Uncategorized

Zuciya Da Kwanji Book 1 Chapter 3

 

 ZUCIYA DA KWANJI 
BOOK 1___3

Na Maimuna Idris Sani Beli

Tsawon wasu mintuna, sannan momi ta yi musu iznin su tashi. Abdullahi ya fara mikewa, sanna Fatima ta bishi a baya har zuwa katafaren falon da aka sauke shi. Suna shiga falon ya soke hannu a aljihu ya kuma canja fuska, sannan ya

juya mata baya. A gajiye kuma fuskarta a bace ta nemi kujera ta zauna tana faman harara a duhu, tunda bai san tana yi ba. Sun kwashe fiye da mintina goma a haka,sai da ya jiyo maganganun su safiyya a kusa da falon sannan ya juyo ya dube ta, duba irin wanda duk kwakwalwar mutum ba zai iya karanta abin da zuciyarsa ta boye game da ita ba.

 Ba ta ko dube shi ba, ta zabga tsaki, ta je ta zuba masa gasassun ‘yan shila wanda kamshinsu ya gauraye falon. Ta kwashe lemunkan da suka zube wanda ya fara hucewa, ta mayar fridge ta dauko masu sanyi duk ta dire kan center table. A cunkunshe ta ce. “Ga shi nan”.

Ya hadiye dariyar da ke damunsa, ya ce “Don me ba zaki kawo min nan ba? Ta zabga masa harara kamar idonta zai fado,

Ta ce “Don ni ba baiwarka ba ce, idan ma ba zaka ci ba, ka bar shi”. Ta dauki lemon kwakwa ta wuce kujera ta harde ta fara kurba, shi ma sai ya mike ya je ya dauki lemon kwakwar yana tsaye ya dire gwangwanin sannan ya zauna ya fara cin naman cikin gwaninta da kwarewa yana amfanin da wuka da fork. Ta saci kallonsa ta yi tsaki cikin ranta ta ce, duk yadda aka yi ya lakanci barin matansa da gabza shi ya zagaya restaurant ya barje. Duk sai haushinsa ya kara kumeta. 

Yana gamawa ya koma muhallin da ya tashi, wato na kusa da ita. Bai dubeta ba, sai ya dubi agogonsa ya ce “To ni zan wuce”. 

Ta yi tsaki kawai ba ta tanka ba. Ya dube ta da kyau, fuskarsa na rinewa da bacin rai, kawai shi ma sai ya zabga tsaki. Ta dago da sauri ta dube shi. 

Ya murza hannu rai a bace, idonsa cikin nata ya ce “Ji nan malama, neman kudi fa ba bariki ba ne mene ne za ki dinga yi min tsaki ke ba tsaka ba, wai ba ku kuka gayyato ni ba, ni ban miki ba ku karbi kudinku in san na yi, ina fatan ya sanar da ke ba daudar talauci ya kankare min ya dauko ni ba….. Uzurinsa kawai na kalla na karbi tayin”. 

Maganunsa suka ci gaba da kona mata zuciya amma ta rasa kalaman raddi, sallamarsa zata yi ya yi gaba su koma fafutukar neman wani tunda shi tsaurin idonsa ya yi yawa, ko kuma shiru zata yi masa ya ci garin? Dole shirun ta yi masa tunda shi ma yana da tasa darajar, idan har suka rasa shi da wuya su Kara sami kamar shi, sai ta ta buge da kallon talabijin shi kuma ya mike cikin sassauta murya ya ce 

“Kamar yadda na fada miki dazun, ba na son fada da masifa, kuma bana son tsaki, ke ni gaba daya ma bana son rainin hankali da wayo, idan kinga in daina zuwa gidanku good and fine kawai sai na dauke kafata ni ma lokaci na ya huta, in yaso sai manya su yi maganar auren kawai”. Ya yi shiru

yana kallonta.

 Ta dade cikin jan numfashi tana daure fuska, sannan cikin huci ta ce “Shi ke nan zan kiyaye, ni ma bana son yawan magana, kuma idan ka zo ka dinga zama a muhallinka daban nima ina zama a nawa….ko daya bana son wannan zaman kunatar ba na son wata mu’amala ta kirki ta shiga tsakaninmu. Sannan kar ka dinga kiran wayata a cikin abin da bai zama dole ba”.

 Ya fara tafiya, yana cewa cikin basarwa “Zan kiyaye”.

 Ta janyo jakarta don ta fanshe muntukus din da ya yi mata, cikin dakewa ta ce. “A’a tsaya ka karbi kudin zance mana”. 

