Uncategorized

Abdul Jalal Chapter 11 Book 1 Complete Hausa Novel

 

Ilham ce da yaseera gurfane a gaban malamin nan, malamin ya kalli ilham sannan yace

“Ya kikazo keka dai yau ina babartaki?” Ilham ta Dan gyara zama

“Malam akwai matsalane fa”

“Matsalar me?”

“Malam, nifa na fara gajiya da wannan wahalar danakeyi akan Jalal, ina ta nawa kokari amma, wata Matsala na kokarin kunno kai, duk wannan wahalar danake yana kokarin fara soyayya da wata yarinya daban, hankalina duk a tashe yake”

Malamin ya numfasa ya kalli Ilham sannan yace

“Anya kuwa dagaske kike yafara soyayya, a aikin damukayi akansa bana tunanin ze iya fara soyayya cikin sauki, har se burinku yacika,”

“Malam nifa tsoro nake, kar inje shirin ya rushe gaba daya”

“Hakane in dai ba wancan sharadin ne ya afkuba, to aikin damukayi masa yana tareda shi har yanzu, koda kuwa yayi soyayya da wata, sedai in wancan sharadi ya karya”

“Wallahi ji nake kamar kawai in aiwatar da me gaba dayan tunda har yanzu yaki yadda ya soni, balle ya aureni”

“Wannan kuma ya rage naki sekije kicigaba da kokari, ko be sokiba daya aureki shikenan aiki ze kammala”

Yaseera ta kalli malamin

“To yanzu malam babu yadda za ayi da wannan shedaniyar yarinyar, tunda akwai yiwuwar ya iya fara soyayya”

“Wannan kuma Ku zakuyi wannan aikin ni nayi muku kokarin da yakamata sekije ki bada himma, zanyi bincike akanta, muga abinda za ayi akanta”

“To shikenan malam zanje in cigaba da kokarin”

“Yayi kyau, abinda ake ciki zan sanarda ke”

Suka mike suka fito yaseera ta kalli Ilham

“Wai Ni kuwa Ilham wace wannan yarinyar”

“Hmm wallahi kanwar abokinsa ce wata Mara mutunci da ita, yaseera yarinyar nan bata da mutunci Sam, idan banyi wasa ba fa zata bata min aiki, kinga rashin mutuncin da take masa amma ko kallonta ba yayi balle ya dau mataki, kuma da nice na gayamasa abinda take masa da tuni ya hukuntani”

“Kince sonshi take, kuma kince tana masa rashin mutunci, anya kuwa son nashi takeyi”

“Nima abinda nake ta tantama kenan, amma nafi tunanin borin kunya suke a gabana amma sonshi take, kinga a yadda nagansu kuwa ranar a gidansu, wallahi bantaba tunanin haka kishi yake ba se ranar”

“Wai ma inane gidansu”?

“A gidansu Nana take fa cousin dinsu ce”

“Muje gidan inga wace ce, inga iya rashin mutuncin nata se mu San ta inda zamu bullo mata”

“To shikenan mu karasa, ki ganta,”

    Hannah ce kwance akan gadonta tana zancen zuci, “mace kamarni ace Jalal yake wulakantawa, ga yadda maza kemin layi amma akan wannan Dan tahalikin, nake wahala har wani cewa yake ko ze aure baze aureniba, na tabbatar ranar Dana kirashi wannan kanwar tasa ce ta daga har take zagina, zanyiwa Jeje aikinsa sannan itama kanwartasa senayi maganinta, nita zaga saboda tana son Jalal, zata ga tsiya, indai Hannah ce ta taro daidanta”

   

  Nana ta fito ta tarar da Jalila a kwance akan kujera tana danna waya

“Jalila zan Dan fita, zanje bayan layi ne Maama ta aikeni”

“To sekin dawo”

Fitar Nana ba dadewa aka turo kofar palourn ba ko sallama, mutane taji tsaye akanta 

“Dan Allah ina Nana”?

Shiru tayi ba tako daga kai ba, balle ta ga suwaye

” magana fa nake miki”

Ba ta dago kanta ba tabada amsa

“Taje akoya mata sallama, inzaka shiga guri”

Yaseera ta kalli Ilham, sannan tace

“Yi hakuri Dan Allah, salam alaikum”

“Wa alaikum salam warahmatullah”

Jalila ta amsa sannan ta tashi zaune

Ta dubesu ta danyi murmushi 

“Sannunku da zuwa bismillah ga guri Ku zauna”

Ilham se wanj hura hanci take

Jalila ta Dan kalli Ilham sannan ta maida idonta kan yaseera

“Nana ta Dan fitane ba nisa tayiba yanzu zata dawo insha Allah”

Yaseera ta danyi murmushi, 

“To mungode”

Suka samu guri suka zauna

Jalila tace

“Ilham ya kike,? Ya Gida”

Ilham tai mata wani irin kallon up and down

“Da nazo nayi miki maganane? Kokuma ke a dole sekinshiga harkata”

“Ko in shiga harkarki ko kar inshiga harkarki babu abinda zaki kareni dashi ko ki rageni dashi, tunda ba abunda nake nema a gurinki nayi hakanne kawai Dan sauke hakkin addinina, ke Yar uwatace musulma, kuma makociya, muna da hakki akan juna shinake kokarin saukewa kawai, bawai wani abuba”

Tabdijan yaseera a zuciyata tace “lallai wannan yarinyar yar duniya ce tana da baki, gashi komai nata abin birgewa yanayin yadda take magana kawai ya isa ya dau hankalin mutum, ga iyayi kuma dajin maganarta kaga shgwababbiya gashi ta iya juya ido in tana magana” yaseera kallon Jalila kawai take 

“Bakuwa bari in kawo miki abin tabawa kafin Nanan ta dawo, naga Ilham se wani cika take tana batsewa bansan menayi mataba”

Jalila ta mike tana tafiya a gayance ta nufi fridge

Lallai dole Jalila ta tafi da imanin duk Wanda yai tarayya da ita dukda Ilham tace mata bata da mutunci amma tana ganin hakan duk cikin iya takunta ne

Lemo Jalila ta kawo musu da ruwa sannan ta kira Nana a waya, ta gayamata tayi baki, Nana tace mata takusa karasowa tana daf da Gida

Yaseera ta kalli Jalila 

“Nagode Yar uwa”

“Bakomai yiwa Kaine bakin Nana ai baki nane”

Ilham bata kuma cewa komaiba, tunda Jalila takuma gaya mata magana, sema haushin yaseera daya kamata ganin yadda ta zage suna hira da Jalila kamar sun saba

Ana haka Nana ta dawo, 

“Yawwa ga Nana nan ta dawo”

Nana ta kalli inda su Ilham ke zaune

“Yaseera dama talaka na ganinki gaskiya akwaiki da zumunci”

“Yanzunma unguwa mukaje nacewa Ilham mu biyo mu gaisa kwana biyu bamu haduba”

Nana tace “hmm kin kyauta ya Gida ya kwana biyu?”

