Hausa novels

Asanadin Makwabtaka Book 2 Page 68 Complete Novel

*ASM Bk2068*

 

 

 

~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~

 

 

 

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

 

 

 

………Har tuntu6e take yi tsabar sauri, tana zuwa part d’in su ta shiga parlor ta wuce Bedroom, tana shiga ta maida kopa ta k’ulle harda saka Key ta juya da gudu ta nufi gado ta Fad’a sai faman numfarfashi take ta zaro ido hannuwan ta har d’an kerma suke sai tuno abunda ya faru take Fuskar Hajiya Maryam na mata gizo, tafin hannunta ta kai ta rufe baki tasa Kuka, Sosae Senator yaji Fatuu ta burge shi da Hajiya na bashi Labarin ta da Haisam Fuskar shi d’auke da Murmushi, suna nan har aka yi La’asar ya tashi don yaje Masallaci yace mata daga can zai wuce G.r.a ya d’an huta, fuskar ta da murmushi tace to ba ga d’akinta ba in ya dawo ya kwanta ya huta yana dariya yace mata to ta bari zai zo ya kwana akan gadon nata itama dariyar take ta mik’e don taje tayi sallar itama, Lokacin da ta shiga cikin d’akin nata anan ta iske Hajiya Maryam aciki pacing up and down sam ta kasa zama tun d’azu abunda take kenan, sai ta zauna sai ta mik’e ranta a tsananin 6ace, Hajiya na shigowa suka had’a ido da ita ba tare data ce mata komai ba ta nufi hanyar toilet, Alwala tayo ta fito ta nufi cikin d’akin, saida ta shimfid’a abun salla sannan ta kai idonta kan Hajiya Maryam da ta zauna a bakin gado k’afar ta d’aya akan d’aya idon ta na kallon wuri guda ta cije le6en ta na k’asa tana d’an jinjina kai, ce mata tay bata ji an kira salla bane ba tare data kalle ta ba tace taji zatayi, saida Hajiya ta fara yin Salla sannan ta mik’e ta nufi Toilet, ita ta fara tashi bayan sun gama ta cire Hijab d’in jikinta ta aje a gefen gado ta koma ta zauna kaman yadda take d’azun sai faman d’an jijjiga jiki take tsananin bacin rai kwance akan fuskar ta, bayan Hajiya ta shafa Addu’a ta juyo ta kalleta na d’an wani lokaci ta d’an girgiza kai, tasan halin ta tana da d’aukar zafi sosae sam bata 6oye fushi,

 

a nutse ta fara mata magana “Yanzu Maryam abunda kika aikata ma Yarinyar nan daidai ne, ita miye laifin ta a ciki ne, kusan fa ita akai ma ba daidai ba ma, an aureta bada sanin ta ba kuma sannan yazo ya hakke mata tunda ita bata san da ya aureta ba abu ya kai ga har da samun ciki yazo kuma ya 6are wanda hakan yasa ta a mawuyacin hali, in rai ya 6aci ai bai kamata hankali ya gushe ba sai a bi komai a sannu asa tunani, komai ki ka ga ya faru to dama can haka Allah ya k’addara, don haka sai mu d’auka dama Allah ya k’addaro Aure tsakanin su” Tunda Hajiyar ta fara Magana bata juyo ta kalleta ba sai da tay Maganar k’arshe sannan ta juya a zafafe tace “Pls Hajjaju stop saying that, komai sai ace kaddara, Yes an san komae sai Allah ya amince yake Faruwa amman harda sa kai, don uban shi in son taimaka mata yake ai akwae hanyoyi da yawa da zai yi hakan, Why not yayi amfani da kud’i akwai abunda basu yi bane balle kuma su da suke yan k’auye ma tuni zai sa a fasa yi mata auren in yay amfani dasu, kuma ma wai miye nashi na damuwa da wanda zata auran kowa ai da kalar k’addarar sa, watak’il in ta aure shi ya canza amman Saboda ya isa da kan shi shine yay gaban kan shi shiga isasshe ko, to zamu nuna mashi haihuwar shi akai ba a komae yake da iko da kan shi ba” tana huci ta k’arasa Maganar, d’an guntun murmushi Hajiya tay “kinga dae kenan Magana ta na kan hanya, kince kowa da kaddarar sa to suma hakan kaddarar su ce kenan shiyasa komai ya juye hakan sai kowa ya rungumi Al’amarin a matsayin hakan” wani kallo take bin Hajiya dashi ta yamutsa fuska cikin k’unar rai tace “Hajjaju na fahimci goya mashi baya kike shiyasa ma har ya samu k’warin gwuiwar cigaba da zama da ita, haba! ta ya zaki goyi bayan wannan kaskantaccen Auren, Auren wulakanci, in ma k’ara Auren zai yi ai wannan ba class d’in shi bace wllh, kuma ba kowa za’a wulakanta ba face Fanan taya ma za’a had’a ta kishi da wancan abun” sai huci take tayi mitsi mitsi da idanu, d’an murmushi Hajiya tay idonta akanta tace mata ba mace bace ita Fateemar kuma miye aibunta, d’an jim tay fuska a yamutse tana ma Hajiya kallo irin na baka zaci jin Magana daga bakin mutum ba,

