💛 HAJAR 💛
By Feenerh_feeche
{3…}
Ƙarfe sha biyu na rana Dr Uthman ya shiga surgery with his well trained team, shi ƙwararren likita ne da ya karanci ɓangaren thorax da duk wani abu that is located in the chest region, alhmdllh surgeryn da Dr Uthman yayi was successful, yana dressing room yana cire kayan da yayi surgery dasu Dr Marwan ya shigo wanda shine yayi masa first assistance, Dr Marwan ya buɗe lockern kayansa yace “gaskiya Dr surgery nan yayi kyau, gashi patient ɗin ya daɗe da ciwon amma kuma komai yayi kyau”, Dr Uthman yace “everything goes well saboda aikinku mai kyau my team members, idan babu ku ai komai bazai yi daɗi ba”, Dr Marwan yayi murmushi yace “still dai kaine 70 percent na success ragowar percent ɗin aka raba mana”, Dr Uthman yace “Marwan next week inada surgery amma bazan samu damar zuwa ba, kaine za kayi heading sai Khaleel yayi first assistance”, Dr Marwan yace “sure Allah ya kaimu”, Dr Uthman ya mayar da lab coat ɗinsa ya wuce office, Halima tace “welcome Dr akwai patient da yake jiranka, zan iya shigo dashi??”, tsadadden wrist watch ɗinsa ya kalle yace “am off amma ki shigo dashi tinda ya riga yazo”, tace “yes sir” ta ɗauki landline ta kira reception tace “hello patient ɗin da yake jiran Dr Uthman ya shigo yanzu” ta katse kiran. babu jimawa patient ɗin ya shigo office ɗin, Dr Uthman ya kallesa yace “referral ne??”, patient din yace “Eh” ya miƙa masa wata takarda cikin envelope, glasses dinsa ya ɗauka ya kwamawa idanunsa kana ya karanta takardar tas yace “mal shu’aibu jeka ka kwanta a wancan gadon” yayi masa nuni da gadon da yake a can edge of the office, mal shu’aibu ya kwanta a gadon, Dr Uthman ya ɗauki stethoscope ya isa bakin gadon ya fara dubasa, bugun zuciyarsa ya fara ji sannan yace “mal shu’aibu kaja dogon numfashi”, mal shu’aibu yayi yadda aka umarce sa, bayan Dr ya gama duk wani gwaje-gwaje ya koma mazauninsa yayi rubutu ya basa yace “tests ne guda biyu, ayi su kafin nan da sati mai zuwa sai a kawomin”, mal shu’aibu yace “nagode likita” ya karɓi takardar ya fita. Dr Uthman ya ɗauki wayarsa yayi dialing numbern Nurse Ruqayyah wacca yayi saving da Love, ya jingina da kujera ya kara wayar a kunne. Nurse Ruqayyah tana zaune a nurse station taji wayarta na vibrating cikin aljihun rigarta, da sauri ta zarota ganin mai kiran tayi murmushi ta kara a kunne tace “my Dr badai harka fito ba??”, daga ɗayan side din Dr Uthman yace “yeh na fito, yanzu ma zan wuce, yaushe zaki wuce gida?”, tace “ohk, zan yiwa wata da za’a yiwa CS Anesthesia ne kafin na wuce gida”, yace “ohk, byee Love”, tayi murmushi tace “byee” ta katse kiran, Nurse Jidda da take kallonta tace “gaskiya Ruqayyah kin afka, yanzu fa shekara biyu kenan kuna tare da Dr Uthman, wai yaushe za muga cigaban wannan soyayyar ne??”, Ruqayyah tayi ajiyar zuciya ta taɓe baki tace “kwana nan zamu girbi soyayyarmu inshallah, kinsan dai cewa iyayena sun san dashi tinda ya tura magabatansa sunje nema masa izinin zance, toh tin lokacin suka so su bada kuɗin aure, amma Daddy yaƙi amincewa yace sai mun fahimci juna tukun, toh dai tin daga lokacin ba a sake maganar kai kuɗi ba, daman bai gama shiryawa ba yana so ya ƙarasa gidansa kuma ya zama rigid a business ɗinsa, to alhmdllh komai dai ya zama settle gida ma har an saka masa padlock ya gama komai, and his business shima alhmdllh, last week yake gayamin cewa zai turo magabatansa a kawo kuɗi sannan asaka rana, though shi baya so asaka sama da three months, amma nasan Daddy bazai amince ba saboda he is not ready, toh kinji yadda muke ciki”, Jidda ta jinjina kai tace “ohk mashallah, Allah ya tabbatar da Alkhairy”, Ruqayyah tayi murmushi tace “Ameen”.