“Lafiya kalau”

Jawwad ne yayi sallama a palourn suka gaisa dasu Ilham

Sannan ya kalli Jalila

“Baby yunwa fa mukeji kuma munji ki shiru, Jalal ze sha magani beci abinci ba”

Kallon Jawwad tayi ta danyi murmushi

“Aini yau banyi girkiba, in kuma kunajin yunwa to kuzo kuyimin wanke² wani yayi gyaran kayan miya” murmushi Jawwad yayi  ya nufi hanyar kitchen Jalila ta mike tabi bayansa, Ilhaam kam Dan bude baki tayi

“Hmm Yaya Jawwad manyan”

Nana ta fada tana Dan murmushi

Ita dai yaseera ta jinjina yadda Jalila take gudanar da

al amuranta cikin nutsuwa, lallai indai da Jalila, Jalal yake 

Shirin fara soyayya to se Ilham tayi dagaske, don Jalila bazata sha wahala gurin sace zuciyar duk Wanda taso ba 

Jawwad ne yake bubbude kwanuka a kitchen

“What are you looking for?”

Yaji muryar Jalila a bayansa, juyowa yayi ya kalleta 

“yunwa fa  mukeji baby” yai maganar yana kwaikwayon JALILA 

“Yi shiru karkayi kuka jeka zan kawo”

“Inyi kuka sekace wani baby, Babyce me kukan allura, kuma nasan in tanajin yunwa ma setayi kuka”

Dariya sukayi gaba daya

Wanda hakan yayi dai² da fitowar Maama tana kallonsu ta window kitchen, kwafa maama tayi ta nufi parlour

Su yaseerana suka gaida maama ta amsa musu sannan tace ma Nana taje tacewa Halima tana kiranta, tajuta ta koma dakinta

Su yaseera suka mike sukace zasu tafi, dama ba ziyarar Allah da annabine ya kawosu ba Dan ILHAM ta nunawa yaseera Jalilane, suna shirin tafiya 

Jalila suka fito ita da Jawwad, suna dariya, Ilham ta kallesu taja uban tsaki 

Jalila ta kallesu “har zaki tafi, yaseera, mungode ki gaida Gida, Ilham ki gaida mummy”

Ilham bata kula Jalila ba itama Jalila bata damuba Dan tasan ILHAM ba amsawa zatayiba, tai waje da kayan abincinsu Jawwad

Nana ta kalli Ilham

“Haba Ilham, Jalila tana miki magana amma kin wani shareta”

“Kinsan bana son rainin hankali, kuma kinsan halintane dan haka ni bana shiga sabgar mutum inaga hankali be isheshiba”

“Kut lallai Ilham amma kinsan da a gabantane dase ta gaya miki wadda tafi takin zafi”

“To yanzu tunda bata nan seki rama mata”

Ilham ta fada tana Harar Nana

“Rufamin asiri, ina ni ina iya shigarwa Jalila fada ai sedai inyi kallo”

“Ya fiye miki”

Haka Nana tarakasu ILHAM had bakin gate suna tafe suna fada,

   

Jalila tabi bayan JAWWAD da kwanukan abinci zuwa part dinsa, oga Jalal yana zaune yana kallo sekace dakinsa, Jalila ta ajiye kayan abincin tareda fadin “wash” JAWWAD ya Dan kalleta “kai baby har kin gaji”

“Niba gajiya nayiba”

“Hmm dagaske?”

“Eh mana”

“OK tunda bakgajiba serve us”

Seda ta kalli Jallal ta Dan hade rai

Ta dau plate tayi serving Jawwad, ta kalli JAWWAD “sekuma me?

“Baby Jalal fa, serve him too”

Yamutsa fuska tayi

“Ni na gaji”

“No Jalila, kefa kikace Baki gaji ba, hakan ba halinki bane”

Kafin tayi magana Jalal ya taso daga inda yake cike da gadara, yasa hannu ya dauke plate din gaban Jawwad da Jalila tayi serving din Jawwad, ya dau spoon ya samu guri ya zauna, ya fara cin Abincinsa

Bayan sun fitane yaseera ta kalli Ilham

“Tab wai yanzu kina nufin wannan itace budurwar JALAL din”

“Hmm gata nan kin dai ganta ko?

” ai ko ta hadu”

“Kamarya ta hadu, kinsan dai na fita kyau ko?”

“Ke dalla wayake ta wani kyau Ilham, duk kyanki akwai qualities din da in kika rasa, to kyan yazama shirme, banda abinki ma dame kika fita, hasken fatarne kawai amma wallahi kyakykyawa CE”

“Au yaseera hakama zakice dame ta fini?”

“Kallifa mu matama kalli da yadda take mana magana INA ga in agaban namijine, gashi ta iya iyayi da siyasa, kincemin fada kuke, amma dukda munzo tare kalli yadda ta mutuntani, gata Yar gayu”

Ilham ta hade rai sosai sannan tace

“Ni duk ban iya wannan abubuwan ba kenan?”

“Bahaka bane ba, amma kin San meyake cutarki”

Ilham ta girgiza kai

“Rashin hakuri, saurin fushi, ga garaje, gaki da sakaci, kinga in bakiyi dagaskeba akwai matsala kina ganin yanda take wani juya ido in tana magana”

“To yazanyi yaseera,?”

