Hausa novels

Haihuwa Da Hanji Page 42 Hausa Novel

Zaune kawai yake a kan couch bayanshi na jingine da jikin kujerar idanunshi a lumshe, tun da ya dawo daga Sallar isha haka yake. Wani iri yake ji lokaci lokaci ya kan buɗe idanu ya kalli kofan ko za ta shigo amma shiru babu ita ba alamunta, sai wuraren sha biyu ya miƙe ya ɗan yi shirye-shiryen shi na bacci ya koma gado ya kwanta sai ya tsinci kanshi da kallon wurin da take kwanciya a kwana biyun yadda inuwarta ke yi, irin rikicewar da tayi ta rungumeshi a daren jiya hannayenta na yawo a cikin sumanshi da bayan wuyanshi ya tabbatar da ana lafiya ne ba za ta taɓa iya hakan ba, sai yaji emptiness da ya rasa na menene, da kyar yayi bacci bayan ya yi overdosing magungunanshi.Ta ɓangaren ta tana so taje ɗakin amma tana tsoro, kila bai huce ba kar taje kuma ya hau ta da faɗa ko ya make ta, haka ta shirya ta kwanta a kan gadonta sai ta dinga tunanin moment ɗinsu na jiya sautin numfashinshi na dawo mata har heart ɗinta na racing a haka bacci ya ɗauketa.Karfe goma na safen Washegari ta fito a shirye cikin half boubou da skirt na lace cream colour da mix of dark pink yayi mata kyau sossai ta yafa pink gyale bayan dan kunne da wani zoben gwal dake yatsanta bata wani saka acessories ba ta fito zuwa babban kitchen ta karbi abincin su ta kai ta shirya a dining kan ta koma wurinsu jannah da Uncle ya kira mijinta ya zo ya dauƙeta yau duk su mama ma yau za su koma gidajensu.Shi kam tun da ya dawo Sallar asuba bacci bai ɗauke shi ba yana zaune kan kujera inda kaman nan ne wurin zamanshi a ɗakin, as usual idanunshi a rufe ruf bai motsa ba har sai da Abeeha ta kira shi a waya akan su Mama za su koma gidajensu ya miƙe ya fito suka sake mishi gaisuwa da ban haƙuri kan suka tafi bayan sun raka su har waje, ya kalleta amma bai tsawalla kallon ba don haushin ta har lokacin yake ji barin ma da ya kalli yadda idanunta suka zama saboda kukan da tayi jiya Dukda ba kowa zai lura ba amma shi with a single gaze ya fahimci lids ɗin are swelled up a little.Bai koma ciki ba motar Sulaiman ya shigo gidan sai suka isa kan kujerun da aka shirya don hutawa a chan gefen gidan suka zauna.”Ya dai? Na ga kaman ranka a ɓace sossai?”Sulaiman yayi tambayar don a hankali Sulaiman ɗin yayi mugun karantar shi har ma ya zama kaman Saleem a wurinshi ɗan zaman da suka yi daga aurenshi zuwa yanzu rasuwar Mammi.”Hakane am just worried sick about one or two things.”Sulaiman ya gyara zama “Toh fa, menene kuma?”Nan ya bashi labarin duk abin da ya faru Sulaiman sai yayi murmushi “Are you jealous?””Menene hakan?”Yayi tambayar kaman bai san me ake nufi da kishi ba.”Rayyan kana kishin Afeefah ne sossai kayi adu’ar sassaucin zafin kishi, anan dai zan baka laifi Saleem ko da bai auri Afeefah ba kaman Yaya yake a wurinta sannan Saleem yana da fahimta am very sure bai san reasons naka bane yasa ranshi ya ɓaci, shima fa mutum ne kaman kai yana da zuciya a kirji, your words are harsh gaskiya kenan..”Ya gyaɗa kai “I know, tun jiyan i wanted to call him amma sai na bari ya huce tukuna. I just lost control tunda ta furta wai aurena kaddara ne kalaman sun min zafi”Dariya Sulaiman ya fara “Kana wasa da So Surgeon General Ryan Khamis, kuma fa babu wani abin zafi a maganan nan kishi ne kawai irin