Ya tsaya cak ba tare da ya juyo ba, sai da ya hadiye dariyar da ta kama shi tsab, sannan ya juyo cikin, mazewa ya ce “To na gode, na manta ma in gaya miki za’a yi bikin wani abokina sati mai zuwa ki ba ni kudin anko, shadda ce ‘yar dubu bakwai da kudin dinki dubu uku”.

Sai ta rasa abin da zata ce masa, kuma don kar ta bayar da kanta sai ta zaro dubu biyar ta mika masa tana cewa. “Aka ce kyauta tukwacin so ko? To tsakaninmu ba haka ba ne, na baka kudin zance ne da ya zama al’ada kuma don in nuna maka ni ce fa mai umarni da hani, kar ka je bikin….” 

Ya yi saurin tare ta da cewa. “To in haka ne kin gaza, tunda dubu goma ta fi karfinki, saboda haka kar wani lokacin ki ga rashin biyayya ta idan kika yi umarni na ki karba”.

 Ya karbi dubu biyar din ya zira a aljihu ya juya zai fita, ba tare da ya bata damara magana ba. Dole ta mike ta biyo shi da sauri har tana hadawa da gudu ta cimmasa suka fito tare a salon tayi masa rakiya. Ya dinga sallama da yaran gidan yana raba musu kudi, ya ba su sama da dubu ashirin, sannan suka jera har wajen motarsa da Fatima suna ‘yar hirar ganin idon mutane, wanda yarfe kawai suke wa juna. 

  Ta ce masa cikin gatsali. “Ka fa yi kokari, kamar ka yi abin a zo a gani”.

  Shi ma cikin gatsali ya ansa mata “Kin san ai ba shi din na yi ba, saboda haka bai kamata aji a bakinki ba, ko kuwa kuna son kalato maganar da kika ce ba kya so? 

  Ta ce, “Rashin so na da ita ba zai hana in yi sharhi akan abin da na gani a baude ba…..” 

  Shi ma ya ansa. “Ba ki ba mara danki kunya ba, don dama na yi miki kallon rashin alkibla”. Yana shirin tashin motarsa ke nan, ita kuma ya barta da tabo a zuciya. Dai dai lokacin da kawu ya shigo, sai ta buge da ce masa.

“To mara mutunci, ga kawu nan sai ka tsaya ku gaisa”. Ba ta jira cewarsa ba ta juya ta yi tafiyarta, amma ta labe tana hangensu da kawu, yadda Abdullahi ya zube kasa yana gaishe da kawu sai ka rantse dan limanin garin ne.

Tana kallo kawu ya dago shi ya dan rungume kafadarsa yana cewa. “Abdullahi ko? A ladabce Abdullahi ya gyada kai cikin bayyana jin dadi, kawu ya ce “Da kyau! Yanzu uwargidan ta yi min maganarka a waya don kai na saki sabgogina na taho. Ka ba ni aron lokacin ka mana zuwa bayan magariba”.        

  Abdullahi ya kara kan kan da kai ya ce “Babu komai”. Yana rike da kafadar Abdullah suka shiga gidan.

Bayana sallar isha’I kawu ya gana da Abdullahi, babu wani dogon bincike don ya yiwa mahaifin Abdullahi farin sani, ba tare da wani shakku ba ya ce masa. “Na ba ka auren fatima tun daga yau, ka turo waliyanka da sadaki su shaida, ina fatan zaka rike amanarta, musammam saboda maraicinta….. Sannan ina yi maka nasiha kar ka bari soyayyar Fatima ta runtse maka ido ka barta ta kangare maka kamar yadda suka yi da mijinta na farko….. Ya canja mata tarbiyya gaba daya kuma yanzu ya zo yana son jefa su masifar zaman haram. Tun daga nan zuciyar Abdullahi ta fara bugawa, ya kasa rufe baki yana kallon kawun har ya kammala maganarsa, sannan ya dora

cikin bayyana murna.

 “Fatima ta zama matata kawu? Da me zan bayyana maka godiyata?” 

