Hausa novels

Asanadin Makwabtaka Book 2 Page 69 Complete Novel

ASM Bk2069

 

 

~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~

 

 

 

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

 

 

………Tana fitowa daga cikin gidan tay ma Tk dake cikin Mota alama da hannunta nan take ya fahimci mi hakan ke nufi ya bud’e kopar Motar da sauri ya fito, bud’e mata K’opar bayan yay tana zuwa ta shige ya maida kopar ya rufe mata ya d’an d’age gira tare da bud’a ido ya koma yaja suka tafi, sai faman jinjina kai take tana cije lower lip d’in ta tana d’an huci,

 

Tana fita Amadu ya matsa gaban gwaggo ganin yadda idanunta sukai ja shima har lokacin ran shi a 6ace yake, kallon shi tay tace miyasa yayi abunda yayi ma Hajiya Maryam, cikin 6acin rai yace “to gwaggo sai mu zuba mata ido taci mana mutunci son ranta, miye laifin mu a ciki ko kuwa don muna talakawa” yar ajiyar zuciya ta sauke “kar ka manta ita d’in ko wacece, ko ba komai Mutanen nan nada k’ima da daraja a idon mu hakan da kayi mata bai kamata ba don kamar rashin kunyan ne, duk abunda ta fad’a ta fad’a ne cikin 6acin rai don tana ganin an mata ba daidai ba” dakata tay tana numfasawa idanunta na kallon gefe shi kuma nashi na akan ta, cigaba tay “Wllh abunda nike ta fargabar faruwar shi kenan, nasan dole irin hakan ya biyo baya shiyasa naso tun farko ace an tuntu6e su sun san da Maganar a nemi amincewar su tukun….” Dakatawa ta k’ara yi ta d’age ido sama, ganin yadda duk ta damu yasa Amadu cewa “Kar ki wani saka ma kan ki damuwa, tunda Hajiya tun farko ita ta nuna abar mata komai nasan in sha Allah zatayi abunda ya dace komai na d’an lokaci ne zaki ga ya wuce” girgiza kai tay ba tare data kalle shi ba tace dole tayi wani abu don ita bazata so silar hakan ace an samu rashin Fahimta ba yanzu na Hajiya Maryam d’in aka gani ba’a san ya sauran Yan’uwan nashi suma zasu d’auki Al’amarin balle kuma ita Matar tashi, tambayar ta yay to mi zata yi ta bashi amsa da abunda ya dace daga haka ta juya ta nufi d’aki ya bi bayanta yana ce mata ta kwantar da hankalinta ba sai tace zatayi wani abu ba yasan Hajiya bazata bari a cutar da Fatuu ba, tana shiga d’akin ta nufi gado ta zauna a baki Amadun ma ya shigo ya zauna gefen ta yaci gaba da rarrashin ta kan kar tace zata yi wani abu don anzo anyi masu barazana su yi Addu’a kawae, ce mashi tay to kawae daga baya da ya ga ta d’an saki ranta ya tashi ya tafi, Zaune tay a wurin tana tunanin abunda ya kamata tayi don ganin Auren ya rabu, k’arshe ta yanke zuwa ta samu Hajiya ta rok’e ta kawae a hak’ura da Auran, tana son ta kira Fatun taji halin da take ciki amman bata so taji abunda hankalin ta zai k’ara tashi wata zuciyar ta raya mata tunda ita bata kira ta ba k’ilan ba abunda ya faru da ita don Hajiya bazata bari ayi mata wani abu ba da wannan tunanin taji hankalin ta ya d’an kwanta.

 