naka… Ai komai ma mukaddari ne daga Allah ta wani mawaki yace Nufin Allah ne! Haɗin Allah ne ko da basa so su gani sai anyi! Ka ga kenan dole da kaddara a komai. I’am advicing kaje ka samu Saleem ku yi resolving issue ɗin nan””Kai! ka fa dameni da zancen kishin nan idan ma kishin ne ai ban yi laifi ba a gaban ka na cire kuɗina na biya sadaki!”Yayi maganan da iyakan gaskiyarshi yana sake kame fuska Sulaiman yana ta dariya.Basu jima ba ya wuce, shima ya shiga ya zari key bai ko bi ta kan abin kari ba ya fice daga gidan kai tsaye gidan su Saleem ɗin ya tafi, bai shiga ciki ba ya kirashi a waya akan yana waje mintuna kaɗan sai ga Saleem ɗin ya zo ya buɗe kofan motar ya shiga ya zauna ba tare da ya ce komai ba.”Ka tashi lafiya?”Rayyan ɗin ya faɗa, bai jira amsar Saleem ba ya ɗora da.”Na zo ne in baka haƙuri akan abin da ya faru tsakaninmu we are not perfect in everything sannan a zaman tare dole watarana a saɓa. A koyaushe kai ke haƙuri da ni I really respect and appreciate you Saleem kuma ka fi karfin duk abinda kake zato a gareni! Saleem…Billahi ban ɓoye maka wanzuwar Afeefah a gidanmu saboda son zuciya ko wata soyayya ba don har yanzu ban sani ba shin ina sonta ko ba na sonta na dai san ban tsane ta ba”Ya ɗan yi shiru kadan kan ya cigaba “A lokacin da muke waya da kai akan Mommy ta kore ta na ganta amma ban zaci saboda kora ne take tsaye a kan titi ba, jin irin damuwar da ka shiga ya sa nayi deciding in koma in ɗauko ta kafin ka samu masalaha da mahaifiyarka, ko da na koma ban sameta ba a sannan aka kira ni ba’a ga Mammi ba cikin damuwar rashin ganinta na tafi asibiti ka san halina farin sani damuwa na ba komai bane illa kar a samu wasu su cuceta ko su zalunce ta sanin bata san gari ba. ko da na isa asibitin sai na samu ashe ita ce ta taimaki Mammi, from there Mammi ta fara ƙaunarta har ta mayar da ita gida ba tare da na ce musu komai akan labarinta ba Dukda na san Mammi da su Abeeha amma ba zan so ta samu matsala a gidan yadda ta samu a naku ba, nayi tunanin faɗa maka sau ba adadi ina tsoron saka ka cikin wani damuwar don na san in har ka san inda take ba lallai ka cigaba da yiwa mahaifiyarka biyayya ba, zai iya zama ka saɓa umarnin ta saboda mace ko kuma shaidan ya ja ka ga fushintan ta hanyar yarinyar, na bari akan daga baya idan kayi settling komai sai na faɗa maka. Unfortunately abun nan ya zo ya faru tsakaninka da ex wife ɗin ka da i even called her name to your ears ka nuna baka santa ba kana da mata…”Daga nan ya bashi labarin duk yadda aka ɗaura aurensu da Afeefah.”Na karɓi auren ne saboda Mammi Dukda ta rokeni ya zama saboda Allah zan yi wa Afeefah komai ko da bata nan zata samu peace of mind na cewa ta barta inda ba zata wulaƙanta ba, na san Afeefah ce tayi adu’o’in duk da kake using na seven days a gidan mu ban damu ba saboda na san ka cancanci fiye da hakan daga gareta, ko da ka samu lafiya kafin mu yi maganan Allah ya kawo ajalin Mammi… Wallahi idan da za ta zaɓe ka Saleem ta tabbatar min za tayi farin ciki a tare da kai zan iya sakinta ka aureta… Saboda burin Mammi shine ta samu farin ciki da natsuwa a duk rayuwar da zata yi. I am terribly sorry da kalamaina na jiya i hope you forgive and forget ban san me ya hau kaina ba.”Ya sauƙe numfashin wahala don ya gaji