 

“Hajjaju wato na lura dae kin za6i faranta ma bare fiye da naki ko, kin sani matuk’ar auren nan aka ce ya d’ore ba wanda zai cutu irin Fanan, don Allah duka yaushe aka yi auren nasu da za’a ce har an yi mata kishiya, da mi zata ji ne da damuwar lalurar dake tare da ita ko kuwa da wannan damuwar da ake neman k’ara mata, wai ko don cikin da ta samu ne yasa kike goyon bayan auren, Saboda ance Fanan nada lalura ai ba yana nufin bazata haihu ba, tunda anata kokarin nema mata magani sai a bari zuwa wani lokaci aga in bata haihu ba sannan ai tunanin auro wata, kuma shi in ba don ya nuna irin halin nasu na maza ba da ba yan goyo bane ba har alk’awari yayi mata zai zauna da ita a halin da take ciki koda kuwa bata haihu ba shine tun ba’a je ko ina ba zai watsa mata k’asa a ido ya nemi tarwatsa mata zuciya wato ta mutu ma shi ba damuwar shi bane, to wllh bazan zuba ido ta cutu ba Saboda wata kaskantatta can” tana kaiwa k’arshen Maganar ta kai hannu ta warto wayar ta ta mik’e, har ta nufi hanyar k’opa sai kuma ta dakata ta juyo ta kalli Hajiya data bita da ido ta d’an sassauta d’aure fuskar da tay tace mata sun gama Maganar zata fita, d’an murmushi Hajiya tay ta sani duk irin zafin zuciyar ta mai d’a’a ce a gareta yanzu ma tasan Saboda tsoron abunda zai iya faruwa da Fanan yasa ta zauna tana ta mata Magana cikin 6acin rai kuma bata d’auki hakan a wani abu ba don ta san yadda soyayyar d’a da Mahaifi take, kai ta d’aga mata alamar sun gaman ta juya ta nufi kofa, cikin nuna ma kopar k’arfi ta bud’eta ta fuce,

 

Kuka Fatuu tasha har ta gaji tay shiru don kanta, kiran sallar la’asar ya tada ita taje tayo Alwala tazo ta kabbara salla, bayan ta gama zaune tay kan abun sallar ta langa6ar da kanta jikin gado ta shiga duniyar tunani. Hajiya Maryam na fitowa daga d’akin Hajiya Visitor room ta nufa, tana shiga ta d’aga wayarta tana k’ok’arin yin kira ba tare data zauna ba, d’an kai da komowa ta fara lokacin da wayar da ta kira ta fara ringing , Haisam zaune kan kujera a cikin d’akin da yake aikin injiniyancin shi kira ya shigo wayar shi, hannu ya kai saman desk d’in gaban shi ya d’aukko wayar, bin screen d’in yayi da ido ganin mai kiran lokaci guda ya yanke ba lafiya tasa ta kira shi ba ba kamar da yake dare ne kuma yasan tasan lokacin da suke ciki, shima abu ne ya ishe shi bacci ya k’aurace mashi yasa shi zuwa wurin yay zaune yayin da Fanan ke d’aki tana bacci, saida kiran ya kusa yankewa yay picking ya kai wayar kunne, sallama yayi mata tayi mashi banza cikin cool voice d’in shi ya gaida ita aikuwa kaman tana jira a fusace tace “Ka rik’e gaisuwar ka ban so, ai bamu da girman da zaka gaishe da ni tunda kai isashshe ne ka kai kayi gaban kanka, ashe Haisam baka da Mutunci ban sani ba! mu zaka wulakanta ka nuna bamu kai ba a wurin ka, kai ka Haifi kan ka ne ko mu muka haife ka da har zakai Aure ba tare da sanin mu ba, da izinin wa kaje kai auren???” Shiru yay bai da niyyar tanka mata aikuwa hakan ya k’ara hasala ta cikin daka tsawa tace “bazaka bud’e baki kai man Magana ba don ubanka” d’an lumshe ido yay ya bud’e, in ba ya manta ba tunda yake ba’a ta6a zagin shi haka ba, slowly ya bata hak’uri yace yayi ne don taimako, a fusace tace “then what are u waiting for da baka saketa ba kaman yadda kuka tsaran? Mi ya zaunar da ita” shirun ya k’ara yi saida tace bai jita bane sannan yace “Hajiya ce ta hana”