“Waima tukuna naji yayan Nana yana batun akai musu abinci shida Jalal, Abincin ma ita take kai musu”

“To inaga ita take kaimusun mana” Ilham tai maganar cike da damuwa

“Cab wato ita take kaimusu abinci, lallai ILHAM da sauranki, gaskiya akwai tendency na JALAL yafara soyayya, kuma abinda kike gudun yafaru”

Ilham ji tayi kaman ta Dora hannu a ka ta fashe da kuka

“Yaseera ya zanyi, nikam indai nabari shirin mami ya rushe batareda ta dau fansar nan ba nayi asara

Wallahi yaseera se yanzu nagane son gaske nakewa Jalal, wallahi zan iya komai akansa”

“Kina wannan sakalancin zaki iya komai akansa? Malama ki dage Dan wallahi wannan yarinyar da bariki zatayi zata Tara abun duniya,

Yanzu ki saurareni, batun kice kin gaji be taso ba, duk masifar daze miki kidena zuciya da shi, sannan kidena jin tsoransa, sannan kidinga kokari kema kina dafa abinci ki bashi, in wataran beci ba wataran zeci”

Ilham ta Dan girgiza kai

“Yaseera gani kike shawo kan Jalal abune me sauki ko? Mugun Dan taurin Kaine, ga shi jarababbe, yaseera tsawon shekarun nan danayi a gidansu ko inda yake bayaso inje, am about to give up”

“Ita Jalilan dayake daga mata kafa ba mace bace kamarki, iya bariki kawai tafiki, ki bar wani batun seya soki malama kawai ya aureki a wuce gurin”

“To yaseera insha Allah zan kuma jajircewa, Wallahi nida zuciyata tafara bani kawai inyi duk me yiwuwa kawai inyi me gaba daya”

Da sauri yaseera ta kalleta

“Baki da hankaline? Inkuma aka samu akasi fa”

“Nima abunda yasa nafasa kenan”

“Karki kuskura ki fara, kibi komai a hankali”

“To shikenan yaseera, zan cigaba da kokari”

Haka yaseera taita zigata sannan sukayi sallama, Ilham ta shiga Gida yaseera kuma ta tafi

  Hannah ta kira wayar Jalal harta gaji dama seyaga dama yake amsa wayarta, yau ta kudurce wa ranta kome ze faru sedai yafaru Dan Gida zata bishi, lokaci yayi da yakamata tafara wasan kwallo dashi daga shi har kanwar tasa dole sugane wace Hannah, 

Jalila bin Jalal tayi da kallo, wannan akwai Dan rainin hankali, shima Yaya Jawwad sekace Jaraba kowa da gidan ubansa ya zauna a can amma shi inbe bishiba shi ze biyo shi, a ranta tace kacigaba zan rama ne wannan wulakancin da kakemin bakaci bulus ba

A zahiri kuma ta ba sar ta kuma serving din Jawwad

“Yawwa Yar Baby, mungode sosai”

“To yayan Baby, permit me to leave”

“U can leave dear”

Tana komawa cikin Gida Maama ta kuma aikenta gidansu Jalal, waita karbo kaya anjima wasu customers zasuzo tun safe Jalila take aiki bata huta ba gashi bata son abunda ze hadata da Ilham, ba tayi musu ba ta juya ta kuma tafiya aiken da akayimata, 

Tana fitowa taga wata mota a tsaye a kofar gidansu Jalal, harta gifta mortar, aka danyi reverse da motar saitin inda Jalila take, sauke glass din motar akayi wata matashiyar budurwa ce a cikin motar

“Sannu dai” tacewa Jalila

“Yawwa sannu”

“Dan Allah tambaya nake”?

” Allah yasa nasani”

“Naga kamar  cikin gidan nan zaki shiga”

“Au kamace baki tabbatarba”

“Ohh sorry Dan Allah Jalal nake nema”

Kallonta Jalila tayi, tayi nazarinta na wasu yan mintuna sannan tace

“Me Jalal ze miki”?

” inason ganinsane”

“Baki da lambarsane?”

“Nakira bata shiga”

“Injiwa zance masa”?

“Kawai kice masa yayi bakuwa”

“Bahaka nakeba, inkina son ganinsa kifadi sunanki”

“Hannah ce, koke ce Ilham din da Jawwad yake gayamin kanwarsa da kike sonshi”

Da sauri Jalila ta kalleta, ta Dan kuramata ido wasu yan mintuna sannan tai murmushi

“Hannah”

Jalila ta maimaita

“Yeah I am Hannah”

Jalila ta kuma murmushi

“Zata iya yuwuwa nice Ilham kuma zata iya yuwuwa bani baceba, for now bazaki ga Jalal ba ki tafi kawai inma kin tsaya bazan bari ya fitoba, kune masu kara ingiza lalacewarsa, kalleki, kalli shigar jikinki a matsayinki na ya mace kina yawo half nicked, kinzo gurin namiji saboda abun kunya, me kike tsammani in mutane suka ganshi da ke, kibari in yaje inda kuke haduwa kya Ganshi amma ba anan ba, juya kikoma inda kika fito” Jalila ta hade rai tareda nuna mata hanya.

Karewa Jalila kallo tsaf Hannah tayi, ta tabbatar Jalila Sa ar kanwarta ce, badan kartayi karyaba setace kanwa ta biyu ma, bude motar tayi sannan ta fito ta kalli Jalila sama da kasa, ta danyi murmushi sannan tace

“Ni kike kora kike cewa in tafi in bar nan gurin”

“Au tambayata ma kike, lallai na fuskanci saboda irinku ake double period a class, saboda ba kwa dauka a daya”

Mamakine yacika Hannah, tace

“Bari in gaya miki wani abu dabaki saniba ni…..

Jalila ta dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu tareda fadin

” NO need saboda babu wani abu me amfani ko me mahimmanci Wanda ze amfaneni dazaki fada, as I said it before, kibar nan gurin in ba hakaba zan baki mamaki”

“Ni Hannah zaki bawa mamaki”

“Kwaraikuwa kedin”

Nuna Jalila tayi da Dan yatsa zatayi magana, batayi maganarba Jalila tasa hannu ta sauke yatsan Hannah

“Duk wata magana muyita amma ba a nunani da Dan yatsa, daga haka nagama magana dake, nabarki lafiya, inkin gadama kicigaba da tsayuwa”

Jalila na zuwa nan a zancenta ta shige gidansu Jalal tabar Hannah tsaye sororo tana mamaki 

Jalila ta shiga cikin gidan da sallama, Ilham tana palourn tana danna waya tayi mata banza, Jalila ta kuma nanata sallama amma Ilham mirsisi taki amsa sallamar Jalila