matuƙa da maganan, Saleem ya ɗauki ruwa dake tsakiyar su ya buɗe mishi ya miƙa mishi sai ya karɓa ya kurba kaɗan ya mayar mishi sai suka ɗan murmusa.”Kishi ne ya hau kanka ba komai ba””Ana kishi haka siddan ne? Dazu Sulaiman ya gama ranting about that!”Saleem yayi dariya yace “Lallai kai sabon shiga ne, ai ba’a kishi babu So irin nakan nan ma mai zafi ne ƙanwata ta ma zuciyarnan dabaibayi ba zaka farga ba sai ka gama zurmawa saura mu saka ƙasa kawai mu binne”Murmushi mai sauti Ryan yayi bai ce komai ba. Saleem ya dube shi yana sauƙe numfashi “A haƙiƙanin gaskiya nima a sadda na dawo na kwana da tunanin actions ɗina na jiya, kawai na saka a raina cewa ban samu labarin bane ta yadda ya dace hakan ya haddasa saɓanin da muka samu. Tun a jiyan tun da na fita daga gidanku na riga da na sakawa raina har Abada Afeefah matsayin ta ɗaya da su Samha a gareni, ban san wani irin rabo bane ya haɗa ku ban san me Mammi ta hanga ba ta haɗa ku but i believe har karshen rayuwarku Afeefah ba zata yi kuka da kai ba muddin ta iya tafiyar da kai! Menene burina dama?”Ya ɗan ja numfashi “Burina ɗaya da Mammi shine ta samu rayuwa mai kyau and am very sure tunda ta karɓi auren take zaune lafiya she accept it with all her heart and soul to na me zan damu? Abeeha… She’s so brave kalaman ta sun shigeni sossai da sossai am also sorry for what happened Ina yi muku Fatan alkhairi i also hope and prays za ka bani daman zama ɗan uwan da ba ta da shi a rayuwarta”Murmushi Ryan yayi ya ɗago ya kalleshi “Anya zan amince? ai sai ku haɗe min kai Thats the role that Sulaiman is playing fah”Saleem yayi dariya.Kallon gidan Ryan yayi “Why are you guys still here ba ku takura ba?”Saleem ya ɗan yi tsaki yana sake kallon gidan shima “Mun takura fa kawai rasuwar nan shi yayi delaying ɗina da yanzu mun koma Nan gidannan nawa na Malali already an gama komai maybe gobe we move out”Kai ya gyaɗa suka sake hira kaɗan a kan aiki kan suka sallami juna Rayyan ya fice Saleem ya koma ciki hankali kwance.Ya dauki hanyar unguwar su kenan aka kira shi a waya ya duba ya ga uncle Musa ne, dagawa yayi cikin ladabi suka gaisa “Ina so dama na ganka ne Ryan idan ka samu dama ko yanzu ka zo.””In shaa Allahu Baba gani nan zuwa”Juya motar yayi ya nufi Unguwar sarki inda nan ne gidan uncle musan yake.Yana zuwa ma ana kiran azahar yayi alwala suka shiga masallacin tare suka yi sallah kan suka dawo ciki, an kawo mishi abincin rana don haka a tare suka ci kan uncle Musa ya dube shi “Ryan ka san idan mamaci ya mutu ana so a yi gaggawar sauƙe mishi duk wani nauyi har gado, Toh zaman dai ya kamata mu yi da Abeeha da jannah ne amma sanin kana gaba da su kuma kai uba ne a gare su yasa na fara kiran ka, wannan takardu”Ya miƙa mishi ya karɓa yana dubawa Dukda komai na Mammi ya sani, haka komai na su Abeeha da jannah na wurin babansu dake hannunshi wanda Mammi ta sakar mishi yake kula musu da shi duk ya sani.”Mamanka ta ce in tabbatar maka ita ta baka halak malak har abada baya cikin abinda za’araba nata”Da sauri ya kalli Uncle Musa.”Rabin dukiyar ta ne fa anan””Eh, ta saka hannu zaka gani lawyer ɗinta ya saka akwai kuma shaidu akan hakan. Ta mallaka maka rabin abinda ta mallaka wanda gado ne daga wurin mahaifinta kyauta”Dukda arziki baya gabanshi kyautar ya