★Umma na zaune akan kujera tana zuba ƙullun kulele cikin fafaffun gwangwanayen da aka shafesu da Manja, Sa’adatu ce ta fito daga ɗakin Maama taci kwalliya, wata riga da skirt ta saka na material mai rawa, kayan sun ɗameta sosai da kyar take tafiya ga takalmi mai uban tsini a ƙafarta, mayafin da ta saka dashi gara babu, fuskar nan ɗaɗau tasha hoda da mai, Baba ya fito daga ɗakinsa ya kalleta sama da ƙasa yace “ina za kije Sa’adatu?”, Sa’adatu ta zumɓuri baki tace “Baba daman bikin wata ƙawarmu ake, yau ne ɗaurin aure”, yace “toh wa kika tambaya da zaki fita a haka?”, Sa’adatu ta yamutsa fuska tace “na gayawa Maama ai”, Baba ya sake kallon shigar jikinta yace “koma ɗaki babu inda zaki”, ta tsaya tana ƙunkuni da murguɗe-murguɗe, ya zabga mata carbin hannunsa a baya, ya sake ɗaga hannu zai zabga mata ta ruga da gudu tana gurɗewa ta afka ɗakin Maama, Nabilah da take laɓe a jikin labule ta tuntsure da dariya tace “Baba ya matsa lamba”, Maama ta miƙe ta fita waje daman kaf tana jin abinda ya faru, Baba ya juya zai koma ɗaki Maama tace “haba mal ya za ai ka daddage ka daki yarinya budurwa haka, inaji dai ta gaya maka na bata izinin fita shine kake mata wannan dukan”, ya juya ya kalleta yace “indai ni na haifi Sa’adatu to ban amince ta fita a haka ba”, Maama ta ɗaga murya tace “Toh ai ba kai kaɗai ka haifeta ba malam, nice nan uwar Sa’adatu kuma ta samu amincewa ta”, da karfi Maama tace “ke Sa’adatu maza fito ki kama gabanki, Allah ya tsare”, Sa’adatu daga ƙuryar ɗaki tace “Tom Maama gani nan fitowa”, Baba yace “Rabi ki cigaba da ɓata tarbiyyar ƴaƴanki, yaran nan ko makaranta sunƙi zuwa, ba arabi ba boko, wallahi muddun baki canza ba wataran zakiyi kuka da idanunki”, Maama ta zabga uban salati tana tafa hannaye tace “Malam da sanyin safiyar nan kake ƙoƙarin yimin baki, kana kiramin kalmar kuka da idanuna, na shiga uku ni Rabi yau na gamu da jafa’i”, Baba ya girgiza kai yace “ƴaƴanki bazasu taɓa koyi da ƴar uwarsu Hajara ba, yarinya mai son karatu”, da gudu Nabilah ta antayo daga ɗaki tace “Baba Allah ya tsaremu muyi koyi da wannan tabbatacciyar shegiyar yarinyar”, sai a lokacin Umma ta tanka tace “ke karki sake kiran ƴata tabbatacciyar shegiya na gaya miki”, Maama ta rangaɗa wata shegiyar guɗa tace “ahayye, da Mu’azzam da Hajara duk shegu ne, da tsohon cikin Hajara da Mu’azzam yayayye kika zo gidan nan”, Umma tace “ga ubansu nan, kuma shi yasan ƴaƴansa ne”, Maama ta tafa hannaye tace “laha’ila ha illallahu, kuji fa wai Adamu ne uban Hajara da Mu’azzam, yau naga inda ake liƙawa mutum ɗan shege ta ƙarfin tsiya, wallahi ƙarya kike faɗima Sabra ce kaɗai ƴar Malam amma wallahi Hajara da Mu’azzam saidai ki nemo musu uba”, Baba ya nuna Umma yace “faɗima karki sake cewa komai, koma ɗakinki”, Umma ta rufe ƙullun kulelenta ta shiga ɗakinta, Sa’adatu kam tunda taji tsakar gida ya fara ɗaukar harami ta rungume cogen takalminta ta fita sum-sum tamkar munafuka tayi soro, Baba ya kalli Maama yace “Allah ya shiryeki Rabi idan kinada rabo” ya koma ɗakinsa, ai Maama saida ta gama kumfar bala’i ita kaɗai sannan ta koma ɗaki, Nabilah tace “Maama kinga har yanzu Maimuna bata dawo ba sai kace wacca aka aika wata duniyar”, Maama ta zabga tsaki tace “inajin ta tafi sabgar gabanta”.