 A nutse kawu ya ce “Ba godiyar na fi bukata ba, amanar na fi kaunar ka rike, kuma ina horonka da hakuri a cikin sha’aninta, tana da murdadden hali, amma tana da sauki kai idan an fahimce ta, saboda haka mu’amala da ita na bukatar hankali da azanci, kar ka ba ni kunya don Allah, saboda ko kadan ba na son damuwar fatima,yadda ka ji ina jaddada maka amanar nan tata, haka mahaifinta ya yi min satin da zai rasu, kamar dama yasan rasuwar zai yi, shi yasa kullum nake addu’ar Allah kar ya jarrabe ni a cikin lamarinta, kai ma ina horonka da wannan addu’ar don ba zam rufeka ba. Nasan Fatima kyakkywa ce matuka, wadda sai jarumin namiji zai iya tsallake shu’umancinta, ko ba ka san kyakkyawan mace na da hatsari ba?” 

  A nutse Abdullahi ke gyada kai. “Na sani kawu, na sani. Duk na gane karatun da kake min, insha’allahu zan yi bita. 

  Karfe goma da rabi na washe garin ranar da dare, yana gurfane a gaban mahaifinsa wanda ya nemi izinin gani tun safiyar ranar, shi ne ya ba shi wannan lokacin saboda yawan jama’a.

“Ina fatan babu matsala Abu Turab”(Alkunyarsa ke nan).

  Abdullahi ya kara rusunawa ya ce “Allah gafarta malam babu matsala”. Sai kuma ya yi shiru ya shiga sosa kai. Uban ya gama nazarinsa tsab, sai kawai ya zuba masa ido, suka dauki wani lokacin a haka, sannan malam ya nuna masa agogo ya ce “Ba ka lura da dare ne? Ga lokaci na tafiya a matsayinka na mai iyali, ba daidai ba ne ka je kana buga musu kofa”.

  Abdullahi ya kara lankwashe kafa, kansa a sunkuye ya fara magana “Allah gafarta malam wata kyauta aka yi min, shi ne na zo in sanar da kai”. Kallonsa kawai malam yake ba tare da ya tanka ba, “Wani bawan Allah ne ya kirani, ya ce ya aure min ‘yarsa”.

  Sai malam ya kara dubansa cikin tattare ido ya ce “Saboda ya tsammaci ba ka da mata?” Abdullahi ya girgiza kai a sunkuye. 

  Malam ya ci gaba da cewa “Uhum bude baki ka bani labari, kai ka fara nuna sha’awarka akan yarinyar ko kuma sai da ya baka ita sannan ka ji a ranka dama kana da bukatar kara aure a irin wannan lokacin?” 

  Abdullahi ya girgiza kai, amma ya kasa amsawa da fatar bakinsa, har malam ya gaji ya dora. “Wane ne wannan mutumin, kuma me ye dangantakarka da shi?” 

  Numfashin Abdullahi ya kai gwauro da mari, sannan ya kokarta ya amsa. 

 “Prof ne a nan jami’ar bayero, yana karantar da tattali sunansa, Prof. Alkasim Najib kuma ba ni da wata dangantaka da shi kawai na je gidan ne shi ne ya yi kirana ya ce ya bani auren ‘yarsa”

   Malam ya ci gaba da kura masa ido fuska a bace, ya ce “Me ya kai ka gidan?” Abdullahi ya muskuta, amma ya kasa magana. Can malam ya kara gyara zama ya dube shi da kyau, ya ce “Abuturab saurare ni da kyau, ina da bukatar amsar dukkan tambayar da na yi maka saboda kar in yanke maka hukunci bisa rashin adalci, ka gane ko? Kai ka kai kanka gidan Prof. bisa nuna kana son ‘yarsa?” 

  Kan Abdullah a sunkuye ya gyada kai, ba tare da fuskar malam ta canja ba ya ce “Yanzu Abu Turab kana matsayin almajiri zaka kai kanka gidan ‘yan boko neman aure? Tafiyar ku zata zo daya Abu Turab? Anya? Tarangahumarka fa ta fara isa ta, duka shekarunka nawa da zaka hadawa kanka wannan zafin? Mata uku a lokacin guda, biyu ma ya ya ka iya da su?

   Abdullahi ya kara kan kan da kai ya fara bayar da hakuri, malam ya tare shi a fusace. “Wai don me zaka ba ni hakuri? Bude baki zaka yi mu tattauna, ina son sanin alkiblarka akab wannan aure auren. Aure uku cikin shekara hudu idan na ga kana da hujja. Me kake tunani game da mata da kake son cusa kanka cikin lamarinsu?” 

