga bakin ki kawai ki aikata abinda nace miki ,ki tabbatar ya bar duniyar nan nanda lokaci kankani,zan kawo miki abinda zaki saka mishi acikin abinci,zai mutu kuma ba wanda zai zargi wani abu,idan kuma aka samu kuskure .yayi shiru tare da sakin wuyan ammi wacce ke kakari tana kokarin shekawa.

Tari sosai ammi keyi,lokacin da mutumin ya saki wuyanta sannan yayi tafiyarsa cikin sauri yana ƙara gyara rufin fuskarsa.

Saida ammi ta samu nutsuwa kafin ta bar gurin ,kai tsaye dakinta ta nufa ,gaba ɗaya awahale take,

Bakin gado ta zauna cike da damuwa tana tunani,can dai ta dauko akwatin sarkokinta,abin yayi matuƙar tsorata ta lokacin datayi arba da akwatin sarƙar fattu ba komai acikinta.

Wani dan gajeren ihu ta kwalla cikin tashin hankali,tana dube dube cikin akwatin ,waye ya daukemin sarƙar nan?na shiga ukuna wayyo ni ammi .da sauri suhaimat ta shigo dakin ammi ,dan kuwa taji ihun da ammin ta kwalla.”uktee lafiya ?naji kina ihu?suhaimat ta fada cikin damuwa tana rike ammi.

“Ba komai suhaimat na Dan bugene “ammi ta fada cikin tashin hankali.

Kallonta suhaimat keyi cikin rashin yarda da abinda ya fada,amma koma dai menene tunda taki faɗa shikenan .

“To mukam muna ta shiri anjima jirginmu zai tashi .zanje in Kara duba yarinyar can “suhaimat ta fada tana kallon ammi.

“Karkije suhaimat ,karkije,na roƙeki,ki rufamin asiri karkije “ammi ta fada cikin tashin hankali tana kama hannun suhaimat.dan tana tsoron kar ace sarƙar ta koma gurin fattu ne kuma suhaimat ta gani ta gane yarta.

Cike da mamaki suhaimat ke kallon ammi,anya kuwa kalau take?ji yadda ta wani rikice daga cewa zani ganin yarinyar can.

Kai gaskiya akwai wani abu aƙasa.

Cikin hade fuska suhaimat tace “uktee ki fadamin menene dalilinki  da baki son na haɗu da yarinyar can?me kike kullawa akanta ?menene hajjarki ? suhaimat ta fada cikin haɗe rai tana kure ammi da ido.

Karanta Littafin>>> Macizai Ne Page 1-10 Hausa Novel

Zato ido ammi tayi tana kallon suhaimat ,kafin cikin in Ina ta fara magana “su…haim..at ……

Hmmmmm muje zuwa masu karatu.

Mrs babi ce💘💘

Share and comment fisabilillah.

More comment

More typing.

Back to top button