Uncategorized

Abban Sojoji Chapter 3 Complete Hausa Novel

 

“`The father Of Soldiers“`

        

Story 

     &  

       Written 

       By 

      Hafsat Bature

          (Boss Lady)

Dedicated to my beloved sisters. 😍   

‘Yan kame-kame ta shiga yi hankali a tashe tana wurwurga ido, ” wannan d’an daudun daga ina kuma aka samo shi?” Daya daga cikinsu ya tambaya yana kallon ta , hantar cikinta ce ta ji ta kad’a , su duka sauraren ta suke yi su ji mai zata ce?

Motsi ta soma yi da lips dinta alamar tana so ta ce wani abu “Amm… Amm..” Duk ta bi ta dabarbarce. Jin muryar Azumi yasa Sehrish sauke ajiyar zuciya, karasowa ta yi tana fadin “Afuwan y’an samari ban yi maku bayani game da sabon d’an aikin da aka kawo domin ya rinka taya ni aiki ba.” 

Kasa kunne suka yi suna sauraron ta , dafa kafadar Sehrish ta yi tare da cewa “Sunan shi tukur daga yau zai rinka taya ni aikace aikacen cikin gidannan ,’

Ta kare maganar tana kallon kowannan su tabe baki yyi  ba tare da sunce komai ba dama haka ta yi tsammani , don haka taci gaba da cewa “tukur bari na gabatarka maka da kowannan su saboda ka kiyayi zama dasu ,”ita dai ba ta ce komai ba saboda a rud’e take , 

Azumi ta soma gabatar mata da su daga na farko “Wadannan biyun da ka ke gani sune tagwaye  in ka lura komai nasu iri d’aya , suna da son zolaya musamman idan abun mugunta ne sun fi auki a nan na farkon sunansa Jahan shine babba sai twin brother dinsa Ayaan” 

Tana gama wa dasu ta matsa na kusa dasu tace “wannan kuma sunan shi Kanal yusif sarkin tsafta , bai cika son surutu ba kuma baya son kallo , na gefensa kuma shine Khaleed bai da matsala shi indai za ayi masa abunda ya ke so ba tare da ya tambaya ba ,

Download>>> Maciji Ne Complete Hausa Novel Document

Duk Sehrish na sauraron wannan bayanin na azmi , bayan ta kammala da na hannun damarta ta koma other side din taci gaba da cewa “wannan Junaid kenan sarkin murmushi, duk yadda za’a bata mai rai baya fushi sai in an kuresa , yana da son wasa faran faran da jama’a, burinsa a bashi kulawa  a bangaren ci kuwa ba’a magana ,” karasa maganar tayi tana y’ar dariya , shima dariyar yake yi haka zalika wasu daga cikinsu sun d’an murmusa , 

Sehrish tagane sa shine wanda ta fara zuba ma abinci mai kyakkyawan murmushin nan

“n6a kusa da shi kuma fawan kusan halinsu daya da Junaid ,  sai jabir da irfan basu da matsala in dai ba tsokanarsu akayi ba.” 

Murmushi sehrish tayi taji dadin wannan gabatarwar , sai dai ranta na bata cewa wadannan kananun ne , akwai sauran mutun goma daga cikin sojojin da basa nan , su kuma koya zasu kasance !?

A tare da azmi suka yi saving dinsu abincin har suka kammala kowannnen su ya kama hanyar makwancinsa , tattara  plates din da kulolin sukayi a tare suka kakkauda komai izuwa ma’ajiyarsa , 

daga nan sehrish tayi ma azmi sallama ta koma bedroom dinta , tana mai jin dadin fara kasancewarta a wannan awesome family din Babbar damuwarta shine , da tazo a matsayin namiji a maimakon mace batasan ya abun zai kasance ba ranar da asirin ta ya tonu.

Tunda samu gadon nan ta haye ta soma minshari bata kara sanin meke wakana ba sai da tajiyo kwankwasar kopar da azumi take yi mata ,

A firgice ta farka tana neman mayafin da take nad’e kanta da shi , can ta hangosa kasa ashe anan tayi wurgi dashi, daukowa tayi ta hanzarta daure kanta dashi, sannan ta tashi ta nufi kofan ta bude mata, fara’a azmi ta sakar mata ” am sorry na Katse maka bacci ko naga ana kiran sallah ne raina ya bani baka yi ba nasan an sha gajiyar tafiya ga aikin da mukayi da dare ,” 

Cikin y’ake sehrish tace “a’a wlh naji dadi da ki ka tashe ni saboda banyi sallah ba amma ynx zanje na yi, 

Azumi tace “ok in ka  kammala karfe 7 ka fito akwai aikin breakfast na jiran mu”  reeshi ta amsa da “toh ” sa’annan tajuya ciki” 

Cikin sauri ta shiga toilet, sai da tafara cire gashin bakin da aka sa mata ta tura sa cikin aljihun wandon ta, sannan taje bakin fanfo ta daura alwala , ta fito tana yarfa hannun ta, hijabi ta dauko ta zura sannan ta shimfid’a kafet, ta soma yin sallar,