 

“Hajiya ce zata zauna da ita ko kai” d’an jimm yay sai kuma yace “I can’t argue with her” shiru tay cikin ranta ta fara tunanin kenan ba don Hajiya ba zai saki yarinyar ne, d’an sassauta murya tay tace mashi shikenan zata yi Magana da Hajiyar he should be expecting her call kowane lokaci don ya saki Yarinyar, amsa mata yay da toh tace tasan Fanan bata sani ba to Kada ya sake ya bari ta samu labarin har zuwa lokacin da zai sake ta nan ma da toh ya amsa mata tay mashi sai da Safe ta kashe Wayar, bin wayar yay da kallo tun bayan daya cireta daga kunnan shi, can yay sigh ya fara latsa ta na d’an wani lokaci ya dakata ya zuba ma Screen ido kaman mai kallon wani abu…,

 

tana ta zaune a wurin cikin duniyar tunani, a hankali take kai hannu tana goge yar kwallan dake zubo mata daga cikin idanuwan ta da har sun d’an kumbura, wayar tace ta fara ringing ta d’aga kai ta kallo ta a saman gadon, ganin zata iya jawo ta yasa ta kai hannu ta jawo tan ta kalli screen d’in, Abbas ne mai kiran nata har saida ta d’an ji sanyi dama duk yau bai kirata ba, d’aga kiran tay ta kara wayar a kunne muryar ta can k’asa tay mashi sallama, bayan ya amsa ta gaishe dashi ya amsa daga haka tay shiru, jin yanayin muryar ta yasa shi tambayar ta lafiya nan ma tayi shiru, ce mata yay ta fad’a mashi inda matsala cikin rawar murya ta fara fad’i mashi duk abunda ya faru, sosae Muryar Abbas ta bayyana rashin jin dad’in abunda ya farun ya shiga bata hak’uri daga baya ya tambaye ta game da reaction d’in Senator nan ta gaya mashi komae tana gamawa ya furta “Alhamdulillah, dama nasan ta 6angaren shi ba za’a samu wata matsala ba, itama Momy Maryam d’in kawae tana taya d’iyar ta kishi ne ba wani abu ba, so kar kisa damuwa a ranki in sha Allah komai zai daidai ta na d’an lokaci kad’an ne” a hankali ta amsa mashi da to,

“Yanzu kin ci Abincin ne?” D’an girgiza kai tay tace mashi a’a,

“Ya zaki sa damuwa har ta hana ki cin Abinci hakan ai sai wani ciwon ya kama ki, ba wani Abincin da zaki ci ne?” bashi amsa tay da eh tace amman bari taje ta dafa indomie yace ta d’an jira ba sai ta dafa ba, har zai cutting kiran sai kuma taji yace bata tambaye shi Mijin ta ba, tura baki tay kaman ya gani yay yar dariya yace koda yake ai yanzu tafi shi kusa da shi daga haka ya katse, wayar na ruk’e a hannunta ta maida kan ta jingina da gadon kaman yadda take ada ta runtse idanu ta sake fad’awa duniyar tunani wanda duk na Haisam ne, gama wayar su da Abbas bada jimawa ba aka k’wank’wasa kopa ta bud’e idanunta ta kallo kopar zuciyar ta na harbawa da sauri da sauri, mik’ewa tay a d’arare ta nufe ta hannun ta har yar rawa yake da zata bud’e, tana bud’ewa suka had’a ido da Saude tana mata murmushi itama ta k’ak’alo d’an murmushin tayi mata a sanyaye ta gaishe da ita, hannu ta kai ta kamo hannunta guda suka nufo cikin parlon, akan kujera ta zaunar da ita itama ta zauna nan ta fara lallashin ta tace ita bata ma san abunda ke Faruwa ba don tana baya sai yanzu da aka kira ta a waya ai da tun d’azun ta kawo mata Abincin kuma itama ai data kirata sai tazo ta kawo mata amman zama da yunwar ga damuwa ai sai suyi mata illa, tasata gaba Saude tay saida tasa taci Abincin sosae daga baya ta k’ara kwantar mata da hankali kafin ta tafi. Bayan Hajiya Maryam ta yi waya da Haisam a bakin gadon cikin d’akin ta zauna hannunta ruk’e da wayar ta d’aura ha6arta saman shi, tunanin ta yadda zata 6ullo ma Hajiya har ta amince a saki Fatuu ta shiga yi, ta d’an d’auki lokaci a haka kafin ta idasa hayewa saman gadon ta kwanta da tunanin zata yi mata Magana anjima. Da daddare bayan kowa yayi shirin kwanciya Hajiya Maryam ta nufi d’akin Hajiya ta shiga da sallama Hajiya dake zaune a bakin gado sanye da kayan bacci idanunta na sanye cikin glasses tana duba wayarta ta amsa mata ta nufo ta, a bakin gadon daga d’an gefe ta zauna tayi mata sannu da hutawa da d’an murmushi Hajiya data d’ago kai ta amsa mata, shiru suka d’an yi Hajiyar ta maida idon ta akan Wayar ita kuma tana kallon k’asa, juyowa tay ta kalli Hajiya tace mata dama Magana take son su yi ne ta d’ago tare da jinjina mata kai idonta a kanta alamar ita take jira,

