Hausa novels

Halysaah Page 103 By Khaleesat Haydar

Khaleesat na goge hawayen da suka ki tsaya mata a hankali ta bi bayan Hajiya Shafa’atu ta maida ta har part din Ajay, sallama aka kai ta tayi ma su Aunty Farida za su koma Kano ranan, zaunawa tayi a parlon ta sunkuyar da kanta har sannan hawaye yaki tsaya mata, Hajiya Shafa’atu tace “Kiyi hakuri, it’s always like this for every lady, Allah ya baku zaman lafıya da mijin ki” Ita dai Khaleesat bata dago kanta ba tayi shiru, Hajiya Shafa’atu tace “Allah ya maki albarka” Daga haka ta fita daga parlon, Khaleesat ta jinginar da kanta jikin kujera tana kuka a hankali, tayi minti goma zaune inda take taji an bude kofa ta daga kai da sauri, hada ido suka yi da Junaid, ta sauke idonta ta mike a hankali ta wuce cikin daki ta tura kofar, sai a sannan ta fashe da kuka sosai, Ajay ya zauna parlon not for anything but because of Aunty, bai son yana nisa da bangaren nasa don kar ma ta shigo, jinginar da kansa yayi da kujera yana jin kansa na masa ciwo sosai, message ne ya shigo wayarsa ya juya yana kallon wayar da ya ajiye a gefe, message din Jay ne, hakan yasa ya zauna da kyau ya dau wayar, hours ago yayi masa message sai yanxu yayi masa reply har ya cire ran reply dinsa, ya fi minti uku kamar dai yana kokarin gano menene a message din kafin ma ya karanta, daga karshe dai ya shiga cikin message din a hankali, it took him 2 minutes to read and understand the long text, yayi ta kallon screen din baya ko kiftawa still re-reading the message, daga karshe ya ajiye wayar a hankali ya mayar da kansa ya jinginar da kujera. Hajiya Nafisah na zaune tare da Aunty a dakinta tana kallonta tace “Ki kwantar da hankalin ki Fulani, wallahi waje uku duk magana daya ake gaya min, an tabbatar min lallai auren Junaid bazai je ko ina da yarinyar nan ba, yanxu haka jin sa yake kamar an dora masa jalala, ba shi da yanda zai yi da ubansa ne, ai ba wai lalacewa aikin ki na baya yayi ba kamar yanda kike tunani, aikin na nan daram bai lalace ba, wannan ba auren da zai je ko ina bane wallahi” Aunty tace “Ni duk ba wannan nake son ji ba Nafisah, ke irin wannan santaleliyar yarinyar under same roof tare da shi me kike tunanin zai faru next? Ai ba batun aure zai dade ko bazai dade ne damuwata ba, what if kwatsam aka ga yarinyar da ciki? Ko da ya rabu da ita in dai tayi ciki ai na shiga uku Nafisah” Hajiya Nafisa tace “To Banda abun ki Fulani mutumin da kika kashe makudan kudi duk domin ya dawwama a haka ba aure ina ruwansa da mace kuma balle har yayi mata ciki, kika san wani irin aiki aka yi da ko sha’awar auren ma bai yi shekara da shekaru? Ai bana jin zai ji ko dar don yana under same roof da yarinyar nan wallahi, mutumin da ko budurwa kina gani har yau yaki yi ai kin san ba lafıya garesa ba” Aunty tace “Gaskiya hakan bai gamshe ni ba Nafisah, Bazawara ce fa yarinyar tasan aure shi ne bai sani ba, what if ta gano matsalar tasa immediately? ga kabilarsu da lakani iri iri da karya tambaya, ai abinda baki sani ba Nafisa sakinta da zai yi cikin gaggawa babu bata lokaci shi zai tunxura Mai martaba ya sallama ma duniya shi har ma ya sauke rawanin Yarima dake kansa, na fa san halin sarki, kawai yanxu duk yanda Junaid zai watsa masa kasa a ido ya kunyata sa a idon al’umma ne target din mu Nafisa, kuma ba komai zai yi ya ja hakan ba sai