   Kai tsaye kuma a nutse Abdullahi ya amsa. “Neman ilimi nake a cikin lamarinsa, don ina so dacewa da alkhairinsu, kuma ina neman tsarin ubangiji daga dukkan sharrinsu. Ban taba mafarkin zalunci a gare su ba, don haka nake neman toshe duk wata kofa da zan iya zaluntar da su ko da bisa kuskure, idan ka tuna, aurena na farko zabin kai na ne, amma ban yi dace tana da tarbiyya ba. Na biyu kuma ku kuka zaba min malam, amma Allah ya sani bana kawar auren mace irinta, don haka har yau a cikin rudu nake. Don haka na nemi wannan auren saboda ta dace da irin matar da nake wa kaina fata, sannan ‘yar mutanen kirki ce ina hasashen zata dinke duk wata baraka a cikin sakokin zuciyata”.

 “Me ka tanadar wa adalci?” Tambayar da malam ya yi masa ke nan bayan ya dire.

 Shi ma ya kuma amsawa a takaice “Niyya da kyakkyawan fata”. Malam ya jima cikin nazari cikin kada kai, sannan ya nisa ya ce “Abu Turab ina maka fatan aikinka ya yi dai dai da hikimar zancenka, amma ka sani bayan wannan zan bibiyi matar da aka ba ka don sanin irin gidan da ta fito. Idan na ga zaka iya tafiya a turban daya zan bar maku aurenku, sharudana a nan su ne; Kar na kuma jinka da neman aure nan kusa, sannan duk wani hukunci da zaka yanke a gidanka ya zamana da sanina kafin ka yanke shi, kar na kara jin ka tura ‘yar wani gidansu. Ina fatan ka fahimce ni”.

 Abdullahi ya gyada kai yana mai godiya sannan mahaifinsa ya ce. “Allah ya yi maka albarka, Allah ya jagoranceka, ya ba ka ikon yin adalci a tsakanin matanka”. Cike da farin ciki

Abdullahi ya dinga amsawa”amin amin. 

  Fiye da sati daya abdullahi bai kuma waiwayar gidan su Fatima ba, gaba daya a tsorace yake, kar binciken mahaifinsa ya cafko komarsa ya wargaza masa shiri, saboda haka nutsuwa ta kaurace masa har ya fara yardarwa kansa taranguhumar da mahaifinsa ke masa kirari ta dace da shi.

   Rashin zuwa nasa ya ɗan dami fatima, don har ta fara zargin ko ya janye, har ta kasa daurewa sai da ta sanar da Alh a waya, shi kuma ya nemi Abdullahi ya nemi ba’asi inda ya amsa masa cewa,

 “Babu komai sabgogi ne suka sha kaina, amma zan yi kokarin samun lokaci na je ko da bazan same ta ba”.

 Cikin muryar bayyana damuwa Alh ya ce “Yauwa ka kokarta don Allah, kar ka wargaza mana shiri, kasan kawun nata wani bahagon mutun ne, idan ba a yi da gaske ba sai ya shawo kanmu, kusan mutane hudu na tura kamar kai yana cafko su? Kai kanka na tabbatar dalilin mahaifinka ya karbe ka”

 A takaice Abdullahi ya ce ” Na sani”. Da haka suka yi sallama. Bayan kwana uku da wannan

wayar mahaifinsa ya kira shi a waya ya karbi lambar Prof a wajensa, wannan ma ya kara kada cikin Abdullahi kwarai, kwanaki biyun da suka biyo baya ya yi su ne cikin damuwa da dar dar. Zahirin maganar shi ne, malam ya nemi izinin ne na zuwa neman wa Abdullahi auren fatima, Prof ya yi murna kwarai, don shi ma ya shiga fargabar dauke kafar Abdullahi, jiya haka ya dinga surfa wa fatima da fadan cewar ita ta kore shi. Cikin farin ciki ya yiwa ‘yan uwa da abokan da suka kamata, su taya shi karbar wadannan manyan baki waya, ranar kuwa duk suka hallara. A takaice a wannan zuwan nasu suka kawo sadakinsu dubu hamsin, ba a tashi wannan zaman ba sai da aka kulla auren fatima da Abdullahi da shaidun da ba su haura sha biyu ba, aka yi musu fatan alkhairi da fatan samun zuria’a ta gari. 

Tirkashi!

Fatima ba labari, Abdullahi ma haka, sun zama ma’aurata a wani irin yanayi mai shayar da mamaki, to bare kuma Alhaji. Su kawu suka raka su motocinsu cikin karrama juna da yiwa juna godiya. sannan aka rabu duk suna ganin mutumcin juna.