Karasawa Jalila tayi tasa hannu ta fizge wayar hannun Nana

“Haba kekuwa, kome nayi miki a rayuwa be kyautu inyi sallama kimin banza ba”

A fusace Ilham ta kalleta

“Bani wayata malama”

“Kiramin mummy, seki karbi wayarki”

“Ke kin isa kisani aiki,”

“Ban isaba alfarma na nema”

Sannan ta bawa Ilham wayarta,

Ana haka mummy tafito da alama unguwa zata fita

Suka gaisa da Jalila, Jalila ta gayamata Aiken da akayi mata, mummy tace taje yanzu fita zatayi in ta dawo zata aiko,

Da haka Jalila ta fito ta tafi gida,.data fito ta tarar Hannah ta tafi, Jalila a ranta tace kin kyautawa kanki dakika tafi ai

    Hannah tana barin gurin takira wayar Jeje ta tambayeshi ina zasu hadu yagaya mata, ta nufi gurin kai tsaye, tana zuwa ko tasameshi a can, yanayin fuskarta kawai ya nuna masa akwai matsala, saboda yadda take huci

“Me idon zinare, lafiya kuwa”?

” ina fa lafiya, gidansu Jalal naje, saboda yan kwanakin nan baya daga wayata, naje nasamu wata a kofar gidansu, wata yarinya taci min mutunci”

“Kamarya taci miki mutunci, miye hadinki da ita?”

“Ina kyautata zaton itace budurwar tasa, da Jawwad yake fada Ilham take kowa, hada cewa bazata bari ya fito ba, sedai injira muhadu inda mukasaba”

“Jalal din, to karya takeyi barazana ce kawai, uwar da ta haifeshi ma bata isa ta hanashi abinda yyi niyya ba, balle wata Ilham, gayen da soyayya bata gabansa, kema kinciri tuta ne da yake sauraronki, amma ya akayi kika San Ilham dince”?

“Na tambayeta amma ta rainamin hankal, Amma nayi mamaki, yanda nake zaton Ilham din na dauka wadda zanyi maganice a take amma naga itama a tsaye take Dan bata da kunya”

Dan shiru Jeje yayi sannan yace 

“Tabbas Ilham ma masifaffiya ce amma bana tunanin ta kai yadda kike fada haka”

“Hmm, bakaga wulakancin datayi minba kuma na girmeta, sena raina rashin kunyata Dan fafur hanani magana tayi, mamaki da takaici suka cikani”

“Gaskiya Hannah kin bani kunya duk bakin naki, kinsan a duniya Jalal ya tsani mace ta dinga juyashi”

“Ba a nan takeba Jeje hausawa kance yaki Dan zamba ne Dan haka, zan nuna mata duk Wanda yarigaka kwana ze rigaka tashi, idan takamarta rashin kunya, nikuma takamata bariki, zan daga shi har ita zan basu mamaki”

   Jalila ta sanar da Abba zuwan captain Rasheed da yayansa domin kawo musu ziyara, Yaya farinciki sosai da jin haka, Jalila ji take kamar ta janyo ranar Saturday su Hanan suzo, se murna takeyi 

Daren yau dai Jalal yasaci jiki ya tafi gurin shan giyarsa, yaje babu dadewa be fara shaba, mayyar tasa tazo wato Hannah, tazo ta nemi guri ta zauna tai shiru batace komaiba 

Ya Dan kalleta, yanayin fuskarta ya nuna tana cikin damuwa,

“Ya akayine sarkin matsala, mekuma ya faru?”

Ta dago ta kalleshi, tayi kalar tausayi sannan tace

“Jalal kwana nawa ina kiranka kaki ka daga wayata, naturomaka messages kaki reply haba Jalal, gashi aka cimin mutunci saboda kai, yakamata ka tausayamin”

“Ya akayi aka cimiki mutunci sabodani?”

“Kanwarka mana”

“Wake nan?”

“Wace kanwar kake da ita, banda wadda Jawwad yacemin tana Sonka?”

Shiru ya danyi yana kallon Hannah, tacigaba da magana

“Ranar nakiraka baka dagaba, ita ta daga ta min rashin mutunci ni kana cemin Mara kamun kai amma me kanwarka take a gurinka shabiyun dare, har tana gayamin bacci kake ta zageni hadda cemin mayya”

Shikam Jalal kasa cewa komai yayi se ido da ya zuba mata,

“Har yanzu ni banga cin mutuncin dakike fada tayi miki ba”

Kallonshi tayi

“Au hakama zakace? Metakeyi a gurinka shabiyun dare harta daga wayarka?”

“Meye kuma na bin diddgi ina ruwanki dame take a gurina shabiyun dare?”

” haba Jalal,Yauma nakasa jurewa da rashin ganinka Dan haka naje gidanku, na hadu da ita a kofar Gida daga tambayar kana ina ta dinga zagina

Harda cewa baka isa tahanaka abu kayi ba Dan haka bazata bari ka fitoba, saboda baka tsallake maganarta, tana juyaka yadda taga dama, haka ta dinga fadar maganganu, abun ya dauremin kai”

Dan dagowa yayi da sauri

“Inji Ilham din?”

“Eh mana, ni babban bakin cikina yadda ta dinga gayamin miyagun maganganu saboda kai, wallahi Jalal ba Dan kanwarka bace senasa ankoyamata iya magana, harni zata cewa mutuniyar banza? Ita ma ai ta banzarce tunda zata iya zuwa dakinka shabiyun…….