 

“Mun yi Magana da Haisam ya fad’a man ke kika hana ya saki Yarinyar can, kinga kenan shima ba wai son zaman yake da ita ba kawai yayi maki biyayya ne don haka ni ina ganin tunda shine mai zama da ita kuma ba so yake ba sai ki bashi dama ya rabu da ita hankalin kowa ya kwanta” d’an murmushin dattako Hajiyar tay jin abunda aka ce Haisam d’in yace, gyara zaman glass d’inta tay idonta akan Hajiya Maryam a nutse ta fara magana “Kaman yadda kika ce biyayya yay man yaci gaba da zama da ita to kema ina son kiman biyayya ki bi yadda nike so, ki yi masu Fatan Alkhairi a auren shikenan komai ya wuce” wani kallo take bin ta dashi baki bud’e alamar Al’ajabin Maganar tata rai 6ace tace “to wai Hajjaju akan mi zaki mashi dole ya zauna da ita ne, ya aureta don taimako da nufin zai saketa sai a sa ya saketan barin shi ya ci gaba da zama da ita ba komai zai ja ba sai 6acin rai” girgiza kai Hajiya ta fara yi “Ba zai rabu da ita ba Maryam dole yaci gaba da zama da ita, in kece ko Fanan a matsayin ta bazan so abunda kike so mata ba” ta k’are Maganar tana girgiza kai bakinta a kwa6e, yarfa hannu tay ta yamutsa fuska tamkar zata saka kuka cikin breaking voice tace “Wai Hajjaju ya kika za6i faranta ma bare ne fiye da naki, kin san idan Fanan ta samu labarin nan ba K’aramin mawuyacin hali zata shiga ba, dame zata ji don Allah ko so kike zuciyarta tay bursting ne, sai nike ganin kaman kin fi damuwa da ita yarinyar ma fiye da Fanan, in don haihuwa ne a ba Fanan d’in time mana kaman yadda nace d’azun duka ai ba dad’ewa sukai da yin auren ba ko” shiru Hajiya ta d’anyi still idanunta na akan ta sai faman huci Hajiya Maryam din take ta gumtse baki idanunta sun Kad’a da gani kiris ya rage ta saka kuka, cikin kwantar da murya Hajiya tace “idan aka zo Maganar Adalci Maryam baka duba bare ko naka indai Adalcin tsakani da Allah za’ai, koda Fateema take 6are ai itama tana da dangi kuma suna son ta suna son farincikin ta, sannan Maganar halin da Fanan zata iya shiga ita ai Musulma ce kuma inada yak’inin tana da cikakken imani hakan kuma na nufin ta yadda da k’addara mai kyau ko akasin hakan don haka in sha Allahu ina sa ran zata rungumi hakan matsayin k’addara kaman yadda ta rungumi ta lalurar ta ake ta neman Magani” Kuka ne ya taho mata tace “Hajiya kar azo ai dana sani, na fad’i maki har Alk’awari fa yayi ma Fanan kan bazai k’ara aure ba koda bata haihu ba kuma akan hakan suke zaune in taji ya k’ara auren nan har matar ta samu ciki mi kike tunanin zai iya biyo baya don Allah, dama kuma ga yanayin ta” cewa Hajiya tay in sha Allahu ba abunda zai faru kuma tasan lokacin da yay mata Alk’awarin ya riga ya auri Fatuu ne don haka shi yasan yadda zai rarrashe ta, a k’arshe ta tabbatar mata da indai ba yarinyar ce tace bata son zama dashi ba to wllh ba zai saketa ba, mik’ewa tay zumbur ta nufi hanyar fita Hajiya na kallonta ta kwa6e fuska.