Bayan sallar isha’I kawu ya shigo gida, momi ta shigo ta same shi, ko zama bai barta ta yi ba ya yi mata umarni da kiran fatima. Ba tare da ta nemi ba’asi ba ta fita sai ga ta tare da fatima.Tadurkusa ta gaishe shi.sannan ta koma gefe ta zauna. Ya dube su gaba daya cikin raha ya ce.

“Sai na ba ku albishir din tare ko?” Bai jira cewarsu ba,ya dora da cewa. “Dattawan Abdullahi sun zo, cikin ikon Allah har an daura auren, ungo sadakinta ba ta”. Ya mikawa momi kudin. Momi ta rafka guda, amma fatima sai ta yi mutuwar zaune.

  Fatima ba ta sami kebe kanta ba saboda dan bikin da jama’ar gidan suke mata, sai ta yi kiran wayar Alh. Yana jinta cikin kuka sai hankalinsa ya tashi,ya hau tambayarta cikin rudewa, da rarraunar murya ta amsa masa. “Wai me ya karfafa maka gwiwar hada ni da aure da Abdullahi ne? Me ya saka tsammatar masa kyautata muradanmu?” A birkice ya hau amsa mata. “Kanin abokina ne, mutum ne mara wargi, sannan yana da tausayi,ya nuna kulawarsa game da mu da nuna damuwarsa akan matsalarmu,don haka na mika masa kokon bararmu tare da hikimar kawu ba zai yarda zaki yi auren kisa wuta da shi ba…. Wai me ya faru?

Ta tsayar da kukanta tana goge hawaye, ta ce.

“To Allah ya takaita”. Ya ji kamar ta doki kokon

kansa da tabarya, ya ce.

 “Ki fada min abin da ya yi miki”. 

Ta fari numfashinsa da cewa ” Babu abun da ya yi min. An daura auren ne yau da magariba”. Shi ma sai ya ji labarin a wani hagunce, bakinsa na rawa ya ce, “Ban gane ba? Sam bai sanar da ni ba, alhalin dazu ma mun yi waya da shi”.

 Fatima ta hadiye wani kututun takaici ta ce, “To waya sani ko shima bai sani ba, don ni ma ba ni da labarin sai bayan daurin auren, shi ya sa na fara tsoron lamarin. Alh ka yi ganganci da ka dauko dan malamai ka hada ni da shi, ina shakkar idan Abdullahi bai zame min matsala a numfashi na ba”.

 Nan take shi ma tsoron ya cika shi ya ce, “Me yasa kika yi hasashen haka?”

 Cikin karaji ta ce. “Haba! Kana ganin yadda aka yi min aure shigen na lokacin sahabbai, ranar da kawu ya fara ganinsa. Fa, washegari da safe. Ya yi kirana ya ce min. ” Na ga Abdullahi jiya, har na ma ba shi aurenki, saboda haka sai ki kiyaye, a yanzu dai dai kike da Matar aure, sadaki kawai kike jira da shaidu”. Yau kuwa suka kawo sadaki aka kulla aurenen, sai dazun aka sanar da ni”.

Numfashin Alhaji ya kai gwauro ya kai mari, amma sai ya hadiye ya ce. “Har yau ban gano inda aka haifi matsalar da kike mana hasashe ba”.

  Kai tsaye ta amsa masa. “Ka raya wa ranka hujjar da Abdullahi zai gabatarwa mahaifinsa kafin ya saki aurena a cikin sati biyu? Labarin da na samuwajen momi duk ‘ya’yan gidan su Abdullahi na yin abu ne bisa jagorancin mahaufinsu. Sannan idan ma zai sake ni na tabbatar a matsayinsa na dan malamai zai yi min saki ne na sunnah, wato saki daya wanda yana iya sakina a yau, gobe mahaifinsa ya sa shi lallai ya mayar da ni, na mayu fa Alh? Idan ma ba a yi haka ba, ni kuma in zo gida na riski tashin hankalin kawa, kila silar da zai haramta mana komawa aurenmu ke nan, duk ba ka yi wannan tunanin ba Alh? Me yasa ba ka hada ni da wanda ba shi da wata kyakkyawar nasabar da za a duba ba?”. Sai numfashin Alh ya shiga sassarfa ya ce, “Duk ban taba wannan hasashen ba, na fi la’akari da adalcinsa….”

 “Dakata! Ka daina maganar adalcin nan don Allah, ka san duk adalci da zai maka bai kai wanda zai yiwa kansa ba, da me ka shirya kalubalantar adalcinsa idan ya ki sakina?”

  “Kinga, zan kira shi a waya yanzu….” Ya tari numfashinta ba cikin hayyacin sa ba.