” Enough malama, karki kuskura ki zagi kanwata, kuma wallahi duk abunda yasameta a kwanan nan kikuka da kanki, Ilham ba mutuniyar banza bace, ni shedane, ki kiyaye baki isa ki zageta a gabana ba, and then zanje gidan in sameta, zatayi bayani”

Yana zuwa nan ya tashi ya tafi yabar Hannah baki a bude, saboda mamaki se yanzu takuma tabbatarwa kanta tsawon wannan lokacin, har yanzu Jalal be fada tarkon sonta ba kenan tunda har ya fifita Yar uwarsa akanta kenan ya fara son Ilham, amma ko ba komai tasan abunda ta fada din nan ze tunzirashi, gaba dayanku, sena nuna muku ni gogaggiyace a bariki

Jalila hartayi shirin kwanciya Abdallah ya kirata suketa hira dashi da ita da hanan, a wannan lokacin kiran JAWWAD yaita shigowa amma line busy, Jawwad ransa babu dadi ya kwanta, yana tunanin dawa Jalila take waya tsawon wannan lokacin

          

Tunda Jalal ya tafi yake tunanin ya akayi Ilham ta daga masa waya, meya kaita part dinsa shabiyun dare ( besan Jalilace ta amsa wayarba, lokacin da bashi da lafiya”)

Shi babban takaicinsa ma cewar da tayi inta hanashi abu be isa yayiba, yaushe yake shiga harkarta dazatayi masa karya, ta zubar masa da kima a gurin wata mace daban aikuwa se ya hukunta Ilham Dan baya son karya (Ilham zata amsa query maimakon JALILA 😂😂)

Ya koma Gida yana zuwa ya tafi part dinsa don kuwa by now yasan mutan gidan sunyi bacci, yanazuwa yai wanka ya canza kaya sannan yasha giyarsa iya son ransa sannan ya kwanta bacci

Daren ranar Ilham tayita sake² yadda zata canza takunta na zama a gidan, domin Janyo hankalin Jalal kanta Dan wannan karon ta sawa zuciyarta lallai seta cika burinta.

Da safe Jalila kaman yadda ta saba tayiwa halima Karin karatun Qur’ani sannan suka  tashi sukayi aikace² daya kamata suka hada breakfast

Kamar kullum Da sassafe Jalal yake zuwa saboda suna motsa jiki, in sukayi suka gamane we yayi wanka ya canza kaya, a gidan, 

Ya lura da rashin walwala na Jawwad amma bayaso yafiye takura masa, bayan sungama exercise ne Jawwad yai wanka yaketa shirin tafiya makaranta, saboda ze shiga lectures karfe tara

JALAL ya kalleshi ” wai yanaga Janata shirin tafiya makaranta breakfast dinfa”?

“Nakoshi”

Dan zare ido Jalal yayi 

“ka koshi kuma, me akayi maka ne? Naga se fushi kake, meyasa kake so ka tafi makaranta bakayi break fast ba”

“Haka nan, yau bana son cin abincine”

“Ban yadda da abunda kafada ba, baka fiye yin fushiba, kana iya boye damuwarka, amma tunda nagane kana cikin damuwa nasan matsalar babbace,”

Dan murmushi kawak Jawwad yayi “meyasa bazaka yadda ba ne?”

“Shikenan naji amma ban yadda ba”

Jawwad ya cigaba da shirinsa, Jalila ce tai sallama

Jawwad ya amsa tareda basar da ita yacigaba da shirinsa, dama JALAL ba amsawa zeyiba

“Barka da safiya Yaya Jawwad”

“Yawwa barka”

“Naga kana shirin fita abincinfa?”

“Nakoshi”

“Meyasa?”

Shiru yayi mata yasamu guri ya zauna yana kokarin daura agogonsa, 

JALAL yana kallonsu bece musu uffan ba 

kan hannun kujerar da Jawwad yake JALILA ta je zauna, tasaka hannu ta karbe agogon hannunsa

Dagowa yai yana kallonta, ba tareda ta kalleshi ba tace

“Gayamin meyasa yau bazakaci abincina ba? Laifin menayi maka?”

Y miko mata hannunsa tareda fadin

“Babu abinda kikayimin, ban agogona kar in makara”

janye hannunta tayi 

“Ko shine yayi maka wani ABU?”

“Shiwa”

“Wancan” tafada tana nuna JALAL, gaskiya JALILA Yar rinin hankali ce

Jawwad yace “ba sunansa wancanba,”

“Yaya Jawwad na fuskanci ninayi maka laifi, Dan Allah kayi hakuri”

Dan kuramata ido Jawwad yayi, ta damu sosai

“Jalila me kikeso ayi yanzu?”

“Kaci abincin, sannan ka dinga kulani”

Murmushi Jawwad yayi Wanda seda hakoransa suka fito yanayin yadda tayi maganar ya birgeshi matuka

“Baby meyasa baki daga wayata ba jiya da daddare for more than 30 minutes wayarki busy”

“Yasalam Yaya Jawwad Hanan ce fa kasan gobe in Allah ya kaimu zasuzo, ita ta kirani taketa min surutu labarin makaranta, Gida, da sauransu, muna gamawa siyama ma takirani, naso in kuma kiranka, se nayi tunanin kayi bacci ne,

Amma tuba nake yayana bazan kumaba insha Allah”

“Baby bazan iya fushi dakeba Sam, kawo abincin”

Jalal ji yayi kaman yasamu bulala ya zanewa Jawwad jikinsa, saboda bacin rai dama akan wannan, shugabar marasa mutuncin yake ta wannan fushin gaskiya Jawwad Dan wahala ne

Tea Jalila ta hada masa ta zuba doya da miyan sos ta bawa Jawwad 

“Nagode sisyna, amma kinsan mu biyune yaya Jalal fa, shima a bashi”

“Ya jira Ilham in tazo ta hada ta bashi,”

“Kai Baby, meyasa hakane nida Jalal dayane, indai zakiyiwa Jalal haka nima zaki iya yimin”

“A gurinka ne daya ni….. Bata gama maganar ba

Kamar yadda yai mata jiya yanzunma Jalal zuwa yayi ya kwace na hannun Jawwad yai tafiyarsa kan kujerar da ya taso

“Yaya kana kallonsa ko?”

“To Baby ya zanyi indai bazaki bashi Abinci ba abun akaina ze kare, nawa ze karba ya cinye”

Zuciya Jalila tayi ta mike tareda fadin

“Ai sekuyi tayi,”

Murmushi Jawwad yayi sannan ya kalli Jalal

“Bros meyasa ba kwa jituwa da baby ne, why”?

” saboda bazan iya wannan shirmen da rashin aikin yinba, kalli saboda abunda be taka kara ya karyaba kake ta fushi, na dauka wani abun akayi maka, Ashe saboda wannan uwar rashin kunyan ne, shirme kawai”

“Allah yabaka hakuri, amma bazaka ganeba Jalal”

“Ameen naji bazan ganeba din”

Jawwad yagama breakfast dinshi ya tashi ya shiga cikin Gida suka gaisa dasu Abba, sannan yacewa Halima Dan Allah in Jalila tagama abunda take ga dakinsa nan a temaka a gyara masa daga nan yai waje domin tafiya makaranta

   Ilham da kanta ranar tayi breakfast, bata bari masu aiki sunyiba, dukda ba wata kwararriya bace a fannin girki, tagama tayi kwalliya  ta kai part din Jalal amma baya nan ta ajiye masa takoma dakinta, har gurin karfe Tara ba Jalal babu alamarsa, se zarya take koya dawo amma bata ganshiba

   Halima taje daki ta sanarwa da Jalila sakon Jawwad

Nana ta kalleta

“Aifa ke yanzu kin kade haka zasu maida ke kamar baiwarsu” 

“Nana kenan meye abun bauta a ciki,?”