Bayan sun iso G.r.a sun shiga cikin gidan a gaban kopar shiga ya parker, bayan ta bud’e ta fito ta nufi ciki, Parlon Senator ta wuce wanda Had’add’an gaske ne ya tsaru ta samu wuri ta zauna, ganin bai a ciki yasata kiran shi ta sanar mashi ta iso, bada dad’ewa ba ya fito yana sanye da farar Jallabiya tun bayan daya dawo daga Masallaci ya koma ya kwanta zuwanta ne yanzu ya taso shi, a kujerar gefen ta ya Zauna Fuskar shi a sake ta gaishe dashi ya amsa daga haka tay shiru kanta a k’asa tana kallon Carpet 6acin rai bayyane akan fuskar ta, tambayar ta yayi tayi breakfast ne tace mashi a’a sai ta isa yace bari dai a kawo mata tayi anan, bata ce komai ba ya matsa can daga gefen kujerar inda landline take aje saman wani table, kira yay ya bada Umarnin akawo Breakfast, after some minutes sai ga wani cook ya shigo hannun shi ruk’e da babban tray dama aikin shi kenan girka ma Senator d’in Abinci in yazo bada iyalin shi ba, har zai kai inda dining table yake Senator yace mashi ya kawo nan, gaishe da Hajiya Maryam yay ta amsa k’asa k’asa ba tare da ta kalle shi ba ya d’aura a saman c-table Senator yace ya ja mata shi gabanta, saida yayi mata Magana sannan ta fara ci shi kuma ya fara daddana wayar shi da ya fito da ita, bata wani ci sosae ba ta cire hannunta ganin haka yasa Senator yi mata magana tace mashi ta k’oshi, k’ara kiran cook d’in yay yazo ya kwashe kayan, shiru suka yi Senator na cigaba da danna wayar can ya d’ago ya ajiye ta agefen shi yay yar ajiyar zuciya a nutse ya fara mata Magana yace miyasa zata tafi, kallon shi tay tace mashi ba komai kawae ta canza ra’ayi ne, shiru yayi yana kallon ta da d’an murmushi ita kuma idanunta na k’asa tana kallon Carpet har lokaci fuskar ta ba annuri,

 

cigaba yay “nasan don abunda ya faru ne, ina son ki kwantar da hankalin ki abi komai a sannu sannan ayi fatan hakan ya zama Alkhairi kaman yadda Hajiya ta fad’a bamu san mi Allah ya 6oye a tattare da Al’amarin ba” kallon shi tay cikin 6acin rai tace “Kenan kaima Yaya goyon bayan auren kake?” d’an murmushi yay yace mata kawae yayi nazarin Maganar Hajiya ne shiyasa, Fuska a yamutse tace “Yanzu shikenan ya nuna bamu da iko dashi ya yi gaban kan shi sai kuma a k’yale shi hakan Yaya ai cin Fuska ne, gaskiya dole mu nuna mashi ba a komai yake da iko da kan shi ba kawai asa ya saketa” ta k’arasa tana d’an Jujjuya kai, numfasawa yay yace “ni ina ganin hukuncin da Hajiya ta yanke akan shi ya nuna ana da iko dashi, yaje yayi aure ba tare da sanin mu da niyyar zai saki Yarinyar kinga in aka sa ya sake ta shine yay abunda ran shi ke so amman matsa mashi ya zauna da itan hakan zai sa dangin yarinyar su san ana da iko dashi kuma mu ba k’ananun mutane bane, sakin ta kuma hakan gaskiya ina ganin zai zama k’aranta” idanun ta ne suka ciko da k’walla cikin karyayyar murya ta fara fad’in gaskiya ita bata goyi bayan yaci gaba da zama da ita ba duka yaushe yayi aure kuma in ma Auren zai k’ara wannan ai bata dace da shi ba ba sa’ar auren shi bace, shiru Senator yay still da d’an murmushi akan Face d’in shi don yasan dalilin da yasa duk take wad’annan abubuwan, rarrashin ta ya shiga yi yana nusar da ita aikuwa sai tasa mashi kuka tana fad’in shikenan ba wanda zai yi tunanin halin da Fanan zata iya shiga duk sun goyi bayan 6are sun za6i faranta mata da mi ake so Fanan taji ne ko don suna tunanin bazata haihu bane, nuna mata yay bai ji dad’in wannan Maganar da tayi ba sam ai yayi tunanin Fanan ta su ce da ta haihu da kar ta haihu hakan ba abun damuwa bane a gare su kuma don ance tana da matsala ai hakan ba yana nufin bazata haihu ba kawai yana son ta gane shi Al’amarin irin wannan in Allah ya kawo kamata yay a kar6a ai fatan ya zama Alkhairi ba kamar da Hajiya ta nuna tana so sai suyi mata biyayya su bi da Addu’a, hak’uri ta bashi kan Maganar da ta yin ya k’ara lallashin ta daga baya sukai sallama ta mik’e shima ya tashi don ya rakata. Bayan ya dawo inda ya tashi ya koma ya zauna ya d’auki wayar shi ya shiga kiran Haisam, picking yay tare da yin yar sallama Mahaifin nashi ya amsa mashi, bayan ya gaida shi yace mashi sun ji abunda ya aikata ya kyauta hakan ya nuna masu basu da amfani a wurin shi, hak’uri ya bashi yace mashi yayi don taimako ne, ce mashi yay to miyasa ya k’i sakin ta kaman yadda akai dashi har abu ya shiga tsakanin su, shiru yay bai ce mashi komai, sigh Senator yay yace mashi yana son ta kenan dama shiyasa har hakan ta faru don yaci gaba da zama da ita, Slowly yace mashi bada niyya bane kuma Hajiya ce tasa yaci gaba da zama da ita, d’an guntun murmushi Senator yay yace “Kenan baka son ta?” Shiru Haisam d’in yay, da d’an d’aga murya yace ya bud’e baki yay mashi magana kaman yadda yake mashi bai kira shi don yaja mashi aji ba, in bai son ta ya fad’i a raba su kowa ya huta, har saida Haisam d’in yay d’an guntun murmushi jin abunda yace dama ya saba ce mashi hakan in yana jira yay mashi magana,