 

Bayan ta koma d’aki kai da komowa ta shiga yi ta cize baki, abun ya matuk’ar d’aure mata kai yadda Hajiya ta kafe, a tunanin ta koda cewa akai Fanan bata haihuwa kwata kwata Hajiya bazata matsa ayi mata kishiya ba tunda abun na gida ne, dogon tunani ta shiga a k’arshe zuciyarta ta bata wani tunani kan dalilin Kafewar Hajiyar, A daren Hajiya Maryam ta yanke komawa lagos a yadda take ji ba don dare yayi ba da bazata ma kwana ba, a daren tayi duk wani cuku cukun tafiya saidae ba jirgin da zai je Lagos direct washe gari sai dae Kano ta yanke tafiya Kano d’in daga can sai ta hau na Lagos, a ranar baccin ta ragagge ne Saboda tsabar 6acin rai har gani tay daren yayi mata tsawo, Washe gari tana gama sallar Asuba ta hau shiri duk da bada wuri jirgin nasu zai tashi ba, Misalin k’arfe takwas na safiyar ta kira Senator take sanar dashi zancen komawar tata, tambayar dalilin tafiyar ta a yau yayi tace mashi hakanan ta canza shawara yace da yaushe jirgin nasu zai tashi ta fad’a mashi, ce mata yay in ta shirya kafin ta wuce ta same shi a G.r.a tace to, Misalin k’arfe tara da yan mintuna ta gama shirin ta tsaf cikin wani dandatsetsen leshi ruwan Madara da fulawowi maroon da golden brown, ba K’aramin had’uwa leshin yay ba idanun kansu zasu shaida maka tsadar shi don kuwa d’an dubu d’aruruwa ne, a da tazo da shirin fita taje wasu wurare kafin ta koma, gyale da jaka da takalma maroon ta saka ta fiddo wasu sarka da yan kunne da yan hannu na zinari ta saka ta fito a babbar macen ta, tana janye da d’an madaidaicin trolley d’in kayanta ta fito, Bedroom d’in Hajiya ta wuce bayan ta tura K’opar da yar sallama ta shiga, ganin Hajiyar bata cikin d’akin yasa ta kai idon ta wurin toilet nan ta gane tana ciki ta nufi bakin gado ta zauna, bada jimawa ba ta fito idanunta suka sauka akan Hajiya Maryam d’in ta nufo gadon itama ta zauna, kallonta tay ta gaishe da ita bayan ta amsa ganin tayi shiru yasa ta tambaye ta lafiya ta ganta cikin shiri da safe ko wani wuri zata ta girgiza mata kai kafin tace zata koma ne, d’an jimm Hajiya tay sai kuma tay d’an guntun murmushi tace “an 6ata maki rai shine kikai Fushi zaki tafi kenan” shiru bata ce mata komai ba idanunta na kallon k’asa, Hajiya ta k’ara cewa “shikenan bazan hana ki tafiya ba Allah ya tsare, kin yi Breakfast ne?” Girgiza mata kai tay tace in ta isa tayi ta gyad’a kai, d’an shiru sukai can ta mik’e ta kalli Hajiyar tace ta wuce, Addu’ar Allah ya tsare ta k’ara yi mata ta kama trolley d’in ta juya, har ta kusa k’opa Hajiya ta kira sunanta ta dakata ta juyo, “Kiji tsoron Allah, Kada soyayyar d’a ta tunzura ki kice zaki cutar da yarinyar can domin duk abunda kai ma d’an wani kaima za’ai ma naka ne, idan ranki ya 6aci Kada ki bari hankalin ki ya gushe, ki d’auki Al’amarin a matsayin Alkhairi sai kiga ya kasance hakan, tada hankalin ki shi zai taimaka wurin faruwar abunda kike gudu, ki gaida man Mazajena da K’awaye na” d’an jimm tay tana kallon ta kaman bazata tafin ba can ta furta mata ta gode ta juyo tana janye da trolley d’in ta fice,

 

Itama Fatuu a jiya bata yi wani baccin kirki ba wanda ta samu yake d’aukar ta ba wani mai nauyi bane gashi cike da mafarkin abunda ya faru tsakanin ta da Hajiya Maryam, kiran sallar farko na Asuba ta farka taje tayo Alwala, bayan ta fito ta zo ta kabbara raka’atanil fajr data gama ta d’aura da karatun Al’qur’ani har lokacin sallar Asuba yayi, bayan ta gama yin sallar kwance tay akan prayer mat d’in cikin sa’a bacci ya d’auketa, Misalin k’arfe tara saura ta farka jin jikinta duk ba dad’i yasa ta tafi toilet tayo wanka, bayan ta fito ta shirya cikin riga da wando, wandon skin tight ne bak’i sai rigar ta kai mata har gwiwa tana da gajeran hannuwa jikinta bak’i da fari ne, bata sa hula ba sai gashinta dake fake yayi tumm, bayan ta gama gado ta koma ta zauna tay tsuru, tana jin yunwa amman fargabar fita take sai kawai ta kai hannu ta d’auko wayar ta daga kan Bedside drawer ta fara dannata, bata dad’e da zama ba aka k’wank’wasa kopar ranta ya bata k’ilan Saude ce amman duk da haka saida taji tsoron bud’ewa, bayan ta bud’e taga Sauden ce suka gaisa harda ce mata tayi kyau inama Angonta na nan sai yafi ganin kyaun kwalliyar yar dariya tayi tace ita ai ba wata kwalliya tayi ba, daga baya tace mata ta fito tayi Breakfast gashi can ta kawo tace to, ce mata tayi ta fito suje taci a gabanta kaman jiya tay yar dariya tace mata zata ci Allah sannan ta fito,