Bayan ta kammala sallar wata irin hamma ta rinka ji, ga bacci bai ishe ta ba ga kuma yunwa don jiya da daddare bata nemi abincin ba gashi available 

Agogon dake manne jikin bango ta kalla akwai sauran lokaci don haka sai ta baje saman sallayar taci gaba sharar bacci, ba ita ta tashi ba sai wurin karfe 9 na safe  hankali a tashi ta wartsake, ganin cewa wannan ce rana ta biyu da fara aikinta gashi zata fara bada matsala, cikin hanzari ta cire hijab dinta ta hada da kafet din sallan ta adana su a saman gadonta, sannan ta zaro gashin bakinta da take likawa ta manna sa a fuskarta, ta gyara nad’in mayafin kanta ta fi ce,

A kitchen ta Sami azmi ta kammala shirya komai na kalacin safen , duk sai taji ba dadi sukuku ta isa gare ta ta ce “barka da safiya nayi laifi dan Allah ayimun uziri,” 

Babu alamun bacin rai a fuskar azmi ta ce ” karka damu tukur, ba wani abu nan gaba dae aguji yin hakan”

Sehrish ta amsa da toh insha Allah yanzu wani aiki zan yi ? 

Ba wani aiki kawai abunda ya rage ynx  kabi bedrooms din kowannan su ka Sanar dasu su fito su yi breakfast ya kammalu,”  azmi ta karashe maganarta ta tana kallon ta, 

Cikin zullumi sehrish ta fita ta tunkari jerin dakunan dake a downstairs , na farko ta fara kwankwasa wa shiru ba’a bude ba , kara knocking tayi da karfi , har sai da ya isarwa mai dakin , muryarsa tajiyo ashake yana cewa “who’s trying to disturb me? d’aga murya tayi tare da cewa “tukur ne sabon mai aiki,” 

“Shigo ciki” ya ba ta izni , turo kofar tayi tare da kutsa kai ciki, har cikin ranta dakin ya yi mata kyau bedroom kamar na mace saboda kyau ga tsafta sabanin wasu mazan da idan ka shiga dakunansu kamar wurin safkar y’an gudun hijra saboda tsaban tarkace da har mutsi, 

Download>>> Ingarman Namiji Complete Hausa Novel Document

“Idan ka kammala kalle kallen naka sai ka sanar dani abunda ya kawo ka,” muryarsa ce ta dirar mata a kunne sai lokacin ta mayar da idonta akansa , kwance yake a baje  saman katafaren gadonsa rabin jikinsa yayi covering dinsa da lallausan blanket , Yusif kenan 

Cikin en ina sehrish ta ce “am ..emm dama an kammala breakfast ne shine aunty azmi tace nazo na sanar daku.”

ta kammala maganarta ta tana wasa da yatsun hannunta , jin shirun bai ce komai ba ya sa ta dagowa ta saci kallonsa , samun shin tayi yana yamutsa fuska alamar an takura masa cikin lallausar muryarsa ya ce “Idan ina jin yunwa ai ba sai anzo an tayar dani ba ni zanzo da kaina ciki na ne ko cikin wani? ya tambaya yana kallon ta , 

Cikin sauri tace “cikin ka ne” ok fi ce ka ban wuri , ya fada tare da jan bargonsa ya idasa rufe face dinsa , 

Kamar wacce kwai ya fashe mawa a kai haka ta fita salalau salalau , a cikin ranta kuwa tana jinjina ma isa irin tasa ” tab aiki y ganni ni sehrish daga abun arziki, wannan shi ake kira da samun wuri tusar asuba, Allah sarki mukam ya’yan talakawa don uban mutun kar Allah yasa ya nemi abinci har rana ta fadi ya ga in za’a a damu dashi kasha iya barcinka yunwa ta taso ka, ka lallaba ka je neman kason ka wani sa’in ma an manta dakai, su kam wadandannan genius din bibiyarsu akeyi suzo suci suna make wa,” 

Ta karasa tunanin nata a dai dai lokacin da tazo kofar dakin the next person , knocking tyi  bugu d’aya taji ance “Come in” 

turo kofan tayi ta bude Samun shi tayi zaune saman sallaya jikinsa sanye da jallabiya ga kur’ani yana karantawa gwanin burge w, da alama wannan zaiyi saukin kai a cewarta 

“Barka da safiya yallabai an tashi lafiya” sai da ya kai aya sannan ya juyo ya kalle ta ya ce “da ban tashi lpy ba zaka ganni ina karatun Qur’ani ne?  to fah ta ambata acikin zuciyarta , shin mai ya kawo ka ma tukunna ? ya tambaya yana kallon ta a matsayin namiji, 

Muryarta na rawa tace “dama an kammala breakfast ne shine …..” Interrupting dinta yayi tare da cewa “shine me ? kai shashashan ina ne da zaka fadowa mutun haka kawai tunda sanyin safiya,kama hanya ka fi ce tunkan nayi football dakai”  (Jahan).