kaɗa shi sai yana jin sabuwar Soyayya da kuma tsananin kewa na Mammin, idanunshi suka sauya sossai ya kalli uncle da ya sake cewa “Wannan kuma sauran rabin abinda ta mallaka ne na su jannah shima ta ce ne in bari a hannunka kai zaka zauna da su idan suna bukata ka basu idan sun bar maka ajiya ta tabbatar za ka juya musu yadda ya kamata”Karɓa yayi yana jin wani iri sossai da sossai. Da kyar ya haɗa natsuwar shi wuri guda yayi godiya wa uncle ɗin kan ya fice daga gidan ya nufo gida.Yana parking wayanshi ya ɗauki ringing ganin ogansu ne yasa yayi picking tare da saluting maganan mintuna biyar suka yi ya sauke wayan tare da bude media group dinsu, news dake yawo ya zubawa idanu sama da mintuna goma ba tare da ya sani ba kan yayi baya baya ya jingina da kujera wani irin abu na tsaya mishi a tsakiyar zuciya, sossai news din ya jijjigashi amma yana iya kokarinshi wurin ganin ya danne don in ka kula har jikinshi rawa yake sai lumshe ido yake yana buɗewa lip dinshi na ƙasa a ɗan datse tsakankanin hakwaranshi.Sai da ya gaji ya buɗe murfin motar ya fita ya nufi cikin gida, a babban parlor ya samu jannah da Abeeha suna zaune shima ya zauna suka gaishe shi ya amsa da kulawa ya dubi jannah “Yaushe kike shirin komawa ne kam?””Dama yau ne to kuma ya tafi Abuja ɗazu yace in zauna kawai gobe zai dawo in ya dawo zai biyo ya daukeni sai mu wuce gida”Cikin girmamawa tayi magana. Ya gyaɗa kaiNan ya musu bayanin gadon su tare da fitar da papers ɗin ya ajiye.Abeeha tace “Ni dai Yaya bana bukatar rike komai a hannuna gaskiya, babu abinda ka rage mu dashi ko da Mammi ke raye baka barta ta mana komai da kuɗinta ba don haka ka haɗa duka ka riƙe a wurinka kawai.”Jannah ma tace “Gaskiya nima dai babu abinda zan yi dashi a yanzu, kana min ko da nayi aure baka daina ba shima kuma bai rageni da komai ba for now ka bar wannan a hannunka yaya”Kai ya gyaɗa ya dubi Abeeha “Gobe zan tafi wani aiki chan Gabas maso yammacin ƙasar nan ban san adadin kwanakin da zan yi ba don haka ki duba ki rubutu duk abinda za ku bukata da safe zan kaiku shopping sai a saya”Godiya ta mishi da Adu’a. Ya miƙe ya nufi sashensu.Afeefah na zaune shiru cike da tunaninshi, bai karya ba hakan ya dameta sossai har take jin babu daaɗi sai tunani take ko ina ya je? Ko yana lafiya? Tsoronta ma ya sha magani? Kar zazzabi ya dawo mishi yana ta yawo a rana duk ita kaɗai dai ta yanke dole zata bashi hakuri ta kuma fahimtar da shi ba da wani manufa ta aikata abinda ta aikata ba.Ta miƙe zata fita wurin su Abeeha kenan shi kuma ya shigo, kallo ɗaya ya mata ya ɗan ɗauke kai sai yayi sallama yadda zata ji ta amsa tare da cewa “Sannu da dawowa Ya Saraki”Ya ɗan lumshe ido ya buɗe kan ya ce”Yauwa”Daga haka ya wuceta ya nufi ɗakin shi bai bata daman magana ba kenan har yanzu fushi yake, jiki a sanyaye ta fice wurin su Abeehar anan take jin labarin wai zai tafi wani Assignment gobe ba lallai ya dawo kusa ba jikinta ya sake yin sanyi ƙwarai har bayan Magrib bata san me zata yi ba, luckily ko da ta ajiye mishi abincin dare ya ci.Bayan tayi isha ta gama shiryawa cikin cotton Light blue riga da wando dogo na kayan bacci ta ɗora navy blue hijabinta har ƙasa ta nufi ɗakinshi don ta yanke zuwa kawai ta bashi hakuri kar ya tafi yana fushi da ita.

Back to top button