 

Hajiya Maryam na fitowa sukai kacibus da Saude data dawo daga part d’in su Fatuu, gaishe da ita tay ta d’aga mata kai kawai ta mik’a mata trolley d’in tace ta biyo ta dashi, suna fitowa harabar gidan tay mata nuni da parking space da hannunta tace ta kai shi can ta je ta kirawo mata Tk tace mashi ya jirata anan, amsa mata da to Saude tay ta nufi parking space d’in tana tafiya tana waiwayen ta ganin ta nufi part d’in su Fatuu, Har Fatuu taje dining area d’in ta tuna da bata d’aukko cup da sauran abunda zata buk’ata ba ta juyo ta nufi Kitchen, hannunta ruk’e da plate da tea cup da spoon a saman shi ta fito zata koma dining, tana fitowa daga corridor zatai kwanar dining area taji an turo kopar parlon da sauri ta kai idonta suka shiga cikin na Hajiya Maryam, wani mummunan Fad’uwa gaban ta yay ba shiri ta saki abun hannunta nan take cup d’in yay tsalle ya fad’o ya d’aki tile ya tarwatse, tsaye tay cak ta zaro idanu zuciyar ta na wani irin harbawa ganin yadda Hajiya Maryam d’in ke jefa mata wani kallo fuskar ta ba d’igon annuri, daurewa kawai Fatuu ke yi amman jikinta har ya fara rawa daga ta ciki a yadda take ji tamkar ta watsa da gudu ta shige d’aki, cikin parlon ta k’araso tana tafiya a k’asaice ta tsaya a tsakiyar parlon, d’an d’aga murya tay tace ma Fatun ta k’araso wurinta ne ta d’an girgiza mata kai kafin ta fara tahowa cikin parlon a d’arare, a d’an nesa da ita ta tsaya murya na d’an rawa ta gaishe da ita tay mata banza still idanun ta na akanta ba alamun sauk’i a cikin su, cike da yarinta ta Fatuu tay tunanin wai ko don bata ce mata ta zauna ba yasa tay tsaye cike da k’arfin hali tace mata ta zauna aikuwa tamkar ta watsa mata wuta ta k’ank’ance ido a fusace tace “Samun wuri! Wato Ni zaki kalla ki ce ma in zauna! daga gidan ku aka kawo kujerun ko kuwa?” Da sauri ta girgiza mata kai a hankali tace tayi hak’uri….a zafafe ta amshe “Ke zan ce ma kiyi hak’uri ki tattara ki bar gidan nan don kuwa bai dace da ke ba baki samu kar6uwa ba, idan kuwa kika k’i to kuwa kin tattaro ma kan ki abunda bazaki iya d’auka ba, in ba ganganci irin naku ba k’auyawan mutane ke ko a mafarki kin isa kiyi kishi da d’iyata balle kuma a zahiri, wato har kuna da k’warin gwuiwa har haka ko? Fad’a man Asiri kukai ma shi don yaci gaba da zama dake ko??” a rud’e Fatuu ta hau girgiza mata kai aikuwa ta daka mata wata uwar tsawa “K’arya kike! dole Asiri ku kai mashi shi da Hajiya shiyasa har ta goyi bayan yaci gaba da zama dake” kuka Fatuu ta saka tana fad’in wllh su ba Asiri sukai masu ba Hajiya ce tasa yaci gaba da zama da ita, wani kallon rashin Arzik’i take bin ta da shi tun daga sama har k’asa, ada Haushin ta take ji yanzu kuwa abun sai ya juye zuwa tsana can ta buga wani uban tsoki ta d’aga yatsa tana nunata tace “To zan baki shawara tun cikin Arzik’i ki fita daga rayuwar shi, kice baki son cigaba da zama da shi idan ko ba haka ba to rayuwar ki zaki jefa a matsala don kuwa provided that am alive d’iyata bazatai kishi da ke ba da kowa ma, idan har baki d’auki shawarata ba kika fita daga rayuwar su ta lalama ba to zaki danasanin da har ki mutu bazaki daina ba don sai na salwantar da kaskantacciyar rayuwar ki, ta yadda ko kallon gidan nan aka baki shawarar kiyi sai kin zagi wanda ya baki shawarar balle ta kai ki ga cigaba da zama a cikin shi, kinsan Asirin ma mataki mataki ne iya nauyin jakar mutum iya girman wanda za’ai mashi, if u wise enough nasan zaki abunda ya dace” daga haka ta juya, har tayi d’an taku ta dakata ta juya ta kai hannu ta ruk’e kunnanta guda ta furta “idan kunne ya ji to gangar jiki ta tsira!!!” daga haka ta nufi k’opa ta fuce, Fatuu na ganin ta fita ta juya da gudo ta nufi Bedroom, Lokacin data fito bakin part d’in su a parking space ta hango Tk tsaye jikin Mota har ya saka trolley d’in nata ciki, da yatsa tay mashi alamar ya fito da Motar ta tsaya a wurin, yana tsayar da Motar ta bud’e baya ta shiga yaja suka fita su Officer na d’aga mata hannu a K’ok’arin su na su gaishe da ita don ta saba yi masu Alheri bata ba Tk Umarnin ya tsaya ba hakan yasa ya wuce, Suna zuwa gab da gidan su Fatuu ta nuna gidan tana tambayar Tk nan ne gidan su waccan yarinyar da aka kai gidan Hajiya ko yace mata eh, Umarnin ya tsaya a gaban gidan ta bashi, bayan ya tsaya ta bud’e kopar ta fito tace mashi tana zuwa, cike da isa ta nufi gidan Tk dake kallonta ta cikin glass ya girgiza kai a fili ya furta “Allah ya kad’e fitina”, a bakin kopar shiga cikin gidan ta tsaya tana bin tsakar gidan da yake wayam ba kowa da kallo, Sallama tayi shiru ba’a amsa ba hakan yasa ta d’aga murya tace “ina masu gidan nan?” Amadu ne ya fito daga cikin d’akin shi yana sanye da jallabiya, wani kallon rashin Arziki ta bi shi dashi shima kallonta yake don ya ganeta, gaishe da ita yay bata amsa ba tace mashi ina take da alamun rashin Fahimta ya tambaye ta wa ya lura da yanayin ta kaman ba Arzik’i, “Kai da waye a gidan?” Ta tambaya ta yamutsa fuska, kafin ya bata amsa gwaggo ta fito daga cikin d’aki hannunta ruk’e da tsintsiya dama shara take shiyasa bata ji sallamar ta ba, juyawa Hajiya Maryam tay ta kalli Gwaggo data tsaya bakin k’opa tana kallon su don ta lura kaman ba lafiya ba,