sakin wannan bazawara, saboda shi rikakken dan iska ne kin ga ai har Jakadiya na tura ta taho min da yarinyar ya hana a zo da ita wajena, ni akwai wanda ke bani sleepless night a duniyar nan irin Junaid kuwa? Ina bakin cikin bude ido in gansa Nafisah, Tun yana karami nake kashe kudadena a garurruwa daban daban ni ce har Nijar da Mali, in baki manta ba har poisoning yaron nan na taba yi, muka yi planning da Jakadiyata ranan za a kai sa gidan kakarsa na bata poison din sai taje can ta faki ido in an basa abu ta zuba a ciki yanda babu wanda zai yi zargin daga masarautar nan ne abu ya samesa an san ko ma me ya ci a gidan kakarsa ya ci, kakar ta dama masa fura ta tafi dauko zuma ta zuba masa Jakadiya tayi maza ta juye poison din nan a furan, poison fa mai karfi Amma yaron nan sai da yayi surviving yayi kusan wata uku a asibiti can kasar waje, to meye ma ban yi ba akan Junaid Nafisah? Wani irin abu ne ban hada masa ba amma sai ki ga ya tsallake” Hajiya Nafisah ta sauke ajiyar zuciya tace “Duk ban manta ba Fulani, yanxun ma ai ba gajiya zaki yi ba, kuma idan kika duba banda Jawwad sai Mai martaba sai kuma kakarsa waye kika ga ke yin sa a family ko kuma yake damuwa da lamarinsa? Hatta mai Martaba kinsan yafi concentrating kan yaranki da Jawwad akan wani Junaid, Ai hakan ma wata nasara ce babba a wajen ki, kafin fa ace Junaid sau daya ance Walid sau ashirin a masarautar nan, ya zama kamar mujiya cikin mutane babu me shiga sabgarsa, sannan a yanxu haka kinsan ba lafıyayye bane, wuyarta ya shigo gidan nan yayi ciwace ciwace kenan, kin ga kuwa ai baza ki ce babu nasara ba, komai dama a hankali ake bi ai, yanxu ne ma ya kamata ki tashi tsaye ki zage damtse tun da har aka yi masa aure da yarinyar nan ta shigo in to the picture, kuma duk inda na kira sai ace ayi hankali da ita wallahi idan ba haka ba a sha mamaki, kar taje duk ta rusa maki shiri a shiga uku” Cike da damuwa Aunty tace “Wallahi abinda aka ce min kenan Nafisah ya hana ni bacci jiya, tun a jiyan na aika Jakadiya kauyen su ina saka ran nan da kwana uku zata dawo, kin san bata da wasa barin in taga abu ya dameni, to wannan auren in sha Allahu babu inda zai je sai ya rabu da shegiyar yarinyar nan, idan ya so idan ma Jawwad din za a mayar ma oho dai babu abinda ya sha min kai, ni dai Junaid ne damuwata tunda na dau alwashin shi da aure sai dai yayi a lahira idan ana yi, duk Aseeyah ce ta ja min wannan bala’in gashi tun shekaranjiya na kasa baccin kirki sai uban ciwon kai” Hajiya Nafisah tace “Nima nan da kwana uku mutumin yace zai aiko da sakon ta mota” Aunty tace “Wallahi ko nawa aka ce in dai Junaid zai saki yarinyar nan zan bada ni dai” Hajiya Nafisa tace “In Sha Allahu zai rabu da ita Fulani ki kwantar da hankalin ki, dama Shafa’atu ce babban munafuka kilan ita ce ma tace masa kar ya bari a kai yarinyar bangaren ki, kuma gobe naji zata tafı gida, komai zai zo mana cikin sauki, to wai ya batun Hadiyah ne naga ba a kawota ba har yanxu” Aunty ta tabe baki tace “Wannan kuma su ta shafa ina ruwana, na dai ji suna cewa za ayi fixing date din walima, ni wannan ba damuwata bace” Hajiya Nafisa tace “Lallai kam” Bayan isha’i Ajay ya samu Mai martaba a chamber dinsa, zaunawa yayi kansa a kasa ya jira har Mai martaba ya gama wayar da yake sannan ya daga kai ya kallesa, Sarki na kallonsa yace “Akwai wani