 

“Tunda Hajiya na so zan ci gaba da zama da ita” d’an ta6e baki Senator yay da murmushi irin na ka gane Mutum ba gaskiya ya fad’a maka ba, “ita Daughter ka sanar da ita ne?” Ya tambaya yace mashi a’a,

 

“to kai k’ok’ari ka sanar da ita kasan yadda zaka kwantar mata da hankali don Momyn ku ta d’au zafi sosae rashin tada hankalin ta shi zai sa ta kwantar da nata hankalin” amsa mashi yay da to, tambayar yaushe zai dawo yayi yace sai ya samu time tunda bai dad’e da dawowa ba,

 

“Ok, amman kai k’ok’ari ka dawo da wuri kar ita kuma ta nan d’in a shiga hakkin ta, in ta gama Karatun sai ka d’auketa kawai ta dawo nan” amsa mashi yay da to cike da tsokana yace “kai da alama ma sai ka wuce ni, tun yanzu kayi biyu gaba sai ka cike biyun dama an ce kyan magaji ya zarta” murmushi mai d’an sauti Haisam d’in yay shima Dad d’in nashi murmushin yake dama tamkar Abokai haka suke akwae kyakkyawar fahimta a tsakanin su, ce mashi yay shikenan Haisam d’in yayi mashi godiya shi kuma ya sa mashi Albarka sukai sallama.

 

 

Saude na shiga cikin parlon bayan ta kai trolley d’in suka yi kacibus da Hajiya ta shirya cikin doguwar riga kanta sanye da hula, ganin ta nufi hanyar Dining yasa Saude ta bi bayanta don tay serving d’in ta Breakfast, bayan ta zauna Saude na zuba mata ta tambayi ta kai ma Fateema tace mata eh tun d’azu ma bayan ta dawo ne ta had’u da Momy Maryam shine ta bata trolley ta kai mata parking space, da d’an murmushi Hajiya ta girgiza kai tace ta tafi kenan, d’an jimm Saude tay ranta ya bata ta fad’i mata inda taga ta nufa don hankalin ta bai kwanta da zuwanta part d’in ba, fad’i mata tay cewa bata kaiga tafiya ba lokacin da suka fita taga ta nufi part d’in su Fateema, Yanayin fuskar Hajiyar ne ya canza ta maimaita ta je part d’in su Fateema to mi ya kaita, Saude tace itama bata sani ba, fara yin Breakfast d’in tayi Saude ta tambayi akwae wani abu da zata yi mata, tambayar ta tayi ita tayi breakfast d’in ne tace a’a tace to ta je tayi in ta gama ta zo zata rakata part d’in su Fateema ta amsa mata da to.

 

Tun bayan da Fatuu ta ruga ta shige cikin Bedroom ta fad’a kan gado tana kuka sosae, tana cikin kukan ta fara bugun katifa da hannun ta a fili take fad’in “Ko ma mi akai man kai kaja man Ya Haisam! Baka damu dani ba, ka tafi ka barni Saboda baka so na baka k’aunata…, ni kawai ka zo ka sake ni na hak’ura da kai, na daina son ka, na daina……” Haka tay ta sambatu sai ta tashi zaune sai kuma ta koma ta fad’a saman Katifar, ba K’aramin kuka ta sha ba daga baya ta sassauta yin kukan tayi lamo akan Katifa ta k’ura ma wuri guda ido tana fitar da numfashi da sauri da sauri idanun ta sun yi jajur a ranta tana tunanin yadda zatay Haisam ya saketa, tunanin ko ta kira gwaggo ta fad’i mata halin da take ciki tay wata zuciyar ta raya mata hakan ba K’aramin tayar mata da hankali zai yi ba, tunanin Abbas tay shima ta raya tasan kota fad’i mashi hak’uri zai bata, a k’arshe ta yanke kawai taje wurin Hajiya tace mata bata son Auren tasa ya saketa tunda dama ai saida tace tana son cigaba da zama dashi sannan ta tare, tana haka aka turo kopar Bedroom d’in tay zumbur ta tashi zaune idon ta akan kopar ta zaro su sam ta manta ta kulle Saboda a yanayin da ta shigo, wani irin bugu da k’arfi zuciyar ta ta fara yi don a tunanin ta ko Hajiya Maryam d’in ce ta dawo, sandar data ga an sako yasa hankalin ta fara kwanciya, shigowa Hajiya tay ta yafo mayafi tana sanye da glass ta tsaya a bakin k’opar tana kallon Fatun, ganin haka yasa ta saukko daga saman gadon ta zagayo inda take, daga gabanta ta tsaya cikin rawar murya ta gaishe da ita tay d’an murmushi ta amsa kafin tace “ana nan ana ta shan kuka ko” sadda kanta tay k’asa bata ce komai ba Hajiyar tace mata ta biyo ta ta juya, bin bayanta tay har lokacin kanta ba kallabi, cikin parlon suka shiga Saude na zaune akan armchair Hajiya ta nufi L-shape ta zauna Fatuu na niyyar zama kan Carpet ta nuna mata daga gefen ta tace ta zauna, bayan ta zauna ta sadda kan ta k’asa Hajiya ta fara magana, “Maryam tazo duk ta firgita ko?” shiru tay bata d’ago ba sai d’an jan majina da take,