  Ita ma ta tare shi cikin sheshekar kuka “Kar ka kira shi, kasan yana da iyali, zasu iya sauraron abin da za ku tattauna….. Kawai mu zuba wa sarautar Allah idon,ni dai rayuwata tana cikin wani hali……” Duk suka rude, ita kuka Alh kuka, soyayya ke nan ruwan zuma.

*************** **************

 Abdullahi ba shi da labarin auren, sai washegari ranar da ya doka sammakon amsa kiran mahaifinsa, wanda ya ce masa ya biyo kafin ya wuce wajen aiki. Tunda ya shiga gidan gabansa ke faduwa saboda yadda ya ga jama’ar gidan na masa wani irin kallo, har aka yi masa iso ya isa falon mahaifinsa. Bayan ‘yan gaishe gaishe malam ya ba shi albishir.

  

Yana rufe baki ya amsa. “Dama na kiraka ne don na sanar da kai jiya ni da iyayenka munje gidan Prof kuma sun karɓemu cike da girmamawa, ka yi kokari ka fita hakkinsu ka ji? Ni kaina na yaba da gidan da ka nemo aurenka irin su Prof a wannan zamanin sun yi karanci”.

Abdullahi ya yi shiru kawai, shi kaɗai yasan abin da ransa ke saƙa masa.

 “Ka je ka fara shiri daga yanzu, ni ma bana son a dauki lokaci ba ta ta re ba, don kar mu zama kananan mutane”.

 Abdullahi ya jima cikin shiru, sannan a kunyace ya ce, “Nan da sati daya ya yi malam?”

 Malama ya dan murmusa, ya ce “Allah ya nuna mana”.

 Abdullahi ya wuni ne cikin nazarin yadda rayuwar aurensa na sati biyu zata kasance, wai ya ya zai tunkuri wannan rayuwar ne? Da me zai yi tunkahon da zuciyarsa ke raya masa akan auren fadimatu? Da wacce hikimar zai tari kalubalen da zai dinga shigo masa, dalilin auren a cikin gidan da waje? Wannan lissafin ne ya hana shi sukuni a wunin wannan ranar, har bayan sallar isha’I inda ya hallara a gidansa. Girki uwargida sadiya ne, ita ke ta dawainiya da shi a katafaren falon inda ya langwabe yana bayyana gajiya, yana kishingide a kujera idonsa lumshe, kana kallonsa zaka gane ba a fata gajiyarsa ta tsaya ba har ma da zuciya.

 Sadiya ta dinga nazarinsa, sai ranta ya raya mata kawai miskilancin nasa ne ya motsa, domin tun shigowarsa bai mata maganar da idan an jera zata cika layi hudu ba. Duk da haka ba ta yi zuciya ta bar masa dakinsa ba, sai ta kame ta ci gaba da kallon talabijin. Daidai wannan lokacin kiran Alh ya shigo wayarsa, ya daga wayar sannan ya gyara kishingida, a kasaice ya yi sallama.

 Kawai sai Alh ya fara da tuhumarsa. “Ashe har an daura auren tun jiya, amma jiya da na kiraka ba ka sanar da ni ba?”

 Kai tsaye Abdullahi ya amsa masa “Haka ne, an daura tun jiya, sai dai ni ma ba ni da labarin

sai yau da safe malam ya yi kirana ya ce da ni an daura min aure”. Hantar sadiya ta yi masifar

kadawa, ta dora masa ido babu ko kakkautawa tana kallonsa yana yamutsa fuska, yana sauraron kashedin da Alh ke masa. “To sai ka yi kokarin cika alkwari, kuma in son ka ci gaba da dauke kafa a wajenta tunda an yi mai wuyar, kar ka sake ka taba min mata ka ji ko?”

 A takaice Abdullahi ya amsa,”To”.

 Alh ya ce masa “Yaushe ne tariyar?” 

 Abdullahi ya mayar masa da amsa “Na sanar da malam nan da sati daya nake son ta tare, ya kuma amince min, don haka zan yi kokarin

ganinta a gobe….. Ka dai tsumaye ni nan da sati uku”. Jikin Alh a sanyaye ya yi masa sallama ya ajiye wayar, shi ma ya fara shan jinin jikinsa cikin lamari, ya fara jiyo kashin gaskiya a cikin hasshen fatima, me yasa komai sai da malam za a yi?