Jiki na rawa Sehrish ta fi ce zuciyarta na bugawa saboda tsananin tsoro, dafe kirjinta tayi domin ta samu natsuwar karasawa ga daki na gaba,zullumin ta kar asamu wanda zai kai mata duka don ta lura cewa fusatattu ne, ba mai sauki a cikinsu farawa da iyawa ta fara fuskantar haka nan gaba batasan mezai biyu baya ba.

Next room kwankwasa tayi tana jira taji an bata iznin shiga amma shiru , sake buga kofan tayi da d’an karfi da alama kowanane mamallakin dakin nan ya datse kofar ne,

Jin alamar ana tunkaro kofar yasa ta natsuwa, bude kofar yayi fuskar nan a daure kamar Alkubus “lafiya”? ya ambata rai a bace.

Har ta bud’e baki zata yi magana tajiyo muryar wani daga can cikin ɗakin yana cewa “Wai wane ne”?

“Wannan shashashan sabon mai aikin ne,” wanda ke tsaye a gabanta ne ya basa amsa, sai lokacin ta gane cewa dakin twins ne wato kamar yadda suke y’an biyu haka ma wurin kwanansu d’aya ,” 

Tuni taji zufa ta ke to mata ganin wancan dake daga ciki ya taso , dukkan su sleeping dress ne riga da wando ajikinsu kala daya milk colour masu kyan gaske, 

Download>>> Ni Na Raineta Complete Hausa Novel Document

Jerawa suka yi tsaye a gabanta kowanne na kallonta alamar sun ma rasa wane hukunci zasu yi mata saboda ta katse masu baccinsu, 

Gudun kar ta ja ma kanta bugu yasa ta ce “Am…Da ma breakfast ne an kammala shine aunty azmi tace a zo a sanar daku,” 

Kallon juna su kayi tare da cizon labba atare, Ayaan ne yasa hannunsa ya kamo kunnanta ya idasa shigo wa da ita ciki , ba karamin zafi sehrish taji ba har sai da tad’an saki y’ar kara “ko da gigin wasa next time ka kara attempting zuwa tashe mu bacci na rantse saika yabawa aya zaki sususu kawai,”  ya karasa maganar tare da sakin kunnan nata cikin sauri sehrish ta fice tana sharar kwalla don ba karamin zafi taji ba, 

Sai da ta samu wuri ta tsugunna ta gama matse yar kwallarta sannan ta tunkari sauran dakunan kowane daki taje da abunda zata tarar na wulakanci, yanzu dai gashi ta tunkari saman bene last room da ya rage ta shiga,

Sai da ta tabbatar ta share dukkan ruwan hawayen da ya zubo mata sannan ta kwankwasa , kusan 3 times tana knocking a na karshen ne taji wata sanyayyiyar murya tace” shigo ciki.” 

Da sallama tashi ga wani irin daddadan kamshi ne ya ratsa hancin ta, har sai da tasa hannu ta d’an matse hancin saboda scent din ya kai mata karo, 

Samun shi tayi a kwance tsakiyar gado wani irin sabon salon kwanciya da bata taba gani ba, up yake fuskanta ya rungume fillow a kirjinsa ga wani filon a tsakankanin laps dinsa ya makalkalesa, fuskar nan dauke da murmushi just like always, Junaid kenan sarkin smiling,       

Karasawa tayi gaban bed din yadda zaiji ta dakyau ta ce “barka da safiya’  Zuciyarta na mata dar dar gudun karya yi mata abunda sauran su kayi mata,

A hankali ya bude idonunsa ya sauke su akanta “menene”? ya ambata cikin kasalalliyar murya,

“Breakfast ne ya kammala” ta fada tana kallon kyakkyawar fuskarsa da jajayen lips dinsa, 

Cikin shagwaba ya ce”wlh naji dadin zuwanka tukur dama tundazu nakeso na tashi kasala ta hanani pls taimaka min na mik’e” ya idasa maganar tare da mika mata hannunsa , 

Waro ido waje tayi domin wannan yafi sauran iyayi, fuskarta tamkar zata yi kuka gaba daya ta rasa me zata yi tun nan sehrish tagane kuskuren da ta tafka na zuwa amatsayin namiji bata da wani zabi fa ce tayi abunda ya ce if not her secrets will expose, 

Download>>> Ana Dara… Complete Hausa Novel Document

Mika masa hannunta tayi ya ruko cikin nasa, nan take taji wani irin yanayi a tattare da ita mara misaltuwa, lallausar fatan hannunsa ba karamin gigita ta tayi ba saboda softness dinta, a cikin ranta tace “wannan wani irin hannu ne mai laushin gaske da dadin tabawa, daga jin wannan hannun bai taba wanki ba,” 

Gam ya ruke hannun nata a yunkurin ya taso ya janyo ta gaba d’aya ta rikito ta fada masa, dalili kuwa karfinsa ya rinjayi nata nesa ba kusa ba, 

