Hausa novels

Fentin Zina Page 25 Hausa Novel

*****Ihu fateema tayi mai kara sosai tana kiran sunan addanta tana fadin adda meya same ki? Adda ki tashi dan Allah kada ki tafi ki barni bazan iya ci gaba da rayuwa babu keba ba, ta fashe da kuka tana jijjigata.Karan ihunta ne ya shigo da mama rabi da gudu ganin halin da suke ciki yasa ta karaso itama cikin dakin ta hau jijjigata da dai taga babu alamar numfashi a jikin Ameena sai ta mike tace da fateema. Barin sa driver ya tada mota mu kaita asibiti gyara mata hijabin zanzo mu fita da ita yanzu.Ta fita da hanzari ta isa gurin mai gadi ta tambayeshi driver fa yace ana cikin daki ya dan kwantabaya jin dadi ne.Cikin damuwa tace subhanallahi Allah ya sawwaka yasha magani?.Eh yasha domin jikin ma yayi sauki shiyasa ya kwanta domin ya huta in taso shi ne hajiya? Baba maigadi ya tambaya.No kabar shi ya huta din karbo mun makullin motar kawai sai tunda bai maido ba tun da safe daya fita da ita.Toh kawai yace ya shiga dakin ita kuma ta tsaya jiran shi anan har suka fito tare da drivern yace barka da fitowa hajiya ai jikin nawa yayi sauki zan iya kaiki koma ina ne da izinin Allah.Toh shikenan barin fito asibiti zaka kaimu bakuwata ce babu lafiya.Allah ya bata lafiya. Suka hada baki suka ce.Daga haka bangaren dada ta shiga da sallamar ta, bata falon don haka hanyar da zata sada ta da dakin dadan a kofar daki ta tsaya tayi sallama dada ta amsa tare da bata izinin shigowa.Zama tayi a kasa tace Ameenace babu lafiya yanzu haka a sume take shine nikeson kaita asibiti.Wani zabura da dada tayi har saida yaso bawa mama rabi tsoro da sauri dada ta mike ta dauki hijabinta dake gefen gadonta tace muje maza taso yi sauri.Ta fice daga dakin tana hadawa gudu gudu sauri sauri ta bar mama rabi a baya tana mamakin yadda dada ta nuna da rashin lafiyar Ameena lallai yau ta tabbatar so gamon jini ne haka tabi bayan dada da har ta shige part dinta gurin Ameena.Suna isa asibiti aka karbeta a emergency don jini ne keta gangarowa daga kasanta duk ya bata mata jiki.Dakyar likitocin suka tsaida jinin dake zuba suka ceto ta daga fadawa doguwar suma.Shugaban sune ya fito yana goge zufa da hand ki, sauran suna mara masa baya yayinda wasu suke tura Ameena a gadon marasa lafiya domin kaita dakin hutu.Daidai inda su mama rabi suke suna safa da marwa ya tako ya tsaya yana cewa ku biyoni office. Daga haka yayi gaba suna bin ahi a baya.Zama yayi a kujerar shi suma suka zauna a kujerun dake gaban table din suna fuskantar sa.Gyaran murya yayi yace mun godewa Allah daya bamu ikon ceto rayuwarta, amma yaya aalakaar ku da ita wannan mara lafiyar.Mama rabi tace wannan ta nuna dada, kakar tace, ni kuma kanwar mamar tace sannan wannan sai ta nuna fateema.Sai yanzu likitan ya kalli gefen da fateemar take ai baisan sanda ya mike yana nunata ba yana fadin taya hakan zata faru?.Mama rabi tayi murmushi tace kwantar da hankali likita wannan da kake gani kanwar ita mara lafiyar ce.Ajiyan zuciya ya sauke yana zama yace aiko kamar tayi yawa har na kusa ficewa a guje in barku yaseen.Dukkansu dariya sukayi sai dada ce ta dakatar dasu ta hanyar fadin likita ya jikin jikata yake me kuma kuka gano yana damunta?.Gyara zaman gilashin idon shi yayi sannan ya tattara hankalinsa gaba daya ya bude file din Ameena dake gabanshi ya danyi rubutu kadan kana ya dago yana dubansu yace, abu biyu ne dai muka gano yana damunta a yanzu sannan ba kananun ciwuka bane dukka biyun musamman idan akayi duba da shekarunta, na farko mun sameta da ciwon hawan jini ma’ana dai tana yawan sanya damuwa a ranta sosai kuma bata barin kanta isashshen bacci da