Hausa novels

Haihuwa Da Hanji Page 16 Hausa Novel

Kaman yadda ƙa’idarsa take ba ya hanzari ko gaggawa a koma menene sai ya sha Ƙamshin nan dai wane saraki haka a yanzu ma, sai da saleem dake sanye da khakin sojoji full 6/6 don hatta agogon da Ke ɗaure a tsintsiyar hannunshi da ƙatuwar backpack na bayanshi duk na sojojin ne ya sauƙo kan ya buɗe motar ya sanyo jiki.Yau sanye yake da wata farar kaftan da aka yi wa ɗinkin zamani ya matuƙar zauna mishi kuma farar fatarshi ya ƙara haskaka, daga takalmi har agogon fatar dake ɗaure a tsintsiyar hannunshi farare ne, kanshi babu hula sai kwantaccen gashin shi na ainihin Fulanin asali da ke sheƙi, ganin Dr Sulaiman ya ɗan ba saleem mamaki shi ma kuma Sulaiman ganin su ya sa ya taso daga jikin motar shi ya isko su Saleem ya fara miƙawa hannu fuska a sake suka gaisa kan ya miƙawa Ryan shi ma ya karɓa suka gaisa cikin ‘yar nuna sanayya amma fuskar nan kadaran hadaran.Magana suka cigaba da yi da salim da ta shafi Lafiyar Afeefah shi dai Rayyan tun da suka gaisa ya zaro wayanshi ya kuma mayar da hankalinshi kai don hirarsu ba huruminshi bane.Tun da ta hango su gabanta ya yanke ya faɗi, abin da za ta cewa saleem ya kawo Sulaiman gidan ke ta kai komo a ranta, tafiya take tamkar hawainiya saboda bugun zuciya, su ukun duka kwarjininsu ya wani rufe ta tun kan ta iso inda su ke, Zaratan samarin masu jini a jika cikakkun maza kuma kamilallu, kowanne kuma gwani ne a nashi fagen kyaun da kamala.Ji ta yi kafafunta ba za su iya daukar ta ba a sadda mai fararen kayan ya ɗago idanu suka shige zuruf cikin nata.”Rayyan!”Sunan ya yi ringing da matukar ƙarfi a kwakwalwarta, wannan idanu ba za ta taɓa manta shi ba tuni ya mayar da kanshi kan wayanshi amma ita ta daskare ta kasa motsa kowani gaɓa na jikinta, idanunshi sun fi yanayi da na maguna kwayar wani surkin kala ne da kan rikita lissafin duk wadda ya zubawa su, ƙasan lid ɗin tamkar an zana mishi kwalli zirrr baƙi sidik hakan sai ya kara saka idanun zama na daban da sauran mutane, idan idanun suna duƙe za ka zaci a rufe suke saboda tsawon lashes ɗin sa ga su baƙake kaman gashin kansa da na girarsa.”Afeefah!!”Saleem ya faɗa da ɗan karfi a karo na uku, firgigit tayi ta dawo hayyacinta. “Ƙaraso mana kin tsaya daga chan”Bai sake magana ba har ta ƙaraso inda suke daga shi har Sulaiman idanunsu na a kanta.Da kyar ta iya buɗe baki tace “Sannu da isowa Ya Saleem””yauwa Afeefah””Ina yini?”Kai kawai ya ɗan gyaɗa mata hakan ya sanar da ita cewa lokacin da ya kamata yayi magana da ita ya wuce.”Yaya Sulaiman ina yini?”Muryarta da ya karye ya ƙara sanyaya yana fitowa a slow, ɗago ido Ryan yayi ya kalleta daidai tana ce mishi shima Ina yini? Ya kau da kai kaman bai gane da shi take ba, daga shi har saleem sun fahimci chanzawar muryarta, shi Ryan kam ma mamaki ne fal ranshi don a yanzu abin da ya sa ya sake kallonta tuna abin da saleem ya gama faɗa mishi bayan ya ɗauko shi daga Airport wai son yarinyar nan yake, in ba janyowa kai raini ba shi bai ga abin ba ya tabbatar a auren ƙauye sun kusa ajiye irin ta. Tsaki ya ja a fili yana furta “Man we talk later!”Ya faɗa cikin muryarshi mai cike da ginshira sai Muryar ya bata tsoro ta tuna ranar da yake daka mata tsawa da hanzari ta ɗago idanu ta sake kallonshi, ya miƙawa Sulaiman tender fingers ɗin shi da kaman zai fidda jini don haske da taushi suka yi musabaha, yana