 

“Fad’i man mi tazo tayi maki ne” d’agowa tay ta d’an kalli Hajiyar a hankali tace mata ba komai idanunta cike tab da k’walla, yar hararar ta tayi cikin wasa tace mata ba tambayar ta take ba umarni ne ta fad’i mata duk abunda ya faru, cikin rawar murya ta fara fad’i mata tiryan tiryan duk abunda ya faru, kwa6e Fuska Hajiya tay ta jinjina kai a fili ta furta sunan Hajiya Maryam d’in, sosae Fatun taba Saude tausayi tana ta kallon ta tana d’an girgiza kai,

 

“To yanzu ke mi kika yanke kenan” Hajiya dake kallon Fatun ta tambaya aikuwa kaman tana jira tace mata bata son Auren tasa ya saketa, ta6e baki Hajiya tay “tayi nasara kenan akan ki, ke baki san duk barazana bace dama abunda take so kenan ta tsorata ki kice baki son Auren” kallon Hajiyar tayi da runannun idanu kwalla kwance a cikin su tace “Hajiya tunda dai basu son Auren don Allah ki raba mu kawai” Fuska a kwa6e take kallonta har ta rufe baki sannan tace “Waye bai son Auren, mu ba duk muna so ba ko baki ga Mahaifin shi ya kar6e ki hannu biyu ba, itama Mahaifiyar shi ina sa ran zata amince don duk abunda Mijinta yake so to itama tana so nasan zata fahimta, itace fa kadae ta nuna bata amince ba kuma itama ba wani abu yasa ba kawae tana taya d’iyar ta kishi ne ba kamar da yake itama ba kishiyar ce da ita ba shiyasa take ta wannan tada jijiyar wuyar”,

 

cikin muryar kuka tace “to amman tace fa zata yi man Asiri ni tsoro nike tayi man wani abu ko ta kashe ni” yadda tay Maganar har saida taba Hajiya dariya ta ta6e baki sai kace wata yar k’aramar yarinya, Hajiya ta lura Maganar ta tsorata ta sosae, hannu ta kai ta dafa Shoulder d’inta tace “Ki kwantar da hankalin Fateema nasan Wacece Maryam fiye da kowa tunda ni na haife ta, duk abunda ta fad’a maki ba abunda zata yi maki don ko k’adangare bata iya kashewa balle Mutum….” Katse Hajiyar tay tace “ai dama ba ita zata kashe ni d’in ba a Asirin da tace zata iya sakawa” yadda tay Maganar Hajiya ta kwaikwaya tace mata “Waya fad’i maki zata iya yi maki wani Asiri, duk fa burga ce ba wani abu ba kin wani tashi hankalin ki, kawai so take ta kwatar ma yarta mijin naku ya kasance nata ita kadai, kin san jik’an nawa badai nagarta ba son kowa k’in wanda bai samu ba shiyasa ake rububin shi, kiga fa ita matsayin d’a yake a wurinta itama d’iyar tata matsayin Yaya yake a wurin ta ko ba Aure akwai alak’ar yan uwan taka amman duk da haka suke k’wak’war shi, dama kinsan shi abu mai kyau da inganci shi yake siyar da kanshi, ko ke baki son shin ne?” ta d’age mata ido, dabarbarcewa Fatuu tay ta waro ido Hajiyar tace ta fad’i mata indai bata son shi to sai ta raba sun, kasa bud’e baki tay tayi Magana sai faman kikkafta idanu take ganin yadda duk suka kafeta da ido yasa ta sunkuyar da kanta zuciyarta na harbawa, Murmushi Hajiya tayi haka ma Saude, k’ara kai hannu Hajiya tay ta dafa kafad’ar ta tace “Ki kwantar da hankalin ki Fateema, ki jure duk wani abu da za’ai maki ki d’auki hakan matsayin yak’i akan abunda kike so, kinsan shi abu mai nagarta wani lokacin dama ba’a samun shi cikin sauk’i” tana yin Maganar Fatuu ta d’ago ta kalleta a hankali tace mata ita bata son shi Hajiyar ta harareta tace “K’aryar ki tasha k’arya yarinya, wannan d’an gold d’in jik’an nawa ai ba macen da zata ce bata son shi ai na riga na gano kina son shi tuni” d’an tura baki tay itama Hajiya ta tura mata nata harda yar harara aikuwa bata san lokacin data saki yar dariya ba har hak’oranta suka d’an bayyana, sosae ta kwantar mata da hankali har ta washe ta tambayi tayi Breakfast d’in tace mata a’a, Saude tasa taje ta d’aukko kayan daga kan Dining table ta kawo su nan kan c-table tace ta had’a mata, tsare Fatun tay saida taci sosae ta tabbatar ta k’oshi sannan tace taje ta d’aukko mayafi su tafi part d’in ta tace to, harda jakar Makarantar ta ta d’aukko don tayi Karatu suka tafi.