Wani irin bugu zuciyarta ta shiga harbawa duk tabi ta susuce ta rasa inda zata tsoma kanta, tashi ga yanayi mara misaltuwa, tsigar jikinta duk ta tashi tsaye hai kam, karo na farko da ta fada jikin namijin da ba muharramin ta ba, gashi ko riga babu jikinsa d’an short ne dai-dai guiwarsa,

Kamar anyi mutuwa haka sukayi tsit, junaid kam yarasa meyasa yaji tamkar maca ce ta fada masa a jikinsa shaukin daya ji ya basa mamaki, ita kam sehrish ji take kamar an manna mata magnet a jikinsa sam tagaza yunkurin tashi

Kasala ce ta rufe mata jiki sai da ta tattaro dukkan sauran karfin daya rage mata a jikinta ta yunkura ta mik’e cikin sauri ta zame jikinta daga nashi ta fi ce da gudun gaske kamar walkiya haja yake kallon lamarin, 

Tunaninsa me yasa d’an aikin ya shiga feelings haka kodai d’an daudu ne mai bin maza ba shakka kuwa haka ne, ya fada aransa 

A bangaren sehrish kuwa da ta fita a guje dakinta ta koma, tana tura kofar tashiga ta maidata ta datse sannan ta jingina da kofan tana shesshekar kuka, 

ta riga da ta san ta yi kuskure tun farko cikin raunanninyar muryarta ta furta ” Omg! i ave made a mistake Ya Allah makes it easy for me, 

A cikin 2 weeks sehrish ta gama fita hayyacin ta, a tunanin zata huta a wannan katafaren gidan amma ashe ba haka bane, aikinsu Junaid kamar zai kashe ta, ga wani karen tsana da twins dinnan Jahan da Ayaan suka sa mata, yini take tana aiki tun safe har dare basa so suga tana hutawa sunfi so suga tana aiki kamar ansa mata battery, kullum sai azmi ta turata taso su suzo suci kalacin su na safe, haka Zata bi dakin kowannansu daya bayan d’aya, kowa taje tadawa da irin wulakancin da zata kwasa saboda jan kunnanta da suke yi har fatar kunnan tayi jawur, ga gyaran dakunansu, wanke toilet dinsu, gugar kayansu duk ita ke yi, wani lokacin ma idan suka ga babu aiki tana hutu sai su tattaro kayansu dake cikin laundry basket su bata ta wankesu tas, in azmi tace musu ba da injin wanki suke amfani ba dak sai suce ae wankin hannu yafi fidda kaya suyi kyau, 

Download>>> Yaro Ne Complete Hausa Novel Document

Baiwar Allah lokaci guda ta zama wata zararriya wani sa’in ko bacci take yi sai ta dinga jin muryoyinsu nayi mata gizau a kunnanta suna cewa “tukur tukur tukur kur “

 Girki kad’ai azumi ke yi saboda sunce sauran aiyukan bana ta bane na d’an uwansu namiji ne wato tukur mai aikinsu, 

Akwai lokacin da suka shigo atare suka same ta, ta kammala goge goge tayi aiki ta gaji, ta samu wuri saman 3 seater ta kwanta tana hutawa asalima batasan bacci ya dauke ta ba, 

Kayan wanki suka shiga suka dauko kowa dana sa, bata yi aune ba sai  dai taji ana zazzage mata jibgin kaya a jikinta, haka take faman hakuri dasu,

Yau ba ta makara wurin shiga kitchen ba, azumi ta taras tana gyara naman kaji, ba qaramin mamaki azmi ke bata ba sam ba ta gajiya da aiki kamar engine, gashi ta kware a wurin iya sarrafa abinci ta iya girki 

“Barka da safiya aunty azmi” ta fada tana kallon ta , da murmushi a fuskarta tace “yawwa mlm tukur ya gajiyar jiya? Sehrish ta ce “Alhamdllh” 

“Yau ba a makara ba kenan” azmi ta tambaya,  sehrish  ta ce “eh” 

Zame hannun tayi daga gyaran naman da take yi, can cikin kitchen din tashi ga kofar da store yake ta bude, wasu manyan doyoyi ne ta dauko guda 3 lafiyayyu, tazo ta ajiye a saman table din da suke yanke yanke a saman sa da sauransu, ” gasu nan a fere su da kyau in ka gama ka shiga store za ka ga crack din kwai ka debo 20 a cikin roba a farfasa su,” 

Amsa wa kawai take da toh, wuka ta dauko ta fara daddatsa doyar , a natse take ferewa , junaid ne ya fado mata a ranta tunaninsa ta soma yi “har yanzu nagaza gane masa ni bansan meyasa ya ke da shagwaba ba kamar karamin yaro  gashi da shiga rai uwa uba ga kyau kai dukkansu ma kyawawa ne idan har akace mun na zabi daya cikinsu to tabbas zanyi ruwan ido, amma fa gaskiya junaid na daban ne inason namiji mai shagwaba mai kyakkyawan murmushi domin murmushi alama ce dake nuna cewa mutun nada saukin kai, matsala da shi son jikin tsiya shi a tunaninsa ni namiji ce baijin komai ya rika ruko mun hannu baisan yana sani cikin yanayi ba.