“Tab lallai aikuwa zasu rainaki, tun yanzuma gashi, ke zakiyi musu girki, ki gyara musu daki, agaisheki nikam bazan iya wannan wahalar ba”

Jalila tayi murmushi

“Nana kenan, meye a ciki, duk abunda nayiwa Yaya Jawwad ko wani Wanda ya rabeshi ban fadiba, kaina nayiwa”

“Hmm Allah ya temaka, kema wataran zaki gaji Dan matsalarsu bata karewa”

“Ai bazan gajiba Hajiya Nana, kema gara kisaba gaba akeji”

Jalila ta mike ta tafi gyarawa Jawwad daki, ta tarar Jalal yagama karyawa ya bar kwanukan a gurin, ko tartare kwanukan guri daya beyiba

Jalila ta kalleshi ta kalli gurin da 

Jalal ya bata

“Mtsewww Dan Allah malam in an gama cin abinci hade kwanukan akeyi ba a cinye abincin ciki a bajesuba,”

Jalila tafada a fili tareda kwashe kwanukan tai cikin gida, kodaga kai beba Balle ya kalleta

  Ilham tagaji da jiran da Jalal, tasan dai baze wuce gidansu Jalal ba Dan haka ta dau mayafi ta nufi gidansu Nana, tana zuwa part din Jawwad ta nufa, kaitsaye Dan tasan baze wuce nan ba tunda motarsa tana Gida, taje ta tura kofar palourn 

Jalal ta hanga a zaune a kan carpet din palourn  Jawwad, da remote a hannunsa, shiga tayi cikin palourn da sallama ya Dan dago ya kalleta, ta karasa shigowa cikin dakin

“Ina kwana Yaya Jalal”

“Lafiya kalau”

Ta Dan gyara zama, “Yaya na hada maka breakfast ne shine…..

” da can ke kike hadamin?”

“A a Yaya amma….

” tsaya dama ina son magana dake, me kika cewa yarinyar da tazo nemana jiya”?

“Ni kuma?”

“Akwai wata a gurin nan bayan ke?”

“To aini jiya ban hadu da kowa ba”

“Nima rainamin hankalin zakiyi”?

“A a Yaya Jalal ni ba wata wadda tazo nemanka damuka hadu”

“Ilham wallahi zan tattakaki, 

Sa anki ne ni? Nace me kika cewa Hannah jiya, nizakiyiwa karya!!!”

Hade rai tayi itama dan bata gane inda rainin hankalin Jalal na yau ya dosa ba, ta mike tsaye ta kalleshi

“Ni ban San mezance maka ba kuma, nagayamaka abunda nasani ni ba wata wadda muka hadu jiya, kasake dai tambayarta”

“Ni kike gayawa haka?”

“To me kakeso ince?”

Ransa ne ya kara baci ya kalli Ilham

“Ni kike kallo kike gayawa wannan maganar? Ke kinyimn laifi kuma ki tsaya kina gayamin magana, kuma uban wayasaki kika dagamin waya har kike zagin Wanda ya kirani? Kwana biyu kinga nayi sanyi shine kikemin rashin kunya ko?”

Mamakine yacika Ilham wannan wace kasurgumar makaryaciyar ce take mata sharri haka, to mema zatace masa ne

Maganar yaseera ce ta fado mata “kidena jin tsoransa”

“Au to kar in kare kaina, kana gayamin magana akan abunda bansan nayiba, sekuma inyi shiru wannan lokacin ya wuce Yaya Jalal nima nadena daga maka kafa ina kallonka kana min wulakanci, se wasu maganganu kake Wanda bangane inda suka dosaba, duk saboda kawai ina sonka, so fa ba karya bane ba, kuma ina nan akan bakana, duk macen datayi gangancin shigowa rayuwarmu senayi maganinta, ka dawo hayyacinka Dan ni……

Tas ya dauketa da mari, dafe inda ya mareta tayi, tana kallonsa

” ke kin isa ki tsaya a gabana kina gayamin abunda kika gadama, kinje kinyimn karya, kina cewa wai ban isa inyi abunda ba kyaso ba ke a wa? Wani matsayi kika taka a gurina da kike da wannan ikon,”?

Sauke hannunta tayi daga kuncinta, ta kalli cikin kwayar idonsa

“Matsayin kanwarka kuma masoyiyarka na taka, ka gayawa ita wadda ta gaya maka hakan, ta tinkareni ni da ita tayimin, ba wai ta koma bayan fage ba, kuma wallahi daga yanzu kadena jibgata a banza kasawa zuciyarka bashi kakeci seka biya wannan abun da kakemin, kuma wallahi indai ina raye baka da wata mata in baniba seka aureni, baka da imani Jalal ko sau daya yakamata ka dubeni da idon rahama, kodayake kai babu tausayi a zuciyarka”

Kuma harzuka yayi,

“Ni kike gayawa haka, ke wace irin Jaka ce da ba kya ganewa ana so dolene, bana sonki kuma bazan taba sonki ba, Jahila kawai fita kibani guri kafin in sauya miki, kamanni, kinsanni sarai bana son hauka amma kullum ke haukanki kara yawa yake shiyasa ko shirginki bana shiga fita dallah” 

Tundaga waje Jalila take jiyo hayaniyarsu Dan haka da sauri takarasa,

ILHAM ta kalleshi sannan tace

“Jalal duk haukan da yake kaina be kai Wanda yake kanka ba amma na dage nakesonka a haka wani irin mutum ne kai”

Wani Marin yakuma bata,.yana shirin karamata ne Jalila ta shigo da air freshener a hannunta, zata gyara dakin Jawwad ganin abunda yake faruwa yasata rugawa da sauri ta shiga tsakanin Jalal da Ilham, ta janye Ilham baya, sannan ta kalli Jalal