 

 

Bayan jirgin su Hajiya Maryam ya sauka Mijinta Dr Mohammed ne yazo d’aukarta da yake Weekend ne yana gida yana hutawa, tun da ya ganta ya Fahimci tana cikin 6acin rai dama kuma ba ranar sukai da ita zata dawo ba, saida suka hau hanya ne yake tambayar ta abunda ke faruwa nan cikin 6acin rai ta bayyana mashi, shima ya jinjina Al’amarin amma da yake mutum ne mai sauk’in kai sai ya shiga rarrashinta ya nuna mata abi komai a hankali kaman yadda Hajiya tace, shiru kawai tayi dama tasan ba lalle ya d’auki abun yadda ta d’auka ba balle har ya goyi bayan ta d’auki mataki, bayan sun iso gida sun fito daga cikin Motar yaron gidan dake cikin ba flowers ruwa ya nufo inda suke yana masu sannu da zuwa Dr ne kad’ai ya amsa mashi ya fiddo trolley ya bashi ya kai ciki suma suka nufi ciki tare, Bedroom d’in ta suka wuce ta zauna a bakin gado shima ya zauna a gefen ta cikin salon nuna kauna ya shiga k’ara lallashin ta kan ta kwantar da hankalin ta, har lokacin ranta a 6ace yake tace mashi kenan shima goyon bayan auren yake yace mata a’a kawai tunda Hajiya tana so ba yadda za’ai dole suyi mata biyayya ta d’an ta6e baki kawae, yaran su ne suka fara shigowa yi mata sannu da zuwa don basu san ta dawo ba saida mai aikin su da ta ga dawowar ta ta sanar masu, saida Dr yaga ta d’an saki fuska sannan ya tafi, Abraham ne ya lura da yanayin Mahaifiyar tasu da Yazo yi mata sannu da zuwa yana fita ya wuce d’akin Farha don ya sanar mata, tana zaune a bakin gadon gaba d’aya ta rasa abunda yake mata dad’i sai tunanin ta ina ma zata fara take lokacin Farha ta shigo tana sanye da vest da d’an guntun wandon jeans fararen cinyoyinta tas masu k’auri don zuwa yanzu ta k’ara girma da k’iba sun bayyana, kunnuwanta sakale da earpiece ash d’in sumar ta ta faka ta a tsakiyar kanta jelar ta saukko bayanta, had’a ido sukai da Mom d’in nata ta sakar mata d’an murmushi ta nufe ta, a gefenta ta zauna ta kai hannu ta cire kan earpiece guda daga cikin kunnanta tayi mata sannu da dawowa da turanci ta d’aga mata kai kawai, itama ta lura da yanayinta da Abraham ya fad’a mata ta kai hannu ta kama hannunta guda tace “Mom what’s happening, u look all worried, kince a can zaki Weekend amman miyasa kika dawo yau?” Kallon ta kawae tay ba tare data ce komae ba Farha d’in ta d’an yamutsa fuska a shagwa6e tace “pls Mom tell me mi ke damun ki ne?” d’an hucin numfashi tay tace “I can’t Spend the Weekend there Farha….” Shiru tay tana jinjina kai 6acin rai shimfid’e a kan Fuskar ta, kan Farha ne ya d’aure da alamun mamaki tace mata Mike faruwa da bazata iya yin Weekend a gidan Hajiya ba,