Muryar azmi ce ta katse mata tunanin nata “sai kayi sauri fa tukur naga alamar yau shiririta kake ji,” 

Mayar da hankalin ta tayi ta ci gaba da ferar doyar, bayan tagama tayi mata shape, gaban tap taje ta zuba ruwa ta wanke ta tas, ta dawo kan eggs din da cokali ta farfasasu ta dauko Whisk abun ƙaɗawa ta k’ada shi ya haɗe jikinsa, kayan kamshi azmi ta miƙa mata ta karba ta zuzzuba a ciki, bayan tagama ta shiga soya wa da doyar.

A kalla suna yin abinci kusan kala 8 na breakfast hada kayan snacks irinsu bugger, donuts, pancake, soyayyiyar ayaba (plaintain) chips doya da kwai, chicken pper soup, pasta wit stew , coffee , slide bread, gasasshen kifi, fried meat tarkace iri iri , 

Mafi rinjayen aiki azmi ke yi hakan ba karamin taimakon sehrish ta yi ba saboda bakomai ta iya ba,

“Ka je ka fara tado su lokaci karya kure tunda mun kammala da wuri” A cewar azmi da take shisshirya kayan abincin wanda zata je ta jera a dining, 

Download>>> Kamanni Complete Hausa Novel Document

fita sehrish tayi da sauri gaban ta na ɗar ɗar gudun abunda zata taras wurinsu, 

Dakin kanal yusif ta fara zuwa, bayan ya bata iznin tashigo, ganin shi daga shi sai short towel a west dinsa ya sa ta yin ƴan kame Kame da alama daga wanka ya fito duba da yadda ruwa ke ɗigɗiga daga jikinsa, 

Sam ta gaza control ɗin kanta har sai da ya juyo ya kalle ta dayake a gaban dressing mirror yake, ganin yadda mai aikin ya zuba masa ido yasa shi jan dogon tsaki tare da cewa “Stupid ! Why are you Looking at me? Ina namiji kana namiji amma kake kallo na anya kai ba ɗan iska ba ne? 

Sunkuyar da kanta ta yi tare da cewa, “An gama shirya…’ Bai bari takarasa ba ya ce “Na ji but this is the last warning da zan yi maka as from today bana bukatar sai an zo an sanar da ni in sauko in ci abinci,” 

Cikin girmamawa ta amsa masa da ta toh insha Allah hakan bazai sake faruwa ba, fi ce wa tayi ta wuce dakin khaleed har cikin zuciyarta taji dadin abunda yusif ya ce mata saboda ita hutu ne a gare ta,

Shima khaleed kusan hakance ta faru ya ce baya bukatar ana zuwan masa ɗaki da safe haka indai ba shi ya bukata ba, 

Wuce wa tayi dakin twins kwankwasa tayi taji shiru ba a bata izinin shiga ba amma kofar a bud’e take, a matsayin ta na me ragaggen hankali sai ta kutsa kai tashi ga kwata kwata babu su a saman gadonsu sai dai wani abu daya tayar mata da hankali, gurnani da wani irin nishi tadinga ji daga cikin toilet dinsu alamun akwai mutun ciki kona ce mutane ciki, tamkar ana sukuwa saman doki yanayin sautin.

Hakan ba karamin firgitar da ita yayi ba sai ranta ya riƙa bata cewa kodai wani ne bai lafiya a cikin toilet ɗin da bukatar tayi sauri taje ta sanarwa azmi abunda ke faruwa, juya wa tayi da sauri zata fita sai taji ana koƙarin buɗe kofan, tsayawa tayi tana kallon kofan toilet ɗin taga ikon Allah, a tare suka fito daga toilet din Ayaan ne ya fara fito wa sai jahan biye a bayansa dukkansu sanye da gajeran towel a ƙugunansu,

Gaba ɗaya tabi ta firgita sam basu lura da ita ba don haka ta lallaba ta fice cikin saurin,

Jikin ta a mace take tafiya abubuwa iri iri ne suke zo mata a ranta ” dama mutum biyu na shiga toilet a lokaci ɗaya, menene dalilinsu nayin hakan? Shin nishin da naji da gurnanin nan na menene ? Allah wa alamu ta tambayi kanta sam ba ta kawo wa ranta wani abu ba amma hakanan take jin tabbas da akwai matsala a tattare da twins din nan.

Download>>> Dr. Bobby Complete Hausa Novel Document

Bedroom din fawan ta wuce tun kan tashi ga take jin sa yana waya, tsayawa tayi bakin kofan tana saurarinsa  “baby nifa bana so a samu matsala bakisan halin yayyen mu ba muddin suka gane cewa ina mu’amala da mata to tabbas sai sun kusa kashe ni,” 

Rass taji gabanta ya faɗi ” mu amala da mata kuma wata irin mu’amala kenan? 