 

“In k’araso ne?” Hajiya Maryam d’in ta tambaya tana kallon gwaggon shekeke, aje tsintsiyar da parker gwaggo tay ta nufo su, daga gaban Hajiyar ta tsaya da k’ak’alallen murmushi don tana kallon Fuskar ta tasan akwai matsala, gaishe da ita tay kaman bazata amsa ba sai kuma kaman an mata dole ta amsa daga haka gwaggo tayi shiru, d’an matsowa gaba tay yadda gwaggon zata jita da kyau, cikin isa ta fara Magana, “Mun ji abunda ya faru tsakanin d’an mu da jikar ki, to na zo inji cigaba da zaman su tare na minene? Taimakon ta yay to don mi zaku goyi bayan su cigaba da zama ko baku san yana da Mata bane?” Shiru gwaggo tay kanta k’asa abunda take ta fargaba game da Auren kenan don sarai tasan wacece Hajiya Maryam, cigaba tay “in dai kunsan halacci to bai kamata ku goyi baya ba, tun farko yakamata ace kun yi Magana akan ya saketa kaman yadda ku kai da shi, saidai kuma in dama akwae wata a k’asa kuna so kuyi amfani da damar don cimma wata manufa, to idan dai hakane wannan ba matsala bane ki fad’i man ko nawa kike so zan baki ta ruwan sanyi ki raba jikar ki da mijin Y’ata don bata kai tayi kishi da ita ba balle har ta zame mata matsala!” Yar ajiyar zuciya gwaggo ta sauke cikin kwantar da murya ta fara bata hak’uri tace ita wllh basu da wata manufa akan auren hasali ma itama bata goyi bayan auren ba tun da farko kawae don abun ya juye ne kuma Hajiya ta nuna tana so, a zafafe ta katseta da fad’in “tunda baki goyi baya ba sai kema ki nuna baki so, ba jikar ki bace ke kike da cikakken iko da ita!” D’an jim gwaggo tay yanayin fuskar ta ya sauya a sanyaye tace “Kiyi Hak’uri, Hajiya tana da girma ne a wuri na bazan iya musa mata ba” tamkar ta gaya mata magana taji a hasale tace “to kin mata biyayya don tana so mu kuma sauran dangi yanzu bamu so ba muyi Na’am da auren ba don haka bazamu kar6e ta ba sai ki maido abun ki in dai da gasken ba ki da wata manufa akan auren, bijire ma hakan daidai yake da bijirema Farincikin kowannan ku, zan iya k’arar da duk wani abun da na Mallaka akan bijirema hakan don kuwa ba zan ta6a zuba ido wata kaskantatta ta zama shamaki ga farincikin Y’ata, tana son Mijinta shima kuma yana son ta don haka basu buk’atar wata ta shigo rayuwar su, a shawarce sai kiyi abunda ya dace” ta k’are Maganar tana jinjina kai had’i da kanne ido,