 

“Gidan Hajiya ya zama gidan 6acin rai Farha” ta kai hannu ta cize Yatsa, a shagwa6e Farha ta hau yi mata magiyar ta fad’i mata abunda ke faruwa tana d’an jijjiga hannunta da ta rike, Labarin abunda ya faru ta shiga bata baki sake Farha ke kallon ta har ta gama sannan da tsananin mamaki ta maimaita Ya Haisam yayi Aure ba tare da sanin kowa ba, gaba d’aya ranta bai bata Fatuu bace da yake ba komai ta fayyace mata ba saida ta tambaye ta wadda ya aura tay mata bayanin ta nan take ta ganeta ta wani irin zabura sai kace wadda shock yaja, baki bud’e cike da Al’ajabi tace “U mean he married that bitch!!” Uhmm kawai Hajiya Maryam ke fad’a, hannu Farha ta kai ta cire d’ayan kan earpiece d’in ta jefar tare da wayar a saman gado ta mik’e ta fara kai da komowa tsananin 6acin rai kwance akan fuskar ta ta wani kalan had’e rai sai huci take kai kace ita akai ma kishiyar, komawa tay ta zauna ta fara fad’in “impossible Wllh! That bitch can never be Sis Fanan’s rival” nan da nan Fuskarta ta hautsine tay jajir har ta fi ta uwar nuna 6acin rai, cigaba tay “That’s why from the day I first saw her i hated her completely, she’s a gold digger!” shiru Hajiya Maryam tay sai d’an cize baki take tana jinjina kai, suna haka wayarta ta fara ringing ta kai hannu gefenta ta d’aukko, ganin Hajiya ce mai kiran yasa ta d’an yin jimm kafin tay picking ta kara a kunne tare da yin sallama, gaisawa sukayi tayi mata an isa lafiya ta amsa tace mata ana nan anata fushin tace Uhmm akwae,

 

“Naji abunda kika je kika yi ma Yarinyar nan, wato don kin ji nace sai in ita tace bata son Auren shine kika je kikai mata haka don ki tsoratar da ita ko, anya Maryam! Yanzu Saboda soyayyar D’iya kike neman bijire man, a tunanin ki yanzu in ta nuna bata son Auren bazan gane ke ki ka sa ba? shikenan tunda kin za6i Farincikin d’iyar ki ita kad’ai kiyi duk abunda kike tunanin yi ban hana ki ba tunda kin za6i ki kauce hanya, sai dai ki sani a Matsayina na Mahaifiyar ki ban amince kiyi ma Yarinyar nan wani abu ba, ki gaishe man da kowa” daga haka ta katse kiran, wurgi tay da Wayar ta kai hannu ta bugi katifa tana yamutsa fuska tamkar zata fashe da kuka, nan da nan kwalla suka taru cikin idanunta ta fara fad’in miyasa Hajiya zata za6i Faranta ma 6are fiye da nata, ruk’e hannunta Farha ta k’ara yi fuska a yamutse tamkar itama zata saka kuka ta shiga lallashin ta tana tambayar mi Hajiyan tace mata, fad’i mata tay ta hanata ta d’auki kowanne mataki akan Yarinyar, fuska a kumbure kamar zata fashe tace mata ta daina damuwa idan suka yi hutu ita zata ce gidan sai ta fitar da ita da tsiya, jin haka yasa Hajiya Maryam samun sassaucin k’unar da zuciyarta ke yi Saboda tasan halin Farhar bata da Sauk’i dama itama ta nuna ma Fatun zata iya mata Asiri kawai don barazana amman sam bata bin Malamai ko bokaye iyaka ta bada ayi mata Addu’a kaman akan business d’in ta ko wani Al’amari, yanzu kam sai taji ta samu Mafita, nan ta fara kitsa ma Farhar wutar da zata hura ma Fatuu in ta je a 6oye ba tare da Hajiya ta sani ba har tasata da kanta ta bar gidan.