Abdullahi na ajiye waya sai ya lumshe ido don haka sadiya ta yi mugun kuluwa, a kuntace ta

ce “Abu Turab wa aka daurawa aure?” Ya yi firgigit ya tashi zaune kamar wanda aka tasa daga bacci ya ce, “Oh yi hakuri, dazu na yi ta kiran wayarki na ji ta a kashe, zan sanar da ke an ba ni aure har an daura shi a jiya, yau malam ke sanar da ni”.

 Maganar da a zane ba ta fi sadara uku ba, amma girmanta ya zarce na gwaron dutse a

kwakwalwar sadiya, sai ta rasa abin da zata ce, kallonsa kawai ta ke kirjinta na bugawa,dakin na zagayawa da ita. Ba tare da ya direta ba ta tilastawa kanta yin magana bayan da numfashin ta ma ya karbi nasa aikin na tafiya cikin sassarfa. “Na yi nadamar aurenka Abu Turab, babu wani alkhairi a ciki aurenka wallahi….” Ya tashi zaune a hanzarce, ya kuma ware ido yana kallonta sosai. Ba ya mamakin fitowa wadannan kalaman daga bakinta, don ya yarda rashin arzikin sadiya ya wuce nan, sai dai ya kasa sabawa, sam ya tsani rainin hankali sai dai a yau nasihar malam ta yi masa birki, kawai sai ya sanya ido yana kallonta har ta sami damar dorawa. “Ai ko na mamajo ne kai iyaka ke nan. Cikin shekaru hudu aure uku, ba za a hada biyar ba sai ka rufe kofa, haka kawai da kuruciyata ka tara min kishiyoyi? Ni ban haifa na kana auro ‘ya’yan wasu suna neman jaza min ciwon zuciya, ayi magana ka ce malam ya yi maka aure kamar wani dan akuya, idan haka ne gaba daya ma auren malantar ba shi da wani amfani”. Har yanzu ya kasa tanka mata, idonsa dai na kallonta kai tsaye, fuskarsa kuma ta ki byar da wani karatu da zai sa a fahimci matakin da zuciyarsa ta dauka, watakila hakan ne ya sanya Sadiya mikewa ta ci gaba da zazzaga masifa. “Ni wallahi idan babu hali sai dai ka bani tikiti na na ware. Ba zan yi ta zaman hakuri da kai babu tsatso ba, amma kai kullum idonka akan mata, ka tara mu ridi ridi babu wani abun arziki, ko kai har yau ba ka yarda kai ne ba ka haihuwa ba, ka ke lilon tara mata?”

 A wannan karon sai ya tanka, kuma cikin murmushi wanda ke bayyana walwalar zuci. “Ya ya za a yi na ki yarda alhalin na riga na gada? Kin san ‘ya’ya talatin din. Da ke cikin gidanmu a ruwa iyayenmu mata suka sha?”

 Sai ta kara butsarewa cikin tsabar fitsara ta ce, “To idan ma ba ka gada ba Abu Turab, babu shakka an fitar da zakka, kuma babu ta inda ido ya mutu kwalli ya tono shi”. 

 Shi ma tana rufe baki ya amsa cikin halin ko’in kula da son tura haushi, “Haihuwar kawai na rasa, amma Allah bai hana ni komai ba bayan ta ciki har da ba ni damar na auro na kuma aurowa, ko zan dace da mai tsarkin zuciyar da zata karbe ni hannu bibbiyu ba tare da ta tsangwame ni ko ta tsangwami kanta ba. Kinga sai kiji mu luf in yaso dangi su haifar mana ‘ya ‘yan da zasu ji kanmu.

 Maganar ta yi masifar bakantawa sadiya rai, musamman da ta tuno lokacib da zai auro hindatu irin wannan tabarar ta dinga yi masa, amma bai taba damuwa ba,sai ya dinga nuna mata shi kansa ba da son ransa zai yi auren

ba, don dai ba zai iya yiwa malam musu ba ne

kawai. To wannan ta kayatar da zuciyarsa ke nan da har yake neman cin fuskata akan aurenta? Amsar wannan tambayar ta fara kada hantarta tun ma kafin ta santa, ya ya amsar zata samu? Abu Turab ba shi da kirki idan bai ga dama ba, soyayya ba ta hana shi rashin mutuncinsa idan ya motso. To da wanne KWANJIN zata kubuta daga fifita amaryarsa da zai iya yi idan ya fi kaunar amaryar a kanta?