Ta jefa wa kanta tambaya zuciyar ce ta bata amsa “duk wata mu’amala da mutun ke gudun a san yanayin ta to tabbas ba mai kyau bace,” 

Wani irin miyau ta haɗiye lokacin da ta samu amsar tambayarta , sai da ta samu natsuwa sannan ta kwaɗ’a sallama,  jin muryar mai aikin nasu yasa fawan saurin yin rejecting kiran ya yi throwing phone ɗin nasa saman gefensa, rai abace yace ” wai wanene ” 

Ko izinin shiga ba ta samu ba, murya na rawa ta ce “tukur ne dama an kammala shirya breakfast ne” 

Wani irin dogon tsoki ya ja tare da cewa” Naji sai me”? 

Jiki a sanyaye sehrish tabar kofan ɗakin nasa ta wuce na irfan, ita kanta ta shaida cewa yau babu sa’a ynx fargabanta me zata taras ɗakin sauran.

Kwankwasa kofar ɗakin nasa tayi , da wata irin kakkausar murya taji ya amsa mata da cewa”Uban wanene” kai kanaji kasan yasha ya bugu har takai masa aka.

Saboda tsoro bata basa amsa ba ta yi gaba da sauri, tun a lokacin ta gane cewa tabbas akwai matsala kuma sam bai kamata tana bin kowannan su ɗaki don tayar dasu ba, ta gama yanke shawarar sanarwa azmi cewa baza ta ƙara zuwa ba, tun da cikinsu ne in suna jin yunwa dakansu zasu fito su nema.

Gaba ɗaya a firce take da lamarin kan ta ya gama ɗaure wa, ɗakin Jabeer ta wuce tana sa hannu ta kwankwasa kofa , tana jiyo har mutsinsa ta ciki sallar karya ya kabbara , shiga ciki tayi abun saiya daure mata kai,  Sallah karfe 9 na safe.

Har zata juya idon ta ya hango mata kwayoyi na shaye~shaye ga kwalabe kuma a gabansa.

Shi duk a tunaninsa yayansu ne kanal yusif amma jin shiru yasa shi katse sallar ya ɗago ya kalle mai aikin, wani mugun kallo ya wurga mata tare da nuna mata hanyar fita ya ce ” karka kuskura ka ƙara zuwan min ɗakina in ba haka ba saina canzama kamanni shashasha,” 

Abun da bai sani ba ita sam ba ta san kwayoyin menene a gabansa ba, a tunaninta bai da lafiya ne shine ya ajiye magunguna zai sha.

Download>>> Walijam Complete Hausa Novel Document

Ficewa ta yi a ranta tana cewa” Allah ya ba ka hakuri,” 

Saura ɗakin shagwababben sarkin murmushi, har tsoran zuwa ta ke yi saboda manne mata da yake yi,

Tunkan ta shiga take jin muryasa yana faɗin “Coffee i need coffee pls ” cikin magagin bacci ya ke wannan sambatun na neman coffee,

knocking tayi masa kusan sau uku kafin taji muryarsa yana cewa “wanene shigo ciki mana,” 

Gyarawa tayi ta shiga ciki samun shi tayi kamar yadda ta saba samun shi irin kwanciyar nan tasa daya saba, kamar wani karamin yaro haka yake,

Karasawa tayi gabansa tare da cewa”barka da safiya junaid , tukur ne,” ta idasa maganar tana kallon cikin idonsa daya buɗe, 

A duk lokacin da ta kalle sa wani irin natsuwa da kwanciyar hankali ne ke shigarta, murmushi taga yana sakar mata dimple din nan nasa masu lotsawa guda biyu suka bayyana, 

“Ohh tukur ne am really happy to see u, dama yau inaso ka taimakamin tun jiya nakeson wanke sumar kaina na kasa amma yau kam tare zamu shiga toilet ka taimakamin,” a wani shagwab’e ya ke maganar.

Sehrish kuwa waro ido waje tayi jin abun da ya ce wannan da alama wata rana cewa zaya yi tayi masa wanka, 

Cikin sanyin murya ta ce “ka yi hakuri dan Allah ba yadda za’ai na bi ka toilet sam a tsarin aiki na a gidan nan ba’a ba mai aiki izinin yin hakan ba,

Wani irin kallo ya wurga mata kafin ya ce” wa ye wanda ya tsara wannan dokar? bayan ni ne silar da aka kawo ka aiki a gidannan, tukunna ma kai ba jinsina bane? to kodai maca ce tayi shigar maza bansani ba,” 

Jin wannan maganar tasa yasa sehrish jin faɗuwar gaba tuni ƴan hanjin cikin ta suka ƙaɗa har ta soma tunanin anya Junaid bai gane cewa ita MACACE ba NAMIJI ba !? duk tabi ta rikita kanta 