daddare wadanda sune sukayi leading to abunda ya sameta, sannan binciken mu ya nuna cewar akwai abunda taji ko ta gani wanda ya daga hankalinta har hakan ya sanya zuciyarta shiga halin kakanikayi wanda ba don Allah ya taimaka ba zata iya samun gagarumar matsala karshe ta iya rasa rayuwarta, sannan cikin jikinta dakyar muka samu ya tsaya amma akwai magunguna da zaku saya in Allah ya taimaka tayi amfani dasu yadda ya kamata zamu dace sai dai ina gargadinku daku kula da lafiyarta sosai kada ku bari wani abu daya danganci bacin rai ko makamancin haka ya dinga matsowa kusa gareta.Tunda likitan ya soma magana gabaki dayansu jikinsu ya mutu sannan sunyi matukar kaduwa da jin abunda ke faruwa musamman fateema da harta soma kuka ba tare da la’akari da inda suke ba ta hau cewa mama rabi. Kin gani ko mama kinga abunda nike fada miki dazun ko don wallahi banida shakku ko tantamar innace ta jefa addata a cikin wannan halin da take ciki a yanzu, fisabilillahi so take ta mutu ne? Ni ina sonta idan kowa zai gujeta ni abarni da ita ai kowa baifi karfin kaddara ba wannan wace iriyar rayuwace dan Allahhhh…. Ta karasa tana fashewa da kukan daya fi na farko don gani take kamar addanta zata tafine ta barta.Mama rabi ta jawota jikinta ta shiga rarrashinta har tayi shiru, dada kam tama kasa cewa komai sai bisu da ido take yi tana tuna irin maganar data fadawa Ameena ne a safiyar yau din kuma ta dau alwashin bazata kara fada mata magana mara dadi akan kaddarar data samu kanta a ciki ba. Dakyar ta bude baki tace likita zamu iya ganinta?Gyada kai yayi kafin yace zaku iya ganinta amma ba’a bukatar hayaniya a gurin so ku kula please.Insha Allah cewar mama rabi suka mike suka fice.Tun daga kofa suke kallonta yadda ta fada kamar ta shekara tana ciwo fuskarta tayi fayau ta kara haske sosai idanunta a lumshe suka karasa kusa da ita, dada ta dafa goshinta nan take taji kwallar tausayin ta yana taruwa a idanunta tace cikin karfin hali, Allah ya baki lafiya Ameena Allah ya tashi kafadun ki.Zata cire hannun daidai Ameena ta fara motsi da bakinta tana cewa cikin halin rashin lafiya da kuma sarewa, dan Allah kuce inna ta yafe mun mutuwa zanyi kada ta cigaba da fushi dani, ku tayini neman gafarar ubangiji bayan na mutu. Ta karashe hawaye na bin gefen kumatunta sai ta bude idanunta akan Fateema ta sauke su ta yafice ta da hannu. Fateema ta karaso idonta cike da hawaye tana jiran kiris su soma zubowa.Fatyna ki mun alkawari suk rintsi duk dadin so bazaki bada mutumcinki ba kamar yadda nayi!.Hawayen da take rikewa ne suka shiga zubo mata tace adda kibar wannan maganar kinji.Ta girgiza kai cikin hawaye tace nidai kimun alkawari domin bana son rayuwarki ta shiga irin yanayin da tawa rayuwar ta shiga, ki mun alkawari zaki dinga mun addu’ah a ko wace sallahr da zakiyi.Adda bazaki mutu ba, cuta ai ba mutuwa bane.Fateema kirjina ciwo yakeyi sosai.Kuma fateema ta fashe da shi da sauri ta fita daga dakin, harta da mama rabi da dada duka hawaye sukeyi domin yanayin jikin Ameenan abun tsoro ne abun daga hankali ne.Sai data koma bacci tukun dada da mama rabi suka fito waje, anan ne dada ta titsiye mama rabi kan zancen da taji fateema nayi a office din likita, babu damar tayi mata karya shiyasa ta warware mata komai ai kuwa ran tsohuwa ya baci sosai don ta inda take shiga ba tanan take fita ba, ita dada a matsayin uba take a gurin su mama rabi domin da da baban ita dadan da kuma mamar mahaifinsu mama rabi uwa daya uba daya suke auren dangi ne akayi musu.Dada fa ta dau zafi sosai cewa ma take a Kira Mata rukkayar zata ji dame take takama ne da zata hargitsawa yarinya