kokarin buɗe mota idanunshi suka sake shige wa cikin nata, daga ita har shi suka yi saurin kawar da idanun ya shige ya ja ya bar gidan.Saleem ya dubi Sulaiman ya ce “Nima kaman zan shiga daga ciki jikina kaman an min duka”Sulaiman na murmushi yace “Ai dole, a huta gajiya mazan fama”Suka yi musabaha kan ya nufi ciki, ya zaci Afeefah ma za ta yi wa Sulaiman ɗin sallama ta biyo bayanshi sai ya ɗan waiga nan ya ga sun matsa jikin motar Sulaiman ɗin yana mata magana a hankali ita kuma tana dariya, tuni duk wani walwalar fuskarshi ta kau, ranshi ya shiga suya bai iya ya shiga main parlorn ba ya bi ta baya ya haye sashenshi, backpack ɗin kawai ya ajiye ko zama ya kasa yi ya dawo jikin Window yana kallonsu, kusan mintuna talatin suka yi suna hira kan ya ga Sulaiman ya buɗe mota ya fiddo wasu ledoji ya miƙa mata.”Ga shi umma wai na kawo miki”Tayi murmushi mai kyau cike da jin daaɗi tace “Allah sarki umma, ka yi mata godiya na ji daaɗi sossai Allah ubangiji ya kara girma da lafiya”Wayanshi ya zaro yana furta “Ko kuma ki yi mata da kan ki ba”Ido ta zaro kan ta yi magana ya shiga ƙiran ummar, bayan ta ɗaga da sallama ya ce “Ummar mu ga Afeefah tana so ta miki godiya”Kaman za ta nitse haka ta karɓa ta shiga gaisheta tana yi mata godiya, Albarka Ummar tayi ta sanya mata kan suka yi sallama ta miƙa mishi wayar tana ɗan tura baki na fushin yadda ya saka ta jin kunya, murmushi yayi “Kar ki sa na narke fah Afeefah”Tayi murmushi Ya miƙa mata wani leda mai girma da farko kin karɓa tayi sai dai da ya matsa ta karɓa ɗin tare da godiya suka yi sallama ta nufo ciki.Da hanzari Saleem ya ɗauko wayanshi ba ta ko kai ga shiga ɗakinta ba ta ga saƙon shi “Menene ke tsakani ki da Sulaiman?”Muƙut haka ta haɗiye wani miyau kaman yana gabanta, da sauri ta shige ɗakin ta ajiye ledar tare da zame mayafinta ta jefa kan katifa ta fara safa da marwa cikin tunanin amsar da za ta bashi, sam bata so yayi fushi da ita da kyar ta iya rubuta mishi “Babu kawai kyautatawa ce da suke min shi da ahalinshi”Shiru ba reply, ta san ba wai ya yarda bane kuma kila shirun nan da ya yi fushi yayi, ta kasa zaune ta kasa tsaye haka ta yi ta saƙe-saƙe ita kaɗai, ƙiran Magrib ne ya katse ta jiki a sanyaye ta shiga bayi tayo alwala ta zo ta gabatar da sallah ta zauna nan tana karatu.Sulaiman kasa zuwa office yayi haka kawai yake sake tariyo kallon da saleem ke yiwa Afeefah, ji yayi ko ya je office ba zai taɓuka komai ba yana buƙatar shawara da mahaifiyarshi don tamkar ƙawarshi haka take.”Wash Allah na!”Ya faɗa yana kwantar da kanshi a kan kafafunta, ta sa hannu ta shafa sumanshi “Ya dai likita?””kawai gajiya ne umma””faɗamin gaskiya ko dai kai da surkar tawa ne?”Ya ɗan yi shiru kan ya ce “Ina tunanin umma saleem na son Afeefah, ko dai ita bata sani ba ko kuma ta sani tana min wasa da hankali ne””Saleem shi ne ɗan masu gidan da take aiki?”Kai ya gyaɗa mata”Kuma Baaba ta tabbatar min kaman yarinyar tana shan wahalan gidan aiki haka ne?”Nan ma ya gyaɗa kai fuskar shi babu walwala”Kaman saleem ɗin ne kawai yake taimaka mata, kuma kaman ba ta da kowa don dole ne kawai take zaune gidan””Ka kwantar da hankalinka Sulaiman, kila ba soyayyar ba ce tsakaninsu sai kyautatawa don ya na tausayinta, kila kuma yana son ta ɗin amma yana tsoron bayyana mata don iyayenshi, zai ma iya yiwuwa ya sanar mata ɗin amma ta ƙi bashi haɗin kai don babu