Gaba daya tashin hankali da rashin hakuri suka bayyana a fuskarta, sai huci take kamar in ta bude baki za a ga hayaki, idonta a kansa, wannan yasa ya yi saurin yin fuska bayan ya dube ta a sakarce, idonsa cikin nata, ya ce, “Kuma ya ishe ki haka! Kishi ba hauka ba ne, kar ki nemi ki zage ni” Bai ba ta damar magana ba, ya daga wayarsa ya kira Hindatu, yana ajiye wa sadiya ta sauke fushinta cikin debe kauna. 

“Wai Abu Turab idan na zage ka me zaka yi? Ya hadiye dariyar da ta cika masa ciki “Kin fi ni sani. Billahillazi idan amaryar ta zo sai in nuna miki iyakarki, in dinga hada mata kwananta da naki in ga abin da zaki yi, za ki ce in fita in bar miki gidanki ne tunda ke kike aure na? Ba ta sami bakin magana ba, sai ga Hindatu ta yi sallama ta shigo. Ta same su a hargitse, sadiya a tsaye tana cika da batsewa, Abu Turab a kwance ya hada girar sama da ta kasa. Tana neman gurin zama ya tare ta 

“A’a kar ki zauna! Miƙe ke ma idan kina da kwandon taki rashin kunyar ki juye min. Ya nisa sannan ya ci gaba Aure aka daura min jiya, ma’ana kishiya na yi muku”. Duk da maganar

ta caki zuciyar Hindatu matuka, amma sai ta hadiye kasancewarta mai dabarar boye fushi

da bacin rai, muryarta a sake ta ce. “Da gaske?”

Ya saci kallon sadiya,ya kara murde fuska ya ce “Akan me zan muku karya? Wallahi da gaske ne, kuma cikin satin nan zata tare”. Hindatu jima tana dubansa,tana kuma satar kallon sadiya, ko zata ji zafin aurensa tana sa ran sanyinsa saboda sadiya, domin mace ce mara kaunar zaman lafiya, Allah kuma ya ara mata dama, tauraron sadiyar ya fi nata haske a idon Abu Turab, duk da munanan halayenta, ke nan Hindatu zata yi farin ciki da auren Abu Turab musamman idan amaryar zata danne tasirin sadiya. Da murmushin da ya ratsa har zuci, hindatu ta dube shi ta ce.

 “To don me zan juye maka kwandom rashin kunya, alhalin dama nasan kana da sauran kofofin? Ka auro biyu ma ni yanzu na shirya, abin da ba a kaina a su zauna ba?”

Wadannan kalamai da hindatu ta fada sai suka kara tunzura safiya ta ga yarfe kawai Hindatu ta ke mata. Ta yo kanm Hindatu da bala’I. “Abin da ya fi haka ma kina da lokacin ki fada tunda a daure kika ganshi, dama kin san da wata a ciki kika shigo saboda haka dole wasu su biyo bayanki. Ni ce nasan darajarsa a sabonsa ko mijin mace dubu ne ba hudu ba, auren soyayya ai ba karya ba ne”.

Sai da ta jima da sauke numfashi sannan Hindatu ta mike tana amsa mata.. “Allah ya yi mana tsari da soyayyar fatar baki, salon soyayyar ke nan kike juye masa kwandon rashin kunya? Ni da ba na sonsa yake tsammanin mun shuka irinta a gidanmu? To Abu Turab ba mu da halin hana wannan aure, sai dai muce Allah ya sanya alheri, Allah ya sa badi war haka ka cike gurbi” 

 Babu alamun wasa da shakka a fuskarsa da muryarsa, ya amsa “Ba amin ba, ai wannan matsayin mace biyu zata shigo, ina fatan daga kanta in kulle kofa, babu shiga babu fita.

Ita kanta Hindatu ta ji ciwon maganarsa, amma nan da nan ta watsa ta kan sadiya. “A’a wannan sai dai ka fada wa mai auren saoyayya, ni me amsa sunan abin da ahnnunka na dama ya rika me zan dorar? Duk da ka watsa mata kasa a ido ba ka ce ita ke amsa matsayin mace biyu ba”. Ba ta jira cewarsa ba bare ta saurari hayaniyar sadiya ta fice daga falon. Shi ma ya mike ya kule a bedroom har da murza key yana sauraron gorin da sadiya ke lika masa iri iri har da na sharri sannan ta koma kan hindatu.

Zamu dakata a nan sai Allah Ya kaimu gobe inda za mu ci gaba daga inda muka tsaya.

Ga masu bukatar Audio kuma za su iya saurara ta hanyar taɓa wannan hoton dake ƙasa. Mun gode da ziyarar Aihausanovels.

Back to top button