Mijin Marigayiya Page 13 Hausa Novel
A nan wajen aka nuna masa benchi ya zauna yayinda ita kuma aka turata a kan gadon marasa lafiya aka shige da ita dakin bincike.Tana kwance a kan gadon yayinda take amsa tambayoyin ma’aikaciyar jinya sai wata ma’aikaciyar wadda taji suna kira matron ta shigo, ma’aiakciyar ta juya tana kallon matron tana cewa ‘Matron wannan fa sai an yi mata scaning, cikin nan na jikinta kamar ficewa zai yi duk da dai tace bata fara bleeding ba ama dai tana jin alamunsa.’Matron din ta karaso ta tsaya a kanta, tace ‘Ah! Wannan ai Khadeeja ce, wa ya kawota?’Jin an ambaci sunanta ya sa ta bude idonta a hankali, ta yi murmushi a gajiye lokacin da suka hada ido ta gane wadda ta ambaci sunan nata. Cikin sanyin murya tace ‘Anti Iyami.’‘Na’am, Khadeeja. Wa ya kawoki?’‘Muatapha ne.’Ta juya ta kalli abokiyar aikin nata tace ‘’Yata ce ai, itace wadda mukayi biki kwanaki fa yarinyar Habiba wadda nace miki chiildhood friend dina ce.’Da fara’a tace ‘Aaah! Allah sarki, to abun ya zo kenan haihuwa yakin mata.’‘Ai kuwa. Bari na kirawo Dr. Jamil ya zo ya duban min ita sai muje na kaita scanning din muga ko za a iya sallamrta a daren nan.’Har ta juya zata fice Khadeeja ta riko hannunta, ta juyo tana cewa ‘Akwai wani abu ne Khadeeja?’Tayi murmushin yake ta goge kwallar da ta gangaro daga gefen idonta tace ‘Kada ki sallameni Anti Iyami, ki yiwa Mommy waya ta zo ta daukeni gida zan tafi.’Ta dan rankwafo tana shafa kanta tana duban fuskarta tace ‘Ok, kada ki damu, ki samu ki huta tukunna likita ya duba ki. In sha Allahu yanzu zan kirawota ko bata zo ba da safe idan na tashi daga aiki sai na tafi da ke gidan Mommy din. Kada ki damu.’Ta juya ta fice yayinda Khadijan ta mayar da idonta ta rufe.Tare da likitan suka dawo, bayan ya duba Khaddej aka je aka yiwo scanning tare da Mustaphan aka dawo. Bayan likita ya duba scanning din yace cikin jikinta ya lalace fita zai yi, don haka za ayi mata wankin ciki sannan akwai allurai da ruwa da za a saka mata.Da kansa yaje ya siyo komai ya kawo sannan suka koma wajen Khadeeja tare da matron; a nan Khadeejan take sanar da shi cewa martron kawar Mommy ce.Ya sake gaisheta cike da girmamawa, bayan ta amsa ta dubi Khadeejan tace ‘Likita ya ce cikin jikinki ya lalace don haka za a yi miki wankin ciki, ga magunguna kuma ya rubuta miki sannan ga drip idan an gama wankin cikin zan saka miki kinga yau a nan zamu kwana da ni da ke.’Tayi murmushin yake, ta dubi Mustapha tace ‘Ka tafi, ka bar yara a gida. Anti Iyami zata kirawoka idan akwai wani abu tunda ka ga tare zamu kwana ma, zuwa da safe zamu yi waya in sha Allah.Matron ta fice ta basu waje. Bayan ta fice ya matsa kan Khadeejan yana saha fuskarta yace ‘Sannu, kin bani tsoro fa.’Tayi murmushi.Ya cigaba ‘Kafin safiyar tayi sai ki samu ki yi mi message din duk abinda kike so na taho miki da shi, idan kuma Allah ya sa da safen zasu sallameki ma shike nan sai kawai na zo mu tafi. Na yi maganar abici ma Anti Iyami tace na bari zata kawo miki, but in ana son wani abu kiyi min magana sai na saka miki kudi a account dinki ko transfer ne sai kiyi musu.’Ya sa hannu a aljihunsa ya zaro wayarta ya mika mata yana cewa ‘Ga wayarki, ba zan kirawoki ba don kada na dameki ko na tashe daga bacci, but please da kin farka ki kirawo ni.’Ta karba tana murmushi tana cewa ‘Ok, ka gaishe min da su Yaya Afaf.’Ya fice ya barta a kwance.Yana fitowa ya sami Anti Iyami da abokan aikinta a station dinsu, yayi mata sallama bayan ta karbi lambar wayarsa sannan ya wuce.………Tun a daren Anti Iyami ta kirawo Mommy ta sanar da ita halin da ake ciki, sai dai bata gaya mata cewa Khadeejan tace gida zata taho ba. Ta dai sanar da ita cewa tana hannunta idan akwai wani abu zasu ji zuwa wayewar gari.Tana tsaye aka yiwa Khadeeja wankin ciki sannan aka bata daki, ta saka mata drip da alluranta sannan ta hada mata sahyi mai kauri. Ta sakata a gaba bayan ta shanye sannan ta zuba mata shayi da kwai ta cinye sannan ta ajiye mata saucer da kankana da lemon bawo tace ta shanye kafin a jima.Ta sha tambayoyi a wajen Anti Iyami wadda take kokarin gane dalilin da yasa Khadeejan take son tafiya gida; sai dai bata sami komai ba don da a tunaninta ko Mustaphan yana abusing dinta ne.ita kuma ta sanar da ita kawai bata da lafiya ne sannan kuma ga aikin gida da raino wanda yayi mata yawa shi yasa take son ta je gida ta huta. _______ A gajiye ya shiga gidan wajen karfe tara na dare, yana shiga yaran suka taso da gudu gaba daya tun kafin ya gama rufe kofar motar suba cewa ‘Abba ina Anti Khadeeja?’ Ya dauki shukura ya kana hannun Nasreen yana cewa ‘Tana asibita, likita ya kwantar da ita, amma gobe in sha Allahu zan je na taho da ita.’Ya tattara su suka shige cikin gidan.Yana shiga bayan Ummi tayi masa sannu da zuwa ya sallameta ya fito ya rakata sai da ta shiga gida ta kirawo masa babanta yayi godiya sannan ya koma gida. Sai da ya biya sallar Magriba da Isha’I duk da yunwar da yake ji sannan ya zo ya zauna a parlor a gajiya, ya dubi Afaf wadda take kwance tana yin game a tab dinta yace ‘Afaf dauko min flask da kayan shayi.’Ta mike ta shiga kitchen din, jimawa kadan ta futo dauke da kayan shayin bayan ta ajiye tace Abba babu ruwan zafi a flask ka jira na dafa maka, wanda Anti ta zuba mun sha shayi dashi mu da Ummi.’‘No, barshi kawai. Dauko min zobo ki kawo min ragowar abincin da kuka ajiye na ci, yunwa nake ji.’ Kafin ta bashi amsa Habib yace ‘Abba ai tun kafin ku fita zobon ya bare a nan, ka manta? Kuma dama shi kenan wanda Anti ta zuba ragowar na jiya ne.’Kafin yace wani abu Afaf tace ‘Abba babu fa abincin ma sai dai ragowar rice and stew, gaba daya dankalin muka cinye kuma da peppersoup din, amma akwai ragowar watermelon a fridge. Ko na dafa maka indomie?’Ya kalleta yana shafa kai na dan lokaci, ya ma rasa me zai ce mata sabod yanda gaba daya ya jigata saboda yunwa, coke kawai ya samu a asibiti da wani guntun burodi ya ci. Ya zata zasu rage abincin amma wai duk sun ciye.Muryar Afaf ce ta katse shi tana cewa ‘Bari kawai na dafa maka indomie din Abba.’‘No, bari na shiga kitchen din na gani.’ Ya fada yana mikewa tsaye.Ya dan dauki lokaci yana kallon kitchen din bai ma san ta inda zai fara ba; har ya dauki tukunya zai dafa indomie sai kuma ya tuna ai akwai cereal, don haka ya mayar da tukunyar ya ajiyeta a muhallinta. Ya zuba ruwan zafi a kettle ya jonaYa zuba ruwan zafi a kettle ya tafasa ya hada cereal, ya ajiye ya fiddo kankana daga fridge ya yanka sannan ya dauko ya dawo parlor din.Yana zama Shukra ta matso tana dariya ‘Abba zan sha golden morn din.’Ya bita da kallo da cokali a hannunsa; bata taba bashi takaici ba kamar a wannan lokacin don ya tabbatar sun koshi tunda gashi sun cinye duk wannan uban abincin da Khadeeja ta dafa. Ya dubi Afaf yace ‘Tashi ki dauko cereal, ki hado min da tea flask da komai na hada mata.’Kafin Afaf ta dawo Nasreen tace ‘Abba nima zan sha.’Don haka tana kawowa ya sa ta koma ta karo kofi, ya hada musu cereal din su biyun.Babu wadda ta sha cokali uku a cikinsu, suka tashi suka bar masa a nan. Kafin ya gama cinye nasa abincin duk sun fara gyangyadi don haka ya sa Afaf ta dauko musu kayan baccinsu ya shiryasu bayan ya rakasu sunyi brush sun yi fitsari. Bayan sun kwanta sannan Afaf da Habib suma suka shirya, Afaf ta zauna a gefen gado tayi tsuru-tsuru shima Habib sai ya hau katifarsa ya kwanta yana zare ido.Yana tsaye daga bakin kofa yace ‘Yaya dai Afaf? Ki kwanta mana, ko akwai wata damuwa ne?’Ta jijjiga kai tace ‘Kawai tunawa nayi da Mommy, itama muna bacci ta mutu.’Ya gaji sosai ga kansa yana sarawa, babu abinda zai iya yi musu na lallashi, ya bude baki a gajiye yace ‘In sha Allahu babu abinda zai sami Anti, kuyi addu’a ku kwanta kuyi bacci kawai.’Halifa shima ya tashi zaune yana share kwalla ‘Wallahi Abba ni ba zan ma iya baccin ba, Allah ya sa dai kada Anti Khadeejan ma ta mutu ta barmu. Har yanzu idan na tuna Mommynmu sai na yi kuka.’Kafin yayi magana itama Afafa din hawaye ya fara bin fuskarta, ta sunkuyar da kai ta sa masa kuka harda shassheka.Ji yayi kamar ya dora hannu a ka ya sa ihu; ina ma yaran nana zasu barshi ya huta, yanzu ya zai yi da su? Manyan cikinsu da yake ganin sune ba zasu bashi matsala ba sune suke so su hanashi bacci. Ya karasa ya zauna a kusa da Afaf ya rungumota yana cewa ‘In sha Allahu babu abinda zai sameta, ku daina kuka kuyi mata addu’a Allah ya bata lafiya. Goben nan ma zaku ga an sallamota.’Ta fara share hawayenta, Habib wanda shima ya taso ya dawo kusa da ita yace ‘Abba to ka kirawo mana ita a waya mu yi mata sannu.’Ya zaro wayarsa daga aljihu yana cewa ‘To ai da bana son kiranta saboda kar na dameta don an yi mata allurai, ban sani ba ko harda ta bacci a ciki. Amma bari na kirawota sau daya idan ta daga shikenan idan kuma bata daga ba sai mu hakura da safe ma sake kira…