macen da za ta yi kuskuren jefa kanta inda ta san ba’a ƙaunarta ko kuma inda za ta sha wahala”Numfashi ya sauƙe “Umma haka kawai nake jin kaman ba zan sameta ba””Ka cigaba da kyautata mata domin zuciya tana son mai kyautata mata, idan har matarka ce za ka aureta, ni ma zan so ka sameta don na tabbatar wacce ta iya mallake zuciyar My Son ba ƙaramar nagartaccciyar mace ba ce”Ya miƙe zaune yana murmushi “Umma za ki fara taya autocinki zolaya ta ko?””Ai gaskiya ne sabon shiga, duk ka bar komai obvious sai gano ka muke yi dubi duk yadda ka ruɗe daga sanin tana da wani saurayin”Ta ƙarasa da dariya.”Duk ba za ku gane bane umma ni dai na yi nan”Yana ji tana cewa “Toh zo ka ganar da mu mana”Yayi murmushi kawai. Allah ya gani shi karan kanshi ba zai ce ga sadda ya fara jin son Afeefah a ranshi ba, kawai dai ya san ta yi mishi kyau ranar da ya fara ganinta, sanyin muryarta idan tayi magana sai yake jin tamkar ƙanƙara ake zuba mishi. Ko da ta bar asibitin bai wani sa hope ɗin sake ganinta ba amma daga ranar da ya je ya isketa cikin fitar hayyaci sai ya ji tamkar an soki zuciyarshi da mashi barin ma da ya gama fahimtar tana shan wahalar rayuwa a gidan, sannan ya san babban burin ta a rayuwa shi ne ta yi karatu ta zama wata public figure da za’a yi alfahari da ita, kaman tana da wani ciwo ne da take jin ba zai taɓa warkewa ba har sai ta yi nasara a duniyar ta, ba ya jin zai iya bar wa saleem ita za su buga wasa ne duk wanda ya iya allonsa ya wanke.A daren da misalin ƙarfe tara ya ƙira layinta, ta gama wanke-wanken dare kenan da yau yayi yawa sossai saboda abincin da aka yi kalolin daban-daban, sai duba wayan take ko za ta ga saƙon saleem don gabaɗaya ranta babu walwala, ko da suka haɗu ko kallonta bai yi ba kuma ta sake mishi saƙo babu reply.”Assalamu Alaikum warahmatullah”A natse ya amsa “Wa’alaikissalam gimbiyar mata”Tayi ignoring sunan da ya ƙiratan “Ka koma gida lafiya?””Da an damu da ni ai da an neme ni, ni da ya zama dole na ba gashi na kira ba. Ya kike?”Har za tayi magana ya katse ta “Wait!! Kina lafiya ko? Ya na ji muryarki duk cike da damuwa da rashin Walwala ba yadda na bar ki ba?”Ta ɗan ja numfashi tana tafiya kwance daga zaunen da take jingine da gini.”Kaina ke ɗan ciwo””Eyyaa so sorry, kina da ORS?”Ta girgiza kai tana amsawa da “A’a””Ki sha pcm da safe zan zo in auna jinin ki sai in taho miki da ORS ɗin, ciwon kai bashi da daaɗi musamman ga ke da jininki sauƙa yake kuma kin san ya fi high BP hatsari”Idanu kawai ta runtse bata san me zata ce ba tunda ta riga ta yi suɓutar baki ta ce kanta na ciwo zuwa kam sai ya zo to kuma saleem da har yanzu bai sauko daga fushin ɗazu ba fa?”Kina ji na kuwa Afeefah?””Eh ina ji, na ce da ma ka barshi in na yi bacci zai daina””hmmm ke dai kawai in na zo ɗin zan ƙira ki, kwanta ki huta Allah ya baki lafiya”Yana kai nan ya katse wayan ba ya so ta hana shi zuwa haka tayi ta juye-juye har bacci ya sure ta.Washegari tana gama goge-goge ko ɗaki bata koma ba sai ga ƙiran shi, gate kawai ta wuce don ta karɓa da sauri kan saleem ya tashi ya ganta “Sannu da zuwa””kin tashi lafiya?”Yayi tambayar yana ƙare mata kallo, ita kam ko me ta saka kyau take mishi “Alhamdulillah ya su umma?””Umma na gaishe ki da jiki ta ce in miki sannu””Na gode sossai”Leda ya fitar ta zare ido, ko kayan jiya bata buɗe ba saboda damuwar fushin saleem da ita yanzu kuma ya sake