Muryarsa ce ta sake katse ta “Am asking you ! answer me,” dakyar voice ɗinta ke fita “ba haka bane, kawai a ganina bai da ce ba ina matsayin mai aiki nayi hakan,”

“I command you to do that! ae mu ne masu gidan kuma umarnin mu ake bi,” 

Cike da isa junaid yayi maganar,ba yadda sehrish ta iya a dolen ta, tabi umarninsa, haka ya tashi yana yauƙi yana cika yana batse wa kamar bashi bane mai murmushin kashe zuciyarnan ba, 

Download>>> Matar Hariji Complete Hausa Novel Document

Miƙewa ya yi daga saman bed din ya sauko daga shi sai shorts a jikinsa, bin jikin shi tayi da kallo fari sol ba tarin gashin jiki a skin dinsa , ga kirarsa dai dai wa dai dai, kusan hasken fatarsa dana twins jahan da Ayaan ɗaya ne akan na sauran don haskensu ba irin na nan bane zai iyiyuwa cikin iyayensu akwai farar fata, mahaifiyarsu ko mahaifinsu, 

“Idan ka gama kallon zamu iya shiga ciki ko” ya ambata yana kallon ta, gaba yayi cikin toilet din tabi bayansa zuciyarta na ɗar ɗar tsoranta kar ya ce zai cire shorts ɗinsa a agaban idonta batasan ya zata yi ba, 

Da farga jikin ta na rawa ta dauko ɗaya daga cikin jerin shampoo dinsa na wanke kai, juya tayi da nufin ta nuna masa in da wanda ta dauko yake amfani kar asamu matsala, samun shi tayi yana kokarin cire shorts ɗin jikinsa, aiko a firgice ta saki roban shampoo ɗin ƙasa, ta karasa da gudu ta cafke hannayensa dake a saman mararsa gam ta ruke su, kallon juna suka shiga yi na wani lokaci, shi mamakinsa wai namiji ne ke gudun ɗan uwansa namiji a ganinsa is not a bad thing don ka cire kayanka gaban jinsin ka, ita kuwa miyau kawai take haɗiya gabanta na faduwa sai faman huci take kamar wadda ta yi ƴar tseral, Tuni hancin ta ya soma tsattsafo da zufa, tsoranta wane hukunci zai yi mata a sakamakon abunda tayi, ita dai tayi hakan ne don da abunda zata gani na tsiraicinsa kwara koma meye yayi mata tasan ba laifinsa bane, laifin ta ne da tayi shigar namiji, 

Zame hands ɗinta tayi daga rikon da tayi masa, hannayenta ta aza a saman kanta tare da faɗin “nashiga ukuna am so sorry sir am just out of sense,” duk a riki ce tayi maganar,

‘Stop calling me sir! Cos may be am just your age mate, call me wit my name Junaid, 

Ya karsa maganar tare da ƙara gyara gyara shorts ɗinsa yace ” get out of my sign,” 

Cikin sauri ta nufi hanyar fita har ta 6uɗe kofan tajiyo muryarsa yana cewa” Am watching you!” juya kanta tayi ta kallesa da yatsunsa yayi mata nuni da idonsa alamar zai sa ido akanta,

Cikin sauri ta fi ce tana faɗin ” Insha Allah junaid bazaka gano komai ɗangane dani ba zan ta addu’a ina rokon Allah yaci gaba da rufamin asiri har nasamu na hada kudin aikin Husanna nabar maku gidanku, 

ta fada acikin zuciyarta (abunda sehrish ba ta sani ba wannan gidan is part of her destiney)

Azumi ta kammala shirya musu abincin sai da kowannansu ya mula yasha iska sannan suka firfito, one by one duk sun shirya cikin kakin sojojinsu, banda mutun ɗaya junaid wanda ke sanye da  jeans a jikinsa tare da farar tshirt mai dogon hannu ta ɗanyi tighting ɗinsa, 

Kowannan su ya samu wuri ya zauna, sehrish ce ta fito frm the kitchen don ta fara saving ɗinsu, azmi kuma ta wuce bedroom ɗinta don dama already ta sanar da ita cewa zata shiga ciki tayi wanka don tasha aiki,

Hannu ta har kekkerwa yake yi saboda tsananin tsoran guyabarsu, junaid ta fara kallo tare da cewa”me zan zuba maka’? Kafin ya buɗe baki ya yi magana fawan ya kar6e da cewa”saboda shine babba acikin mu !” 

Ayaan ya ce “thats what i was trying to say! Wannan house boy din ba karamin ɗan iska bane shi junaid ɗin special salary ya ware maka ne ɗayasa kke kokarin fara zuba masa abincin? ya tambaya fuska a ɗaure yana kallon ta, 

nan fa hankalinta ya tashi ita batayi don wani abu ba ashe abun yana damunsu,

Muryar Jahan ce ta katse ta “Nima na lura da haka in banda iskanci ka rasa wanda zaka fifita sai karamin kanin mu wanda ko aiki baya zuwa sai dai yazauna kamar mace a gida,’ ya ƙarasa maganar yana wurga masa harara.