abu ne?” Ajay ya sauke idonsa a hankali “She will be resuming school in few days time, gobe za mu koma America, ur highness” Sarki yayi shiru yana kallonsa, can yace “Ohk, but I think ka bari ranan Wednesday don gobe za ku je gidan Hajja, a barta ta yini a can” Ajay yayi shiru don jibi ne Wednesday din, can yace “To Allah ya kai mu ranka shi dade” Bai jima a parlon ba ya mike ya nufi kofa sarki ya bi sa da kallo har ya fita, Ajay na komawa bangarensa ya bude kofar da makulli ya shiga parlon, zaunawa yayi saman kujera ya dafe kansa da yayi masa nauyi sosai, babu abinda ya ci a abincin da ke parlon, tun daxu yake kokarin yaga zuciyarsa ya goge text din da Jay yayi masa amma the more he is trying to erase the content off his mind the more yake kara sticking to his mind, ya dau remote din Ac ya kashe, ya mayar da wutan parlon mara haske sosai sannan ya kwanta saman 3 sitter ya lumshe idonsa to calm himself a little. Wajen karfe biyun dare Khaleesat ta dau hijab dinta har kasa ta saka sannan ta tura kofar Bedroom a hankali don dama a bude yake ta leka cikin parlor duk da babu haske sosai ta hangosa kwance saman kujera, mamaki ne ya cikata don at first ta zata kunnenta ne ke jiyo mata kamar ana magana a parlon, fitowa tayi daga cikin dakin ta tsaya bakin kofa tana kallonsa, amma she couldn’t grab anything he was saying, a hankali ta kai hannu ta kunna wutan parlon zuwa me haske taga yayi sharkaf da zufa, ko canza kayan jikinsa bai yi ba, har sannan kuma idonsa a kulle yake and he was still murmuring and turning his head, karasawa tayi ta dau remote din Ac dake kusa da shi ta kunna Ac din parlon ta duka tana kallonsa don he doesn’t look okay, tsoro taji ya kamata ta dan koma baya, a America sau biyu tana kamasa yana sambatu and it was so funny to her then don surutu kawai yake, but this is totally different, sake komawa baya tayi a hankali tana kallonsa, can ta kai hannu ta dan bubbuga kujeran da yake kwance, ya bude ido da sauri, zai juya tayi maza ta matsa daga wajen don kan kace me sai gashi ya fado kasa daga saman kujeran, mikewa zaune yayi ya hade rai yace “Ke…” Sai kuma ya fara kokarin tashi taga ya nufi Bedroom dinsa da sauri, ita dai ta bi sa da kallo, bandaki taji alamar ya shiga ta mike tana kallon kofar Bedroom din, amai taji kamar yana yi, a hankali ta koma ta zauna kan kujera, ta ma rasa wani tunani zata yi, bayan kusan minti ashirin ta mike ta nufi dakin ta tura kofa gently tana kallon ciki, kwance ta gansa saman gado ya rufa har kansa da Duvet ya kashe Ac, sai dai ba ta inda take kwanciya ya kwanta ba ya koma can daya side din, duvet din ma sabo ya dauko, tana ta tsaye bakin kofa sai kuma ta juya a hankali ta koma parlor, throughout night din bata yi bacci ba tana zaune parlor, lokaci lokaci sai taje kofar dakin ta tsaya tana kallonsa gashi har sannan bai cire duvet din da ya rufe fuskarsa ba, wajen karfe biyar saura bacci ya dauketa saman 2 sitter ta farka a firgice ta sauko daga kan kujeran ta nufi Bedroom dinsa, dai dai nan ya fito daga bandaki da towel, bata san sanda ta juya da sauri ta fito daga dakin ba kamar warce ta ga wani mugun abu, direct ta shige bandakin dake parlor ta kulle kofar ta sulale kasa. Sai da Khaleesat taji alamar ya fita daga parlor don zuwa Masallaci sannan ta dauro alwala ta fito daga bandakin, Bedroom