★Washe gari da misalin ƙarfe biyu da Rabi na rana, Hajar ce ta fito tsakar gida sanye da uniform ɗinta na islamiyya, daga bakin rariya ta hango Naseer yana goge kaushi tace “yaya ina wuni”, yace “lafiya Hajar makaranta za’a tafi”, tace “Eh, Sabra nake jira”, yace “toh Allah ya bada sa’a”, sai kuma ya miƙe ya tsaya a bakin ƙofar ɗakin Maama ya kwalawa Maimuna kira, saida ya sake kiranta sau biyu sannan ta fito tace “yaya gani”, yace “ke bazaki fito ki tafi makarantar ba”, tace “yaya wace makaranta kuma??”, ya daka mata tsawa har saida ta firgita yace “islamiyya mana”, ta fara inda-inda tana mutsuttsuka hannaye tace “daman yau bazan je ba, Maama bata nan, Nabilah da Sa’adatu suma duk sun fita, wa zan barwa ɗakin Maaman??”, yace “shiga ki sako kayan makaranta ki wuce ki tafi”, tace “toh yaya wai wa zan barwa ɗakin..”, kwalla mata mari yayi har saida ta bugu da bango yace “duk abinda kuke agidan nan kawai kallonku nake, yaushe rabon da kije makaranta, zaki wuce ko saina tattaka ki”, a guje Maimuna ta afka ɗakin Maama tana gursheƙen kuka, ta buɗe Ghana most go ta ɗakko zumbulelen hijab ɗin islamiyya wanda rabonta dashi wajen wata huɗu, yaci uban squeezing yana warin ajiya, ta lalubi inda Maama take ajiye padlock ta ɗauka ta fito, Naseer yana tsaye a bakin ƙofar bai tafi ba ya kalleta ganin squeezing ɗin da hijab ɗinta yayi yace “ƙazama”, Maimuna ta kulle ɗakin ta rufe fuskarta da hijab ta cigaba da kuka, Naseer yasa ƙafa ya kwarfeta ta baje a ƙasa yace “miƙe munafuka, ai Maama ce ta kyaleku kuke yin abinda kukaga dama, wallahi daga yau kika sake fashin makaranta saina tattaka ki mara kunya”, da gudu tayi waje tana kuka, Hajar ta rufe fuskarta da hijab tana tiƙar dariya a zuciyarta tace (Allah shi ƙara), Sabra ta fito suka kama hanyar islamiyya. Hajar tana zuwa ajinsu Abubakar Siddiq wanda shine ajin sauka ta tarar har an fara bitar Al’qurani tinda sunyi sauka, saida aka gama bitar sannan Zainab ta taɓo Hajar tace “me yasa jiya bakizo ba?”, Hajar tace “kinsan shirye-shiryen NECO muke, to jiya akai mana online registration”, Zainab tace “nima ai naje registration ɗin kuma nazo islamiyya”, Hajar tace “nida na kusa samun matsala, ai ina gaya miki saura ƙiris ayi NECOn bana ba ni”, Zainab tace “A saboda me??”, Hajar ta kwashe kaf abinda ya faru ta gaya mata, Zainab ta zabga mata harara tace “dalla malama gafara can, wai da kika ƙi haƙura kika shafa masa kwatamin mene ribarka?”, Hajar tace “zuciyata tayi sanyi aii”, Zainab tace “ki ringa haƙuri ƙawata dan Allah”, Hajar tace “uhmm nidai akai min saina rama wallahi”, Zainab tayi murmushi tace “mutuminki fa ya shigo ajin nan yafi sau ashirin jiya”, Hajar ta yamutsa fuska tace “wa kenan??”, Zainab tace “wa kika sani bayan ya sayyadi Nura..”, Hajar ta juyar da fuskarta tana murmushi……….✍️
Download Hajar Hausa Novel Document By Nafeesa Yusuf Nagoda
Click the below green button to read the novel online
READ HAJAR PAGE 4 COMPLETE NOVEL
Proceed with your download by clicking the below button
Some Of Related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page : Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page : @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel: Ai Hausa Novels
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.