“Wannan abun kunya kake aikatawa karasa inda zaka zage kwanjinka se akan mace, macen ma kanwarka, me yake damunka haka”

Daka mata tsawa yayi

“Matsa ki bani guri ko in hada dake, in tattakaki”

Itakam Ilham gefe tayi tana maida numfashi saboda taji zafin marukan da yayi mata,

JALILA ta kalleshi up and down

“To ka tattakanin mana ragon maza, karasa inda zaka nuna karfinka sekan mace, in karfi kakeson nunawa seka tafi gaidan dambe, jarumin namiji bada zuciyarsa yake yanke hukunciba da kwakwalwarsa dakuma hikima yakeyi, ba wai jibgar mace ba” 

Kallon  JALILA yayi idonsa cikin nata yana nazarin meze mata

Ilham daga inda take tsaye sukaji  tace

“Wallahi Yaya kowace tayimin wannan sharrin idona idonta kagaya mata senaga bayanta, kuma Marin dakayimin bashi ka dauka, don ka dauki alhakina, niba wadda muka hadu jiya amma ka hukuntani akan abunda bani nayiba, duk laifukan nan ba Wanda nasan nayi maka kowace karya tayimin,

Tayi nasara wannan karon nima ta saurari abunda zan mata koma wace munafukarce dani take zancen wallahi” ta karasa maganar tana hawaye, se yanzu JALILA tagane inda fadan nasu ya dosa, amma ta juyo ta kalli Ilham

“Kekam Iska na wahalar dame kayan kara, kalli tun ba yauba kike shan wahala a hannunsa ya dakeki, ya zageki, sekace ubanki kekuma dayake zuciyarki kin Yar kare ya cinye se manne masa kike kumayi, ni banga abun mannewa a gurin wannan abunba”

Tafada tana kallon Jalal, wani irin huci Jalal yakeyi, yama rasa me yakamata yayi, 

“Ke saurara, ba ruwanki a cikin rayuwarmu, uwar shishshigi, kuma ma inda Sa hannunki acikin abunda yake yimin zan baki mamaki wallahi,”

Ta daga jajayen idanuwanta ta kalli Jalal

“Wallahi Jalal wahalar dani din nan dakake shekara da shekaru, wallahi se ka biya duk randa kazo hannuna seka zubar da hawaye fiye da Wanda na zubar, zan fito maka a ainihin Ilham dina babu daga kafa ko ragawa tsakanina da kai, koni ko kai kokuma duk wani munafiki dake shiga tsakaninmu”

Yinkurowa yayi zeyi kan Ilham, JALILA takuma shan gabansa 

“Dan girman Allah ka kyaleta”

Hannu daya yasa, yai wurgi da Jalila daga gabansa tayi gefe

Ilham kuma ta tsaya kyam taki tafiya

Tas! Tas! Guda biyu a jere

“Dan kaunar da kakewa manzon Allah karka kuma dukanta, jininka cefa, kanwarka ce, indai so yana zama laifi, Ashe wataran zaka iya rabuwa da Jawwad”

Cak ya tsaya be juyoba amma

Jalila tacigaba da fadin

“Kome tayi maka kishinka ne  yasa tayi, baka tunanin alhakinta yakamaka ne, at least kaima ka sota mana koda irin na yan uwantaka ne kalli yadda ta……………..

(Zancigaba da hakuri, har lokacin da burinmu ze cika akan JALAL da mahaifiyarsa)

Wannan kalaman da Jalila ta haba ji Ilham ta tabayi a wayane suka dawowa Jalila Wanda hakan yasa takasa karasa abunda tayi niyyar fada

Juyowa yayi ya nufo inda Jalila take, Ilham na ganin haka ta sulale ta gudu, yazo gaban Jalila ya tsaya

” meyasa ba kyajin maganane? Ke dole sekin gayamin me zanyi? Rayuwarki daban tawa daban, meyasa kike hakane, ke in dai baki shiga harkata ba ba kyajin dadi, meyasa ba kya ganewa ne, kinsan metayimin ne?

Ya karasa maganar cikin shouting, Dan ja da baya Jalila tayi kadan 

“Eh nasani, nasan me tayi maka, kuma ba ita tayiba nice nan nayi”

Kallon Jalila yayi

“Kana mamakine? Ni ce nan matar tagani tace in kirawoka nace bazakazoba, ban damu da koma me tagaya makaba, saboda zatayi hakane dan tasa kamin wulakanci, Dan mace irin wannan dayawa maganganunsu karyane dakuma makirci, a zatonta nice Ilham shiyasa tagaya maka karya da gaskiya, abun kunyane a ganka da mace irin wannan,

Haba Dan Allah koba ka dena abunda kake Dan komaiba kabari Dan Allah, dakuma kare mutuncinka, abokananka dayawa, wasu suna karatu, wasu suna sana a, kowa na kokarin Gina rayuwarsa amma kai kullum kokarin wargaza taka kakeyi, kaji tsoron Allah kuma ka kiyayi matan bariki, wannan data zo gurinka kowa ya ganta yasan mutuniyar banzace, amma kalli abunda kayiwa kanwarka saboda ita, kukwana Gida daya Ku tashi amma baka da abokin gaba se ita dakuma mahaifiyarka Wanda hakan shine babban abun kunya, kayi tunani maana, kayi wani abu akan rayuwarka,”

Idanuwansa ne suka kuma yin ja, jijiyoyin kansa suka daddga, ya rintse ido kalaman Jalila na cigaba da dukan zuciyarsa, wani irin huci yake kaman kumurci, wani abu yake kokarin tunawa amma yakasa, sema jiyayi kansa yana jujjuyawa, bude idonsa yayi akan Jalila

Gabanta ne ya fadi! Ganin idon Jalal yana caccanza kala, daga Ja zuwa baki, gashi kuma ta kasa matsawa daga inda take,

“Fita ki bani guri, bana son irin wannan maganar, kifita nace!!!”