dinsa ta shiga da sauri, ta dau wayoyinsa da Counter dake kan gado ta kai masa parlor ta ajiye kan kujera sannan ta koma dakin ta kulle da makulli. Da safe sai da aka kwankwasa mata kofa taji muryar warce ke yawan shigowa wajenta a masarautan sannan ta bude kofar, bayan sun gaisa da matar that is in her late 40s tace “Ranki shi dade dama kumallo ne aka ajiye maki tun daxu baki fito ba, shi ne Yarima yace a maki magana, sannan wai zaki shirya za ku fita nan ba da dadewa ba in sha Allahu Khaleesat dake kallonta a hankali tace “Da wa?” Cikin ladabi tace “Wallahi ban sani ba Ranki shi dade, haka dai Yarima yace a sanar maki….Khaleesat tace “To Nagode” Matar tace “Allah ya taimake ki, yace zan duba maki shigar da zaki yi idan ba damuwa” Khaleesat tace “To” Bayan Khaleesat tayi breakfast da taimakon wannan matar tayi shiga ta alfarma, and she looks just like a princess, sosai tayi kyau ba kadan, matar dai sai murmushi take mata tana kara yaba kyan da tayi, da alama matar ta jima a masarautar kuma ta lura kamar da ita kawai Ajay ya fi interacting a duk gidan, cikin ladabi matar tace “To Gimbiya wacece, har yanxu ban san sunan gimbiyar yarima ba” Khaleesat ta sauke idonta tace “Sunana Halysaah” Matar tace “Maa sha Allah, ni kuma za ki iya kirana da Yakumbo, mahaifiyata Jakadiyar marigayiya matar sarki ce wato warce ta haifi Yarima Junaid, saboda zaman amana da aka yi da mahaifiyata shi yasa har yanxu nake gidan nan mahaifiyar tawa kuma ta rasu da dadewa, amma na fi karfi a bangaren girke girke na gidan nan, yawanci duk ni ke yi ma Yarima girkin abinda zai ci, Ina sa ido sosai a duk abinda ya shafi abinda Yarima zai ci a gidan nan” Ita dai Khaleesat bata ce komai ba, Yakumbo tace “Allah ya baki miji mara hayaniya sai tarin makiya, rayuwar mijin ki a gidan nan abun tausayi ne ainun, akwai abubuwa da yawa dake faruwa wanda ba sai na bude baki na gaya maki ba da kanki zaki fahimci hakan a hankali cikin gidan nan” Ita dai Khaleesat kallonta kawai take, Yakumbo tace “Yanda dan uwansa Jawwad ke jan sa jiki Allah ya baki ikon yi masa fiye da haka kema don a yanxu kin fi kowa kusanci da shi, Allah ya baki ikon yaye masa duk damuwarsa na shekara da shekaru a gidan nan” Daga haka Yakumbo ta kamo hannunta suka fito daga dakin, Ajay na zaune parlon ya jinginar da kansa da kujera yayi nisa tunanin da yake, lokaci daya ya gyara zamansa ganinsu, ita dai Khaleesat tun da ta kallesa sau daya bata sake kallonsa ba, Da ladabi Yakumbo tace “Ranka shi dade, baka yi kumallon ba” Ajay yace “Na sha tea, driver na jiran mu” Daga haka ya mike ya nufi kofa, Yakumbo ta kalli Khaleesat tace “To ku je Gimbiya Halysaah, Allah Ubangiji ya tsare hanya” Khaleesat tace “Ameen Nagode” Bin bayan Ajay tayi tana tafiya a hankali, tun da aka kawota gidan sai ranan ta fito haraban masarautan, ta shiga back seat da aka bude mata, bayan ta shiga da kusan 3 minutes Ajay ya shiga back seat din shi ma, a haka suka bar gidan tare da wata mota dake biye da su a baya, Ajay yayi instructing driver din ya kashe Ac din motar, suna fara tafiya da minti goma ta dan kallesa ganin ya kwantar da kansa taga bacci yake, ta kalli driver din motar, sannan a hankali ta kai hannu kusa da forehead din Ajay duk da bata taba sa ba amma she could feel he was running temperature, all through the ride bacci