tunani ta kasa daukar kaddara, dakyar mama rabi ta shawo kanta akan zuwa anjima zata kira mata ita. Dada taja kwafa ta koma ta zauna a kujerun da aka tanada a gurin. Duk fateema na jin su amma ita yanzu babban burinta kawai taga addanta ta samu lafiya.Ai kuwa dada bata manta da batun kiran da tace ayiwa inna ba, mama rabi ta kirata ko bari su gaisa ma dada batayi ba ta amshe wayar daga hannun mama rabi tace ina fatan hankalinki guda ko? Ta yadda zan san kina fahimtar abunda zan fada.Da sauri inna tace sannu dada ina yini ya aiki.Time gaisuwarki rukayya, domin ba shi nake bukata ba, wai shin rukayya ina hankali da tunaninki ya tafi kike neman ki halaka diyar da kika haifa da cikin ki saboda kawai Allah ya jarrabeta meyasa baza ki karbi kaddara ba toh kul dinki kada na sake jin kin furtawa wannan yarinyar kalmar da zata tashi hankalinta.Dada ita Ameenar ce tace miki na fada mata wani abu?.Oho miki tunda baza ki san menene abu mai kyau a gareki da iyalinki ba.Dada Ko fahimceni nifa ba wani abu nace mata ba kawai fa cewa nayi ni a halin yanzu na tsaneta bana jin soyayyarta kamar sauran ‘ya’yana kuma fa…..Ke dalla rufe mun baki ashe baki da wayo ban sani ba rukayya? Ta tabbata dai kece kike son ganin bayan ‘yarki.. A semtata har kina fada mun abunda kika fada mata ba tare da fargabar komi ba, toh ki sani yanzu haka Ameenatu tana kwance a gadon asibiti kuma a sanadiyyar kalamanki don haka ki rubuta ki ajiye wallahi idan ta mutu saina daure ki domin ke zan daurawa alhakin kisan.Toh ni me nayi kuma dada? Kuskure tayi kuma nake kokarin nuna mata kuskuren ta..Hum shashasha haka ake nuna wa mutum yayi kuskure halan? Kin dai ji kunya kuma wallahi tun wuri ki gyara idan kuma ba haka ba ki kuka da kanki. Daga haka ta kashe wayar ta mikawa mama rabi tana fadin, ni dai bansan irin halin rukayya ba wallahi sam.Dada ai komai sai hakuri kawai.Yau Ameena ta samu sauki sosai har ta tashima ta dan zaga tare da fateema kuma sosai taji dadin jikinta sai da ta gaji kamin suka komo dakin da suke da gado, basu tarar da mama rabi ba taje ta wanke plates din da aka ci abinci dasu. Suna zama wayar fateema tayi kara, koda ta duba baba malam ne mai kiran ai kuwa cikin zumudi da zakuwa ta daga wayar tana gaishe shi bayan tayi sallama.Ya Amsa Yana tambayar ta mai jiki tace da sauki sosai baba alhamdulillah, toh masha Allah Allah ya kara afuwa tana ina?.Gata nan baba. Ta fada tana mikawa Ameena wayar ta karba tana cewa baba ina yini.Lafiya Ameenatu ya jikin.Alhamdulillah baba da sauki.Allah ya kara miki lafiya diyata.Ameen baba, dan Allah ka kara tayani baiwa inna hakuri wallahi ina cutuwa da rashin walwalarta gareni.Kada ki damu kedai ki cire duk wata damuwa a ranki komai zai zama tarihi. Allah ya muku albarka ki kula da shan maganin ki kinji ko.Toh baba..Suka ajiye wayar dukkan su cikin jin kewar juna.Ba’a dau lokaci ba wayar inna ta shigo, fateema na gani tayi saurin dauka ta fita waje son sam bata son abunda zai tayar wada addanta da hankali.Assalamu alaikum ina yini inna.lafiya ta fada a dakile kana ta dora da cewa wato har nayi lalacewar da zaku kai karata gun dada? A zatonku ta mun me? Ta dake ni kuke so ko ta tsine mun?Wallahi inna babu wanda ya fada mata wani abu domin ma ko maganar bata hada mu ba.Idan ke maganar bata hada kuba ita waccar isassar ai ta fada mata domin tasa Rabi’iatu ta kirani ta karbi wayar taci mutumcina sosai.Wallahi inna adda bata san komai ba don bata ma da lafiya Allah.Ki mun shiru ko in saba miki don yadda nike jin raina na tafasan nan komai ma zai iya faruwa……. *EESHERT ADAMU* *MATAR MAJEEDADI* ✍️

Back to top button