Ya dinga maganar cikin karaji daga baya kuma ya sulale, ya yanke jiki ya fadi

Tsorata Jalila tayi ta Dan ja da baya amma taga ko motsawa beyiba daga inda yake, a hankali ta tako tazo inda yake kwance, ta leka fuskarsa, taga idonsa a rufe amma fuskarsa tayi Ja sosai ga jijiyoyin kansa duk sun daga sun kumbura, sekuma hawaye da yake fita ta gefen idonsa, se sauke numfashi yaketayi  hankali, a hankali ya Dan motsa yasa hannunsa biyu, ya danne kansa yana girgiza kan nasa 

“Wai meyasameka?” Ta tambayeshi

Bece mata komaiba, sema numfashinsa da yake fita da sauri yanzu

“Yasalam na shigesu toni ya zanyi, kar ace wani abun nayi masa”

Ta kuma kallonsa “kanka ne yake maka ciwo?”

Shiru bece komaiba 

Tarasa ma mezatayi, ko Yaya Jawwad zan kira a waya wata zuciyar tace A a karki daga masa hankali yanzu yana makaranta

Ruwa ta debo a kofi, ta karanta wasu ayoyi saga cikin al Qur’ani

Ta daga kofin ta Dan dinga zuba masa a kansa 

A hankali numfashinsa yafara komawa normal, a hankali ya sauke hannunsa daga kansa, sekuma yafara bacci

“To ko aljanune da shi in ba hakaba ya za ayi idon mutum ya dinga canzawa”

Tashi tayi ta fara gyra inda yakamata a dakin tanata tunani kala² yana nan yanata bacci a gurin ta wuceshi ta fita ta Koma cikin Gida

Tana zuwa dakinsu Nana ta dubeta

“Kekam INA kika zauna haka tun dazu nake nemanki fa”

“Yaya Jawwad na gyarawa daki daga nan, na zauna a gurin flowers nayi tilawa”

“Hmm yayi kyau”

Daga nan JALILA ta bar dakin in bahakaba Nana zata cigaba da yimata tambayoyin Daba tasan dame zata bata amsa ba

Tunani ne yacika zuciyar JALILA to dama maza ma suna da Aljanu, Dan tafi kyautata zaton JALAL aljanu ne dashi,

Jalal kam bayan wani lokaci ya tashi daga baccin da yayi, ya mike yaje yayi wanka, ya koma kan gadon Jawwad ya kwanta abunda yafaru dazu yake tunawa, ji yayi zuciyarsa na kokarin fara bugawa da karfi Dan haka da sauri ya kauda tunanin daga zuciyarsa

Koda Jawwad ya dawo daga makaranta, ras ya Tarar da JALAL kaman ba abunda ya faru

    Jalila kokari take ta kauda tunanin Jalal tayi harkokinta, takoma shirin karbar bakinta dazatayi, amma abu ya gagara abunda tagani yau tareda Jalal yau yabata mamaki, a hankali mafarkan da ta dingayi akansa a baya suke dawo mata kaman lokacin takeyi, yau Sam bata da nutsuwa kaman wata Mara lafiya haka take gudanar da 

al amuranta na yau.

Hankalinta ya karkata akan son sanin waye Jalal dakuma son gano ainihin abunda ke ran Ilham game da son Jalal da ta keyi

Tayi nisa sosai a tunaninta Halima ta dafata

“Sayyada Jalila meyake damunki yau naga ba kya walwala, ko akwai matsala ne?”

Jalila ta danyi firgigit

“Leemart ba wani matsala,”

“Gaskiya ban yaddaba akwai abunda yake damunki”

“Kawai tunanin ummina nake”

“Allah sarki, ai kince tana zuwa sati me zuwa ki kwantar da hankalinki”

Murmushi Kawai Jalila tayi, suka cigaba da aikinsu

Da daddare Jalila ce ta kaimusu abinci amma taga Jalal normal kaman ba shiba, ko kallon inda take beba, balle ya kulata itama batasa akanta ze kulatanba amma se kallon mamaki take masa mussaman in ta tuna yadda idonsa ya dinga canza kala, ga kumburowa da jijiyoyin kansa suka dingayi

Jawwad ne ya dinga tsokanar Jalila wai duk murnar zatayi bakine yasa jikinta yayi sanyi haka ita dai sedai tayi murmushi kawai tai musu seda safe

Bayan sun gama cin Abinci ne Jalal ya tafi Gida Dan soyake ya kwanta da wuri bacci yakeji, yana kwanciya maganganun Jalila suka dinga dawo masa 

Tashi yayi ya zauna, yai shiru ya Sa hannunsa a sumarsa ya rike yana Dan juya kansa a hankali

“Why meyasa nake aikata wannan abubuwan, meyasa bazan dena ba, nima banaso,”

Bugun zuciyarsa ne yafara karuwa yaji kansa yana kokarin fara juyawa

Da hanzari ya mike ya nufi fridge dinsa ya cika cikinsa da giya ya baje a gurin

Jalila tayi shirin kwanciya Hanan takirata ta dinga yimata surutu amma Sam Jalila sama² take amsamata Dan ba komai take ganewa ba, haka sukayi sallama da Hanan, Jalila wadda a wannan lokacin dazaka tambayeta me sukace a wayar bata saniba Dan hankalinta ba akan wayar yake ba

Haka Nana ma ta isheta da tambayoyin meyake damunta, tarasa amsar dazata bata 

Daga karshe tace mata bacci takeji

Sukuku haka Ilham ta wuni tareda tambayoyi fal zuciyarta na son gano, abunda yafaru makircin Jalila ne kokuma wani abu daban, gaba daya tarasa meyake mata dadi

Ta kira yaseera ta gayamata komai ita kanta yaseera kanta ya kulle amma tace ta bari da safe zatazo su hadu

   Koda Jalila ta kwanta bacci gagararta yayi, se tunani, da tambayoyi fal zuciyarta, a haka bacci barawo ya saceta

Jalal ta gani a daddaure da sarka a cikin wani daki a galabaice, se a man gudan jini yake, wasu mutane masu bakaken kaya a zagaye dashi se kara matseshi suke da sarkar, JALILA tanata magiya su sakeshi kar ya mutu, daka mata tsawa wani yayi a cikin su

“Ke uwar shishsigi!!!! Kinfara mana katsalandan a cikin aikinmu damukayi shekaru munayi, kishiga hankalinki, inba hakaba kema zaki shiga cikin aikin Dan bazamu bari ki rusamana aiki ba”

Daga can taga Ilham ta shigo dakin ta zare wata wuka ta nufi Jalal

“Ilham me zakiyi haka, Dan uwankine fa in kika kasheshi fa”

Domin Sauke Cikakken Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Back to top button