 

Washe gari Lahadi da Yamma Senator ya koma Abuja bayan ya k’ara zuwa wurin Hajiya sun tattauna game da Auran tace mashi yay k’ok’arin fahimtar da matan shi yace in sha Allah, anan ya iske Fatuu suka k’ara gaisawa har yana tambayar ta in tana son wani abu tana murmushi tace ba abunda take so yace mata ta dage da karatu, da daddare bayan sun gama cin Abinci ya buk’aci ganin matan nashi a part d’in shi, bayan sun zo a nutse ya fara masu bayanin dalilin kiran nasu da Hajiya tay, gaba d’ayan su sun ji Al’ajabin Maganar ba ma kamar Mahaifiyar Haisam d’in, bazaka gane yadda ta d’auki Al’amarin ba daga yanayin Fuskarta ta tambaye shi mi Hajiya Maryam tace game da hakan, bai 6oye mata komai ba game da yadda ta ji zafin abun dama abunda tay tunani kenan a cikin ranta dole tasan baza su ji dad’in abun ba, ba kamar da taji yarinyar har ta samu ciki, jin tayi shiru yasa shi ce mata bata ce komai ba ta d’an watsa hannu tace to ita mi zata ce kawai dae Haisam bai kyauta ba ya zaiyi abu irin wannan ba tare da neman shawara ba tun farko gashi yanzu rayuka na neman 6aci na Hajiya Maryam aka gani ina ga ita Fanan d’in, nunawa tayi ita tana ganin gara a raba su kawae zai fi da azo asamu rashin Fahimta,

 

Aunty tace “Gaskiya ni ina ganin in aka ce a raba su ba’ai ma Yarinyar Adalci ba kaman yadda Hajiya tace tunda shi ya fara sanin ta yanzu in aka raba auren dole sunanta zai canza zuwa bazawara, kuma ni ina ganin yana son ta ne shiyasa tun farko ma ya auretan ko kuma daga baya ya fara sonta shiyasa har abu ya shiga tsakanin su, haka da bai son ta sai inga kaman bazai yarda yaci gaba da zama da ita ba” d’an jimm Mom d’in shi tay alamar tunani kafin tace “zai iya auren ta don ya taimaka mata kawae and zai iya cigaba da zama da ita tunda Hajiya na son hakan koda bai son ta” gyad’a kai Aunty tay “hakane, nasan halin shi sarae zai iya kasancewa hakan, amman dai kamar yadda Hajiya tace ina ganin muyi masu Fatan Alkhairi kawae don ni ina ganin dama can Allah ya k’addaro matar shi ce shiyasa ma har suka san juna” jinjina kai Senator yayi Mom d’in Haisam da yanayin fuskar ta ya sauya tace basu ganin Hajiya Maryam zata ga suna supporting d’in shi Saboda d’an su ne basu damu da halin da Fanan zata iya shiga ba, Senator ne yace to tunda Hajiya haka take so ai dole su bi abunda take son sannan yasan damuwarta Saboda tunanin halin da Fanan zata shiga ne idan Allah yasa bata tashi hankalin ta kamar yadda take tunani ba yana ganin komai zai daidaita, cigaba da tattaunawa sukai daga baya suka bar part d’in nashi,

 

Bayan Mahaifiyar Haisam ta koma Bedroom d’in ta, a gefen tanfatsetsen gadon ta daya sha k’ayataccen bedsheet ta zauna tay shiru tana kallon wuri guda da alama zurfin tunani ta shiga, sam ta kasa gane mi take ji game da Al’amarin, wayarta ta d’ago ta fara k’ok’arin kiran Haisam, bayan ta fara ringing ya d’aga suka gaisa tace mashi taji abunda ya aikata ba tare da sanin su ba batare da kuma yayi zurfin tunani ba mi zai sa yayi Aure da sunan taimako bazai yi amfani da wata hanyar ba, hak’uri itama ya bata tace tunda yaje yayi gaban kan shi ai dole suyi hak’uri amman yasan yadda zai yi ya fad’i ma Fanan ba tare da ta tada hankalin ta ba yace zai yi hakan in sha Allah cikin nuna k’auna yay mata Sallama tace Uhmm kawai, bayan sun gama wayar d’an jimm tayi sai kuma ta fara k’ara yin kira, Jidderh ta kirawo tace tazo d’akinta tana son ganinta, after few minutes ta shigo tana sanye da doguwar riga kanta ba kallabi sai bak’ar sumar ta wuluk da ta faka hannunta ruk’e da wayarta ta nufo gefen gadon ta zauna tace gata,

 