 

ba K’aramin 6aci ran Amadu yay ba ganin yadda take ta gaya ma Mahaifiyar shi Magana daurewa kawai yake yana danne zuciyar shi, tana zuwa ga6ar data kira Fatuu da Kaskantatta yaji bai iya jurewa ya matso inda suke rai 6ace yace “Hajiya gaskiya ita ba kaskantatta bace, don tana talaka hakan ba yana nufin bata da galihu ba, a wurin Ubangiji duk d’aya muke wanda yafi tsoron shi yafi bauta mashi shi ya fi ba wai mai kud’i ba ko nasaba kawai mutane ne ke bambantawa, in Allah yayi mutum mai kud’i ba hakan na nufin yafi son shi ba ko rayuwar shi tafi amfani ba haka talaka ma ba yana nufin Allah bai son shi ba ko rayuwar shi bata da amfani, ki sani gaba d’ayan mu Allah yayi mu a yadda muke ne don mu bauta mashi don haka gaba d’ayan mu rayuwar kowa talaka ko mai kud’i nada amfani, kuma Maganar aure ai bamu muka sa ya aureta ba, hasali ma bamu san yadda akai ba saidai muka ji zai aureta balle kice ko dama da niyya, sannan Maganar zaman su ma bamu muka rok’a ba tun farko shi ya k’i sakin ta aka zo kuma aka buk’aci zasu ci gaba da zama tare Saboda biyayyar mu ga wadda ta buk’ata muka amince, in zaki ga laifin mu kan hakan shi miyasa bazaki ga laifin shi ba da tun lokacin bai bijire ya nuna bazai cigaba da zama da ita ba, mi yasa tun farko bai saketa ba kaman yadda akai dashi ba, Maganar hallaci kuma ai shi muka yi, ya aureta don ya taimaketa daga baya kuma an buk’aci suci gaba da zama a tare in muka k’i ai kinga mun yi butulci kenan amincewar da mukai kuma hallaci mu kai domin d’an halak shi yake maida Alkhairi da Alkhairi, Yanzu tunda baku amince da auren ba duk miye abun zuwa da tada jijiyar wuya kusa ya sake ta mana……..! A fusace ta kai hannu zata wanka mashi mari ya goce Fuskar shi a tamke yana huci nan da nan Fuskar shi tay jajir kaman an watsa jini abunka da Fari, itama Hajiya Maryam d’in huci take tana mashi wani kallo mai cike da tsantsar 6acin rai zuciyarta tana boiling da burning a lokaci guda, cikin wata irin murya ta nuna kanta da yatsa manuni tace “ni kake gaya ma magana haka!!!” D’an tura baki yay yace “ni ba Magana na gaya maki ba saidai in ke kika d’auka haka amman duk abunda na fad’a ai daidai ne, ikon baro gidan nata na a hannun ku sai ku sa ta…….” Tsawa gwaggo ta kwatsa mashi cikin harshen fulatanci tace ya bar wurin, wani kalan murmushin yaro bai san wuta ba sai ya taka Hajiya Maryam tayi tace “ki k’yale shi, yay man duk rashin kunyar da ya iya ai gada yay tun daga tushe, kowa ya san baku da kunya ai, bama iya hakan kuka tsaya ba gashi nan kun addabi K’asar mu” idonta da suka sauya kala akan shi tay Maganar nan da nan idanun gwaggo suka ciko da k’walla, nuna shi tay da yatsa tace “Ni ba sa’ar yin ka bace, kaff dangin ku ma ba sa’ar yi na, idan kaci gaba da yi man rashin kunya You will definitely find ur self behind BARS….!!!” A tsiyace ta furta Kalmar Bars d’in ta cize hak’ora, Shiru yay bai ce komai ba gwaggo na girgiza mashi kai alamar kar ya tanka sai huttai yake kamar wanda yay gudu da gani dai ba k’aramar zuciya gare shi ba, juyawa tay kan gwaggo ta had’e yatsanta biyu suna making sound tace “Zan yi komae don Farincikin Y’ata in kuma tabbatar bata samu wata matsala ba in kin so zaki iya yin hakan ga Jikar ki…….” Tana kaiwa nan ta juya cike da tafiyar isa ta nufi hanyar k’opa ta fice…….

Asanadin Makwabtaka Book 2 Complete Novel Txt

Back to top button