Ran Junaid ba ƙaramin baci yayi ba, abun duk saiya bashi haushi musamman da Jahan yace masa kamar mace, wani irin ƙululu bakin ciki ne ya tsaya masa a maƙogwaronsa,

duk wannan abun da suke kanal yusif na jinsu bai ce komai ba haka zalika sauran y’an uwan nasa su irfan, sauraronsu kawai suke yi dama basu cika shiga faɗansu ba.

Download>>> Macizai Ne Complete Hausa Novel Document

“Nima abunda nagani kenan Jahan kullum zaman kashe wando ya iya bai da wurin zuwa daga buga ball sai atake masa abinci a plate yaci yayi haikam ƙarshen wata nayi Babban yaya ya turo masa da dollars a account shiyasa gayanan duk yafi mu kyan gani,’ fawan ne yayi maganar yana kallonsa daya ke suna facing ɗin juna a table ɗin,

ganin yadda suke ta faman yada masa magana a gaban ɗan aikinsu tukur yasa shi cewa “Ya Isa haka ! Ku ce koma me zaku ce! in da na gode ma Allah ma ba da son raina nima nake zaune gidan ba! Ciwo ne kuma zai iya samun kowa acikin ku!,’ ya karasa maganar idonsa sun cicciko da kwalla,

Ran sehrish dake tsaye ba ƙaramin baci yayi ba ganin yadda manyan suka kasa dakatar dasu daga gaya masa magana musamman kanal yusif da yake babbansu a yanzu, 

Dariya fawan yayi tare da cewa ” aikin kenan! daga magana ƙaɗan sai ka nemi zubarwa mutane da hayawa kamar kafi kowa ruwan hawaye a …’ bai idasa maganar ba yaji saukar ruwan tea mai zafi a fuskarsa Allah yaso ba tafasasshe bane, ihu ya saki tare da faɗin “innalallahi junaid baka da hankali ne! ni ka watsa wa ruwan tea! wlh bazan yarda ba saina rama, 

Hannunsa ya zura ya dauki kular da farfesu ƴan ciki mai zafin gaske ke aciki ya yunkura zai watsa wa junaid, da gudu junaid ya tashi , shima fawan ɗin yabisa kamar tom& jerry haka suka rinƙa zagaye wurin,

Hankalin sehrish ba karamin tashi yayi ba bata ta6a sanin haka suke ba wannan ai sai suyi kisan kai.

Ga haushin ƴan uwan nasa da take ji hankalinsu kwance sai ma umarni da suka bata ta zuba masu abincin nasu su ci, saving ɗinsu take yi amma hankalin ta nakansu Junaid da fawan dake ta faman ƴan guje guje , tsoran ta kada fawan ya zuba masa farfesun nan a farar fatar nan tasa mai laushin gaske don tasan tuni zaiyi mummunar ƙuna.

Har ta kammala saving ɗinsu ta koma ɗaki cikin rashin kwanciyar hankali, a bangaren su fawan kuwa dake faman faɗa tunda junaid ya samu ya shige room ɗinsa ya datse kofar, a dole fawan ya haƙura a zuwan Zasu haɗu ne ae ba kwana zaiyi a rufe ba, 

Gaba ɗayansu sun fita tana jin tashin motocinsu, cikin sauri ta fita domin da ma ta ƙagara su fita taje ta sanarwa junaid ko ya samu yazo ya ci kalacinsa,

A falo ta gamu da azmi tana goge goge, cikin girmamawa tace”sannu da aiki aunty azmi me zai hana ki bani na idasa aikin tun da dama ni nake yi kinyi aiki sosai nasan kin gaji,”

fuskarta a sake ta ce” kada ka damu tukur ai an jima na nan, yanzu dai abinda zaka yi kabi bedrooms ɗinsu ka gyaggyara tsaf don Allah,’ 

Sehrish ta amsa mata da toh wuce wa upstair tayi ɗakin junaid babbuga kofan tayi, muryarsa taji yana cewa”wanene”?

Gyara muryarta ta yi tare da cewa”tukur ne mai aiki dama naga baka ci breakfast ɗinka bane,’ 

Ɗan guntun tsoki yaja tare da cewa”Naji a kawomin a ɗaki na zanci,’ 

Amsa sehrish tayi da toh sannan ta juya time ɗin da ta sauko azmi har ta kamma gyara falon yayi fes gwanin burge wa sai ƙamshi dake tashi, kai matar taji daɗi ga iya girki ga iya gyaran wuri ya koma kamar sabo uwa uba ga kyan hali, sehrish ta faɗa a ranta tana dan murmushi, 

Kitchen ta wuce nan ma ta samu azmi ta gyarasa komai tsaf, shirya masa abincin tayi a tray, ta koma ɗakinsa nasa sai da ta jira ya 6uɗe mata sannan ta shiga.

Domin Sauke Cikakken Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Please Share and drop your comments

Back to top button