“Akwai wani yarinya Neighbor d’in Hajiya I can’t remember her name amman sun saba da Hajiya sosae….” Katseta Jidderh tay da fad’in “Sis Fatuu?” d’an d’age ido tay alamar tunani tace ta dai manta sunan k’ilan itace da sauri Jidderh tace bari ta nuna mata picture d’in ta ta gani in itace, shiga cikin gallery d’in wayarta tayi ta bud’o hoton Fatuu ta nuna mata tana gani ta shaida Fuskarta tace mata itace, tambayar ta Jidderh tayi miya faru da ita da d’an alamun rudu Mom d’in nasu tay d’an guntun murmushi tace ba komai she just wants know about her, cikin rashin fahimta Jidderh tace mi take son sani game da itan, tana d’an yarfa hannu tace kaman ya halayyarta take da mu’amalarta da Mutane haka, Murmushi Jidderh tayi harda gyara zama don tana bala’en k’aunar Fatuu nan ta shiga fad’i mata halayenta tace tana da kirki sosae ga faran faran ga son mutane gashi tana da dad’in zama bata da wuyar sabo kuma daka zauna da ita sai kaji ta burge ka, nan ta fad’i mata farkon saninta da ita lokacin data dawo daga Yola tazo gidan Hajiya da kayan Fulani har hoton da suka yi ranar ta bud’o mata da tasa Haisam ya turo mata don ta rasa shi, labarin tsakaninta da Ya Haisam abunda ta sani da wanda Hajiya ta basu labari ta shiga bata, tace mata yanzu haka suna gaisawa don ta zama kamar k’awarta ma, tambayar ta tayi zasu yi shekaru d’aya tace “No na girme ta da kusan 3 years ma, kawai dai she has a good shape kinga hips d’in ta kuwa Mom wllh kyace ba nata bane in kin ganta sun yi haka…” ta mik’e tana gwada ma uwar yadda hips d’in Fatuu suke ita dai sai murmushi take, komawa Jidderh tay ta zauna tace mata wai miyasa take son sanin abubuwa game da ita ne, shiru ta d’anyi tana rolling eyes ta kalleta da murmushi tace “Now she’s part of this Family” waro ido Jidderh tay baki bud’e alamar mamaki cikin daurewar kai tace bata gane ba, ce mata tay Yayan su ya Aureta cikin rashin fahimta ta d’an waro ido tace Ya Nameer, yar harara ta wurga mata tace Nameer d’in da bai a K’asar Big bro d’in su take nufi, k’ara waro idanu waje tay tana kallon Mom d’in nasu da itama take kallonta ta d’an ta6e baki da d’an murmushi, cike da Al’ajabi ta tambaye ta yadda akai ta zama Matar Ya Haisam d’in nan ta fad’i mata, aikuwa ta washe baki cike da Murna tace “Oh my God! am so Happy to hear that Mom, wllh na dad’e ina masu sha’awar auran juna don sun dace sosae ba K’aramin fahimtar juna zasu samu ba, kaman fa shi ya raine ta Mom, bai son 6acin ranta bata son 6acin ran shi itama, sosae jinin su ya had’u baki ga yanda suke kulawa da juna ba, tun bayan dana santa dashi naga sun bala’en yin matching saidae kuma nasan ba zai aureta ba Saboda Maganar auren su da Aunty Fanan kuma lokacin tayi k’arama ma, daga bayan nan data girma inta ji inama suyi aure, ashe da rabon zasu yi d’in” cike da Farinciki take Maganar sai faman washe baki take, d’an d’aure Fuska Mom d’in tayi tace ai raba Auran za’ai nan da nan murnarta ta koma ciki tay mata wani kallo kaman zatai kuka tace “but why Mom, Don Allah kar a raba su” d’an ta6e baki tay tace Auren na son kawo rashin fahimta don Momy d’in su ta Lagos ta d’auki zafi sosae sannan Fanan ma tasan in taji za’a iya samun matsala, Fuska a yamutse Jidderh tace ai dama dole hakan ya faru Saboda kishi amman daga baya tasan komai zai daidaita zasu yi hak’uri ita dae don Allah kar su raba Auran, yar harararta Mom d’in tayi tace da yake ba ita akai ma kishiyar ba a shagwa6e ta kama hannun Momyn tana mata Magiya, ganin tana murmushi yasa ta gane wasa take cike da zumud’i tace bari ta kira mata Fatun su gaisa, har ta d’ago wayar ta dakatar da ita tace ba yanzu ba ta bari aga komai ya daidaita itama kar ta fad’i ma kowa cikin yan uwanta tace to, ce mata tay zata iya tafiya ta mik’e tana fad’in zatai ta yin Addu’a Allah yasa komai ya daidaita da wuri su sha shagali don duk abunda akai a bikin Aunty Fanan itama sai anyi Momyn tace Uhmm kawai ta nufi kopar fita tana ta murna ta fice………….

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 da 3 Naira 400 ne za’a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za’a turo shedar biya ta wad’annan nos din 09013804524 ko 08169856268

Asanadin Makwabtaka Book 2 Complete Novel Txt

Back to top button