yake, ita kuwa lokaci lokaci take juyawa ta kallesa, suna isa gidan Hajja bayan driver yayi parking Khaleesat ta juya tana kallon Ajay, har Ikcin bacci yake, da Drivern ya ga haka sai ya bude motar ya sauka, a hankali ta kai hannu forehead dinsa tana kallonsa, cikin muryar bacci ya cire hannunta a hankali yace “Stop it Jay” ita dai kallonsa kawai take, a hankali taga ya jinginar da kansa jikin shoulder dinta ya dan yi sumbatunsa ya ci gaba da bacci, they were like that for more than 5 mins a cikin motar, sai ga wata mota ta shigo compound din Aunty ta sauko daga bayan motar da Hajiya A’isha su ma sun zo gaida Hajja, Khaleesat ta dan gyara zama da sauri barin da taga suna kallon motar Junaid, hakan da tayi yasa ya bude idonsa a hankali, suna hada ido da Khaleesat ya gyara zamansa yana kalle kalle, tuni Aunty da Hajiya A’isha suka nufi entrance din shiga cikin gidan, Ajay ya bude motar ya sauka, ita dai Khaleesat ta bi sa da kallo sannan ta sauka daga motar ita ma, tana biye da shi suka shiga parlor, Aunty na zaune parlor tare da Hajiya A’isha sai Mami bayan sun gaisa, Ajay ya sauke kansa duk ya gaishe su, Hajiya A’isha ce kadai ta amsa gaisuwarsa cikin halin ko in kula, Khaleesat ta duka kasan carpet ita ma ta gaishesu a hankali, sau daya Mami ta kalleta ta kauda kai, ita din ma Hajiya A’isha ce kawai ta amsa gaisuwanta a walakance, fuska daure Aunty tace “Lallai kin cika Munafuka kuma makira yarinyar nan, dama tun da aka kawo ki kin taba gaisheni ne da zaki gaisheni yanxu?” Khaleesat was very shock ta daga kai tana kallonta babu ko kiftawa, Ajay na kallon Khaleesat yace “Ta shi mu je” Kasa tashi tayi, tana kallon Aunty cikin sanyin murya tace “Kiyi hakuri ranki shi dade, ni ban san….” Ajay ya hade rai cutting her short immediately yace “Baza ki tashi ba” Hajiya A’isha tace “Kai dai baka da mutunci yaron nan, in ma dukanta tayi ya kamata kace ta tashi, ko in uwarka ce zaka yi mata haka? Wato kai ga dan iska ko?” Ita dai Mami girgiza kafa kawai take tana kallon direction daban, Ajay na kallon Khaleesat ya wani hade rai yace “Get up” Hajiya A’isha tace “To ta tashi mu gani, kaga sai mu tabbatar er iska kamar ka Mai martaba ya hadaka aure da” Aunty tace “Toh dama mecece in ba er iskar ba kuma er talakawa? Kina jin fa gidan da iyayenta ke ciki ma Jawwad ne ya siya, haka suka asirce sa suka yi ta tatse ma Fulani Aseeyah shi tana gefe bata san abinda duniya ke ciki ba, shi kuwa ubanta barawon babban mota ne don har furson sai da yayi na shekara da shekaru” Khaleesat da shock ya sa ta kasa motsi a inda take durkushe kawai ji tayi Ajay ya dagota lokaci daya, yana rike da hannunta suka bar parlon ya nufi parlon Hajja, Hajiya A’isha ta bude baki tana kallon Aunty da ita ma ta saki baki tana bin Ajay da kallo, ita dai Khaleesat bin sa take ko kwakkwaran motsi ta kasa, Ajay na shiga parlon Hajja yayi ido hudu da Jay dake zaune parlon, ya sauke idonsa a hankali ya sake hannun Khaleesat dake nasa, sosai gabanta ya fadi lokaci daya ta ma mance shock din da take ciki ganin Jay a parlon, Ajay ya karasa ya zauna kan Carpet, Khaleesat bata fasa kallon Jay da yaki daga kai ba ta zauna ita ma kasan Carpet, lokaci daya hawaye ya cika idonta cikin sanyin murya tace “Ina kwana” Mikewa yayi ya nufi kofa ya fita daga parlon Ajay ya bi sa da kallo.

Back to top button