ciko leda? Shi kam ba ya gajiya ne?”Hidimarka na yawa a gareni Dr. Na kan rasa kalaman godiya a gareka, wani lokacin sai in ji tamkar ba na kyauta maka don ka fara ƙaunata tun ba ka san wacece ni ba! Ban san ya za ka karɓeni ba a duk ranar da wani ya tare ka ya ce maka Afeefah annoba ce!”Kallon bana fahimtar zantukan ki yake mata daidai saƙo ya shigo wayar ta sanin saleem ne ya sa dole ta buɗe tana ta ƙoƙarin haɗiye kukan dake zuwar mata “Ki sallame shi za mu yi magana”Ta ɗago ta kalli Sulaiman da har lokacin idanunshi ke kanta.”Zan shiga ciki za mu yi magana””Saleem ɗin ne ya ce ki sallameni?”Ya faɗa cikin wata murya yana ƙara tsare ta da idanu.Ba Ta yi magana ba ta mayar da kanta ƙasa kawai.”Ya za ki saka ni a duhu kuma ki tafi ki bar ni ciki? Me kike nufi a tare ni a ce ke annoba ce? Mutum ya taɓa zama annoba ne Afeefah?”Muryar ta na rawa tace “Kwarai Dr. Sulaiman da za ka iya da ka yi tattaki zuwa Dutsen-wai ka tambayi wacece Afeefah kamal ina da tabbacin bayan nan ko mai sunana aka ƙira maka za ka gudu! Umma ta karɓe ni ne domin itama bata san wacece ni ba don babu uwar da za ta karɓeni matsayin surka muddin tana ƙaunar ɗan ta”Ranta zafi yake mata, tana maganar ne tana tuna mahaifiyar saleem da kyamatarsu gareta ta wani ɓangaren kuma bata ga laifinsu ba don ba laifi bane mutum ya kare abin da yake so.”Ka yi haƙuri ka tafi Dr. bana so sai ka zurfafa kasan ni wacece in karya maka zuciya, na tafi ciki”Tana kai nan ta nufi ciki ta bar shi tsaye, hawaye take zubarwa ba wai duk cikinsu babu mai nagartar aurenta bane sai dai tana ji babu inda za’a karɓeta matuƙar an san wacece ita! Taɓon nan da bata san mafari ba ba zai taɓa goguwa a tarihin ta ba, tabo ne mai raɗaɗi da har Abada za ta cigaba da rayuwa cikin gangar jikin da ruhi mai tarin buruka suka mutu… Da saleem ta ci karo a sadda ta shawo kwanar ɗakinta ido kawai ya zuba mata ko da ta zo bata tsaya ba kawai ta wuce shi yayi saurin shan gabanta.”Afeefah saboda Sulaiman kike ɓata rai da ni?”Hawaye take yi wadda ta kasa sarrafa su cikin rabuwar murya tace “Ba saboda shi bane yaya saleem”Ta sake yunkurin wucewa ya sake tare ta”Ban gane ba bayan ga idanunki nan suna zubar da kwallah Afeeefa?”Cikin Muryar kuka ta shiga cewa “Ina kuka ne saboda na gaji da yaudara ta da zuciyata ke yi na cewar zan samu farin ciki, ina zubar da hawayene saboda na farka daga mafarkin da bashi da tabbas”Shesheka ta ja tana kallon cikin idanunshi”Ka gaya min Yaya saleem a cikin ku biyu da waye zan dogara? Da Kai da mahaifiyarka ta yi Allah ya isa muddin ka yi min maganar da ta wuce ta minti ɗaya ko da Dr. Sulaiman da bai san wacece Afeefah ba?”Wuce shi kawai ta yi don ta san ba zai amsa ba saboda minti ɗayan ya riga ya wuce hakan ya kara rura wutar zuciyarta ƙarfin kukan ya ƙaru, jakar hannunshi ya bi ta har cikin ɗakin ya ajiye ya tsaya ya zuba mata idanu yana jin kukanta na sukan zuciyarshi, idanunshi suka sauya sossai tausayinta da ƙaunarta suka ninku a cikin ranshi.Samha da ke tsaye jikin pampo ta sake hanci da baki tana kallon su ta kwasa da gudun tsiya ta kamo hannun mommy”Mommy zo zo zo ki ganewa idanunki wallahi Ya Saleem ne ɗakin Mayyar chan…”Mommy har tana tripping garin sauri suka nufi bayan a lokacin suka hangi bayanshi ya fito ya nufi hanyar waje, duk su huɗu suka nufi ɗakin kowa da bala’in da ke cin shi a rai…

Back to top button